Showing 18001 words to 21000 words out of 112099 words
Chapter 7 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
ya gaishe ta suka rakata har mota. Dreba na janta tunaninta yayi nisa. Kokonto take yi anya Gimbi bata yin wani abu domin takurawa Maamu? Sannan haka kawai take ji a ranta Bebi kanwarta ce ta kira Gimbi. To me ya hadasu. Da wannan tunanin ta isa gida.
*****
Taxi ce ta ajiye Shuhada a bakin gate din gidansu maigadi ya taho da murnarsa ya tarbeta.
"Hajiya hala babu wanda yasan kina hanya ba'a turo an dauko ki ba daga filin jirgi. Ina Suhailu dan makaranta?"
Murmushi tayi tana janyo jakarta ya karba. Da ta shiga ciki tamkar ba gidansu ba. Duk wani abu da zai nuna sun taba rayuwa a ciki babu shi. Daga kan doguwar kujera ta hango Anti Bebi tana danna waya. Muryar maigadi yana tambayar Shuhada ina za'a kai mata akwatunan yasa ta dago kanta.
"Da na ce kada ki taho gidan nan kinsan ba wasa nake yi ba ko. Zuwa yanzu yaci ace kinsan ni ba tsararki bace"
Zama Shuhada tayi ta dora kafa daya kan daya "idan ban taho nan ba a titi zan kwana?"
Anti Bebi ta mike tsaya tana kallonta. Yaushe ta fara sa'in'sa da ita.
"Ki tattara ki koma inda gyatumarki take"
"Itama gidan mahaifinta ta koma da kika kashe mata aure. Nima da kikayi nasarar kaso min nawa kinga sai nazo mu zauna a gidan nawa mahaifin."
Da yatsa Anti Bebi ta nunata "ba'a ja dani Shuhada. Barin gidan nan shine kwanciyar hankalinki."
Yatsan da take nunata ya kusa tsokale mata ido tasa hannu ta doke shi.
"Kinyi kadan ki koreni daga nan. "
Da yake ta juyawa kofa baya bata ji shigowar Alh Maitama ba babanta. Ita kuwa Anti Bebi ta riga ta ganshi sai kawai ta rike hannun da Shuhada ta doke ta soma ihu.
"Kiyi hakuri don Allah kada ki sake dukana. Indai gidan nan ne yau zan barshi har abada"
Tunani ta fara ko zautuwa Anti Bebi tayi sai taji tsawa daga bayanta. Kafin ta ankara har ya shigo yazo ya rungumeta yana mata sannu. Ita kuwa babu kunya ta cigaba da makale masa a gaban 'yarsa.
Bakinciki fal zuciyar Shuhada ta juya zata bar wurin ya dakatar da ita.
"Ba dole miji ya sakeki ba. Ina kallo kika kai mata duka sannan har na shigo ko gaisuwa babu zaki bar wurin"
Hawaye take yi tace "Daddy kayi hakuri ina wuni"
"Rike gaisuwarki bana so. Kuma ki sani indai zaki zauna a gidan nan ko kallon banza kika yiwa Bebi sai na saba miki."
Anti Bebi ta langabe a jikinsa tana kallon Shuhada kasa-kasa. "Alhajina ka karbo albashin?"
Jakar hannunsa ya mika mata yana murmushi "gashi amma na cire kudin mai gyaran mota da yayi min last week. Idan kin kasa kudin sai ki bani nawa ina son siyan wasu abubuwa"
Shuhada kasa tafiya tayi don tsananin mamaki. Da gaske akwai mata marasa imani masu juya miji kamar waina. Ji Daddy dinsu mutumin da ake gani da mutumci da kima a waje ya dawo tamkar yaron goye a gaban mace.
Kashewa Shuhada ido tayi sannan a hankali tace kadan kika gani.
Da wannan bakincikin Shuhada ta ja kayanta hanyar tsohon dakinta. Anti Bebi ta tace cikin kissa "ki kai kayan dakina kafin nasa a gyara miki naki"
Daddy ya juyo "Bebi kenan, kirkinki yasa kullum nake kara sonki."
Shuhada ko waigowa batayi ba don kada ta ga karin kayan takaici.
*****
Bayan tafiyar Mama da daddare Awaisu da Gimbi suna daki tana masa korafin jikinta na ciwo yace ta kwanta yayi mata tausa.
"Shiyasa rannan Maamu take cewa da ma zan nema miki aikin da zaki tashi da wuri saboda ta kula ni da ke duk aiki yayi mana yawa."
Tashi tayi daga kwanciyar "so take yi na dena aikin?"
"Tace dai tana tausayinki ne. Tun farkon zuwanta ne muka yi hirar"
"Uhmm humm" kawai tace bata kara magana ba. Zuciyarta tana kitsa mata nan gaba Maamu kokari zatayi ta fara juyasu. Wato har aikinta ya tsaya mata a rai.
******
Washegari Maamu ta tashi da gudawa. Tun dare Gimbi tace ayi miyar zogale. Awaisu yana wurin yace Maamu bata ci yana bata mata ciki. Sai Gimbi tace zata yi mata miyar kuka. To dama yanzu komai ta fada ya zauna sai ya amince zata yi din. Da ta tashi bata ce Laminde tayi mata wata miyar ba domin a ganinta barna ne akan 'yar miyar da ake zubawa Maamu kadan a sake kada wata. Haka aka kai mata tuwon da miyar zogale. Duk da tasan yadda yake yi mata amma dole ta ci saboda yunwa. Har su Rumana suka tafi Islamiyya karfe uku tana fama amma ta rasa wa zata fadawa saboda rashin Hausa. Shi kuma Awaisu tun asabar bai kara shiga dakinta ba.
Laminde ta shiga kai mata abincin rana ta ganta tana bin bango saboda rashin kuzari zata shiga bandaki. Taimakawa tayi ta shigar da ita ta koma bakin kofa tana jira ta gama ta fito da ita sai ta fadawa masu gidan. Gimbi ce ta kirawota zata aiketa karbo dinki. Tana zuwa ta fada mata halin da taga Maamu. Gimbi tace to zata duba. Daga nan Laminde ta fita ita kuma ta manta.
Shiryawa taje tayi tace Awaisu yazo ya kaita unguwa. Daya tambaye ta ina zata je tace gidan Anti Bebi. Shi dai yasan da bakinta take fadin halayen Antin wanda yasa basa hulda da ita. Amma ya kasa cewa komai sai mukulli da ya dauko.
So take yi yau ta nunawa Anti Bebi yadda ta fara juyashi sannan idan da hali a dauke hankalin Mama daga sake yi mata tambaya akan Maamu.
Bayan fitarsu Maamu tana kan toilet seat ta kasa tashi saboda gwiwarta duka babu kwari. A hankali cike da kasala ta rinka kiran Rumana da Laminde shiru babu amsa. Tun tana iya kiran har ta koma kuka. Tayi yunkurin tashi ta kasa sai taji kamar zata fadi. Haka ta koma ta zauna tana ta kiran mutanen gidan harda Gimbi. Bacci ne ya dauketa a wurin saboda gajiya da yunwa ga matsanancin ciwon kai. Harisu da Baaba Hure tayi mafarki wai sunzo daukarta. Ta farka a firgice. Rabonta dasu tun ranar da wayarta ta fada ruwa a bandakin. Kwan fitilar ya mutu tasa Rumana ta fadawa Gimbi har sau biyu ba'a gyara ba. Shine suke haskawa da wayarta. Tsautsayi yasa ta fadi har yanzu bata kunnuwa. Tun Maamu tana tunanin wani zai zo har ta hakura ta soma kokarin tashi. Tana mikewa ta zame a wurin ta fadi.
[4:31PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡16
*Batul Mamman*💖
Shuhada ta zuge wata 'yar madaidaiciyar jaka bayan ta gama hada kayan da zata bukata. Tun washegarin dawowarta ta yanke shawarar tafiya Kaduna wurin mamanta. Zama a gidan nan ko kadan bata jin zata tsinci wata riba. A kwana biyun da tayi babanta tamkar hoto haka take ganinsa. Bashi da wani motsin kansa sai abin da Anti Bebi tace. A wani firgice yake idan yana gabanta. Wannan abu ga rabowa da masoyinta Tajuddeen suka hadar mata suka karawa gidan zafi.
Tana share hawaye yayar Tajuddeen ta kirata a waya. Tana dauka kuka suka saka a tare. Ko sati hudu Yayar batayi da dawowa Nigeria ba bayan ta raka mijinta conference Singapore. Kuma a gidan Shuhada suka zauna. Hakuri tayi ta bata sannan ta sanar da ita suna hanya ita da Gwaggonsu zasu zo bayar da hakuri har gida. Babansu ma yanzu zai bi Alh Maitama office ya bashi hakurin wannan cin fuska da aka yi musu. Shuhada cewa take yi babu komai ba sai sun zo ba amma suka dage. Tunaninta kada Anti Bebi ta wulakanta su.
Zama tayi jefi jefi tana leka taga da ta ji karar mota. Tafi son ta fara hangosu idan sun iso taje ta tarosu. Tana cikin leken saboda jin an bude gate ta hango wata mota dark green ta shigo.
******
Kafin isowarsu Gimbi ta yiwa Anti Bebi text tana fada mata zasu shigo ta fito ta ganewa idonta yadda ta mayar da Awaisu.
Dan mayafinta da ta saba ta dan rufe rabin kanta ta fito waje. Yana gyara parking Gimbi tace ya fita su gaisa da Anti Bebi. Kallonta yayi shiru yana nazari sai kuma ya fita din.
Da sauri Anti Bebi ta karaso tazo gaban motar.
"Oyoyo, oyoyo yau ga Awaisu a gidana"
Dan rissinawa yayi zai gaisheta tayi saurin dafa kafadarsa.
"Haba Awaisu dana. Ina kai ina durkusawa, sai kasa a kalleka ai"
Hannunta da tasa a kafadarsa taki cirewa harda karkade masa wani dan zare daga wurin wuyansa.
Wannan abu duk a idon Shuhada. Duk da bata kaunar Anti Bebi batayi zaton mugun halinta harda bin wasu mazan ba sai yanzu. Kuma tasan ko ta fadawa Daddy bazai yarda ba. Abu daya zatayi shine taje taci mutuncinsu daga shi har Anti Bebin ta huce haushi.
Gimbi tana daga cikin mota murmushin fuskarta ya dauke ganin Anti Bebi ta dafa mata miji. Fitowa tayi ba arziki tace su shiga ciki. A nan suka bar Awaisu yana jiran fitowarta.
Suna shiga Shuhada tana fara saukowa daga sama taji Anti Bebi tace "na manta uwar kishi ce kin wani bata rai don an taba miki miji. Dadin abin nima gidan aurena kika zo"
Cikin tsiwa ta amsa mata "Anti kece sai wani dafa shi kike yi. Ni yanzu dai babu yadda za'ayi Maamu ta bar gidan lokaci guda? Kafin na samo kanshi wallahi duk dare yana dakinta ki rasa me suke yi. Wani lokacin sai na fara gyangyadi yake dawowa"
"Gimbi anya baki fini tsiya ba. Wannan da nono na kika sha maza sun shiga uku mata sun ga ta kansu. Yanzu uwa da danta ma sai kin zargi wani abu. Ko don irinku Gimbiya da ina da da wallahi matarsa bata isa ta juya shi ba"
Tafawa sukayi kamar sa'annin juna.
"So nake yi ta koma garinsu kawai ya rinka yi mata aike. Zaman tare damu ne bana so. Duk abi a sawa mutane ido. "
Sai ta dan rage murya har sai da Shuhada ta dan kara bene biyu domin taji da kyau. Dayake wurin zagaye ne basa ganin juna
"Kuma ina so ko za'a dauke hankalin Mama daga kan gidana. Ai na fada miki ranar da tazo yadda muka kare"
Anti Bebi ta hangame baki " Iyye, Gimbiya kina burgeni. Kin cika mace wadda tasan meye 'yancin rayuwa. Wasu 'yan bokon miji da danginsa suyi ta gasa su amma sai su rinka iyayi wai basa bin malamai. Kuma duk karya ne. Tunda da kanki kika nema to kisawa ranki Amina ta bar shiga sabgar da baki sakata ba"
Duk da Gimbi bata so abin ya kai haka ba amma ta fara jindadin mallaka da juya miji. Burinta karuwa yake yi domin yanzu har ogansu a banki take son ya dena mata maganar latti.
Shuhada tana tsaye zuciyarta har bugawa takeyi don tsoron matan nan. Wannan wace irin masifa ce muke daukarwa kanmu akan duniyar da bazata dore ba. Komawa tayi saman a hankali jikinta a sabule. Sai a lokacin taji tausayin mutumin da hannun Anti Bebi ya taba. Lallai ya aurowa kansa masifa.
*****
Karfe biyar da rabi Laminde ta dawo gida. Tasan dama yaran suna Islamiyya. Rashin ganin Gimbi yasa tayi tunanin ko sun kai Maamu asibiti, kwarai taji tausayinta dazu. Ku6ewa ta zauna gurzawa kafin su dawo a bata shinkafar tuwo ta dora. Tana aikin su Rumana suka shigo. Dakinsu ta wuce ta cire kayan makaranta sannan ta shiga bandaki yin alwala saboda an fara kiran magariba.
Tana budewa ta ga Maamu a kwance ko motsin kirki bata yi. Ga jikinta alamun ta sake yin gudawa a wurin. Ihun kuka Rumana ta saka tana kiran Laminde. Sai gata a guje tare da su Haris.
Duk su biyun sun rude suna zaton ta mutu ne. Suna kokarin dagata su Awaisu suka dawo ya tsaya wurin maigadi Gimbi ta shigo. Daula ce ta fada mata Maamu babu lafiya tabi bayanta. Daga bakin kofar bandakin ta toshe hancinta.
"Hmmmm warin meye wannan haka"
Tana kallo da kyar Maamu take bude ido ta jingina da jikin Rumana ita kuma Laminde tana tara ruwa a bokiti da zata dauraye mata jiki tace .
"Maamu ce babu lafiya, a kwance nan muka ganta"
Tabe baki tayi "Toh, to Allah Ya sauwake. Gyara mata jikin kafin na dawo"
Tana fita ta ga Awaisu a falo Haris yana fada masa. Da sauri ta karaso da alamun gigicewa har tana jifa da mayafi.
"Abban Haris juya mu kai Maamu asibiti bata da lafiya."
Duk yadda yake nuna rashin kulawarsa damuwa ce ta ziyarce shi ya ruga dakin a guje. Ganin Rumana ta kasa rike Maamu sosai kafin Laminde ta dauko musu nata sabulun saboda nasu saura guntu da suke amfani dashi anki basu wani. Mantawa yayi da kayan jikinsa ya shiga ciki ya dagata ya saka a bahu sannan ya soma dibar ruwan yana wanke mata jiki da hannunsa yana kiran sunanta cikin tashin hankali kada ta mutu. Da Laminde ta kawo sabulun hannun Rumana ta ja suka fita ta rufe kofar. Rumana tana son komawa Laminde ta girgiza kai.
"Ki bar Kawunki ya sami ladan mahaifiyarsa Rumana. Dauko mata kaya kafin ya gama"
"Namiji ne fa" ta fada tana yatsina fuska. Tuni Kawun nata ya fice mata a rai.
Laminde tayi murmushi "to naji bari naje ya bani nayi mata wanka"
Gimbi ce ta shigo tana tambayar yana ina suka nuna mata bandakin. Muryarsa taji yana cewa "Gimbi zo kiyi mata wanka zan chanja kaya muje asibiti"
Gabanta har faduwa yayi, wannan kazantar ta jikinta zata taba.....
Laminde tana kallonta sai ta shiga tace zata yi mata. Tsoro taji kada da gangan Gimbi ta saketa ta fadi.
Bayan anyi mata wankan ne Laminde ta kula hannunta daya ya kumbura ta wurin babban yatsanta ga dukkan alamu tayi targade. Haka ta shiryata Awaisu da Gimbi suka kaita asibiti. Suna can ya kasa zama har likita ya fito yace suna mata karin ruwa sannan anyi mata gyaran targade. Hankalinsa duk baya jikinsa sai da ya ganta. Da kyar take magana idanu duk sun fada ciki tace ya kirawo mata Harisu a waya. Gimbi jin an ambaci sunan daya makiyin nata ta kasa kunne sai dai bata jin me Awaisu yake fada da yarensu har ya gama wayar.
Juyowa yayi yace "Gobe in sha Allah Yaya Harisu zai zo da daya daga cikin matansa da Baaba Hure. Ina tsammani zasu taho da kanin Maamu ma. Ki kira Laminde a gyara musu dakin baki kafin mu koma gida"
Kirjinta ne ya buga, mutanen da ta raina zasu cika mata gida.
[4:31PM, 2/18/2018] +234 803 369 4017: *KASHE FITILA*💡17
*Batul Mamman*💖
Awaisu bai lura da yadda Gimbi ta chanja da wuri ba daga jin maganar zuwan su Harisu ya mika mata mukullin mota.
"Kije gida ki taho muku da kayan bukata na kwana. Idan kin dawo sai na tafi da motar"
Zaro idanu tayi tana neman amsar da zata bashi domin gujewa kwana da Maamu. Itama Maamu da ta gane me ya fada murya can kasa saboda ciwo tace masa ya tafi da matarsa a kawo mata Laminde ko Rumana. Da ta ga zaiyi gardama tace saboda yara ne. A ranta kuwa cewa take gara ta kwana ita kadai da a barta da Gimbi.
*****
Harisu dakin Baaba yaje ya fada mata Maamu babu lafiya. Hankalinta kuwa ya tashi tace to yaje ya sanarwa 'yan uwanta. Har zai fita ta sake kiransa.
"Dangin mahaifin Awaisu ma ya kamata ka fada musu. Ai kana jin yadda suke yada mana magana wai ya tare a jikinmu baya musu komai"
Harisu ya sha kunu "haba Baaba har yaushe zaki bari zancensu ya dameki. Allah Yana gani yadda duk zuwansa garin nan sai yaje kuma yayi musu alheri. Neman rigima ne kawai"
"Duk da haka kaje ka fada musu ko zasu tura wani yaje dubiya".
"Har na fadawa Awaisun kila muje da kanin Maamu ko wani dai cikinsu. Mu da zamu je dubiya kada kuma a dorawa iyalinsa wahala"
Baaba Hure tayi wani murmushi wanda ita kadai ta san ma'anarsa.
"Baka saba yi min musu ba Harisu. Nace ka fada musu yadda zasu tura wakilinsu dubiya. 'Yan uwanka ma zan sa a kirasu a waya ko mutum biyu a samu. Cikin matanka ka dauki babar Rumana saboda ta gano 'yarta tunda ka hana a kawota hutu. Sauran suma a hankali sai kaje dasu tare ko daya bayan daya"
Harisu kasa motsawa yayi jin wannan hadi na Baaba. Duk girman gidan Awaisu idan sukayi yawa zasu takura musu ne. Ga mara lafiya kuma ga baki da wanne zasu ji.
"Yaya kaki tafiya ne?"
Takalmansa ya saka yayi waje. Ita kuwa Baaba Hure ta gyara kwanciyarta tana jira ya dawo ya kira mata Awaisu ta ji yaya jikin Maamu. Ba komai yasa take son tarawa Gimbi jama'a ba sai bakar maganar da suka yi mata ita da Anti Bebi a rashin sanin bahaushiya ce. So take ta tabbatar Gimbi bata son dangin Awaisu da gaske ne ko kuwa dai 'yar tsama ce irin ta mata da dangin mijinta.
*****
Gidansu Maamu ya fara zuwa inda duka yayyenta maza da kanne suke tare da iyalansu. Bangaren wani cikin 'yan uwan yaje suka gaisa ya sanar dasu abin da ke faruwa. Nan da nan 'yan uwa suka taru ana jajantawa sannan suka ce zasuyi shawara wanda zaije a madadinsu.
Harisu yana fita Hajja Jume matar babban wan Maamu wanda ya dade da rasuwa ta dogaro sandarta ta taho.
"Yanzu labari yazo min za'a tafi wurin Safara'u dubiya ko"
Bashar wanda yake matsayin babba yanzu ya hade rai yana hararar Atika jikar Hajja uwar hada gurmi.
"Tikeke akan gulma zanyi maganinki"
Hajja ta daga sanda tana fada "wanda ya fasa Bashar, nace wanda ya fasa. Yarinya duk kun takura mata kamar ita kadai ce jika. Duk abinku a nan gidan zata zauna. Bani da kowa a gabana sai ita. Tunda tazo ku da iyalanku kun hade mata kai kamar ka jininku ba"
Tikeke ta sunkuyar da kai ita a dole a bar tausayi ce "Hajja babu komai dama na fada miki ne kada a gama rabon waye zaije Abuja gidan Kawu Awaisu a barmu a nan"
Hadi yayi caraf yace "kada ma kusa rai, ni da Yaya Bashar zamu je. Ai ba gayya za'ayi musu ba"
"Wallahi baku isa ba Hadi. Ni zaku nunawa wariya don nawa mijin ya rasu. To ni da Tikeke kamar munje mun gama. Idan da kara ni ya kamata na fadi masu zuwa tunda yaron nan dana ne. Malam da Safa'ra'u ciki daya suka fito ba kamar wasu 'yan uba ba"
Hayaniya ce ta kaure sosai a tsakaninsu karshe aka tsaya