Showing 63001 words to 66000 words out of 112099 words

Chapter 22 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

15945

kyar ta iya jan kafarta ta koma cikin gidan bayan ta hada wayarta. Rita ta dannawa kira tana bata sako zuwa ga Ovi da bokansu


Shirun da yaji daga bangarenta yasa shi kwashewa da dariya har idanunsa na kyalli. Mara kunyar karya ya fada yana komawa wurin motar ya shiga. Dama wadanda suka zo har sum shige ganin yana waya. Gidajensu ya kaisu tare da godiya da alkhairin da ya saba musu.


******
A daki Rumana ta wuni har dare taki cin abinci. Mamanta tayi fadan ta gaji ta fita harkarta amma duk ta damu. Gashi tun baaje koina ba ta wani fige ina ga ta fara zama da Gimbi.


Da daddare Awaisu da Harisu shawarwari suka yi da iyayensu mata akan yadda zasu gabatar da komai na lamarin Gimbi. Da sassafe zasu tafi Abuja tare da Harisu da Anti Baraka.


Yaso ganin Rumana amma baya son zakewa duba da rashin walwalarta tun bayan ta sami labarin shine mijin. Ajiye komai zaiyi yanzu sai ya koma Abuja yayi 'yan shirye shirye da bincike akan Gimbi.


Ranar lahadi karfe takwas na safe sun gama shiri yaransa suma sunyi wanka sunci abinci ana ta fitar da kaya mota. Awaisu yana son ganin Rumana amma yayi wuri.


Dakin Baaba yaje yi mata sallama yayi sa'a Rumana tana kwance akan gado ta kudundune jiki da bargo. Yasan me yiwuwa Baaba na tare da Maamu ya danyi murmushi sannan ya karasa bakin gadon ya zauna.


Yana zama yaji alamun Rumana ta dan matsa baya yayi murmushi wato taji shigowarsa. Ashe tun kafin ya shigo idonta biyu baccin karya tayi saboda shi. Kamshin turarensa ya mamaye dakin a hankali ya bude bargon saitin fuskarta da take kallon bango ta juya masa baya. A saitin kunnenta har tana jin numfashinsa taji ya soma magana a hankali


"Ki kular min da kanki sai nan da wata daya zan dawo in sha Allah. Idan kina bukatar wani abu kada ki tambayi kowa ki kirani"


A takure take sosai ga wani sabon yanayi Uncle ya wani zauna kusa da ita haka. Hannunta ya lalubo ya dora mata waya mai kyau.


"Akwai kudi a ciki kuma na saka miki numbers dina. Zan jira wayarki ta tambayata yaya hanya."


Ji tayi kamar ya sake kwantowa jikinta ta kuwa runtse ido tam. Wani murmushi yayi ganin yadda tayi masa kyau. Ya cigaba da magana "a hankali zan koya miki yi min son so kamar yadda nake yi miki idan kin dawo Abuja"


Bata san lokacin da ta bude ido ba tana mamaki ko su Baaba ne suka fada masa. Kamar ya karanci me take tunani yace
"Indai bazaki rinka yi min magana ba to duk wanda kika yi hira dashi zan roka ya fada min tunda kina min rowar muryarki. Na tafi"


Wani gwauron numfashi ta saki da ya tashi. Sake juyowa yayi "Babu yiwa miji addua? Kina wasa da ladanki da kin magana Princess"


Bargon taja ta rufa har kanta sannan kamar bazata yi magana ba yaji tace "Allah Ya kiyaye"


Fita yayi yana murmushi shi kadai yana cewa "soon Umm Rumana, very soon zan koya miki karatun da ni kadai ya dace na koyar dake."


Ita dai bata fito ba har taji ana ta sallama dasu sannan taji alamun duka an watse daga tsakar gidan. Tashi tayi jiki babu kwari don babu wani abin kirki a cikinta ta daga wayar tana kallo. Waya ce mai kyau ta zamani. Murna ta fara sai da ta tuna batun auren ta cusata a kasan pillow ta koma ta kwanta.


Wurin karfe uku Mamanta ta leko kiranta. Har yanzu Baaba bata dakin gata ko wanka bata yi ba ita tana fushi anyi mata auren dole. Dakin Maman taje tana shiga ta ga Umma yayar Mama dake aure a Lagos. Da yake sun dade rabon da su hadu saboda zamanta a Abuja a kunyace ta gaisheta.


Umma ta dagota tace "yata kamar ba amarya ba duk kin rame"


"Babu abin da take ci sai kuka Yaya" inji Mama


Umma ta bata fuska "wai haka Rumana?"


Bata jira amsarta ba ta dauki plate daga kayan abincin da Mama tasa aka kawo mata ta zuba abinci sosai a kai ta saka cokali biyu tace suci tare. Rumana zata fara gardama Mama ta soma mata fada. Umma tace ta tashi ta barta da 'yarta. Ba musu ta fita ranta duk a bace.


Bayan ta fita ya rage su biyu kawai. Da nasiha Umma ta samu suna ci tare tana fakewa da hira Rumana ta cinye fiye da rabinsa Umma na tsakura. Dama wayo taso yi mata. Suna gamawa tasa taje tayi wanka ta shirya sannan tayi sallar laasar.


Can yamma Umma tasa Hafiza ta dama mata kunu ta shanye sannan da daddare suka ci tuwo tare. Sai da suka gama Umma ta kirata cikin uwar dakin mama tace ta zauna magana zasuyi.


"Rumana kinga da yanayin da aure yazo miki ko"


An tabo inda keyi mata kaikayi ta soma sharar kwalla


"Ba kuka nace kiyi ba. Rumana ki daga hannu ki godewa Allah. Ko kinsan mata nawa ne da kyau da ilimi da komai na tarbiya Allah bai basu mazan aure ba? Duk hukuncin Allah ga bawa alkhairi ne sai dai idan bawan ya bijire "


Shiru tayi tana sauraron Umman.


"Rumana naji labarin komai a wurin Binta kuma na tausaya miki Allah Yasa anyi bayan nazo gari. Sai dai ki sani damuwar nan da kike yi ita tasa mamanki ta kasa kwantar da hankalinta. Wanda hakan ya janyo ta kasa hakura yadda babanki yake ta bata shawara. Shin kina son zama sanadiyar kawo sabani cikin rayuwar iyayenki?"


Da sauri ta girgiza kai. Umma tace "ki koyi hakuri tunda girma ya hau kanki. Aure daraja ce da rufin asiri ga maauratan"


A hankali tace "ko da mijin babba ne Umma"


"Da babba da yaro basu da bambanci matukar sun iya kula da tattalin iyalinsu. Ina so ki nutsu ki sani cewa yanzu ke ba karamar yarinya bace saboda haka ki ajiye duk wata wauta da shirme a gefe. Gimbi da zaki zauna da ita idan kika tafi a haka zaki kwashi kashinki a hannu"


Rumana me zatayi in ba dariya ba da jin wannan maganar. Umma taji dadin ganin ta sake ta hau bata shawara da kwantar mata da hankali. Daga karshe tace


"Binta tace wai sai kin gama secondary nan da kusan wata biyar zaki tare amma mijinki yace a can Abujan yake so ki karasa. To nidai nasan a da ne ake irin wannan auren har ma a shekara amarya lafiya kalau. Yanzu kuwa indai ba so suke a kaiki da ciki ba gara ayi abin da ya sauwaka ki tare kawai"


Gaban Rumana ya fadi ta hau zare idanu. Ita ta manta ma ana tarewa idan anyi aure. Shikenan sai su zauna da Uncle Awaisu......ita kam bazata iya ba.


Umma ta katse mata tunani "Rumana ki sani Allah baYa dorawa bawa abin da yafi karfinsa. Saboda haka ki kwantar da hankalinki ki fuskanci sabuwar rayuwarki. inaso ki kiyaye idan an kaiki ko ruwa kada Gimbi ta baki kisha, addua kuma kada ki kuskura kiyi wasa da ita. Sannan ki sani cewa kina da babban makamin jan hankalin miji wato kyautatawa mahaifiyarsa. Ina mai tabbatar miki tunda Gimbi ta wulakanta masa uwa yanzu ko pure water kika bata wallahi sai kin kara shiga ransa. Ina fada miki don kada ki sakankance wai baya sonta ko abu makamancin haka. Tsakanin mata da miji sai Allah. Sai kiga mace da mugun hali ko kazanta miji yana korafi amma ya saka rabuwa da ita saboda aure rai gareshi"


Maganganun suna ta shigar Rumana har inda Umma tace ta cire zancen saki a ranta ta karbi kaddararta hannu biyu. Idan tayi haka da zuciya daya to lallai zaa wayi gari ta kamu da son mijinta. Abin da kamar wuya take ji amma yadda Umman lagos take ta rarrashinta da bata baki yasa taji zata yi kokari ta daure ta zauna dashi. Amma fa a ajiye maganar aure a gefe ita kam bata girma ba gaskiya nauyinsa take ji.
*****


Su Awaisu sun isa ido na ganin ido. Yara suna ta murnar ganin Gimbi amma taki kulasu ko fitowa daga dakin ta kasa. Sai da suka fada mata da su wa suka zo ta fito babu shiri.


A falo suka hadu Awaisu yana cewa Anti Baraka ta shiga daya daga cikin dakin baki zai kawo musu abinci su ci. Gimbi karasa fitowa tayi ta rinka jan tsaki tana harararsu. Babu wanda ya kulata sai Haris da yake kallon yadda take yiwa yayyen babansa yana jin babu dadi.


Ganin Awaisu yayi hanyar dakinsa suma kowa ya tafi masaukinsa ta bishi dakin sai dai tana zuwa taji ya rufe da key. Wanka yayi ya fito ba dadewa Gambo ya kawo abinci mai rai da lafiya da Awaisu yace ya siyo musu sannan ya bashi mukullan motocin. Duk yadda taso yi masa magana yaki. Gashi bata son basu fuskar ganin yana mata wulakanci.


Shi da yaransa dasu Harisu suka ci abincin suka koshi sannan kowa yaje ya kwanta. Washegari kafin shabiyun rana sun fita Gimbi tana ta tunanin uban me ya kawosu gidan.


Gidansu Gimbi suka je sunyi sa'a iyayenta duka suna gida. Bayan gaishe gaishe Alh Mudi bai boye musu mamakinsa na ganinsu ba saboda baiyi zato ba.


Anti Baraka ita ce tayi musu bayanin dalilin zuwan nasu. Domin shaida harda hoton Maamu a asibiti ta nuna musu. Mama tana gani sai kuka. Idan kaga Maamu a lokacin da cuya kace zata yi rai ma. Shi kanshi Alh Mudi idanunsa ja sukayi yana mai bakincikin Gimbi tsatsonsa ce.


"Alh Harisu wallahi na baku wuka da nama duk abin da kuka ga ya dace kuyi mata domin huce wanan bakincikin kuyi. A matsayina na mahaifinta kuma nayi alkawarin zamuje fika dubo maamu kuma mu basu hakurin bata musu zuria."


Mama kuka ne kawai yaci karfinta ta shige daki ta barsu. Allah Ya isa Bebi.


Alh Mudi ya jajanta musu sosai karshe dai sun tsayar da magana akan Awaisu zasu je har gidan su yiwa Gimbi fada. Mamakin dalilinsa na kin sakinta ma sukayi. A ransa yace idan har ya saketa wallahi taci bulus karawa gaba zatayi wani mai rabon wahalar ya dauka.


Washegari da safe su Harisu suka kama hanya suka koma.


Duk bakin nacin Gimbi fita ta gagara. Ga kudi ta turawa Ovi masu yawa sunce an karbo magunguna amma babu damar kawowa gidan. Gimbi tayi haukan tayi borin duk a banza. Shi tsoro ma yake kada ta bata masa yara.
*****


Yau kwanansu Awaisu biyar da komawa Abuja Rumana tana cin kosai bayan tayi buda baki na azumin nafila da takeyi ranar litinin da alhamis taji wayarta tana ringing. Tun da ya bata wayar bata bawa kowa number ba kuma bata kira ba. Ajiyarta take yi kawai.


Uncle taga an rubuta tayi saurin yin baya kamar shine da kansa. Mama tana kula da yadda tayi ta dan sha kunu tace ta shiga daki ta dauka mana.
Gabanta yana faduwa ta dauka ta kara a kunnenta a dan tsorace.


"Assalam alaikum"


Wani sanyi yaji ya ratsa masa zuciya ya danyi murmushi a ransa yana mamakin yadda yake jin Rumana.


"Princess baki nemana ko? Har yanzu baki fara yi min son so din bane"


"Ina wuni" ta gaishe shi zuciyarta tana ta bugu.


"Ba amsawa zanyi ba tunda baki nemeni da kanki ba. Dama kira nayi naji ko kina da bukatar wani abu"


Murya can kasa tace "babu komai"


"I miss you"


Wani irin faduwar gaba taji shima kuma sai da yaji kunyar abin da ya fada mata. Amma sai ya sami kansa da son jin amsarta


"Baki ji me nace ba?"


Tunawa tayi Umman Lagos tace mata ta karbi kaddararta kuma tayiwa Awaisu biyayya. Budar bakinta sai cewa tayi.


"Uncle I miss you too" kit ta kashe wayar ta dafe kirji tare da kurma ihu. Ita wallahi kwatantawa taso yi a zuciyarta taji ko nan gaba zata iya fada.


Mama ce ta shigo dakin da sauri tace me ya sameta. Rumana dafe da kirji tace
"Babu komai"


Tsaki Maman tayi ta fita daga dakin.


Awaisu kallon wayar ya rinka yi cike da mamaki kafin ya tashi ya bude wardrobe dinsa. Fika zaije gobe tunda zai kama asabar ya dawo lahadi kawai don ya ga Rumana
[15/08, 17:46] ‪+234 803 272 5896‬: *KASHE FITILA*💡39


*Batul Mamman*💖




Bayan Awaisu ya gama hada kayansa sai kuma ya fara tunanin me zai cewa su Harisu idan yaje. Kullum suna waya, karewa ma Harisu ne mutum na karshe da ya kira kafin ya kira Rumana. Kuma bai ce masa zai je ba. Dan tsaki yayi tare da jifa da jakar yana murmushi. Wai shine yau yake kunyar Harisu mutumin da kafin Gimbi ta fara gwara masa kai baya boye masa komai. Da 'yar wani ya aura har shawara zai nema wurinsa akan yadda zai shawo kanta, amma yanzu babu hali. Can kamar an mintsine shi ya tashi da saurinsa ya dauko waya yana dariyar samun mafita.


Anti Ummukulsum ya kira. Duk gidan idan aka cire Harisu to bashi da ta biyunta cikin 'yan uwansa.


Tana daki 'autarta cikin mata wadda ta kasance tsiransu da Rumana babu yawa don bai kai shekara ta bawa Rumanan ba ta kawo mata wayarta da ta bari a kitchen.


Ganin sunan Awaisu ta dauka ta soma tsokanarsa.
"Ango kasha kamshi"


Dariya yayi suka gaisa cikin barkwanci. Dan shiru yayi kamar tana wurin ya dan sosa kai


"Yayata ta kaina alfarma fa nake nema"


"Dama wannan waya cikin dare ai nasan ba a banza ba. Me kake so?"


"Ina son tahowa ne gobe..." dan dakatawa yayi domin jin me zata ce.


Anti Ummukulsum ta nunawa Iman kofa alamun ta fita.
"Awaisu kada ka sami matsala a wurin aikinka fa. Yaushe ka koma har zaka dawo."


"Kwana daya zanyi. Ranar lahadi da wuri zan tafi in sha Allah"


Dan tsoro taji "ko dai wani abu ya faru?"


"Ko daya. Zancen gaskiya amaryata nake son gani"


Dariya sosai ta rinka yi masa tana tsokanarsa wai ya zama sabon shiga. Shi dai bai kula ba ya roketa akan ta san yadda zatayi Rumana ta wuni a gidanta gobe yadda idan ya iso zai taho nan su hadu saboda yana kunyar Harisu.


"Kinga daga tafiyata a ji na dawo bansan yadda zan hada ido dashi ba. Kuma gaskiya ina son ta saba dani a matsayin miji kafin ta tare"


Anti Ummukulsum tace "Da gaskiyarka amma tarewar nan fa naji ana shawarar ko nan da sati hudun da kace zaka tafi da ita tayi karatu zata tare kawai."


Murmushi yayi saboda ko kadan bai so ba da matan Harisu suka dage wai sai ta gama makaranta zasuyi biki. Shi ko me suke bukata zai basu idan ta taho karasa makaranta ta tafi kenan ita da Fika sai ziyara.


Yaji dadi yadda yayar tasa ta bashi hadin kai zata aika Rumana tazo da wuri. Shima cewa yayi yana asuba zai taso


"Amma me yasa baka taho yau ba bayan kun taso aiki?" Ta tambayeshi


" 'Yar taki akwai mulki. Sai yau tayi min kiran da dolena nazo" ya kare yana dariya.


Ji yayi Anti Ummukulsum ta dan dake murya "Ba kayi min dadin baki zan dauko maka matarka ba, wallahi kada kasa naji kunya nan gaba, ka dai san me nake nufi..."


Dariya yake yi sosai harda rike ciki. Sannan yayi mata alkawarin bazaiyiwa Rumana komai ba. Tace gara dai ko meye idan tazo gidansa su karata amma ba da ita ba. Cikin nishadi sukayi sallama ya dan kashingida akan gadon yana danna waya daidai sunan Rumana kamar ji yake kamar ya sake kira.


Gimbi ce ta turo kofar fuskar nan a hade tazo ta tsaya masa a ka. Ko dagowa baiyi ba bare ya nuna mata cewa ya ganta. Hannu tasa ta daki gefen gadon.


"Malam ina da magana"


Har lokacin bai dago ba ta fizge wayarsa tayi jifa da ita can karshen gadon. A daidai lokacin Abba yana yiwa Rumana downloading applications na karatu a wayarta yaga kiran. Sai da ya daga sannan ya mika mata ya tashi yace idan ta gama ta kai masa daki ya karasa. Hannunta har rawa ya rinka yi ganin sunan wanda ya kira. Ita da take jin kunyarsa me zaisa ya kuma kira. Haushi Abba ya bata don da ita ce da kyar idan zata daga wayar. A hankali kamar tana tsoron zai kamata ta dan kara wayar a kunnenta. Muryar Gimbi da taji yasa tayi kokarin kawar da wayar da sauri sai kuma ta fuskanci ba da ita take maganar ba.


Yadda tayi masa jifa da waya haka ya tashi ya janyo hannunta ya wurgata kan gado yana daga tsaye ya dora kafarsa daya a kan gadon tare da dan rankwafowa.


"Koda wasa Gimbi kada ki kara taba min waya bare har kiyi min jifa da ita"


Wata muguwar harara ta sakar masa don bata tsoron ko me zaiyi mata.


"Woooooo ka dai ji kunya ka rasa wadda zaka aura sai 'yar cikinka. Iyayenta kwadayi kai kuma son zuciya. Don kana waya da shegiyar yarinyar nan zaka tsareni da ido kace kada na sake taba maka waya. Idan na taba ka kasheni sai nasan cewa kaji haushi"


"Kin gama?" Ya tambayeta yana kara matsowa kusa da ita.


"Gamawata shine ka barni na fita daga wannan kurkukun saboda auroni kayi ba zaman prison nazo ba"


Tana rufe baki yasa hannu ya kamo labbanta a tsakanin babban yatsansa da manuni ya matse iyakar matsa. Kokarin cire hannunsa tayi saboda azaba har tsakar kanta shi kuwa ya damke hannuwan da hannunsa dayan. Fuskarsa ce ta birkice babu alamun wasa ko kadan.


"Ina so wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zaki zagar min mata. Idan baki sani ba to ina mai sanar dake wallahil azim a cikin abin da bai kai sati biyu ba Rumana ta shiga raina ina yi mata son da bana fata wata mace ta sake samun gurbi a zuciyata irin yadda ta samu. Aurenki Gimbi *kashe fitilar* rayuwata ne ya sanyani cikin duhu. Aurenta kuwa tun a yanzu nasan daidai yake da *kunna fitila* na ga haske a rayuwar da kika mayar bakikkirin"


Yana magana yana murje mata labbanta radadi na shiga ga zafin maganganunsa gareta. Idonta ya cicciko zata yi kuka ya girgiza kansa.


"Kada ma ki fara yi min kuka don baki ga komai ba. Ina fatan ko daidai da rabin son da nake yiwa Princess dina na samu daga gareta. A lokacin ne zakiyi kuka Gimbi. Nayi miki alkawari sai na baki mamaki kamar yadda kika sa kafa kika take soyayyata gareki kika nemi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login