Showing 42001 words to 45000 words out of 112099 words
Chapter 15 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt
kansa ya jigata. Harisu ya nema yace lallai su kaita babban asibiti a cikin Damaturu don gaskiya tana cikin mawuyacin hali. A ambulance aka sakata suka bi bayansu shi da Abba da Anti Baraka.
A hanya suka kira gida wanda suma duka sukayi kwanan tashin hankali suka fada musu an canza asibiti. Dama ana kokarin hada musu abin karin kumallo ne.
Suna isa gado aka turo domin daukarta ganin a ambulance aka kawo mara lafiyar sun san abin babba ne. Wata likita ce akan Maamu tana ta gwaje gwaje. Jininta ma da kyar aka samu don an bulata yafi sau shida basa samun jinin yadda suke bukata. Maamu ta galabaita iyaka don ko magana ta kasa yi sai hawaye akai akai da yake zirarowa ta gefen idanunta. Kusan awa biyu sannan likitan ta fito ta tafi office dinta tana yarfe gumi. Tun kafin ta fita iyalin Harisu suka iso suna ta koke-koke don kallo daya zaka yiwa Maamu kayi tunanin kafin ka matsa ta cika. Cikin yaran ma mutum uku aka taho dasu harda Rumana wadda tafi kowa kuka. Idanunta sun kumbura sosai ga ciwon kai matsananci.
Wani mutum wanda da alama masinja ne yazo ya kira Harisu zuwa ofishin likitar. Yana shiga godiya ya fara yi mata amma bata ko amsa ba ta jefo masa tambaya.
"Mene ne tsakaninka da mara lafiyar nan?"
Dan gyara zama yayi yana tsoro me zata ce ya sami Maamu "Babata ce"
"Babarka? Babarka?? Amma shine...." Ta soma magana murya na rawa sai ga hawaye shar. Hannuwanta biyu da ta dora akan tebur din gabanta tasa ta rufe fuskarta.
Harisu yayi mamaki sosai don sai da ta kwashi kusan minti uku kafin ta ita daidaita kanta ta dago jajayen idanu tana masa wani irin kallo cikin bacin rai
"Lokuta da dama sai ace likitoci suna kashe marasa lafiya bayan kune ba kwa tashi kawo su asibiti sai lalura ta cinyesu"
Harisu ya dubeta "hakane likita amma kowa kika gani baya rasa dalilin faruwar hakan"
Dr. Yana bata san lokacin da ta daga murya ba don ba karamin haushin 'yan uwan Maamu taji ba a irin yanayin da ta ganta.
"Malam babarka tana cikin mawuyacin hali zaka ce kana da dalili? Wannan ciwon fa ba na lokaci daya bane"
hannu tasa ta fara masa lissafi da yatsunta
"Kaga da farko jininta yayi mugun hawa ina tsoron Allah Yasa kada ta sami matsala a zuciya, na biyu ulcer tayi mata mugun kamu har kirjinta ta taba, na uku malaria ta jima da shigarta baa dauki mataki ba. Na karshe shine malnutrition. Wallahi kun zalinci matar nan ba kadan ba"
Duk da fada take yi wani hawayen ne ya taso mata. A awa biyun da ta tsaya kan Maamu tasan ba karamin jin jiki take yi ba. Matar da ko tari ta kasa yi saboda kirji ya rike.
Dr. Yana mace ce mai matukar tausayi da jinkai. Asibitin suna ji da ita. Duk tausayinta kuma a tsaye take bata bata sake da aikinta. Idan kaji ana Dr. Barrister to da ita ake don idan taga mara lafiya kamar akwai cutarwa cikin lamarinsa to fa ta tsaya masa kenan ayi ta dauki ba dadi da ita. Zuwanta kotu yafi a kirga bada shaida idan aka cuci mara lafiya.
Shi dai Harisu tunda ta hau lissafi yake salati. Karamin tsaki ta ja don a ganinta aikin banza ne. Da can baa kula da ita ba sai yanzu da ciwo ya gama cin karfinta.
Mikewa tayi tsaye tana masa nuni da kofa "muje ka sallami masu kukan nan domin damunta kawai zasuyi. Sannan akwai irin abincin da nake so a rinka bata musamman madara saboda ulcer din."
Kai ya gyada ya bi bayanta. Haushin Awaisu yake ji ta yadda da zai ganshi a lokacin baiga wanda ya isa ya hanashi kai masa duka ba. Anya yana ma cikin hankalinsa kuwa. Maamu ce fa mahaifiyarsa. Matar da aljannarsa take tattare da farincikinta.
Da suka karasa kofar dakin sanar dasu yayi su tafi dama shima kukan nasu ya ishe shi. Nan suka fara shawarar masu zama tunda akwai tafiya. Suwaiba autarsu Harisu da uwargidansa aka bari. Yaso zama suka dage akan lallai ya tafi gida ko wanka yayi saboda tafiyarsu ta jiya. Rabonsu da abinci shi da Abba tun jiyan kafin su kama hanyar Abuja. Sai da sukayi musu siyayyar kayan bukata musamman na Maamu suka dau hanya da alkawarin dawowa da sassafe.
*****
Tsaki Gimbi tayi don ganin Awaisu har yanzu yana kwance tun bayan sallar asuba akan abin sallah. Tsaya masa tayi a kansa ta soma mita
"Hala dai yau baka da niyar zuwa aiki?"
Kansa ya rike duk da a kwance yake "Gimbi I feel sick. Jikina duka babu kwari ga fargaba da take damuna na rasa dalili"
Jin ya dauko zancen da take so yasa ta zauna a gefensa ido ya ciko da kwalla zata yi masa kuka "Nasan rashin Maamu a kusa da kai ne yake damunka. Ni kaina abin ya dameni. Kuma ko ka yarda ko kaki yarda dan uwanka bai kyauta ba. Maamunmu ko shine ta haifa tunda a gidan nan take bai kamata ya dauketa bamu sani ba."
Shiru Awaisu yayi yana nazarin maganarta. Ta kuma rissina kai ganin zancen ya soma shigarsa.
"Ni yanzu ta yaya gidan nan zaiyi min dadi babu Maamu? Na riga na saba da ita kamar mahaifiyata. Tana bani shawarwari wanda naga amfaninsu sosai. Ko ba don kanka ba ka dawo min da Maamu zanfi samun kwanciyar hankali "
Kukan munafurci ta rinka yi hawaye kamar famfo. Hankalin Awaisu ya tashi yayi ta bata hakuri da alqawarin zai dawo mata da ita. A gabanta ya rinka kiran Harisu yaji shiru ba amsa. Yace tayi hakuri zai kara nemansa zuwa anjima. Murmushi tayi masa ta fita daga dakin. Zuciyarsa ya ji ta sake shiga kunci sai dai ya rasa meyasa tafiyar Maamu tayi masa dadi maimakon yaji bacin rai. Har kasan zuciyarsa yana jin zamanta wurin Harisu ya fiye masa kwanciyar hankali.
*****
Bayan kwana biyar Rita tana goge falo taji sallama. Bata ankara ba Haris ya taho a guje har yana bangajeta saboda muryar da ya gane. Wadda ya gani ya nufa da gudu sai kuma ya tsaya turus alamun kunya an fara zama samari ya kasa karasawa. Murmushi ta sakar masa kafin tayi magana su Daula taji suna kokarin kayar da ita. Rungumesu tayi don tayi kewarsu duk irin tsiyar gidan.
Ihun yaran ya fito da Gimbi daga daki da waya a kunne suna magana da wata kawa da tayi a gidan Bokan Ovi. Sakin wayar tayi ba shiri tare da wangale baki a dan tsorace
"Laminde"
Laminde ta dan murmusa fuskarta babu yabo babu fallasa. Jikin Gimbi yayi sanyi ta daure tace yaran su saketa haka ta wuce ciki su gaisa sosai.
Laminde ta bi bayansu suka shiga ciki. Ajiyar zuciya tayi da ta tuna yininta na karshe a gidan da yadda al'amura suka kasance. Rabonta da Abuja tun da aka sallamota daga asibiti gashi har an bawa shekara baya. Da ta koma gida ne Allah Ya kawo mata miji tayi aure. Karamin ma'aikaci ne a wani kamfani amma an basu gidaje a Quarters din kamfanin kanana saboda nisa. Shine tazo ganin su Maamu.
A kan kafet ta zauna Gimbi tana ta tsaneta da idanu har sai da tayi danasanin zuwa. Har ga Allah lamarin Maamu ya tsaya mata a rai kuma shine musabbabin zuwanta ta duba baiwar Allah.
Gimbi ta hakimce akan kujera sannan ta sa yaranta suka bar falon suna ta kunkuni. Bayan sun fita ta kalli Laminde
"Ince ko dai lafiya kika zo. Idan aiki kika dawo ni na dade da daukar wata"
Laminde ta kalli Rita. Mace har mace tasa kananun kaya irin wannan tana yawo a cikin gida wai 'yar aiki a zamanin nan da kafin shaidan yazo zukata sun riga sun gama rauni da sabon Allah.
"Na shigo garin ne na leko mu gaisa" tana magana tana dan waige waige ko zata ga giftawar Rumana ta tambayeta Maamu.
Tabe baki Gimbi tayi "basa gidan wadanda kika zo ganin. Sai ince a gaida gida ko tunda ba wurinmu akazo ba"
Laminde ta fahimci korarta akeyi ta soma haramar tafiya. Wani dan saurayi taga Rita ta shigo dashi yana ta dariya suka gaisa da Gimbi da gani sun saba wasa da dariya. Tape ya dauko dama da bironsa a saman kunne yace "Hajiya Gimbi sauri nakeyi fa kizo na gwadaki na bar mutum yana jirana a waje"
Sam ta ma manta da Laminde bata fita ba tace "Kezy ka rainani fa. Ni zan karaso nan ko kai zaka zo"
Da murmushinsa ya karasa gabanta ta mike tsaye. Karamin mayafin da yake kanta ta daure a saman kan dama bai kare komai ba. Nan tela ya hau gwajin dinki fa. Haka ta rinka daga hannuwa yana zagayeta tana cewa so take rigar tayi mata das a jiki saboda dinkin kece raini za'ayi. Laminde ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya. A cikin ranta ta zabgawa Anti Bebi tsinuwa. Tabbas ko da can Gimbi ba wani kirki gareta ba amma ko kadan halayyarta bata yi kama da ta Gimbin yanzu ba.
Sa kai tayi zata fita ta kusa karo da mutum. Da sauri ta kauce Awaisu ya shigo baya ko ganin gabansa da kyau don ko bi ta kanta baiyi ba bare yaji gaisuwar da take yi masa. Gimbi ya kalla da Tela ana nan ana ta gwaji amma ko a jikinsa bare ya hana. Laminde da tayi zaton za'ayi tashin hankali akan wannan gwajin wulakancin sai taji yace
"Inata kiran wayarki baki amsa ba"
Ta dan bata rai "tana daki bana son damu ne"
"Ai gara ki rinka hutawa. Dama takarda aka kawo office dinmu zan cike sunayen masu zuwa workshop Lagos jibi. Shine nayi ta kira in tambayeki nasa sunana ko kuwa"
Kezy Tela ya kwalo idanu yana jin ikon Allah. Duk tsagerancinsa abin ya daure masa kai. Gimbi ta kula dashi da Laminde mai tafa hannuwa daga kofar shigowa falon sai ta fakaice da cewa "amma dai abban Haris ka iya rigima. Wato don kada nace ka tafi ka barni ko. To na yarda kasa sunan amma idan kaje babu ruwanka da yan mata"
Kai ya dan rissina yana mata godiya ya kuma fice. Laminde tabi bayansa ta tsaya suka gaisa da maigadi. Nan yake fada mata ko sati Maamu batayi da tafiya ba. Duk tausayin Maamu ya kamata tace ko akwai number da zata iya samunsu yace bashi da ita. Daga nan tayi masa sallama ta tafi.
*****
Dr. Yana ce ta kalli su Baaba Hure tana ta bata rai "wai don Girman Allah waye wannan Awaisun ne? Haba baiwar Allah tun da ta farfado kullum sai ta kira shi kunki ku kawo mata shi. Mara lafiya na bukatar kulawa bare ma ita da abu yake neman kaiwa zuciya. Indai ba mutuwa yayi ba ku kira mata shi don Allah"
Maamu tana daga kan gadon sai kalmar mutuwa taji ai kuwa ta soma kuka tana cewa shikenan ta kashe shi. Anti Ummukulsum ta gallawa Dr. Yana harara.
"Wai ke wace irin likita ce kullum sai anyi fada dake a dakin nan. Dame kike so taji ne. Ciwon ko irin wannan maganganun naki"
Nurses biyu da suke tare da ita suka soma dariya. Indai da sabo su kam sun saba da jajibo rigima irin na Dr. Barrister. Kanta tsaye take gabatar da komai nata shiyasa wasu basa fahimtar ta. Ga yan uwanta kuwa cewa akeyi gaboncin 'ya'yan fari ke damunta.
Tsuke baki tayi ta maida hankalinta ga Baaba Hure.
"Iya don Allah idan da hali ku kira mata wannan Awaisun ku huta itama hankalinta ya kwanta mu samu ta warke da wuri. Kwanaki haka aka kwantar da wata a dakin nan kuma kan gadon nan ma itama tayi ta kiran mijinta iyayenta suka ki sanar dashi wai saboda ya sakota. Ranar nazo dubata tace in fada masa ya yafe mata amma sharri kishiyar ta kulla mata. In gaya miki washegari ta cika. Iyayenta suna ta kuka da mijin yazo yana son neman gafararta ya gano gaskiya suna cewa da ma sun sani sun hadasu sunyi maganar karshe gashi ta tafi ba'a cika mata burinta ba"
Harisu yana bakin kofa zai shigo yaji tana wannan labarin ya rike baki. Kullum burinta ta tsorata su ne, me zai sa ta rinka dauko zantuka irin haka. Shi kam dole ya nemi babba a asibitin a canja musu likita. Baaba Hure tana hada ido dashi ta taso
"Harisu don Allah ka sanar da Awaisu halin da Maamu take ciki kada ta cika bai nemi gafararta ba"
Dr. Barrister ta murmusa daga gefe. Ko da bata jin yaren taji an ambaci Awaisu ga kuma alamun tsoro a idanun Baaba Hure. Ba don Maamu na jin jiki ba so take ta tambayeta labarinta taji kwaf don a yanzu duka bata yarda dasu ba. A ranta tace kowa cikinsu mulmul dashi sai ita kadai a wannan mawuyacin yanayin.
Bayan ta fita ne Harisu ya zauna a gefen gadon Maamu yana kare mata kallo. Tun zuwansu jininta yaki sauka shi kuma yayi rantsuwa bazai kira Awaisu ba kamar yadda ko waya idan yayi masa baya dauka. Duka 'yan uwansa ya umarcesu kada su kuskura su sake daukar wayarsa. Idan ya damu da ita ya biyo bayanta. Baaba Hure tace ita dai idan har ta isa dashi to a yau take so ya kira Awaisu ya fada masa. Zuwansa ko rashin zuwan ya rage nasa. 'Yan uwan Maamu suma Harisu yace da farko kada a fada musu sai ta dan murmure don a haka bai san inda magana zata tsaya ba. To a yadda Dr. Barrister ta tsorata Baaba suma sai tace a fada musu. Tunda yanzu idan ta rasu basu da madogara zaace ya daukota babu wanda ya sani.
Dan kallonta yayi sannan yayi murmushi tare da kwafa "waccan shu'umar likitar duk ta birkita miki lissafi. Zanyi yadda kika ce Baaba in sha Allah"
Sauran 'yan uwansa dake dakin da iyali suka goyi bayan a sanar din shi yafi ko don gudun zargi nan gaba.
Duk abin da akeyi Rumana tana gefe don kullum sai tazo saboda shakuwarsu da Maamu. Shima Harisun baiyi tunanin hanata ba. Tausayin Maamu take ji sosai a ranta ta fita daga dakin ta bar iyayenta suna magana. Wani dakali ta zauna tana ta tunanin irin ukubar da suka sha a Abuja.
Dr. Yana ta dawo daga wurin Director na asibitin yayi mata kashedi sosai akan yiwa marasa lafiya katsalandan ta fito rai a bace tana kumburi. Rumana ta hango kuma ta gane yarinyar mai shegen kukan nan ce a dakin da ta baro dazu. Wani birki taja tare da komawa ta dafa kafadar Rumana.
A dan firgice ta dago sai ta maida kai da ta gane wace. Dr. Yana ta zauna a gefenta ta fara mata nasiha akan cuta ba mutuwa bace da sauransu. Sai da ta gama ta hau bugun cikin Rumana akan alakarsu da Maamu. Rumana an sosa mata wurin da yake mata kaikayi nan fa ta hau bayani tana kuka ta zayyanewa Dr. Barrister alakarsu da zaman birnin tarayya da suka yi.
"Jakar uba....amma kuna da hakuri wallahi. Har naji babanki yayi daraja a idona "
Saurin dagowa Rumana tayi wanda yasa Dr. Barrister ta dan wayance "kara daraja yayi nake son cewa. Dama da darajarsa na ganshi"
Tashi tayi ta koma office dinta tana ta tunani. Gaskiya taimakon irin wadannan jihadi ne fa wanda bata so a barta a baya. Kai dole ma ta shiga a dama da ita saboda wannan dattijuwa mai siffar salihan mata bata cancanci cin kashi daga wurin surika ba.
"Yadda kika kashe fitilar zuciyarta ina mai tabbatar miki da taimakona kece zaki zauna a cikin duhun ba ita ba" ta fada a fili tana kallon ceiling din office dinta.
[15/08, 17:45] +234 803 272 5896: *KASHE FITILA*💡32
*Batul Mamman*💖
Bayan kamanin rabin awa aka bude kofar dakin. Tura Maamu suka ga anayi akan gado tana kwance ko kwakkwaran motsi bata yi. Kuka ne ya barke daga bakin matan da ke wurin domin duka matan Harisu da su Aunty Suwaiba sun iso. Baaba Hure ce tayi karfin halin hanasu a lokacin Harisu ya bi bayan likitocin. Dr. Yana tasan yana binsu shiyasa bayan sun daidaita Maamu a I.C.U ta fito ta same shi. Yanayin barkwancin nan duka babu afuskarta sai tausayi. Ita ta soma magana da ta karaso inda yake tsaye hankalinsa a tashe
"Mun samu jikin nata ya dan daidaita. Ta kusa samun heart attack ne dazu"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Dr yanzu menene abin yi?"
"Addu'a ita ce za'a cigaba da yi. Sannan gaskiya ku dena taruwa da yawa a dakin tana bukatar hutu. Wannan dakin bama bukatar kowa sai mutum daya itama kuma ba ciki zata zauna ba."
Godiya yayi mata ya juya ya tafi da niyyar hada kansu su tafi gida ta kuma tsayar dashi
"Awaisun nan da take kira har a cikin wannan tsananin ciwon addua take yi masa. Don Allah a karo na karshe kada kace na shiga abin da babu ruwana ku taimaka ku kawo shi. cuta ba mutuwa bace amma tana jin jiki."
Jiki a sabule ya koma kofar dakin nan suka tsare shi da tambayoyi. Ya gama yi musu bayanin me likita tace yayyen Maamu maza suka zo da matansu har da su Tikeke da Bomai kanin baban Awaisu. Harisu yaso sakaya lalurar Maamu amma Baaba Hure tayi musu bayani dalla-dalla.
Nan wurin ya kaure da salati sai da security yazo yace duk su koma waje. A nan ma manyan suka hado aka yanke shawarar su wuce Fika ayi maganar a gida.
Mazansu da matansu manyan haka suka hadu a falon Harisu ana fadar abubuwan da suka faru. Baaba tasa aka kirawo Rumana domin shaida. Ita kuwa bata boye komai ba dangane da yadda suka tsinci kansu a gidan Awaisu. Bomai da ake ganin yafi kowa shiririta ne ya soma magana bayan an sallami Rumana.
"Lallai biri yayi kama da mutum. Idan kun tuna zuwanmu gidan nan abubuwa marasa dadi sun faru. Kuma daga bayanin wannan yarinya Rammana duk mai hankali yasan cewa akwai wata a kasa"
Wanda Maamu take bi ya amshe "abin da ya faru ya riga ya faru sai dai mu kiyaye gaba. Dama Maamu ga zurfin ciki tazo ta hadu da bacin rai dole ya taba zuciya. Ni dai idan da mai zuwa ya kamataa gobe muje mu taho da Awaisu ko yana