Showing 90001 words to 93000 words out of 112099 words

Chapter 31 - KASHE FITILA Book Complete by Batul Mamman.txt

23 Jun 2024

14020

fitar muku da amaryarku"


Bai sake magana ba suka fita. Zasu tafi yarinyar shagon ta biyosu tana magiyar kada dama ta wuce su bata taba jin Fattu tayi tayin kwalliya ba duk da kwarewarta. Nacin da ta kafa musu yasa shi amincewa tare da sharadin ana gamawa idan batayi masa ba bazai biya ba.


Nuru ya fara ajiyewa a gida sannan ya wuce gidansa zuciyarsa tana dokin haduwa da Son So.
*****


Kaf duniya Gimbi gani take babu wanda yake cikin damuwa da bacin rai irin nata. Tasan basu taba zancen daga kanta babu kari ba duk da kishinta amma ko Awaisu zai karo aure ba irin wannan cin fuskar ba. Laifin da yake ikirarin tayi masa har yanzu bata gani ba. Yanzu da bata dauki mataki da wuri ba dama niyar Maamu ya auri Rumana da tuni tasa ya saketa anyi auren. Wane makircin uwarmiji ne bata da labarinsa. Abu daya ta sani tunda bai saketa ba yana sonta har yanzu. Amma ina mafitar dawo da fadarta zuciyarsa ta koma Gimbiyar Awaisu?


Anti Bebi ce ta fado mata. Ba don taci amanarta sun rabu ba ai da itace mai bata shawara. Kuma ta tabbatar da sun dade da mantawa da matsalolin nan saboda ita Anti Bebi ko babu boka zata iya zama da makircinta.


Tsaki tayi dole itama ta tashi tsaye ta nemi hanyoyin da zata tsorata Rumana ta fita da kafarta ko da asiri ko babu. Guda ta jiyo daga falo hakan ya tabbatar mata da dawowar Awaisu. Mikewa tayi zata fita taji kanta yayi mugun sarawa dole ta zauna zuciya na tafarfasa.


Murmushi yake ta yi matan da suke falon suna ta tsokanarsa. Abinci ne kuloli manya uku a wurin suna ta zubawa. Anti Suwaiba tace masa su Baaba suna dakin Maamu.


Yana Sallama Rumana na fitowa daga wanka. Dama bandakin ne farko kafin a shiga ciki babu wanda ya gansu. Cak ta tsaya suka hada ido sai ta koma ciki da sauri ta bugo kofar harda hadawa da yatsanta don sauri. Ihu yaji ta saki daga ciki tana washh yace maganin me gudun miji kenan a hankali sannan ya wuce yana murmushi.


Kafin ya gaishe da Baaba su Anti Ummukulsum suka yi masa caa ana ta barkwanci. Haj Umma yayar Maman Rumana da matan 'yan uwansu maza sune suke tare masa ana ta dariya.


Dadi ya kama Baaba tayi masa sannu da zuwa sannan tace basu gane dakin Rumana ba sannan suna jiransa ya nuna inda zaa jera mata kayan kitchen domin da safe zasu koma.


"Haba dai Baaba kamar ana korarku. Akwai walima da za'ayi gobe bayan magriba tafiyarku sai gata ma. Jibi ku huta"


Anti Baraka tace "amma dai wasa kake yi ko Awaisu"


"Wallahi da gaske nake abokina da matarsa ne suka shirya. Ai dai bazaku tafi muje mu kadai kamar marasa dangi ba"


Duk da suna masa kawaicin basa son dadewa a gidan amma ya kula sunji dadi da har yayi wannan tunanin. Tashi yayi da ledojin hannunsa Hindatu tana shigowa lokacin tace suna jira a raba kazar amarcin a aiko musu. Nan fa ta bude kofar sabuwar tsokana ya fita yana dariya.


Dakin Gimbi ya wuce tana zaune kamar wata sabon kamu yace yasan tunda suka zo bata fita ba taje ta gaishe da Baaba.


"Amma ka rainani Awaisu. Ni Gimbi naje na gaishe da kakar kishiya sai kace wadda aka cewa jeki kya gani" tana magana tana huci


Shi kuwa ko a jikinsa yace "to meye maraba, kuma ina so ki kiyaye Rumana ba kishiyarki bace"


Zaro ido tayi sosai "to meye matsayinta? Kada kace min nemanta kake yi babu aure da yardar iyayenta"


Hannu ya kada yana fita "wannan kuma ya rage naki. Kishiyoyi a sanina miji daya suke aure...."


Yafi minti biyar da fita Gimbi tana ta juya maganar Awaisu a ranta. Me yake nufi???
******


Kafin ya shiga dakinsa ya nuna musu kitchen yace suyi jeren kayan a nan sannan ya bude dakin da ya tanadarwa Rumana wanda duka kayan bukata na dangane da furtuniture da electronics ya zuba.


Daga Fika sun taho da bedsheets da 'yan abin da ba'a rasa ba tunda babu iyayen da zasu so aurar da yarsu sikau.


Wanka yayi ya kwanta don ya gaji da wuri ya fita. Rumana yake son sake gani amma idanun jama'a yayi yawa kada a ga rashin hakurinsa.


Anti Ummukulsum ya kira ya fada mata ya siyowa Rumana riga yana son ta gwada kada gobe a sami matsala. Ya nuna mata baya so kowa ya gani sai goben.


"Ko dakinta kuje ta gwada bari na miko miki rigar"


"Dakinta da mutane ana gyara zan turo maka ita"


Kafin ya sake magana ta katse wayar. Dariya tayi tasan yana son ganin matarsa ne kuma babu dalilin hanawa. Dakin Maamu ta koma ta kirawota. Daga wurin korido suke tsaya tace taje dakin Awaisu yana kiranta zai bata sako.


Gabanta taji yayi wani irin bugu ta kasa ko da daga kafa balle ta tafi. Anti Ummukulsum ta zare mata ido tace ta wuce kafin ranta ya baci.


Yatsanta data matse a kofa ta dagowa Antin idonta cike da hawayen tsoro tace "ciwona ne yake zafi Anti bazan iya zuwa ba"


Haba ta rike tana kallonta "Rumana ke da ba da yatsun hannu kike tafiya ba meye zai hanaki zuwa. Daure kije sai kice nace ya baki magani "


To kawai tace ta nufi dakin nasa rike da hannun da ta manta yana zafi sai yanzu. Anti Ummukulsum ta girgiza kai tana tausaya mata. Tunda suka iso ta kula jikinta yayi sanyi. Zama a matsayin matar Awaisu kadai ya isheta to ga Gimbi kuma a gidan abin yayi mata yawa.


Da kukan tayi sallama ta shiga dakin bayan ya amsa. A bakin kofa ya tarota jin tana kuka.


"Waye ya taba min Son So uhmm? "


Yatsun da ta matse guda biyu ta daga tana nuna masa. So take kawai yace ta fita don ji take kamar ko numfashi tayi a dakin idan ta fita za'a gane. Karo na farko da ta taba shiga dakinsa kenan duk zamanta a gidan. Ba don a tsorace take ba da tace dakin ya hadu kamar mai shi.


Hannun nata ya kalla "me ya same shi?"


"Anti tace nazo zaka bani magani. Matsewa nayi da kofa"


Idanunta sun cika da hawaye yasan tsoro ne ya cikata yace akwai aiki a gabansa.


Yatsun ya kama sai kawai ta fashe masa da kuka. Yanzu duk wanda ya ganta cewa za'ayi daga dakinsa ta fito ko da tace Anti ce ta turata karbar magani.

Hanyar gadonsa ya ja hannunta ta soma turjewa jiki na rawa. Kin sakinta yayi sai ga hawaye kamar an bude famfo. Cikin kuka tace
"Ayya Uncle ni kam naga boni yau din nan"


Dariya yaso yi sai ya matse yace "ina yake" yana zaunar da ita akan gadon.


Kallon rashin fahimta tayi masa yace "kince kinga boni ni kuwa ban ganshi ba"


Kanta ta nuna "ba gashi ba.ni.anan dakin.da.....daa...kai!"


Daga mata gira yayi yana tsaye a gabanta "amma kina da matsala, ke da kika zo karbar magani. Dauko miki zanyi kisha saboda kada kiyi zazzabi"


Yana kallo duka hannuwanta biyu tasa ta dafe kirjinta irin na hankali ya kwanta ta dago kai harda murmushi "ashe magani nazo karba fa. Bani sai na sha a wurin Baaba" ta mike tsaye sai ya sake komawa gabanta ya tsaya.


"Ki dena murna nan din dai zaki dawo ki kwanta. Yarinya sai tsoron tsiya duk kin firgice" yantsun nata biyu ya riko har ta danyi kara sai ta ga ya saka a bakinsa.


Kunya irin wadda bazata misaltu ba ta kamata tayi kasa da kanta jin yadda ya mata a yatsun. Rungumeta yayi yana jin harbawar zuciyarta da gudu. Sun dauki lokaci a haka sannan ya cire yatsun daga bakinsa ya dago kanta suka hada ido tayi saurin rufe nata.
"Ga maganin nan, idan kinji ciwon ya dawo kizo na sake baki"


Yana kallon bakinta ta dan turo shi ido a rufe tace "shiyasa nace maka naga boni don Allah ka barni na tafi kada a nemeni"


"Zaki ganshi dai amma ba yau ba. Kuma babu me nemanki duk 'yan rakiyar nan wurina suka kawoki"


Bakinta yayi ta bi da ido sai kuma ya dauke kansa shi kadai yana ayyana abubuwa.
"Ga kaya can ki gwada na gobe ne"


Ido daya ta fara budewa don bata son hada ido dashi. Ganin ba ita yake kallo ba ta bude dayan tana kallon inda ya nuna. Gaban ledojin taje ta durkusa tana budewa. Kayan sun tsorata ta saboda kyaunsu ta dago rigar tana dariya


"Uncle" tace ya bata rai tayi saurin gyarawa "To Uncle Son So kayan mene ne?"


Komai na Rumana yana burge shi. Sai ya tuna da Nuru yace masa wannan soyayyar kila hadda hakkin rikonta da ya kasa yi a baya Allah Ya jarabce shi da son ta. Hamdala yayi a zuciyarsa shi kam ya dace .
"Akwai walima gobe da na shirya to welcome you Son So"


Tashi tsaye tayi harda tsalle "da gaske? Kuma wannan kayan zan saka? Unc....Son So nagode. Bari naje na gwada"


Hanyar fita tayi ya janyota ta fado jikinsa suka zube akan wata resting chair doguwa a dakin.
"Not so fast Son So, a nan dakin zaki gwada. Kina so kowa yaga kayan ne kafin gobe?"


Yanayin da suke ne ya sa ta shiga tashin hankali ya fada a kwance tana kansa ga ledojin hannunta sun zagayesu. da taimakonsa ta tashi yace tayi sauri ta gwada tunda kiyastawa kawai yayi girman. Takalmi dai yasan size dinta rigar ce baya son a sami matsala.


Tasan bazai bari ta fita da ita ba sai ta nufi toilet. Tana murda handle din yace yanzu yayi wanka ya jika ko'ina. Jinsa kawai take yi bata yarda ba.


"Ki saka a nan kada ki jika musu idan batayi ba zan mayar ne"


Hawaye ya sake gani ya girgiza kai. Su amare wato kuka baya yi musu wahala. Ango na murna suna kuka. Da taushin murya yace
"Ba kya so na kalleki?"


Bata iya amsawa ba sai gyada kai.


"To bazan kalla ba yi sauri ki gwada"


Wurin wani working table da kujerarsa yaje ya zauna inda ya ajiye laptop da takardu. Da sauri ta cire rigarta tana yi idonta kyam a kansa kada ya juyo ta saka gown din. Laushin rigar kadai ya isheta jindadi bata san sanda ta fara juyi ba kasan rigar yana budewa ta soma dariya da tafi.


Dogon takalmin mai madauri ta saka ta tashi sai ji tayi kamar zata fadi. Anya zata iya tafiya dashi kuwa ta tambayi kanta. sai dai fa komai na kayan ya burgeta sosai ta sake yin juyi taji ta tafi luuu zata fadi.


Awaisu da yake ta kallonta ta screen din laptop dinsa batare da ta sani ba ya taso da sauri ya rikota.


Ajiyar zuciya tayi tana kallon yadda komai yayi mata daidai a jikinta. Shima kallon nata yake yi tun yanzu ba karamin kyau tayi ba.


"Kinyi kyau Son So"


Tayi wata dariyar jindadi "thank you"


"Idan takalmin zai baki wahala sai na siyo miki wani da wuri"


"A'a don Allah ina son wannan din. Ina naji zan fadi sai na rike Iman"


"Zaki sa na cewa dreban da ya kawosu ya mayar da ita Fika yanzu. Idan zaki fadi mijinki ne support dinki kinji ko"


"Naji Uncle Son So...nagode"


******
Washegari da wuri suka sake tashi aka karasa duk wani gyara da za'ayiwa dakin Rumana da kitchen. Hatta kayan sawarta wanda suke cikin akwatuna uku manya manya da Harisu yayi mata duk an jere a drawer Anti Baraka ta kwashe mukullan.


Rumana da Iman da sauran 'yan uwansu daki daya suka kwana cikin na baki. Yayyenta mata biyu suma duka tare suke sai Zee da take ta jiran ganin ma'aikatan gidan maza don ta mika kokon bararta. Ita dai ta sami mai aiki a Abuja kowane iri ne yadda a Fika ana cewa a ina take aure za'a ce a Abuja. Nacin da ta kafa musu yasa Mama da kanta tace a taho da ita.


Tun karfe biyar Hajiya Fattu ta iso gidan. Dakin Maamu aka kaita ta gaishe da Baaba sannan ta nemi ganin amarya.


Rumana na shigowa Fattu ta tashi ta tarbota tana kare mata kallo " _perfect_, gaskiya angonki ya iya zabe. Yanzu wanka zaki fara yi kafin mu soma kwalliya"


Baaba ta dafe kirji tana kallon fuskar Fattu da irin kayan jikinta. Sarka har ciki ga su awarwaro ko yaya ta motsa sai kaji kachauu.


"Kece mai mata kwalliyar?" Baaba ta tambaya.


Hajiya Fattu ta wani murmushin burgewa "angonta ma bazai ganeta ba idan na gama"


Baaba tace "kwarai kuwa, Allah Yasa kada yayi tunanin gamo yayi. Bari na baku wuri....Rumana sai ince yau kinga boni da kike yawan kira ra'ayil aini"


Sai da kowa ya fita Fattu ta bata wani mulmulen abu a leda ashe sabulu ne tace tayi wanka dashi.


Rumana ta shiga tana saka masa ruwa kamshinsa mai matukar dadi ya gauraye bandakin. Ta jima a ciki tana wanka sannan ta dauro alwala ta fito.


Man da zata shafa ma ita ta bata. Nasa kamshin ya ninka na sabulun. Dadi ya kamata ta saki jikinta da Fattu. Wasu turaruka masu maiko ta sake bata ita dai komai akace tayi tana yi. Jikinta tuni ya koma wani sulbi da kamshi sannan Hajiya Fattu ta soma nata aikin.


Zee aka bari gadin kofa sai da aka kira magariba Iman ta chanjeta lokacin sun gama shiryawa itama taje ta shirya. Anti Baraka ce tace kowa ya fita Awaisu yace a kaisu wurin taron.


Ya gama nasa shirin cikin wata suit mai bala'in kyau coffee brown sai shirt din light brown da tie shima coffee mai farin stripes Sai takalmi da agogo duka kalar shirt din. Kallon kansa yayi a madubi yayi dariya wai bikinsa ne da Rumana.


Da ya fito ko'ina tsit duk an tafi dama yace kada su jira zai taho da Rumana.


Gimbi ya gani ta fito tana leka falo saboda shirun da taji. Ganin yadda yayi mata kyau sosai yasa ta tsaya kallonsa tana tuhumar kanta me tayi ya rabata da masoyinta.


"Dama yanzu zan fada miki zamu je wurin walima kada kiji gidan shiru"


Harararsa tayi "sai yanzu zaka fada min?"


"Kinga laifina? Naji tsoron sanar dake da wuri kada ki kira bokayenki ku shiga ku fita taron yaki dadi. Sai mun dawo."


Wuce ta yayi sai dai a ransa yana jin wani iri. Tausayi Gimbi take bashi ba na komai ba kuwa sai na yadda taki saduda ta dawo daga rakiyar shaidan...idan mutuwa ta risketa a wannan yanayin shikenan tazo duniya a banza. Mata da yawa suna aikata shirka da sunan soyayya amma idan zasu duba zukatansu sosai sun san cewa son zuciya ne kawai yake dibarsu.


Kofar dakin Maamu aka bude Hajiya fattu ta fito tana masa dariya "ango na cika aikina. Yadda yarinyar nan ta shiga raina na yafe kudin"


Gabansa ne ya dan fadi ganin irin nata adon ya fara nadamar daukota. Matsawa tayi gefe Rumana ta tako a hankali yana binta da ido har ta iso gabansa ta tsaya. Ganin ya kasa motsi bare magana sai tasa tattausan hannunta ta riko shi harda lankwashe yatsun cikin nasa.


Magana take yi a nutse tana lumshe ido "Uncle Son So"


Tun daga kanta har kafa yake kallo "na'am Son So"


Fari tayi da ido "nayi kyau?"


"Mun fasa zuwa wurin muje dakina na sake ganin kwalliyar sai na fada miki ko kinyi kyau"


Juyawa tayi wurin da Fattu take sai dai tuni tayi falo ganin yadda Awaisu ya rude da yaga Rumana. Ita kuwa ta kyabe fuska "Hajiya Fattun nan ce fa tace inyi maka haka idan mun fito zaka ji dadi. Daurewa nayi sosai kuma gashi ta janyo kace an fasa zuwa"


Hannuwansa yasa a kugunta yana sake kallonta. Wani irin rolling Fattu tayi mata bayan ta daura mata wani dankwalin ta ciki kalar rigar saboda kada maikon gashinta ya bata mayafin. Fuskarta sai ta fito sosai. Ga wani kamshi yana fizgarsa ko ta ina. Ba don ana jiransu ba sai ya bata kwalliyar nan a sake wata.


Da kyar ya saita kansa suka fito falo yayiwa Fattu godiya yace kuma idan babu damuwa gaskiya zai turo mata Rumana ta koya mata kwalliya. Dariya tayi tace tana jira sai sun zo.


Kusan tare suka shiga mota ta fara fita suka bi bayanta. Awaisu tuki yake kawai hankalinsa yana kan Rumana. Ita kuma kunyarsa saboda kallon da yake yi mata yasa ta kasa sakewa.


Motoci suka gani a wajen da yawa har yana tunanin anya duka masu amsa gayyatarsu ne kuwa? Wani matashi ne yayi saurin komawa ciki ya sanar da isowar amarya da ango.


Wata waka suka ji tana tasowa daga ciki ana ambaton sunayensu ana wasa amarya Rumana da angonta Awaisu. Kafafunta taji sun soma rawa kamar bazasu dauketa ba Awaisu ya rike mata hannu a hankali yace "yau taki ce Son So kada kiji tsoro ranar farinciki ce"


Sake damke hannunsa yaji tayi suka soma tafiya a hankali Mudan Dan Arewa yana wakesu don gabansu ya dawo yana wakar suna tafiya har suka je mazauninsu suka zauna aka hau tafi.


Maman Gimbi bata je ba amma ita da alhaji Mudi sun fadawa yaran babansu ya auri Rumana yanzu itama mamansu ce. Nasiha tayi musu yadda kwakwalwarsu zata dauka banda rashin kunya ko raini tsakaninsu sannan ta saka musu kayan da Awaisun ya kai yace su yake so su saka yau. A wurin su Baaba suka zauna sai da suka ga zaman su Awaisu suka tashi duka su hudun suka tafi wurinsu.


Mazan na jikin babansu Daula ta rungume Rumana tana cewa tayi kyau akayi musu hoto a haka.


Shuhada ma tazo kwanansu biyu da dawowa daga Singapore. Har wurinsu taje suka yi hoto tace da Rumana sai ta kawo mata ziyara gida. Yadda taga Awaisu bai iya boye soyayyarsa ga Rumana ya tuna mata da T dinta ta sake dankawara Anti Bebi Allah Ya isa.


Taro yayi kyau sosai anci an sha kowa ya tafi cikin farinciki.


Duk da ba'a tashi daga taron da wuri ba amma washegari kafin shabiyu mutan Fika sun kama hanya bayan doguwar nasihar da aka sake yiwa Rumana. Kuka take yi sosai idanunta sunyi ja kamar an zuba barkono. Sai da motar karshe ta tashi ta koma ciki ta bar Awaisu da maigadi suna magana.


Hanyar dakinta da ta fara shiga yau da safe Baaba tayi mata fada shi ta nufa. Tana tafiya taji an damko wuyan rigarta an shake. Da sauri tayo baya ta juyo Gimbi ta gani gabanta ya fadi.


"Yau na tabbatar danginku kwadayayyu ne sannan kuruciya tana cinki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login