Showing 27001 words to 30000 words out of 150358 words
Chapter 10 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
ne dabazasufi 10 ba, sai space babba dawani katon kujera, sai glass sliding door, ga flowers masu kyau an jera awajen.
Sliding glass din akayi, gani tayi wayanan lawyers dinan na jiya da Barrister jiya dukansu sun fito suna sanye da suit bakake sunyi layi akan dakalin saikuma gawani babban mutumi daya sanya wani hadaden embroidered lace akamai, agbada ga sandar girma maikan maciji a hannunshi yana dogarawa kaman baison ya dogara yana tafiya dai dai cikeda isa dakuma iko yafito yakaraso ya zauna kan hakimin kujeran dake wajen, yadaura kafa daya kan daya yana kallonsu, guards din dake wajen ne suka fara zubewa akasa yaranma suka bisu gabaki dayansu suka zube akasa sukai kneeling kan kowa akasa. "Angaishe da Wazirin Sarki"... jin iska na bugunta tako'ina tana kuka kuma taji anyi magana duka atare sanan wajen yay tsit kaman ba'ai hallita ba yasa ta ahankali tacire hannunta dake kan idanunta tana share idanunta dasukai jajir dashi hawaye na zuba, ganin mutumi zaune ga Lawyoyin nan tsaye agefenshi duk ita suke kallo yasa da sauri itama ta tsuggana akasa kaman yanda taga sunyi tawani sake rushewa da kuka sosai dan tasan hala sai ansake mata duka dan laifi takuma yi an tsugunna an gaida sarki ita tana tsaye, ta daura hannayenta akan bakinta tana taushe bakin sabida kar sautin kukan yafito amman ko'ina najikinta rawa yake.
Batare da Wazirin ya amsa gaisuwan suba balle yabasu izinin tashi tsaye yakafe Fatima da idanu yanda ta tsugunna kanta akasa jikinta na bari tana kuka sosai ta taushe bakinta, yara 100+ ne awajen amman ita kadai ke kuka gabaki dayama ma atsorace take. "You"! Yakirata cikin cikakkiyar muryanshi da babu alamun wasa aciki ko sanyi, ko kadan batasan ita ake kiraba tadaiji ance you, wani yaro dake kusada itane ahankali gudun kar ajishi yace "Otun is calling you" da sauri ta dagokanta ta daga jajayen idanunta ta kalli inda suke, ganin ita yake kallo har lokacin ya kafeta da ido kur yasa tamike tsaye ahankali tareda share idanunta jikinta ko'ina yadau kakkarwa kaman mazari, da hannu yamata alamu tazo da sauri ta tafi gaban Mansion din hawa about 10stair case din wajen tayi sanan takai gaban kujeranshi kasa jure yanda yacikamata idanu tayi da sauri tai kneeling down ta kulle idanunta gam cikin harshen turenci tace "please i am sorry, I will not repeat my mistake again, dan Allah karkasa adakeni I am so sorry, please, please" saikuma tafashe da kuka ahankali jikinta nabari har lokacin idanunta akulle wani irin tsorone aranta bana wasaba bata taba ganin irin this set of mutane ba kokuma set of life dinan, she is not use to any of this, arayuwanta daga iyayenta sai Maryam su kadaine in her life, wanan set of people dinfa dabama tasan takamaimen menene su ba, Muslim ne ko Christian.
Gabaki daya compound din yay tsit babu abinda kakeji sai sautin sheshekan kukanta, sosai Waziri ke kallon kyakkyawan yaron da baisan mesaba amman yaron yay mugun capturing attention dinshi at a glance, dan gyaran murya yayi sanan strictly yace "open your eyes" dasauri tabude idanunta dahar sunsoma kumbura tsabagen kuka amman bata kalleshi ba kanta akasa, anatse yace "what's your name"? Ahankali cikin muryanshi bana namiji ba bakuma nq mace ba mai dadin sauraro da intonation din hausan ta tace "My name is Khalid Muhammad" "how old are you"? Waziri yay maganan har lokacin bai dauke idanunshi daga kanshi ba, ahankali tace "I am 19yrs old" shiru Wazirin yayi kaman mai nazarin abu yace "why are you crying? Bakasan kuka namata bane mazan this kingdom basa kuka, so why are you crying"? Hadiye bushashan yawun dayarage abakinta tayi saita shiga kama wandon ta tawajen cinya tanaja tana rikewa tsabagen yanda gabanta kefaduwa kaman yar karaman yarinya tace "I am scared" for the first time sai Wazirin yay murmushi irin na manya dinan, sanan ahankali yace "stop being scared okay" gyadamai kai tayi ahankali itama, sanan yace "stand up and go back to your place" tashi tayi da sauri tajuya tafara sauka daga dakalin Waziri yace "and stop crying and behave like a man" gyadamai kai tayi takoma wajenta ta tsugunna kaman yanda kowa kenan atsugunne har lokacin.
Gyaran murya Wazirin yayi sanan yace "raise" tashi tsaye sukayi, Baban Barrister nanne dan tsohon jiya ya matso gaba rikeda wani book cikin harshen turenci yace "you are all welcome to wanan kingdom din inji Wazirin mu mai albarka, Mai Martaba dakuma tausayi, nasan yawancin ku sunajin yunwa sunkuma gaji amman karku damu abinci mai dadi dakuma makwanci lafiyayye na jiranku a various wajajen aikun ku, idan kunji sunayen ku kufito gaba guards zasu tafi daku wajen aikinku kuci kuyi bacci kuhuta kufara aikatau gobe" akai tsit ana sauraronshi, yafara kiran sunaye, sunayen yara su 20 yakira suka fito akace za'a kaisu poultry house wuce dasu aka sasu a mota, aka sake kiran 20 akace su suna factory house, aka kiran wasu 20 suna water company, aka kira wasu 20 suna farm cikinsu harda Anas yamata bye tana kallo suka kwaso kayansu daga motarsu aka tafidasu awata motar, yarage basufi su hamsin ba a filin, kiran sunayen aka cigaba dayi taji ankirata."Khalid Muhammad" ahankali tafita zuwa gaba, daidai nan taga Waziri yay gyaran murya hakan yasa Barrister yajuyo yaduka yakai kunenshi wajen bakin waje bakin Waziri, yamai whispering abu, gyadamai kai yayi yatashi yajuyo ya kalli Fatima yace "Khalid go back to your place" ahankali tajuya takoma wajen tsayuwanta ta tsaya tana gani aka kira duka yaran tatas aka tafi dasu yarage saura ita daya kacal a filin sanan Waziri yatashi yana tafiyar kasaita ya shiga ciki, Barrister ya kalli daya daga cikin guards din yace "abashi abinci shi Otun zaima aiki" dudda batasan menene Otun ba amman tagane wanan sarkin dayamata magana shine suke kira da Otun.
_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
💫 _DISASTROUS LOVE_💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
_This novel is 500, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turomin evidence of payment to my watsapp number._
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 1️⃣4️⃣
_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
_FREE PAGE_
Barrister na gama maganan shima ya juya yashiga ciki daya daga cikin guards din gidan ne ya kalleta yace "let's go" tashi tayi ahankali har lokacin gabanta nafaduwa ganin yanda take rayuwa cikin maza tabisu, dakin dasu suka kaita, zama tayi ahankali akasa ba'a wani jimaba aka kawo mata lafiyayyen tuwon semovita da miyan egusi gawani dankareren nama dasaida takara bude ido tana kallon naman dan yayi kan wani karamin jariri girma, daya daga cikin securities din dasuka tuko motarsu ne yafashe da dariya dan tuntuni suke kallonshi yace "dalla jibi dan kauye angayamaka nan kano ne, yarbawa haka sukecin nama katun katun, yimaza kaci abinci yanzun nan zaku fita" dukarda kanta tayi tai bismillah tafara cin abincin, tanacin loma daya tafara tari sabida yaji nanma securities din sukahau mata dariya kaman zasu suma da gudu tadau goran ruwa tabude tasha tana kallon abinci gashi shegen yunwa takeji, cigaba da cin tuwon tayi batawani dangwala miyan sosai ba dan yajin yafi karfinta ahaka tacinye tass sanan takarasa shanye ruwan batare dataci naman ba sabida tsoron yaji kaman jiranta ake wani sabon guard wanan uniform nashi daban ya shigo yace "let's go" tashi tayi suka fita bama yabari ta wanke hannun ba saidai ta lashe yatsunta tass sanna taga sunfita daga compound din sunyi compound din white Mansion, bude sliding glass door din guard din yayi suka shiga, wani dankareren falone girmanshi yayi kusan duka gidansu na Kano, wasu lafiyayyun kujeru ne aka zuba dabata taba ganin irinsu ba sai lallausan carpet da tana tafiya akai tana kallonshi dan tunani take ko katifa ne ga dankararen kujeran Waziri dake zaune akai shi kadai a falon yana kallonsu, har gabanshi sukaje guard din ya tsugunna hakan yasa itama ta tsugunna da sauri da yarbanshi guard din yace "Allah taimaki Otun ga yaron nan" gyadamai kai Waziri yayi hakan yasa yawuce yafita saida yarufe sliding door din sanan Waziri yajuyo ya kalleta har lokacin kanta akasa anatse yace "raise and sit" tashi tayi sanan ta zauna akan carpet din ahankali tareda lankwashe kafa gabanta nafaduwa, gyaran murya Waziri yayi cikin turenci yake mata magana dan yasan yaron daga North yake yace "look at me" ahankali kaman wacce ke tsoro tadaga kanta ta kallai kirjinta na dukan uku uku dan yamugun cikamata ido, gyaran murya yasakeyi sanan yafara magana cikeda isa da girman kai da gadara gabaki daya dakuma kakkausar murya yace "nasa anbarka anan ne sabida you are going to work for me" yanunamai kanshi, sanan yasake gyaran murya kaman mai crack throat, ya kalleta yace "your work is very simple, Sarkina yanada yaro daya namiji tak aduniya sunanshi OLUWATOBI TAJUDEEN ADEWALE, right now baya Nigeria but kwanan nan zai dawo, zaka dawo errand boy dinshi, kai zaka dingamai komi dayakeso dakuma yake bukata, aikinka dayane tunda kana tareda shi koda yaushe kadinga haddace kome yakeyi, kodawa yay magana koma meyayi, kullum ina zuwa fada da safe ina barinshi da yamma wuraren shidda, idan nazo zam tafi kafinma nafito inaso nasameki a parking space ka sanar dani komi nashi komi dayayi ranan saikuma ka, aikin ka nabiyu shine daukan rahoton kome prince yayi kazo ka sanar dani kanajina" da sauri ta gyadamai kai ya gayada kai yace "good, sanan duk randa ka kuskura ka sanarda wani aikin dakakemin kashinka yabushe saina batardakai daga doron kasar nan understood" da sauri tace "yes sir" sake gyadamai kai yayi sanan yace "yanzu zan tafi fada zan nunama Sarkina kai sanan nabarka achan har uban gidanka yadawo Prince kagane, daga ranan daya diro kasarnan ranan zaka fara kawomin rahoto kagane" ahankali yace nagane, da hannu awulakance yamai alamun dismiss hakan yasa ta tashi tafice da sauri, abakin kofan Guard yatareta yace "tsaya anan" tsayawa tayi awurin kusan 20min harta gaji da tsayuwa sanan taga wasu manya manyan hadaddun motoci jeep guda uku sai roll royce saikuma taga guards sun budema waziri kofa yafito yana tafiya kaman bazaiyiba yasauka daga stairs yahau roll royce din dasuka budemai kofa yashiga ya zauna suka rufe sanan daya daga cikin guards din ya kalli Fatima yace "zoka shiga nan" saukowa ahankali tayi ta shiga motan dayake nuna mata, ita kadaice abayan motan sai guards guda biyu agaba daya na tuki daya na zaune adayan kujeran taga an tada motar anfita daga gidan.
Tafiyan kusan minti goma sukayi zuwa sha biyar tagansu agaban wani layi mai kama da estate agaban dankareren gate din layin an rubuta OBA OF LAGOS PALACE (FADAN SARKIN LAGOS), ana ganin motarsu masu gadin dake sanye da uniform suka bude gate din sanan suka duka alamun gaisuwa motoci suka shiga ciki suka wucesu, wani dogon layi ne taga sunata tafiya dayaji interlock sanan sukaka second gate taga an kara budewa sanan masu gadin suka duka gaida Waziri kafin su shiga wani irin dankareren gida da girmanshi yayi girman wani kauye ko garima, ga statues na dankareren lion da akayi ya tsaya bakinshi abude kaman zai hadiye mutum, ga wani bangare daban na parking motoci motocin wajen kadai sunfi guda 35 hadaddu gaske irin wayanda bata taba ganiba ga sunayen su customized, gawasu irin flowers dabata taba ganiba ga water treatment plant a compound din dayay kaman roundabout ashema gidan farkon data fara zuwa ba gida bane, guards ne kusan su goma akowani staircase din shiga palace din suna sanye da uniform gajeren wando blue daya tsaya musu a guwiwa saikuma black t-shirt sukai zanzaro dashi, parking motar waziri yayi sanan suka fito suka budemai itama tafito daga tata motar, ahankali yake tafiya kaman bazai takaba haryakai staircase din duka guards din wajen suka zube sunamai kirari da yarensu da batajin meake cewa budemai kofa yayi ya shiga yayinda ita aka tsayarda ita awajen batare data shiga cikiba.
Babban falone ba kadan ba, komi na falon farine da blue, mukarraban fadane zazzaune saikuma wani babban hamshakin mutum dake kan kujeran sarauta yana sanye da full kayan sarki anamai fiffita dudda ga AC dake tashi adakin amman fifita akemai, mutumin yadan tsufa dan akalla zaiyi 70yrs, bakine ga furfura ko'ina agemunshi, kowa na fadan zubewa sukayi akasa sukayi suka gaida Waziri dayashigo yana tafiyan kasaita banda Oba dake zaune akan kujeran mulki, ahankali Waziri yakarasa gaban Sarkin sanan yazube akasa cikeda girmamawa cikin harshen yarensu yace "nagaishe da Sarkina, ubangidana, takawan ka lafiya jikan Oduduwa, Baban ka Sarki, Baban Babanka Sarki, Baban Baban Babanka ma Sarki, takawan ka lafiya Baban AREMO (Prince) OLUWATOBI TAJUDEEN ADEWALE" asanan Sarki yasaki wani kayataccen murmushi yakai sandar sarautan shi dakedan kan zaki na zinare yadaura abayan Waziri yace "sannu da zuwa, tashi kazo kazauna Otun" tashi Waziri yayi yace "godiya nake Sarkinmu Sarkin Haske" kujeran dake gefen daman sarki wanda baikai na sarki girma bane yazauna yana gyara zama, Sarki yadubi mutanen dakemai magana sanan ya kalli Waziri hakan yasa Waziri ya matso da kunnenshi magana Oba yamai sanna yakoma ya gyara zama, gyaran murya Waziri yayi yace "Sarkina yanzu yana bukatan huta, zai huta sanan zaiyi tunanin magananku kome ya yanke zaisa asanar daku" godiya sukayi sanan suka tashi suka fice yarage saura su kadai afalo, Oba yace "tuntuni I've been stressing myself inata magana bakazo da wuri ba but I understand aikin danasaka ne saisa ban kiraka ba amman dukna gaji wlh" dariya Waziri yayi yace "nazo yanzu wahalan ka yakare Sarkina, kome kakeso shi za'ayi jininka yabaka, komunki komunso dole mubika" dariya Oba yayi yace "tom ya aikin yakuka kare" nan Waziri yabashi full details din komi da wayanda suka biya bashi dayaran dasuka shigo hannunsu aikatau sanan yace "amman nataho dawani yaro guda daya yanzu haka ma yana waje" anatse Sarkin yace "why"? Dan yasan kome Waziri zaiyi yanada dalili saisa babu wanda yasan cikinshi da wajenshi sai Wazirin shi nadama Otun, gyara zama Waziri yayi yace "Prince Tobi nadaukarma yaron" ambaton Tobi dayayi yasa Sarki yasaki wani kalan murmushi dayasa shima Waziri yay murmushi cikedajin dadi yace "Tobi kullum in yana gida korafi yake akan masu aikinshi na damunshi suncika girma kaza kaza kaza shi baisonsu baiso suna shigomai daki alhalin idan an barshi ko takalmin shi bazai iya sawa da kanshi ba, saisa danaga yaron nan naji ya shigan mini rai, he is just 19yrs old boy, very handsome boy Sarkina, Fulani Hausa Boy ne from Maiduguri but a Kano suke, he can speak english so communicating da Tobi bazaimai wuyaba, he looks so innocent and charming so I feel for the first time duk muka kori wayan nan manyan guards dinan da Tobi ke complain bayaso muka bashi this 0small boy as his errand boy bawanshi mai kula dashi he will love it and appreciate you, this should be the perfect Boy dazaka bashi a matsayin gift dazaran dayawo koya kagani Sarkina" kayataccen murmushi Oba yakara saki yace "nobody can be better than you Otun, ina alfahari da zamanka abokina dana taso nakuma girma dakai ayanzu kuma muke tsufa tare, wani zubin ma har gani nake kaman kamafini son Tobi" da sauri Otun yakama bakinshi yace "waiwaiwai wai, karkai sabo fa Sarkina, wanan ne abinda ban yardaba, Tobi is your entire life, inhar za'a hada son danake ma Tobi danaka nibama sonshi nakeba compare to naka, that our stubborn footballer, ya maganan nan zamuje kallon final match dinshi na champion league ko haryanzu kafan nan" dan jim Sarki yayi yace "inaso naje but bari muga nanda gobe idan kafan yay sauki idan baiyiba bazamu jeba tunda duka duka jibi ne final match din, I can't wait for him to be back wallahi I miss my Son Otun" murmushi Otun yayi yace "nima nai kewan yaron nan maraji, nasa akawo maka errand boy din dana zabanmai acikin yan aikatau din"? Da sauri sarki yace "yes" kallon Guard din dake tsare kofa yayi hakan yasa yabude kofa yafita saigashi ya shigo da Fatima, suka zube gaisuwa da ita da Guard din sanan yatashi yafita itakuma tana tsugunne takasa dagokai tun bayan first look din datama wanda tana ganinshi taga shine asalin sarkin hala wanda