Showing 99001 words to 102000 words out of 150358 words

Chapter 34 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt

M Shakur   

07 Jan 2025

15390

✍🏾M SHAKUR




EPISODE 5️⃣1️⃣ & 5️⃣2️⃣


_Bayan Kwana Hudu!_
Rayuwa tama Tobi zafi, baitaba shiga kunci da ukuban rayuwa irinwanda ya shiga cikin kwanakin nanba, yay kwanan shi hudu kulle awajen nan babu wanka babu wanki, ana kawo mishi wasu kalan abinci kaman na kare ko kallon abincin bayayi saidai yasha ruwa shima dan karya mutu ne, kullum sai Babanshi ya aiko acemai yahakura ya janye batun sonta yace baiyiba, babu ko mutum daya daya shigo yadubashi cikin yan uwanshi, ya galabaita iya galabaita abinku da wanda baisan wahala ba, baida tunani saina Zara da inda suka sakata, inda take dan yasan tanachan tana kuka yanda beraye suka dameshi haka suka dameta itama, yasan tanachan tana tsoro tana kiranshi.
************








Sarki na zaune afada shida Otun kadai cikin dankareren fadan nan kaman munafukai, kana ganinshi kasan cewa baya cikin hayyacinshi yana cikin damuwa sosai danya nuna akan fuskanshi, suna zaune suna kus kus suna tattaunawa da Allah kadai yasan me suke cewa.


Suna zaune aka bude kofan fadan wani daya daga cikin guard din dake tsaron babban gate din gidan na titi ya shigo, zubewa yayi ya gaida sarki yana musu kirari sanan Otun yace "maiya kawoka"? Anatse Guard din yashiga koro bayani. "Allah gafarci Sarki na, wato yau kimanin kwana hudu kenan da wani mutumi dabaiyi kala da dan garin nanba yake zuwa yana neman izini abarshi ya shigo gidan nan yana neman wata yarinya dayake kira da Zara, yanuna motar prince da aranan da abinda yafaru ke kofar gida ya pakata awaje dan babu kowa agate yana cewa amotan yarinyam keciki, kwata kwata bamu taba tsayawa mun saurareshiba saidai mu sanardashi baida alaka da fada bazai iya shigaba, saime alaka da gidan nan keshiga kai tsaye, idan bakone saidai yay booking appointment na ganin sarkinmu, saiyau dai danaga yadage da zuwa na tsaya na saurareshi yakemin bayanin komi sunan yarinyar Fatima Zara'u Muhammad sanan ya suffantamin yarinyar wacce gabaki dayan kamaninta yay kama da yaron nan namiji dayake mace damuka gano agidan nan, yace yasanta shine zai aureta, saisa naga yanada kyau nazo na sanar dakai kasan kome ake ciki" da sauri da Sarki da Otun suka kalli juna, da sauri Otun yace "jeka shigo dashi maza" fita yayi da sauri, ba'a dauki minti gomaba sai gashi Guard din yashigo tareda Dr Imam dake sanye da jumper na wando da riga nawani lallausan yadi, yay bala'in kyau, yakafa hula akanshi brown dayay matching da takalmin kafarshi brown, kana ganinshi kaga dan hutu fari abinshi banbancin kawai shine baiyi kama da Fatima ba amman shima farine kal, har fada aka shigar dashi, cikeda girmamawa yagaida Sarki da Otun sanan ya gyara zama akan carpet din da aka ijiyeshi, Otun dababu alamun wasa akan fuskanshi yace "who are you? And why are you here"? Anatse yace "My name is Dr Imam Nasir, Hausa from Kano state, i came for one council exam dazaisa nazama consultant of medicine in my field........." yashiga koro musu bayanin yanda yaga Fatima a beach tashiga mota yamusu kwatancen motan harda kiran plate number daya haddace tun ranan hakan yasa suka kara tabbatar da motan prince ne, dan customize license plate gareshi, yace "am her Dr, and her husband to be" daidai nan yay shiru sai shima Otun yakoro mai bayani tundaga yanda ubanta yay biyan bashi da ita har rana irin tayau abinda ke faruwa, dayasa yay shiru yakasa magana yana kallonsu kawai.






Otun da Sarkine suka kalli juna kaman masu communicating da idanu harsuka gama, sanan Otun ya kalli Dr Imam, yace "Dr at this point bama mudamu da biyan bashin 3m dinba, zamu iya manta dakomi mubaka whoever that girl is batare damun kasheta ba, dan we just want to get rid of her, but sharadin is take her far away ta yanda har abada, har abada bazata taba dawowa wanan gidan ba, idan kuma tadawo ka tabbatar da kome mukama yarku ita tajama kanta, wanan gidan sarautan bama zalinci but wanda yaketa hurumi muma ketashi muke, yaranmu basa auren bare dan haka ta rabun mana da d'a" da sauri Imam yace "I can assure you that ko garin nan bazama takara dawowaba ballema tadawo rayuwan danku" gyadakai Otun yayi cikeda gamsuwa, yace "saidai akwai abu guda daya" da sauri Imam yace "menene sir"? Otun yace "abangaren mu munaso muyi abunda zaisa Tobi ya dauka tamutu ne har abada sabida ya manta da ita ya manta da soyayyan ta aranshi, yacireta daga ranshi, sanan yahakura da ita kakap, kanada wani abu dazaka iyama yarinyar dazaisa yadauka tamutune amatsayin ka na likita"? Da sauri Dr Imam yace "yes, akwai alluran dake stopping heart from beating for hours idan akama mutum alluran, zai fara kashema mutum jiki komi naka yakoma so slow kadauka ko mutum yazo mutuwa ne dagaske, saikuma chan zuciyar tai stopping tadena aiki, inhar danku yaga haka zai yarda ta mutu but banda alluran yanzu as u can see ni kadai nazo, a big pharmacy ake saidawa" Otun harda saurinshi yace "tunda kaiba dan garinnan bane, zan hadaka da direba na yakaika pharmacy dazaka samu kome kakeso kaje kadawo yanzun nan muma muyi making namu preparation din atanan bangaren sabida abin should look real" yana maganan yakira direban shi, sanan yasake bama direban kudin siyan maganin sanan suka tafi, Sarki ya kalleshi yace "make any plan dazaisa Tobi bazai dauka munada hannu a mutuwarta ba sabida karya kashe kanshi pls" tashi Otun yayi yace "kabarmin komi, yau karshen matsalanmu tazo" yawuce yafita daga fadan, sarki yasauke ajiyan zuciya yana addu'a Allah yasa matsalan tazo karshe da gaske.








Prince na zaune yana bude idanuwanshi da kyar musalin 1 na rana sabida tsabaragen tsabagen yunwan dayakeji, ga abinci ana kawomai yakici saidai yasha ruwa, alamun tafiya yaji hakan yasa yasake bude ido har aka karaso wajen kofan yake kallo da idanunshi dasuke juyawa saiyaga wanan guard dinan da kullum shike zuwa kawomai abincine yazo rikeda wani banzan kwano da ake kawomai abincin aciki dawani dan karamin kofi na ruwa, ta kofan ya ijiyemai abinci batareda yabude kofanba yana kallon Tobi dayaga ya galabaita sosai yadauke abincin safen dayakawo wanda baiciba yawuce yatafi batare daya cemai komiba, saikuma Tobi na zaune inda yake yaga yadawo yasake kallon Tobi yarike karfen kofan yace "Aremo I want to tell you something" kallonshi Tobi yake batare daya cemai komiba, Guard din looking so disturb yace "kaga kamankai itama yarinyar nan tunda aka kulleta bataci abinci ba ita harma da ruwa batasha ba, yanzu daga wajenta nake itama nakaimata abincin kaji yanda take numfashi kaman zata mutu kuwa? Wlh inhar yarinyar nan bataci abinci ba she can loose her life today, ta bala'in ban tausayi" dasauri Tobi yatashi yazo wajen yana tafiya da kyar yace "listen ka koma tell her injini nace taci abinci sabida tasami energy, tell her I can't live if anything happens to her, tell her she should eat and be strong for me karta damu am coming for her" da sauri guard din cikeda tsegumi yace "kasan baza'a bari nakoma ba kuma zai dare idan natashi zan kaimata abinci dare, bari natafi kafin guards din dake tsarenan sujini shiru su biyo bayana" da sauri Guard din yawuce yatafi Tobi kuma yahau ihu yana jijjiga kofan karfen yana. "Get me out of here kubudeni" fita guard din yayi Otun na waje taredashi kafin guard din yay magana yace "kafadamishi exact abinda nace kafada mai"? Gyadama Otun kai yayi sanan Otun yawuce yatafi yana murmushi, yana komawa fada daidai direbanshi na dawowa da Dr Imam a motanshi atare suka shiga fadan, Otun yacema sarki. "Zomu tafi daji, komi is set" tashi Otun yayi suka tafi dungeon din dashi da Dr Imam da Otun su uku kadai basu bari any guard ya shiga cikiba, suka shiga dungeon din da Fatima keciki suna mamakin yanda wajen yake is being years basuje ba to bama a using dinshi mezasuyi dashi, budemusu dakinta sukayi tana kwance tajuyama kofan baya tagalabaita iya galabaita, dudda taji an shigo ko kadan bata juyoba, tsayawa a kofa Sarki da Otun sukayi shikuma Dr Imam yashiga ciki da sauri yay kanta yace "Fatima Zara" tareda dagota zaune, ahankali takallai da idanunta dasuka kode sosai sukai fayau irin idanun wanda ya wahalu iya wahakuwan nan, fuskanta dukya kumbura ga ciwo ga alamun cizon saura da cizon abubuwa da damama ajikinta abunku da fara, ahankali yashafa fuskanta yace "hey is me Dr Imam, am here to save you" shiru kawai tayi tana kallonshi, wani irin ihu Otun yamai yace "Malam kana batamana lokaci do abinda zakayi before mu chanza mind dinmu mu kasheta" sakinta yayi yadauki kwalban alluran da syringe yabude da sauri hannunshi na rawa ya zuko alluran daidai mil din daya kamata yamata pushing, sanan ya kalleta yace "you will be fine, I will take care of you Angel" yana maganan ta saman riga ya chaka mata alluran adaidai saitin heart dinshi duk tana kallonshi kaman bata hayyacinta sanan ya juye ruwan alluran tareda cirowa yatashi ya kalli Otun yace "done in the next 5sec jikinta zai fara slowing down, within 10min from now zata mutu heart dinta zai daina aiki" nunamai wani dakin yayi Otun yace "kaika boye anan sabida karya ganka yay suspecting anything" sanan ya kwalama guards kira yace "ataho da Tobi nan" itadai tana zaune tana jinsu sama sama dan kunnenta taji yamata nauyi sosai kaman an daura mata block din gini akai.






Sama sama take gani idanunta na mugun juyawa jikinta namata kaman ba nataba, taga an shigo da Tobi dayafice hayyacinshi tsabagen wahala, Babanshi ne yamai wani kallo ya dake yace "am doing this sabida kai d'ana ne, yanzun nan aka sanardani she has not been eating all this while, duk abinda aka kawo mata haka za'a zo afitar dashi, kaman she's dying i asked akawoka dan kagani da idanunka ku sakeshi" ya umarci guards din dawani irin gudu yashiga dakin, tareta yayi yasata ajikinshi yana shafa fuskanta tana kallonshi sama sama lips dinta sun bushe sosai kaman banata ba yace "Zara, Zara, noo no nooo, don't do this to me, niban mutuba sai ke, no, no, food, food, water, water, you are hungry, lemme feed you kisami energy nothing will happen to you I promise, somebody give us water and food" yay maganan da karfi yana jijjigata sosai, ganin yanajin yanda jikinta ke saki ajikinshi yasa gabanshi yashiga faduwa kaman zai fashe, ahankali tadaga hannunta na dama da kyar tana kallonshi da idanunta dake rufewa tanason ta taba fuskanshi but takasa, hannunta yakama yarike ga saikuma yafashe da kuka sosai yakai hannun kan fuskanshi yace "Zaara is me, your Ya Tobi, please don't die my life will be shattered wlh, wlh I love you morethan life itself, Zaraaaa, you are the first woman that makes my heart beat, that makes my heart skip, that makes my heart to skyrocket, you are the first woman I think of, Zaraaa don't do this to me this wasn't our deal pls, is not fair kitafi ki barni bayan nakamu da sonki, I said is not fairrrr Zara" sosai hawayenshi ke zuba a hannunta daya rike akan fuskanshi itama hawaye yagani yafito daga gefunan idanunta sunbi ahankali sun gangara sharr zuwa kunnenta kafin dip zuciyanta yadena aiki gabaki daya tasaki ajikinshi hanunta dake kan fuskanshi yafadi, chak shima ya tsayar da kukan dayake kaman wanda yatabu, yakai hannunshi kan fuskanta ya bubbuga yace "Zara, Zara, Jewel" saikuma chan yay wani irin ihu kaman zai fasa dungeon din gabaki daya. "Zarah!!!!!, Zara......." yama kasa kiranta sabida yanda kirjinshi yabuga kawai yasaketa yay gefe asume shima warwas, da sauri Otun yace "come out Dr" fitowa Dr Imam yayi dayaji komi dayafaru da kukan Tobi, Otun yace "dauketa kubar kasanmu har abada, direba is ready zai kaiku har airport we can do that for you just do that for you danmu nuna maka masarautannan munada kirki" shiga dakin yayi yana kallon fuskan Tobi dako amafarki bazai mantaba yaron daya taimakeshi, tsawa Otun yadakamai yace "I said carry her and leave this house for good" da sauri ya ciccibeta yadauketa suka fice har lokacin yana waiwayan Tobi akwance a sume, motan da aka ijiye musu yasata shima ya shiga sai airport, yana zuwa all he showed was Id card nashi na Dr, yabiya kudin ticket aka bashi wheelchair yasa Fatima dat was still uncountious, karfe 6 dot jirginsu yatashi sun isa Kano wajajen gab da isha'i yana isa yatare taxi ya shigar da ita yabama wanda yabiyosu mai aiki a airport din wheelchair yatafi dashi.






Har gaban gidansu Taxi yay parking lokacin duka duka baifi 10min tafarka ba dan alluran 6hrs ne, yabiya taxi yadauketa ya shiga cikin gidansu da ita, kofar flat dinsu yabude ya shiga da ita ciki da sauri kannenshi duka na falo suna kallo, dawani irin sauri yace "Ray yana get me a stethoscope daga dakina run" dagudu tafita, yace "Rahma get me ice" sanan ya kwantar da ita akasa, ya wurgan dakomi na hannunshi ganin 10min yawuce bata farka ba inbai tadataba zata iya rasa rayuwanta gabaki daya, sanan ya nannade hannun riganshi sama ya kalli Asma yake tsaye yace "fold this hand for me" linke hannun rigan tamai, sanan yadaura hannunshi akan kirjinta ya danne sau uku babu motsi bata farka ba, dasauri yafara no no no Fatima wake up, wake up, yanda yake ihu yasa Ammi dake sama tana hira da Maman mijinta data iso yau daga UK tadan zabura, tace "Granny kaman muryan Imamu nakeji" Matan da aka kirada granny wacce ta manyanta sosai amman kudi yasa bazaka taba ganewa ba, tahadu sosai tana sanye da glasses a idanunta hannunta rikeda supplement na diabetes tace "Imamu kuwa" "Fatima wake up!!" Wanan karan atare sukaji muryanshi hakan yasa itama granny tatashi da sauri itama sukai stairs suka sauka kasa daidai Imam yacire hannunshi dagakan kirjinta yakoma jikin kujera yazauna tareda dafe kanshi ahankali yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un, chak Granny ta tsaya a stairs tana kallon Fatima that was lying there dead gabanta nafaduwa sosai saikuma ahankali takai hannunta kan glasses din idanunta tacire ta kalleta sanan tasake maida glasses din ta kalleta tace "Fadimatul Zara'u!!".










_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._




_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._


_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kUma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ❤




















️💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫






_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍🏾M SHAKUR




EPISODE 5️⃣3️⃣ & 5️⃣4️⃣


Granny takira sunan da karfi dayasa dukansu suka juyo suka kalleta kafin ahankali tabi ta gefen Ammi tasauko daga stairs din tazo inda Fatima take kwance akasa ta tsugunna tana kallonta yanda yarinyar tayi sanan tajuyoda kanta ta kalli Dr tace "Imamu a ina kasan yarinyar nan? A ina kasamo ta" motsin dataji Fatima tayi yasada sauri ta kalleta, Rayyana ce tace "Yaya tayi motsi" da sauri yazo wajen yasake maida stethoscope dinshi kunne yadura akan kirjinta jin heart dinta na beating yasa ya lumshe ido tareda furta. "Alhamdulillahi Rabbil Alameen, she's back" yafadi ahankali duk suna kallon fuskanta yanda take kokarin bude idanuwanta, bude idanun tayi ahankali sanan tadaurasu akan dukansu yan dakin har lokacin komina jikinta yamata nauyi, da sauri Granny tashafa kanta tace "Zara kin ganeni? Baabar kice" shiru tayi tana kallon Baban wani irin, kallon Ammi shi yayi yace "Ammi please amata wanka da ruwan zafi ta chanza kayan nan awanke kan nan nata, sai kubata tea tasha zanje hospital na kwaso magani nazo namat treatment i will tell you everything" gyadamai kai kawai Ammi tayi tana kallon Fatima itama, dasauri Granny ganin yasake zamane yana kallonta tace "wuce katafi mana Imamu" tashi yayi ya kalli Ammi yace "Ammi car key" gaban TV stand tanunamai, key motarta yagani hakan yasa yadauka yawuce yafita daga gidan.






Shadaya saura ya shigo gidan da katon ledan magani, Babanshi yagani da Granny dakuma Ammin shi afalo hakan yasa yadan tsaya yana kallon mahaifin nashi. "Are you standing there kozakaje kasaka mata abinda yakamata" Baban yay magana hakan yasa yawuce sama, adakin Granny yaganta kan gado an mata wanka ansaka mata doguwan rigan atampa light mara nauyi na Rayyana tana kwance kan gado idanunta biyu sai kallo su Rahma take har lokacin batace musu uppan ba, karasowa yayi yana kallonsu yace "tasha tea"? Rahma ce tace "kadan tasha bada yawaba amman" gyadamusu kai yayi ya shiga saka mata ruwa yay allurai a ruwan sanan yamata wani allura a vein ya tsaya chak yazuba hannu a aljihu yana kallonta kaman yanda yaga tana kallonshi da idanuwanta dake rufewa sanan idanun suka rufe tass bacci mai karfi ya kwasheshi yawuce ya sauka kasa kannenshi suka biyoshi, waje yasamu kusada Granny shi yazauna yace "when did you come back from UK Granny"? Murmushi tayi tashafa kanshi tace "nagaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login