Showing 102001 words to 105000 words out of 150358 words
Chapter 35 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
da zama dasu wlh, ni nafison kasata Nigeria, abeg ciwo bata kisa sai in lokaci yayi nadai kwaso magungunana zanyi kwana biyu jibi zantafi Abuja gidan kanin Babanka achan zan zauna sabida consultant dina yahadani dawani abokinshi shima baturene dazai dinga dubani a anan Abujan" gyadamata kai yayi, sanan ahankali tace "muna jinka Imamu a ina kasamu diyata"? Dasauri yace "wai Granny itace Fatimar da idan nazo UK kike cemin kinyi kewa har kikasa naje wani gida anan kano dana dawo nadubo mikisu sabida you lost her father's contact akacemin sun tashi" gyadamaikai tayi tace "itace Fatima Zara diya ga Muhammad, a ina kasanta"? Nan yafara koromusu bayani right from ranan da aka kawota hospital dinsu tana rashin lpy yay admitting nasu har zuwa ranako irintayau. Sosai suka girgiza da Al'amarin, Abba yace "natausayama yarinyarnan wlh, Allah ne yaturaka exam dinan a lagos kawai sabida ka cetota amman cousil exam yawanci ma anfiyinshi a Abuja wanan karanne naga anyi a Lagos, am proud of you Son, shikuma Babanta! Hmm akwai Allah kawai" cikin fushi sosai Granny tace "wani irin akwai Allah Abubakar? First thing tomorrow in the morning tunda Allah yasa kasan gidan Imam zaka tukani nida ubanka ka kaimu gidan inaso naga Muhammad ido da ido ya maimaitamin abinda yafadin maka na gasgatar danni nasan yanda yaeson yarinyar nan tun tana yar karama, inyaso Maryam kesaiki zauna da ita anan gida" gyadamusu kai Ammi tayi tace "In sha Allah" nan suka cigaba da hirarrakin duniya daga baya Imam yatashi yahsiga yadubata har lokacin tana bacci sanan yawuce yasauko yamasu Dad saida safe yawuce yakoma flat dinshi.
WASHEGARI!!!
Karfe takwas Granny tashiga dannamai kira awaya, kiran wayan yasa yabude ido da kyar danyagaji yana dawowa daga sallan asubahi yakoma bacci, wayan yajawo yakara a kunnenshi ahankali yace "Granny" cikeda Masifa dan tanada fama sanan bata tolerating nonsense tace "kasandai kai nida father ka muke jirako" ijiye wayan yayi da sauri yasauka kasa sake dauro wani sabon wanka yayi yafito ya shirya cikin wata ash shadda bugagga yadauki hula yakafa aka yasanya takalmi yafito yana rikeda car key dinshi datun asubahi yacema gateman dinsu ya wankemai.
Flat dinsu ya shiga yaga daga Ammi sai Granny su awajen da alamun sun gaka break harsun watse, gaidasu yayi, Ammi tace "kajeka dubata ta tashi amman bata kula kowaba tea kadai tasha" gyadama Ammi kai yayi yazo zai mota ya shafa fuskar kakan tashi yace "Smile now Granny" hararanshi tayi takalli Ammi dake musu murmushi tace "danki yagama rainani wlh" cikeda wasa Ammi tace "ba'a shiga tsakaninku, keda jikokinki mu namu ido" hararan Ammi tayi tace "ai dama bamuce ku sakaba" dariya Ammi tayi tace "mezakici da dara" ahankali tace "fruits nakesha darana, da daddare kuma tuwon accha zakimin da miyan kubewa danya" gyadamata kai Ammi tayi.
Ahankali tabude dakin datake ciki yashiga babu kowa ita kadaine dansun tafi makaranta su Rayyana, idanunta biyu tana kallon hannunta kawai tai lamo kaman mara lafiya, karasawa bakin gadon yayi yazauna ahankali, saikuma yadauki stethoscope dinshi dake gefen gadon ya sanya sanan yadubata, tareda cire drip din yamakala mata wani har lokacin hannunta take kallo ko motsi batayi da ido yay allurai cikin ruwan sanan ya tsaya jim yana kallonta saikuma ahankali ya tsugunna ta yanda fuskanshi zai dinga ganin kwayan idanunta, murya chan kasa yace "Hey Fatima" saikuma yay shiru ganin batabar kallon hannunta datake kalloba hakan yasa yadaura hannunshi ahankali kan inda take kallo ahannunta, ahankali yace "nasan you can hear me perfectly fine dan yanzu fine, and u can see me, I want you to know that all of us here will support you, you have a full family anan yan uwanki yarenki dazasu taimaka miki, kin dawo daya daga cikinmu, Baabarki is here as well am sure kinganta, just take your time process all this emotions ki manta da duk wani abu dayasameki abaya ki daukeshi amatsayin kaddara sanan kigodema Allah and move on kema kifara makaranta kaman su Rayyana and Rahma, you are free now Fatima u can do anything you want, you have your life, so own it kitashi and be free you have three sisters already anan and let go off the past, now dayakamata kina farinciki karki bari emotions yarikeki na past dinki okay" yay maganan yana kallonta har lokacin tana nan yanda take batare datai motsi ba, gently yajanye hannunshi dagakan hannun nata yajuya yafita ahankali tareda rufomata kofa.
Afalo yasami Granny da Abban shi Ammi na kitchen dayar aikinsu yace "mutafi" gaba yayi suka biyoshi abaya suka shiga mota yajasu har zuwa unguwan su Baba, har kofar gidansu sukai parking dukansu su ukun suka iso, daidai lokacin wani yaro yafita daga gidan da sauri Granny ta tareshi tace "kai jekace ana sallama da Malam Muhammad" da sauri yaron yace "Baban su Habib"? Gyadamai kai Dr Imam yayi yaron yajuya da gudu yay cikin gidan, ba'a wani dauki lokaci ba saiga Baba yafito yaci gayu abinshi yay kyau kaman bashiba yana sanye da jallabiya fara mai kyau yar kanti, ganin Granny yasa yabude idanu cikeda mamaki yakaraso wajen yace "Hajiya, marhaban dasu lale" murmushi sosai Granny tamai tace "Malam Muhammad daman rai kan ga rai" dasauri yace "aikona kiraki baya shiga" anatse tace "wani ciwo nayi da aka hanani amfani da waya kwata kwata" "assha Allah sawake" yay maganan yana bama Abba hannu yana kallon Dr Imam irin kallon bana gayamaka karka kara zuwa gidana ba, ganin kallon yasa tace "jikana kenan Imamu, ga mahaifinshi nan" tanuna Babanshi tace "dashi da kanninshi na Abuja saikuma yata dake UK ne Allah kadai yabani aduniya, wanan ma a Abuja suke ai katuna lokacin yanda nake yawan zuwa Abuja basu wani dade da dawowa kano ba, asibiti babanshi yabude anan, idan kuma ina Abuja ina gidan kanninshi ne kasan anhanani zama ni kadai sabida ciwo" gyadamata kai Baba yayi saikuma ya murmusa yace "bismillanku ai bana barku anan tsaye ba" yay cikin gidan suna biyedashi har zuwa falonsu da babu kowa gashinan agyare kaman yasani yanzun nan yagama gyarawa dan ya tsani datti yara kuma duk sun tafi aiki banda Abida dake bacci da mamanta adaki, Granny ne tabishi tashiga falon Abba da Imam suka tsaya kasancewansu maza dole sai anbasu izinin shiga ai zasu shiga, da sauri Baba yadaga labulen yace "ku shigo dan Allah" sallama Abba yayi yashiga tareda Imam suka sami waje suka zazzauna shikuma Baba yashiga ciki da sauri yadan daddaki Mama dake bacci tana sanye da doguwan riga yace "tashi Ruka munyi manyan baki" da sauri tanude idanunta ta kalleshi, murmushi yamata yadauki hijabi yabata yace "Hajiya ce data taba bani achaba nai aiki aikin ganeta lokacin damuna amarya dani dake da Fateema muna zuwa wajenta" daure fuska tamau tayi tace "Baabar Fatima" da sauri yace "eh" kwafa tayi tanunashi da yatsa tace "saura inga anmaka maganab Fatima kafadi abinda bai kamata ba" daure fuska yayi yace "nace kidenamin maganan yarinyae nan" murmushi tayi tareda sauke ijiyan zuciya ranta fess ta karbi hijabi tasaka sanan ta sauka dagakan gadon, suka fito falon Mama tana kwasan pure water a hannu cikeda kunya kaman na gaske Mama tace "wanake gani haka Baabar Faty ido kanga rai dama" murmushi Mama tamata tace "Rukkaya" anatse tace "naam ina wuni ina gajiya" sanan ta gaida su Abba tace ga ruwa kusha duk sukace sun koshi sun gode akai shiru, sanan anatse Granny tace "Malam Muhammadu wata maganace muhummiya takawoni wajenka" anatse ya gyara zama yace "too too ina jinki Hajiya" gyara zama glass din kan idanunta tayi dake karamata karfin gani sanan ta kalli Baba takoromai bayani tundaga farko har karshe wanda Imam yafadi mata sanan tanisa tace "dudda abinda su mutanen lagos suka bama Imamu labari kace bakason yarinyar, da still yanda kafadima Imamu shima dayazo nemanta saisa nima natako takanas takano dannazo naji da kunnena dan yanzu ahak yarka na gidanmu babu lpy, kuma ayanzu babu abinda yarta ke bukata irinku iyayenta after wahalan rayuwa datasha ayan watannin nan na kimanin watanni shidda dabata gida koba hakaba" tunda tafara magana take kallon Baba ganin yanda ranshi kenan abace yay kini kini darai daga fara ambaton sunan Fatima datayi harta gama, kasa magana yayi Granny tace "kayi shiru" cikeda rage murya trying to suppress his anger yace "Hajiya mun dade muna tare kuma kinsan inajin magananki, amman kinga wanan yarinyar dakike magana nifa ba y'ata bace, kawai nagayamiki y'ata ce sabida nina tsinceta da bomb yatashi agarinmu naganta tana walagigi akan titi, amman nidai ba y'ata bace" da sauri Granny tace "mekake cewa hakane? Idan bakaine ubanta ba waye uban nata Malam Muhammadu? Kamannin dakukayi da itafa"? Cikin dan fushi yace "kama ai ta Allah ce, nataimaka mata nabata abinci nabata sutura tun tana yar tatsitsiya aikam zata iya kamadani, ni Wlh Hajiya ko kadan banson inji kina ambaton sunan yarinyar nan jinake raina yana baci matuka, ni Fatima ba y'ata bace aikoshi wanan yaron" yanuna Dr Imam, "dayazo neman aurenta cemai nayi niba ubanta bane yaje chan yanemo ubanta yabashi aurenta babu ruwana alamarin yarinyarnan bansan komi nataba, bankuma son komi nata" yanda yake hargowa kaman ba salihin mutumin datasani kwanakin bayaba dako magana bayayi mai kunya yasa itama ta tsinke dama Allah yahore mata iya fada, tace "dubanni nan da kyau Muhammadu, kabar ganina da karamin jiki ko d'ana nabiyu kanin wanan....." tanuna Abban su Dr Imam, tace "koshi ya girmeka, ahaihuwa nayi kaman ka, biyu dan bakada wani babba anan dazai tsawatar maka toni na isa, ka saurareni nan dakyau, koda wasa karka sake furta abinda kake fadi, yarka ba yar iska bace, bayar shaye shaye bace ballema ace wani mugun hali takedashi yasa ka tsaneta, a'a, salihar yarinya, baiwan Allah ga dumbin ilimi both na addini da islama ne kakema haka kana cewa ba yarka bace, watakeda shi? Bakuda kowa anan garin, kauyenku gabaki dayama ya bombe kowa yamutu sanan kace zaka wulakanta yarinya, kamaida y'a namiji sabida karufama kanka asiri bayan kasan koyin da Ma'aiki rasulu yahana haramun ne abinda kayi, yanzu kuma an samu an ceto yarinya kuma kace bazaka karbeta ba itaba yarka bace, kaza kaza kaza, wlh kaji tsoron Allah, hakkin marainiyan Allah nan bazai barka bacci ba" tashi Baba yayi idanunshi sunyi jazur yace "hajiya tundadai nabaku girmanki baki bani nawaba kitashi kibarmin gida" dasauri kowa na falon ya kallai, Abba zaiyi magana Granny tadagamai hannu tace "karka sake kasa baki anan barni da fitsararren yaron nan" tajuya ta kalli Baba tace "baza'a fitaba ka daukeni ka fitar dani nace Muhammadu inka isa, kadaukeni kafitar dani inka isa kaji" tai maganan tana kumfan baki itama, baba dayaga tafishi iya hauka saiya koma yazauna tace "kuma anjiman nan zanzo dakaina nadawo maka da yarka, ta zauna akarkashinka" wani kallo yama Mama yace "Hajiya barganin kin taimaki rayuwata, ko Allah ma yasan I appreciate duk abinda kikamin saidai wanan ba huruminki bane, kuma wlh wlh wlh kinda kindaiji rantsuwata sau uku ko, na rantse miki da girman Allah duk randa kokuma ince duk randa yarinyar nan zata taka kafa gidan nan saina koreta saikuma namata illa, Fatima ba y'ata bace, bansonta, bankuma kaunar ganinta har abada, yarinyar nan is nothing but a bad luck, ta lalata rayuwana yanzu da bata rayuwa tamin siga ina aiki, dan haka karki tunanin kawota ma dan wlh ko kafa bazata saka adakin nanba, nafada nakara niba ubanta bane, niba ubanta bane, niba ubanta bane, duk yanda zakuyi da ita kuyi ai bance kowa ya riketa ba, itama yarinyar nafadi mata niba ubanta bane, harnabar duniya banson kara ganin Fatima arayuwata, tajechan duniya tayi duk yanda tagadama da ita, ta tagaiyara, ta kaskance ta wulakance niduk ba damuwata bane yarana biyar maza hudu mace daya wacce take abida su kadai garen" yafada rai abace dayasa jikin Granny sanyi, takai hannu tashare hawayen daya zubomata tasake kallonshi tace "to kasha kuruminka indai inada rai, sanan indai yaran nan nawa na nan, kagansu nan da Muhammad, da Iburahima na Abuja dakuma Aishata ta UK inhar suna raye kodani bana raye wahalan Fatima yazo karshe namaka alkawarin nan, xamu maida Fatima mutum, Fatima zata koma zatai makaranta, zata zama wani abu zakazo zaka cije yatsa sanan zakai dana sani, kadaice Fatima ba yarka bace ko"? Dasauri Baba yace "nafadi nasake, zankuma kara yanzu, Fatima Zara'u ba y'ata bace, karkuma tasake amfani da sunana as surname dinta, niba ubanta bane ehe" murmushi irin mai ciwon nan tayi tace "shikenan, Alhamdulillah natako da kafata nazo naji da kunnena, lawyer na zaizo harnan gidanka yanzun nan yabaka paper kai signing cewa kaiba ubanta bane, dagayau nine uban Fatima, custody dinta yadawo wajena, rayuwace zaka gani Malam Muhammadu" tamike tsaye azuciye ta kalli su Abba da jikinsu yay sanyi tace "kumutashi mutafi" tashi duk sukayi, Granny ta kalli Mama datai dariya tace "ke y'a mace ce, kuma kituna d'a nakowa ne, thank God kinhaifa" dasauri Mama tatashi tace "ahhhh nanfa daya tunda kuka fara abunku kinji nasaka muku baki? Nime ruwana dakike neman yima yarana baki ba gaira ba dalili hajiya haduwan kan titi" dasauri Imam da tuntuni Baba kehanashi magana yace "Granny let's go pls" tabe baki Mama tayi tace "yoo kuyi zancen ku chan ni bani aciki, uba yace ba yarshi bace mekikeso nayi? Yarana ma kadai sun isheni balle nakara da wata daba yar mijina ba" Granny zata kara magana Abba yakamata yawuce yafita da ita Imam yamare musu baya, suka bude bayan mota suka sakata Granny tafashe da kuka sosai, Abba yahsiga baya yana lallashinta, Dr Imam kuma yakoma gaba yaja motar.
Cikin kuka Granny tace "what a cruel world we live? How can a father abandon his 19yr old daughter haka da yanzu tana tender age idan ba'a kulada tarbiyanta ba anything can happen eh? Wanan wani irin abune, giyan wake yasha ne komene, wlh xan nunamai waye ne, har abada bayi kara ganin yarinyar nan, Muhammadu kiramin lawyer mu kabashi sako yaje gidan" babu musu Abba yakira lawyer danshima ranshi abace yake yabashi sakon saida yagama tass sanan tashare hawayenta tace "Muhammadu da yarinyar nan zan koma Abuja tai zamanta dani awajen nasaman mata University tafarayi" faduwa sosai gaban Imam yayi, Granny tacigaba tace "banmaso ta cigaba da zama agarin nan ballema taji tanason zuwa ganin ubanta, zaisha mamaki wlh" gyadamata kai Abba yayi yace "hakan nada kyau, zan kira Ibrahim muyi maganan" babu wanda yakara cewa komi a motan buni buni tana share hawayen datakasa denayi tsabagen tausayin Fatima har sukakai gida.
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a nUmber ta 07012181461_
M Shakur ❤️
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 5️⃣5️⃣ & 5️⃣6️⃣
Parking yayi Abba shiya fara futowa yabudema Granny dake kuka har lokacin kofa yace "Hajiya dan Allah kiyakuri kidena kuka kinga bawani lafiya ce ta isheki ba" yay maganan yana fitoda ita daga mota sukai cikin gida, Ammi dake kokarin saita dinning ne ta tsaya chak ganin an shigo da Granny tana kuka dasauri ta taho takalli Abba tace "Hubby maiya sami Mama kuma take kuka"? Kafin Abba yabada amsa cikin kuka sosai Granny tace "barni kawai yau naga abinda tsawon rayuwata ban taba ganiba, tayaya zaka wulakanta yar karaman yarka? Meta maka? Wani laifi tamaka? Tanada wani mummunan haline? Ka wulakanta yarinya kamaida yarinya namiji, ta wahala, jibi yanda sauro dawata tsiyace duksun cinyeta amman mutumin nan ko'ajikinshi wai bayarshi bace idan mukama kawota saiya nakasata sanan yakorata, duniya ina zaki damu? Talauci nataba ma mutum kwakwalwane wai? Wlh wanan abun yay min ciwo sosai kinji Maman su Imamu, yarinyarnan tabani tausayi matuka" takara fashewa da kuka, bude kofa Imam yayi yashigo kaman ance yadaga kanshi ya shigo Fatima yagani aduke ta tsugunna akan stairs dinsu tadaura kanta akan cinyarta ga cup din tea agefe yasa yamaida kofar yarufe yay stairs da sauri hakan yasa duk suka kalli stairs din, ganinta yasa Granny tasake rushewa da kuka tayi stairs din itama daidai yakai gabanta tsugunnawa yayi ahankali agabanta yakira sunanta. "Fatima" dasauri Ammi data biyo bayan Granny tace "naga ruwan daka samata yakare nacire nasagale, nace metake sha'awaan ci tacemn tea, shine nabata nace bari nazo kitchen ina girki ne, halan tagaji da kwanciya ne tafito" ahankali Granny takai hannunta tadago kanta dagakan kafarta tace "Fatima" dagota sukayi sukaga fuskarta ko kadan babu hawaye ammam the kind emotions dakuma yanayi dake cikinshi zai iya saka kafashe da kuka, gyara zama Granny tayi tazauna kan stairs din sanan takai hannayenta biyu ta tallabo fuskar Fatima tace "Faty Zara na, nasan duk abinda muke cewa kinji amman inaso kisani mudin nan saimunfi miki iyayenki, tun kina karama naroki mahaifinki yabani ke yaki da dake zan tafi UK abina, ki dauki wanan rayuwan da wahalan dakikasha abaya as kaddara, ki manta dakomi