Showing 144001 words to 147000 words out of 150358 words

Chapter 49 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt

M Shakur   

07 Jan 2025

15391

dauki wayan tafito daga dakinta fuuuu babuko dan kwali da sauri Granny ta tashi tace "ke Zara ina zaki ahaka" dan Zara bata taba fita waje babu dan kwali ba, flat din su Dady da Mum tashiga, Amna data ga Zara tatasp da gudu zata rungumeta wani irin tureta Zara tayi Amna tafadi akasa.
Tai cikin dakin zuwa dinning inda daga Mum har Dad ke kallonta ganin yanda ta ture Zara ga granny biyeda ita, gaban Dady ta tsaya direct tamika mai wayanta dake ringing cikeda rashin kunya tace "ai kaine ka auramin wanan mutumin dake kirana ko, toga waya nan kadauki kiran nan kacemai karya sake yasake kirana, sanan kace ya aiko maka da sakina, bana sonshi bana kaunarshi kuma wlh yabari nasashi a idona saina chaka mai wuka yamutu, kanajina ko" duka dakin kallonta suke, shi Dady ma zai iya cewa baitaba ganin kwayar idanun yarinyar ba saiyau, dan koda yaushe kanta akasa cikeda girmamawa take gaidashi.




Da sauri Granny tazo wajen fizgota tayi tace "ke Zara whats wrong with you? Kinsan mekike fadi kuwa" wani kallo tama Granny tace "kin dauka na haukacene? Cewa nayi na tsani mutumin nan, kuma ku kirashi kuraba auren nan dakune kuka hada inba hakaba zanbaku mamaki wlh, saina hanaku xaman lafiya agidan nan, nabaku awa biyu kacal kuraba auren mu kokuma wlh wlh saikun kama baki nafara muku abinda zan muku, ga wayan nan" tawani irin ijiye wayan awurin tawuce tafita daga dakin fuuuu hartana bangaje Granny, kallon Granny Dady yayi yace "is this how this girl is ko something happen to her ne"? Da sauri Granny tace "wani irin is this how this girl is? Zara da ko hannu kasamata abaki bazata cijaba, kodai sun sami matsala da Tajudeen dinne" daidai Tobi nasake kiran wayan dauka Granny tayi kafinma Tobi yay magana tace "Tajudeen kuna fada da Zara ne" "Grannnnyyyy" yafadi sounding so excited to hear from Granny, but jin tambayan datamai yasa gabanshi yafadi dasauri yace "no Granny, we are good, where is my wife Granny" anatse Granny tace "i will call you back" takatse wayan takalli su Mum, Mum tace "fadasukeyi ne"? Girgizamata kai Granny tayi tace "ba fadan dasukeyi kinmaji dadin dayaji dayaji muryana" Mum ce tace "aiko fadama sukeyi it will not make her act this way ai" anatse Dad yace "Yaya da Family na hanyan sunma kusa kawowa Abuja, you guys should talk to her, bari nafita zamu shigo tareda su Yaya" yana maganan yawuce yafice ranshi namai badadi.




Granny ta kalli Mum tace "kodai Aljanu sun shigeta a school ne" dan dariya Mum tayi tace "haba Granny, wani aljanu kuma, yarinyar mai azkar da karatun Qur'ani, wani abune dai, I will talk to her bari nasa yan aiki su daura abinci awuta, amman ai banma taba ganin fushin Zara ba, ballema masifarta" gyadamata kai Granny tayi takasa tsaye takasa zaune har ranta tanaji something is going on, fitowa Mum tayi ganin Granny, na wajen har lokacin tsaye yasa tace "Granny kina tsaye har yanzu, karki damu muje kiga" binta kawai Granny tayi tawuce suka fitadaga side din sukabar Amna ita kadai zaune afalon tana kallon cartoon.


Bude kofa sukayi suka shiga flat din Granny, Zara suka gani zaune kan kujera sai uban zufa tayike ranta amugun bace fuskanta Yaya sosai duk uban AC dakin, ba Granny kadaiba har Mum saida gabansu yafadi, da sauri Granny takarasa kusada ita tace "Zara wai kodai zazzabin ne tun ciwon kan dakikayi jiya wanan zufa dakike yi na lafiya ne iyye jibeki"? Cikin fushi tace "zufan danakeyi ba matsalanki bace" zaro ido Granny tayi tana kallonta, cikeda masifa da ihu tace "kungayamai bani aurenshi kun raba auren dakuka hada"? Wanan karan kasa magana Granny tayi sai salati data fara, Mum ce tace "Zara are you okay kuwa? Tayaya za'a raba aurenki da Tobi dakike s......" wani ihu tayi tace "karki kara hadani da mutumin nan, karki kara kiramin sunanshi akunne na nagaya miki, karki kara, na tsaneshi na tsaneshi nace na tsaneshi" tai maganan tana tashi daga kan kujeran tana ihu sosai tai wajen TV dake kan stand batai wata wataba taja TV sai kasa tana ihu ta tsaneshi, da sauri Mum tadaga Granny tana salati suna kallon yanda Zara ke hauka, dinning tayi tana ihu ta tsaneshi duka kuloli da plate dake kan wajen ta shiga watsosu kasa suna tsalle suna breaking jikake rukuku karan fashewan glass hakan yasa da sauri Mum tabude kofa taja Granny suka fice daidai ana bude gate din gidansu manya manyan motoci suka shigo irin Family car, Dr Imam ke tukin sai babanshi adayan bangaren gaban, Mamanshi da kannenshi na baya, saikuma motar Dady.






Fashewa da kuka sosai Granny tayi dayasa duk sukai parking motoci suka fitoda sauri sukai inda suke, Imam kuma yafito karshe yana sanye da shadda, Abba ne yafara cewa "Lafiya Mama" cikeda tashin hankali ta kalli Imam dake karasowa tace "Imam dubamin Zara, wlh jiya da yamma tai complain ciwon kai sosai, nabata paracetamol guda biyu tasha taje ta kwanta gab da magrib tai bacci, shinefa tun safe naga Zara ta tashi ba itaba, sai rashin kunya take tana sai mun raba aurenta da mutumin nan, shine yanzu kuma tanata fashe fashe adakina kaman ta haukace, Muhammadu bikifa saura kwana takwas nan da kwana hudu yan uwan mijinta zasu diro Abuja mun shiga uku" da sauri Abba yasaketa, sanan ya kalli Imam da kaninshi yace "let's go" bude kofan flat din Granny sukayi suka shiga, gabaki dayan kasan dakin glass ne, tagama da dinning tass akitchen suka jita tana fashe fashe tana watsarda abu, duk basu cire takalmi ba sukai kitchen din, Imam yafara shiga kitchen din ta haukata kitchen din tana ihu, zufanma datakeyi shine zaimafi baka tsoro sabida yanda internally take burning da hatred da kunci, kanta babu dan kwali akanta gashin kanta ya barbaje na hauka, tayi wani irin mugun haske tai kyau sosai kirjinta sun kara cika sosai, duk tsayawa sukayi awajen kofa suna kallonta, juyowa tayi ta kallesu tana kokarin daukan pots ta kalli Baban Imam tace "kaine ai katambayeni ko inasonshi ka daura auren ko wlh kuje kuraba shi na tsaneshi nace, na tsaneshi, kuraba auren nan wkh kona wulakanta ku" tawani watso musu pots din da sauri su Abba suka fice Imam yajuya baya pots din suka sameshi, sanan yajuyo yataho kanta, ihu tacigaba dayi tana jefamai duk abinda tasamu harya karaso gabanta ihu take ta tsaneshi, daukanta chak yayi tana ihu tana kokarin kwatan kanta, yakalli Babanshi yace "Dad check my medical bag a car, and get alluran bacci" sanan yawuce dakinta da ita, shikuma Babanshi yayi waje da sauri zuwa car.




Shigar da ita dakin yayi tana dambe dashi sosai yana mamakinta, hannayenta yakama yabude tafukan hannunta dasukai zufa sosai ya kalla, sanan yakama fuskanta tana dukanshi sosai, yabude su yakalla daidai anbude kofan, yana rikeda ita yafadama babanshi iya yawan dazai zuko sanan yakarba yace "surikemai ita" riketa sukayi yaje tabayanta yadan dage riganta batareda yabari sun ganiba yamata alluran. Ko minti daya baiyi dayiba sai bacci, sakinta duk sukayi suka tashi akanta, Abba yace "subhanallahi meke damunta haka Imam"? Ahankali yana kallonta yace "I don't know Abba" Dad yace "Mum tace kodai aljanu ne" girgiza kai Imam yayi yana kallonta yace "ba aljanu bane wlh, look at her ita kanta wahala take, bakuga yanda take zufa ba am coming" fita yayi saigashi yashigo da wani dan roba da syringe, jininta yadeba sanan yatashi yace "bari naje lab and run some test a jininta, Dad ku zauna agidan please karku fita, men need to be around karta jima kanta kowasu ciwo, I will be back once nasan meke damunta" "Allah maka Albarka" Abba yafadi ahankali, shikuma yawuce yafita, su Granny na tambayanshi bai amsasuba yawuce abinshi.




Hospital wani abokinshi yaje, dakanshi ya shiga testing jininta, gwajin farko yaga tanada cikin sati hudu dayan kwanaki, jimmm yayi saikuma ahankali yacigaba da abubuwan dayakeyi, yayi test sama da 15 duka negative tundaga kan maleria, typhoid, HIV, hepatitis duka negative, hakan yasa wajajen 5 yafito, ya tsaya a pharmacy yasaimata magungunan dayakamata mai ciki tasha, yana mamaki to cikine yasa take fushi haka take hauka dan babu abinda ciki baya sawa, saida ya tsaya yay salla sanan yawuce yatafi, daidai wata mad ride na shiga gidansu, shikuma yana shigowa anguwan yakarasa gate yashiga shima, lokacin daidai bodyguard din Tobi yafito yabudemai kofa, dan tunda yaji muryan Granny da tambayan datamai hankalinshi yaki kwanciya kawai yabi jirgi yazo, yana sanye dawani soft yard paper lace mai bala'in kyau milk yasha guga ga karin guga akayan, kanshi na sanye na hulan yarbawa dayama kwana yay wani kyau, idanunshi sanye da bakaken glasses, kafanshi sanye da palm na Hermes, yay kyau looking damn fresh kana ganinshi kaga ajebota yaro dan gata, black skin nashi nakara₩ shinning kaman daga spa yake.










_NAFJAN COLLECTION_
_Nafjan Collection business ne na shahararriyan CEO dinan wato Nafisa, wacce ta kware akan sana'oi kala kala._
_Tana saida kowani kalan kaya dakuka sani, Riga, wando, lace, shadda, atampa, takalma, na maza, na mata, na yara, na manya, sneakers, cambas, sandals, flat shoe duka, handbags, bagpack, akwatuna, dogayen riguna, agoguna, tana shigo da hadaddun kayan daki daga kasan waje, kayanta arahansu zaisa kama rufe baki, dan tuntubarta ko magana da ita directly zaku iya saminta awanan number wayan 08160472711, kowani kalan abu kuke nema kawai ku danna mata kira dan tambayanta kuji kotana dashi kobatada shi_


_Dankuma magana da ita directly a watsapp zaku iya samunta ta hanyar danna wanan link din.👇_


https://wa.me/+2348160472711


_danyin Yosarin kaya awajenta da sallan nan, just chat her up_ https://wa.me/+2348160472711




































8️⃣0️⃣


Parking shima Imam yayi yafito rikeda ledan magungunan, da papers na test results dinta, ganin Mota dama yasa Tobi ya tsaya dan yadauka Dad ne yagaisa saisu shiga ciki tare dan babu wanda yasan da zuwanshi ganin Dr Imam yasa ahankali yacire glasses din idanunshi yana kokarin tuno inda yataba ganin this face hakan yasa yakasa motsi, karasowa Imam yayi ahankali yamikamai hannu yace "OluwaTobi" hannu Tobi yamikamai bakinshi na motsi trying to mention Imam name daya shigemai hakan yasa Imam yaydan murmushi yace "Dr Imam, you helped me with my bag back then at Lagos" "OMG!" Tobi yafadi surprisingly, saikuma with a very clean heart kawai ya rungumeshi yanda yaran yan gayu keyi yace "Hi Dr Imam, longest time, how have u been" karan buga abu dasukaji yasa dukansu suka juyo, Zarane take kokarin fasa window tafito sabida hango Tobi datayi, dasauri Tobi yakalleta saima yamanta da Imam yay wajen da sauri yace "Jewel"! Daidainan su Dad suka kamota tana ihu sosai hakan yasa yay hanyar shiga flat din Granny, Imam biyedashi, suna budewa su Rahma yagani da masu gadin gidan na tattare glasses da TV daya fashe yayi akasa, hakan yasa ya tsaya turus, Imam yawuce shi yay corridor, inda Granny ke tsaye tana kuka sosai, Mum na Ammi na lallashinta, dan haukan da Zara keyi yawuce tunani, Imam yawucesu yabude dakin datake ciki yashiga, ahankali yakarasa batare daya shiga corridor ba ya tsaya turus yana kallon Granny dake kuka sosai da kowana wajen, bude kofan da Imam yayi yasa yay ido hudu da Zara dake kallonshi da kwayan idanunta dayaga sun chanza mai tana ihu tana I will kill you Tobi! Yakasa motsi yakasa magana, yama kasa tunanin komi, ganin haka yasa Mum tabar Granny da Ammi tazo wajen Tobi tace "saukan yaushe inlaw" kasa bata amsa yayi, ahankali yace "whats wrong with My wife Mum"? Kafinma Mum tai magana sukaji anbude kofan Zara ne tafito da gudu tai kitchen Allah yasa anshare glasses din wajen da wlh taji ciwo akafa, wuka ta dauko tadawo tafito, tayo kan Tobi dayajuyo yazuba mata idanu, dasauri Mum dakowa sukai ihu zasu tareta Tobi yadaga musu hannu alamun sun barta, har gabanshi tazo tadaga wukan daidai tadaura a chest dinshi Imam yawani irin fizge, juyawa tayi ta kalli Imam saikuma tajuyo ta kalli Tobi ahauce, tace "I hate you Tobi! I hate anything that has to do with you, I am not going to marry you, I swear by Allah I will not leave or stay with you, bazan aureka ba, kuma wlh idan basu raba auren mu ba saina illata kowa nagidan nan, I hate you with passion OluwaTobi" cikin wata irin kalan murya datai rauni sosai yana kallon kwayan idanunta sa hatred din yake gani aciki yace "Jewel stop saying this words to me, it hurts, I love yo..........." bai karasa maganan ba tadaga hannu ta tsinkamai wani irin mahaukacin mari, jikake pau!!!!! Yakauda kanshi gefe, dakin akai tsit kowa mamaki ya cinyeshi, zabura Granny tayi tatashi tazo zatai magana yarike mata hannu yace "please Granny! This is an issue between me and my wife, don't interfere" sanan yajuyo ahankali ya kalli Zara dake zufa tako'ina tana kallonshi tana huci kaman macijiya, cikin muryan so da asalin tausasawa da sanyin murya dakuma lallabawa kaman bashita mara ba yace "have I wrong you Jewel? Why are you so angry Baby? What's the matter am here, your Tobi is here talk to me okay, Zaraaaa!!" Yakirata ahankali ataushashe kana ganin yanda yake mata zakasan bakaramin son yarinyar nan nakeba, ido acikin ido tace "I hate you, I don't want the marriage again, I want you out of my life, Divorce me, leave me alone or I will kill you wlh, I hate you Tobi, anytime I see you I will like ending you life, I hate you with passion" tai maganan hannunta narawa kaman ta shakeshi, jiyayi abuya tokaremishi wuya, ahankali yace "you hate me, your husband?" Wani tsawa tadakamai tace "don't ever call yourself my husband again, I hate you! Nace na tsaneka da duka raina, I hate you OluwaTobi, and i will never marry you" haba sharrrrr hawayen dayake rikewa yazubo, zaiyi magana da sauri Imam ya girgizamai kai saikuma yakama kafadarshi yay wajen dakin dashi yana share hawaye jikin kowa yay sanyi, side dinshi Imam yayi dashi yabude falo yashiga, sanan yazaunar da Tobi akan kujera dake share fuska da hannu dan hawaye sai zubomai suke shar shar shar, ahankali Imam yasa hannu yaciro handky yabashi, dagokai Tobi yayi yakarba murya chan kasa yace "thank you" sanan yashiga share fuskanshi Imam kuma yazauna, saida yaga yadan natsu yarage hawayen sanan yace "did you guys had any issue or quarrel ne"? Girgizamai kai yayi yabude baki zaiyi magana saiga wani hawayen, hakan yasa Imam yadaukekai da sauri, cikin muryanshi dake rawa sosai yace "we don't have any issue, the last time I spoke to her was yesterday datamin complain kanta naciwo ninama gayamata tace ta kwanta tai bacci tunda Granny tabata magana, I love Zara sosai, I can't even begin to imagine my life without her" yacigaba da share hawayen, danjim Tobi yayi sanan yaciro result din cikinta ahankali yace "I think you should know this before anyone else" dago jajayen idanunshi yayi ya kalli Imam da takardan dayake bashi, saikuma ahankali yasa hannu yakarba ganin sunan Zara akai, murmushi Imam yayi yace "Zara is 4 weeks pregnant" wani irin zaro ido yayi yakara kallon paper yatabbatae da hakane baisan lokacin dayayarda handky yafashe dawani irin kukan murna da dariya ba, sakawai yatashi yazo kujeran da Imam yake ya rungumeshi tsam tsam, yace "am going to be a father Omg, is that what you just say Dr? Zara is pregnant with My child" saikuka da dariya, abinma yabama Imam mamaki, from what he see koshi baijin yanama Zara son da wanan yaron yarbawan kema yarinyar nanba.






Tashi yayi yace "lemme go and give her drugs with injection she need rest" yana murmushi yabishi da kallo yafita. Har dare suna gidan Zara hauka take sosai, kowa rashin kunya tamai, sai wajajen 9 yamata alluran bacci tayi sanan Imam ya shigo da Tobi, Abba ya tambayeshi akwai wani abune yace babu, anyi bincike babu abinda yahadasu, Ammi tanisa tace "nifa nagoyi bayan abinda Granny tace, Allah aljanu sun shafeta a makaranta ne gaskiya asan abinda za'ayi" jim Abba yayi yace "shikenan gobe zanje gidan zuma na dauko malam yazo yamata rukiya" ahaka akai na'am da xancen, akai akai da Tobi yatafi yace anan zai kwana, babu yanda zasuyi haka suka barshi sunga surukin zamani, abangaren Imam ya kwana, tun Imam na avoiding nashi harya sakemai sosai dan yasan baisan komi kan son dayama Zara ba.




Washe gari tana tashi ta dasa daga inda ta tsaya, karfe goma Dad da Abba suka shigoda Malami, har dakin datake kulle suka shiga yakamata yafara mata addu'a, saikuma yasaketa yafito suka maida kofan suka rufe, duk suka tsaya kallonshi afalo, Abba yace "bakai rukiyan ba ai" murmushi yayi yace "yarku batada aljanu asiri aka mata, nafito ne sabida dole ku komardani naje na kwaso kayan karyan asiri da sihiri" da sauri dukansu sukace asiri, Tobi yataba Imam alamu yamai bayani me malam kecewa Imam yafadimai, Granny tace "wazaima Zara asiri wani makiyi gareta" Malam yace "Allah masani" daukanshi sukayi suka tafidashi, almost 1hr yabata sai gashi sun dawo, wani ruwa a gora na zamzam yafara budewa first of all yasa aka bude bakinta yabata sanan ya danne hancinta dole tasha, yabama Mum wani magana yace "adafa ahada a bucket amata wanka dashi" kafin nan kuma yacigana da addu'a, saida ruwan yahadu sanan mazan suka fita suka kaita bayi tana fada saida suka mata, sanan aka shiryata su Malam suka dawo yana bata ruwan addu'a tana sha, kafin chan tafara amai sosai akasa, Tobi yaje wajenta ya tsugunna tareda riketa sabida yanda take aman yana sorry Baby, sorry Jewel sorry Zara, tun suna kunya sunma dena dan bemasan sunayiba, tass tai aman saiga wanan blue butterfly dinan matacce acikin aman, Malam baiji kyamaba yasa hannu yaciro butter fly din yanuna musu yace "ga asirin nan, dashi akamata sihiri, ni bana duba balle nagaya muku waye, amman Allah yasa kunkira malamai dawuri, shikenan yanzu ta warke, saidai ruwan addu'o'in nan zata dingasha, banda haka tadage da addu'a, azkar, koma waye Allah zai sakamata" godiya sukama Malam aka biyashi, shikuma Tobi yadauketa yasata ajikinshi, yazauna akan gado yana shafa kanta. "Am here Zara, nobody will harm you again okay, I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login