Showing 75001 words to 78000 words out of 150358 words
Chapter 26 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
dakin yayi ahankali ya shiga yaga an saka mata drip, tana kwance tai bacci, gashin kanta sun barbaje tsabagen kukan datasha, tana zufa a goshi sosai dudda uban sanyin dakin daga gani bacci bai dade da kwasheta ba, ba'a lullubeta da bargoba fararen smooth legs dinta akan gado ancire mata kiton yana kasa, ahankali ya ijiye abincin kan side drawer sanan yaja kujeran zuwa gaban gadon ya zauna yay folding dinshi dinshi yana kallonta, daidai lokacin tawani sauke ijiyan zuciyan kuka cikin bacci tareda chanza direction na kwanciyanta tai facing nashi riganta yadage sama hakan ya bayyana fararen cinyoyinta dauke idanunshi yayi da sauri saikuma yatashi ahankali yaja bargon saman gadon yarufa mata akafan, ganin hannun da aka mata fixing karun ruwan ta lankwasashi sanan tadan jwanta akai, yasa ahankali yakai hannunshi yaciro hannun nata yaijiye mata ahankali sanan zai daga hannunshi yakoma yazauna yaji ta kama hannun nashi tarike gamgam, da sauri ya kalli fuskanta ganin bacci take sosai yas yasake hannun yaju tarikeshi ga hannunta tai zufa aciki kaman tarikeshi da hannu dake dauke da ruwa, ahankali yadan sake dukawa zai fizge hannunshi da dabara saiyaga cikin bacci zata fasheda kuka da sauri yakai hannunshi saman kanta yashafa murya chan kasa yace "shiiiiiiiiii sleep Jewel, don't cry just sleep, shiiiiii" ahankali yake shafa gashinta dayaji yamai dadin shafawa sabida taushe yana mata shiiiii haryaga tasaki fuskanta cikin baccin tasake sakin ijiyan zuciyan kuka sanan gently yacire hannunshi daga nata, ya kalli hannun yanda yaga ta shafamai zufa, zama yayi kan kujera yay shiru yana tunani Otun zai nemeta sabida bata kawomai report ba, but mesa Otun xai sata irin aikin nan, tabe baki yayi yace Dad of course dan yasan babanshi da Otun bakinsu daya, bama wanan ba, the question is what will he do with her?? Koda ba'a tambayeshi ba within this days za'a zo afara nemanshi yanzu yaya zaiyi da ita?.
Sai wajajen Magrib drip dinyau yakare yasami Dr a office yace "yaushe zaki sallamemu" anatse tace "yau dana sallameku gabaki daya, but the thing is dole namata massage gobe na tabbatar komi ya narke saita cigaba dashan magani kawai nan da kwana biyu ko uku zata dena jin zafin, gobe kawai idan ka kawota namata massage din naji babu komi kuma basaina saka mata drip dinba shikenan u can go" gyadamata kai yayi sanan yamata godiya yawucr wajw yasameta dan already nurses sun sata a mota ya shiga ya tada motar suka tafi.
Bude motan yayi yafito yabude mata baya batare daya kalleta ba yace "come out" ahankali ta lallaba ta saka kafarta akasa yana tsaye wajen kofan sanan ta sanyo dayar kafan, kafin ahankali ta sauko dan gajeren ihu tayi ta taho zata fadi da sauri yatareta tafadi akirjinshi baice mata komiba ahankali takoma baya kadan sanan yamaida kofan yarufe yay gaba tana biyedashi abaya ahankali suka shiga falon, ganin bata iya tafiya kawai yajuyo daukanta yayi tasake runtse ido yay sama har dakin jiya ya shigar da ita ya zaunar da ita akan gado sanan yaja kujera ya zauna yana kallonta, kasa daga kanta tayi, ahankali yace "do you know your Dad's number"? Gyadamai kai tayi, wayanshi yazaro daga aljihun wandonshi yashiga keypad yabata yace "samin number" hannunta har rawa yake ta karba dudda batasan mezaiyi ba but tasakamai dan shakkanshi takeji, yana kallonta saida tagama yasa hannu ya karbi wayan yay dailing ya kara a kunne.
******
Baya yadawo daga Magriba kenan sunbar yara afalo dagashi sai Mama a uwardaka ke hira yana xubamata labari tana dariya they were looking so happy, daga falo Habib yadauko eayarshi daya makala a chaji ya shigo dakin yace "Baba ana kiranka" karba yayi yace "too waye gashi banda number" Habib shidai yawuce yafita, Mama tace "dauka kasan nakaima shugaban nambanka nace a nemamaka aiki, halan sune dauka muji" karawa yayi akunne yay sallama. "Assalamu Alaykum" jin an dauka muryan dan magidanci yay magana yasa Tobi yamika mata wayan ahankali yace "speak to your Baba" da sauri ta kalleshi, gyadamata kai yayi ahankali for the first time tunda abinan yafaru yaga tasakin mai wani kayataccen murmushi daya nuna asalin farin cikinta da sauri ya dauke kai hakan yasa takara wayan a kunnenta daidai Baba na kara sallama tace "Hello Baba" da duka muryanta kaman ba ita ke kuka ba, ahankali yajuyo da kanshi ya daura akanta, cikeda murna tace "Baba nine, Fatima Zara'un kace Baba" shiru yayi dayasa Mama ta kallai da sauri, awani irin hankali yace "Zara'u" dasauri tace "Baba" saikuma ta rushe da kuka tace "Baba nai kewanka, ya kake, yasu Habib, da Sadiq, ina Abida Baba kana ganin Maryam kawata? Baba ya Maman su Dady"? Duk tajeromai tambayoyin cikin kuka sosai, Mama dataji ya ambato Fatima Zara'u saida gabanta yafadi da sauri ta karbe wayan tasa a speaker.
Ahankali Tobi ya mika mata hannu hakan yasa ta kalleshi saikuma ta kalli wayan tace "Hello Baba kanaji za'ai magana dakai" cikin muryan Baba dayadan dishe yace "okay to, waye"? Karban wayan Tobi yayi yakara a kunne anatse yace "goodday to you Sir, hope u and the family are doing great" anatse Baba yace "Fine" dan ajiyan xuciya Tobi yasauke yace "I will just head to the point, that's the reason why I asked your daughter t give me your number to call you" yasake yin shiru, Mama ta gyadamai kai alamun yace "okay" hakan yasa Baba yace "okay am listening" anatse Tobi yace "Sir I want you to send your account number to me now, I want to make transfer of the 3million naira you took for loan, then u called the organization pay them back by tomorrow morning so that your daughter can be sent home before anyone will notice she is a girl, if she's been cut she might get herself killed or she will face severe punishment including you" wani irin faduwa gaban Mama keyi dan zamata iya cewa tafi Baba jin turenci ita datai aikin abinci a tasha babu abinda batajiba, yanda tasamu Baba a hannunta yanzu har abada Fatima bazata dawo mata gidan nanba, da sauri Mama Baba alamu dayace mai yanazuwa, da sauri Baba yace "I will call u back give me a moment" yana fadin haka Mama ta fizge wayan ta katse sanan ta kalleshi rai abace, tace "kanajina" da sauri yagyada mata kai sanan tace "ka saurareni da kyau duka abinda nafada maka shikaza fadama koma uban waye wanan mutumin daya kiraka.........."
Tunda yafara wayan ta tsaya chak kaman numfashinta ya dauke tana kallon shi, tunda tafara aikin tasan Prince dabanne cikinsu, amman bata taba sanin yanada kirki hakaba, so zai iya rufamata asiri dahar zaibama Baba 3M yabiya bashin sabida takoma gida tacigaba rayuwa cikin yan uwanta, jin kaman ana kallonshi yasa yadago kanshi ahankali hada ido sukayi wani irin fashewa da kuka tayi kawai tafada kan kirjinshi ta kankameshi tana kuka dazaka iya gane na dadine gwanin ban tausayi cikin kuka sosai tace "thank you so much Sir, May Allah bless you" kasa cemata komi yayi saida wayanshi tai ringing yasa tadago tana kuka har lokacin takoma ta zauna da sauri, katsewa kiran yayi alamun flashing hakan yasa yay dailing number back itakuma tana share hawaye tana murmushi sosai tana kallonshi, ganin yanda take murmushi to even make her more happier yasa yasaka wayan a speaker dan daji maybe nan da jibi tabar gidansu takoma wajen Baba ta abinta.
Ringing daya Baba ya dauka yasake sallama, Tobi ya amsa sanan baba yay gyaran murya cikin English dinshi da babu sosai yace "Oga u dey hear me so" cikeda girmamawa irin na yaran yarbawa Tobi yace "yes sir" Baba yace "manage my english is not good, but don't pay anything for that girl, let her rot in that house is non of my business, she is not my child, she is just someone I saved because her mum died a bomb blast din Maiduguri, even if u send me the money I will go bank nace su maido maka ur money and where is the Zara give her the phone" ahankali ya kalli Fatima datai mutuwan zaune yamika mata wayan takara kunne tace "Baba" da sauri yace "kutumar ubanki da Baban, ubanwa yacemiki ni ubanki ne? You are not my daughter am not your father, u are just wacce na tsinta a kauyenmu bayan boko haram sun kashe wuyarki da bomb, you are nothing but a bad luck, ki bayan shekara biyun kin gama aikinki karki sake ki dawo gidana dan ban sankiba, baki bani bani bake, kije kinemi wani uban, ashe kece annobar dake gidana tunda kika fita gashinan arziki ya budun mana ina gab da samin aiki mai tsoka ma, karki sake ki sake kirana da Baba, karkuma ki kara kiran number na, insunga dama su kasheki idan sun gano ke mace ce wlh ko ajikina zan fada musu nima a namiji na sanki kuma dama ke ba abinda na haifa bane kawai yarone dana taimaka, karki sake kirana mai farar kafa kawai annoba, jechan dajin Maiduguri ki nemo ubanki baniba" yana maganan ya katse wayan, dudda bayajin hausa amman zai iya cewa kusan kowani kalma ya fassara ma kanshi ita yakuma san tsaf abinda Baba yace, ahankali yaga ta kakalo murmushi tamikamai wayan nan nashi sanan tasake murmushi ta tashi ahankali tabi ta gefenshi ahankali tace "I want to drink water" sanan tabude kofa tai bene tanabin benen da sauri bata damuda ciwon datakeji ba dan maganganun Baba ayanzu yafi komi ciwo da azaba agareta, idanunta har rufewa suke da duhu mutuwa kawai takeso tayi ayanzu, bude kofan kitchen din falon tayi ta shiga ta shiga neme neme tana kabar dakome tagani kasa tana neman wuka, tashiga bude drawers din kitchen din, nan tai idanu biyu da wuka, mika hannu tayi tadauki wukar daidai Tobi yawani irin bugo kofa ya shigo kitchen din daidai itama tadaga wukan sama zata chakama kanta ta rufe idanunta, wani irin jump Tobi yadaka yawani tadiye kafarta dan yace zaije dagudu kafin yakai wukan ya isa cikinta, hakan dayayi yasa tai kasa wukan yafadi daga hannunta, dawani irin sauri ta tashi zata sake daukan wukan yay Ball da wukan da kafarshi tareda kamota dakarfi tashiga fada dashi tace "leave me alone i want to die, leave me alone, My Father said he is not my father, he said ama kasheni is not his business lemme die first before then" duk yanda take kokawa dashi saida yasata a kirjinshi ya rungumeta tareda matseta sosai yana bubbuga bayanta yace "cry cry, just cry let it out" wani irin rushewa da kuka tayi ta kankameshi kaman zata karyashi, bata tabajin bakin ciki da kunci irin nayauba, duk kukan datake kwanakin baya na azabane da tashin hankali da tsoro, but wanan kukan nayau kukan bakin ciki, kunci, tausayi da sorrow ne, cikin kuka tace "I don't have anybody, I don't have anyone, what's the point of leaving? I want to die" tafashe d_a kuka tana neman kwace kanta amman ina yahanata karfin namiji dana mace ba dayaba, shima idanunshi sunyi jajir bana wasaba.
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍🏾M SHAKUR
EPISODE 3️⃣9️⃣
Yasake sata ajikinshi yana bubbuga bayanta ahankali cikeda tausayin yace "cry as much as you can, i got you okay, you will not die and nothing will happen to you okay Za...raaaa" yakira sunata ahankali kaman bayason yakira tana wani irin kuku dake tsumamai zuciya, he could feel yanda hawayenta suka jikamai riga sosai, ta bala'in bashi tausayi bana wasaba, takasa daina kukan, har wani ihu take irin kukan nan nakaman anmata mutuwa, takusan bata 30min kuka take ajikinshi sosai and baice mata uppan ba banda patting bayanta dayakeyi kawai, sanan yaji dan kanta tai shiru tadena kukan tadan sakeshi daga mugun rikon datamai taciro kanta ahankali daga kirjinshi hakan yasa shima yasake ta gently looking at her face, hannunshi yakai kan fuskanta ahankali ya share mata fuskanta sanan gently yace "stand up let's go inside" tashi tayi ahankali kaman yanda yacemata shima yatashi hannunta yakama yarike yana tafiya ahankali yafitar da ita daga kitchen din sukai stairs juyowa yayi zai dauketa ta girgiza mai kai sanan ahankali tafara hawa kan stairs din, tsayawa yayi batare daya bitaba yana kallonta, tana hawa stairs din ahankali tana rike kukan dataji tanajin zafi sosai amman she just feel like punishing kanta, saida takai tsakiyan benen sanan tarike karfe ta ahankali ta daura kanta akan karfen tasake rushewa da kuka sosai, ahankali yasaki dan gajeren tsaki yahayo, baice mata kalaba kawai ya sunkuceta, yakaita kan gado kwantar da ita yayi ahankali sanan yaja bargo yarufa mata yazauna akan kujeran yace "sleep" gyadamai kai tayi ahankali tareda lumshe ido tanakai hannayenta saman idanunta tagoge hawayen dasuka gama wanke mata fuska. Wayanshi dasuka barine adakin ya dauki ruri mika hannu yayi yadauki wayan yakai kunne, rai abace yace "Dad what" cikin dan fushi Babanshi yace "kasan karfe nawa kuwa yanzu Tobi, 2min pass 12" tashi yayi ahankali yawuce yafita daga dakin abakin kofa ya tsaya yay shiru saikuma yace "ni baxan kwana agida bayau" da sauri Dad yace "mene" danjim yayi saikuma yaki magana, Dad yace "kana ina"? Ahankali yace "a friend yana cikin team player dinmu yazo naija so I went to spend d night with my friend" cikin fada sosai Dad yace "wai bance maka kadena friends ba, Tobi don't you know friends sune makashinka na farko, every fallen heroes dakagani aduniyan nan da friends dinsu akai amfani akai bringing nasu down eh Tobi mesa bakaji" ahankali yace "Dad he's not a Nigerian he's a UEA guy, besides ma baisan waye niba, ni kawai allow me to have fun, kadena kirana in baka ganni ba am fine" shiru Babanshi yayi kanajin yanda yayi kasan baiji dadin abinda dan nashi yayiba kawai dan yaron ua gagareshi ne, kaman bazai sake cewa waji abuba saikuma yace "what about Boy"? Dan faduwa gabanshi yayi saikuma ya dake yace "yana tareda ni anan shima gobe zamu dawo" "shikenan kudawo da wuri" murmushi yayi yace "thank you Dad" sanan ya katse wayan tareda jinginar da jikinshi da bango this is the first time dayake ma mahaifinshi karya, but yazaiyi he can't leave this girl taje ta kashe kanta abanza, bude kofan yayi ahankali yakoma ciki har lokacin tana yanda yabarta idanunta a lumshe, amman kallo daya yamata yagane ba bacci takeyiba, rungume hannunshi yayi yana kallonta aman mai gadi har wuraren 2 alokacinne yaga finally tai bacci, ajiyan zuciya ya sauke yatashi ahankali yabude kofa yafita daga dakin kitchen yawuce duka wukaken kitchen din da fork kwashesu yayi yafito falo yay sama yabude wani separate daki da key sanan yakoma kitchen din coffee yahada yafito yazauna yana sha dan yunwa yakeji sosai tun abincin dayaci a gida, saida yagana sanan ya kashe wuta yataho saman yabude dakin ya shigo sanan yazo yasami gefen gadon ya kwanta ahankali dan wlh bai iya bacci akasaba ko a coach baima sababa, baiwani jimaba bacci yay awon gabada shi.
Karfe 4 daidai tafarka daga baccin, jin kamshin shi duk yacika mata hanci yasa tadan juyarda kanta, ganinshi tayi kwance akan gadon amman da space tsakanin itada shi, ahankali tasake zubamai ido yana kwance da kayan jikinshi ya rufada bargo yana bacci peacefully kana ganin yanda yake baccin kasan baccin ya shigeshi sosai, yayi kyau sosai yana baccin dayake bai kashe wutan dakinba, dauke kanta tayi jin gabanta nafaduwa sanan ta lallaba ahankali without making any sound tasauka, drawer taja tadauki pad daya tawuce bayi tana fadiya ahankali, bude kofan bathroom din tayi ta shiga gyara kanta tayi sanan ta wanko fuskanta daya kumbura sosai tafito, kafin ahankali tawuce tabude kofar dakin ta sauka kasa, kan kujeran falon ta samu ta kwanta ahankali taredajan filon kujeran ta rungume kam kam ajikinta tana tunanin word by word da Baba yafadi mata. Yanzu dama wayau suka mata suka kawota nan sabida Baba bayasonta dashi da Mama tazaman musu annoba? Yanzu dama wanan kukan da Baba yayi duk na karya ne kawai kartaga kaman yana farin cikin barinta gidanne saisa yayi? Saisa daman ko salla tazo saidai yama su Habib dinki tsaf banda ita, saidai yayta bata hakuri baida kudine, da gaske Baba ba mahaifinta bane ita yar wani dabance tsintarta yayi bayan bomb yatada kauyen nasu daya bata labari? Ta tambayi kanta saikuma ta share hawayen dasuka zubomata, tacema kanta "Think Fatima Zara'u, keba yarinya baceba yanzu think, mahaifin daya haifi yarinya bazai taba furta akashe mai y'a ba ko ajikinshi, Baba yace ama kasheni babu abinda ya shares shafeshi ko ayi duk yanda akaga dama dani is non of his business, yace kona gama aikin shekara biyun karma nadawo gidanshi na nemi wani uban, karna kara kiranshi da Baba" ahankali tasake share hawayen daya zubomata tace "maisa nai tunanin daukan raina? Na wahala aduniyan nan sonake naje lahira nasha azaban wuta, duk wanda ya kashe kanshi wuta zai shiga, yanzu abinda zakiyi tunani shine yanda xaki cigaba da aikin harna shekara biyun nan batare da angane ke mace bace ko namiji ba, bayan kin gama aikin saikizo ki nemanma kanki mafita, hawaye takara gogewa ahankali ta furta "Baaaba" itace kadai matar datasan ta sota aduniya, itace mamarta na farko, ita tafara bama Baba aiki idan yafita saita dinga rainon ta matan na mugun sonta, babba ce saidai yaranta dukna kasan waje, bata taba ganin yaranta ba harsukazo sukabar kano lokacin aka tafi da ita wai zasu koma kasan waje tanada ciwon suga, saidai suna waya, tanada number Baba takan kira suyi magana tabata labarin school da position dinta, ko yanzu tana ina oho, da ace tasan inda take da wajenta zata amman tana kasan waje, yanzu dai aduniyan nan ita kadaice, batada kowa, she's all alone, batasan mahaifiyarta ba batasan mahaifinta ba, wanda tasani a mahaifi yae bashi ya haifeta ba, jitayi wani kuka yazo mata takara rushewa da kuka takifa kanta a filo tana kuka tana taushe bakinta gudun karyay kara jikinta har dumi yayi tsabagen kuka.
Ahankali taji saukar hannu akan bayanta hakan yasa tadago kanta