Showing 39001 words to 42000 words out of 150358 words
Chapter 14 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
local dabai wani iya turenci irinka ba, Magajin sarki wanda zai gaji sarautan gidan nan kakema aiki, gather sense dinka together ba'a latti, ba'a cemai no, ba'a tambaya sau biyu, wuce kaje kai wanka be very fast" da sauri tawuce shi ta tafi bayi wanka tayi agurguje tai alwala sanan tadawo jikinta har bari yake ta yafa mayafin data maida na salla tai asubahi sanan ta tashi tana azkar tabude jakan wani set na dogon wando baki, farin t-shirt da black jacket taciro, saka kayan tayi tsaf suka zauna ajikinta sanan tazauna taciro black cover shoe mai tsadan gaske datagani tasaka tadaura agogon dataga shima ansai mata sanan tasaka bow tie din tafito tana tafiya ahankali, Head Guard dake bakin kofa tsaye ne ta kalla tana mamaki toshi baya bacci ne, yana ganinta yay gaba hakan yasa tabi bayanshi har gaban flat din prince yakaita yabude mata kofa tashiga sanan ya mayarda kofan yarufe yatafi abinshi, agogon bangon falon ta kalla taga biyar saura minti goma hakan yasa tai hanyar stairs tana tafiya ahankali yanzu wanan ne rayuwan dazatayi kullum zuwa tada kato, Allah yawadata Baba yabiyasu bashin su yazo yadawo da ita gida, karasa hawa tayi Allah yasa tasan dakin dan jiya sun gyara dakin fess, hannunta tadaura akan handle din kofan gabanta harwani faduwa yake wanan ma shine aiki mafi worst dama an kaita wajen su Anas inda tasan nan wajen zataje tai aikine ba wanan ba da tana mace ita zata dingama namiji komi tana kulada shi tana zuwa aike, wani bangare na zuciyanta ne yace as much as everyone is concern anan bangaren ke kadai ke ganin kanki a mace kowa as namiji ya sanki har Anas din, wani hawayene taji yazo mata da sauri takai yatsanta ta share ahankali tace "sunanki Khalid ba Fatima ba, and this is your life now" addu'a tayi sanan tabude kofar ahankali wani cool sanyin Ac da kamshin sassanyar turare ya bugi hancinta, very dim light ne adakin bai kashe wutan ba but yay switching light din daga normal bright white light zuwa dim, gabanta harwani mugun faduwa yake ta saukar da idanunta kan gadon, tabbas ta hango mutum akan gado but bata ganshiba sabida sakin fararen shara sharan labulen dayayi hakan kuma ba karamin kwantar mata da hankali yayi ba, maida kofan tayi tarufe sanan ta shigo ahankali kaman wacce tazo sata, karan kaman ta taka abu dataji da kafarta yasa ta kalli kasan kafanta da sauri, wata doguwar takarda tagani da rubutu ajiki hakan yasa ta duka ta dauka, wani dogon list tagani heading typing nema ba rubutu ba, heading din na dauke da work routine "I woke up everyday at 7am, the following should be done before natashi....."
_1- Get my bedroom slippers ki ijiyesu gaban gadona ta gefen dama cus ta gefen nake sauka daga gado inna tashi bata haggu ba._
_2- enter my bathroom, makesure everything is intact and in good shape, idan bayin is dirty wash it kafin natashi_
_3- I take bubble bath every morning, open my shower cabinet essentials drawer, and pick L'Occitane Relaxing & Foaming Lavender Bubble Bath, kizuba a ruwan dakike tarawa harsai bathtub din ya cika just leave it that way, before natashi zafinshi zai koma daidai yanda I can use it._
_4- pick my brush open the tap rinse it first sanan kisa toothpaste akai ki ijiyemin ta left side, I pick brush da left and open tap with right hand_
_5- pick two towel, a big and small daga towel from towels closet dake cikin bayin and hang them a hanga, leave them their the small is for my hair, while the big is for body._
_6- after all of those, then you are done with bathroom, come out go to my closet room_
_7- pick up a set of work out outfit for me, keep them on the closet couch._
_8- pick up short boxer and keep it their too._
_9- get a matching sneaker and keep with a matching sock._
_10- pick up a cream, and sunscreen and keep it on the couch too._
_11- select 5 perfumes from the perfume gallery and keep on the couch, with a deodorant, and body spray._
_12- take sallaya and chasbaha to the room and spread it for me on the floor_
_13- go to my kitchen pick up my water bottle and filled it with water, keep it there at the dinning._
_14- if I wake up by 7, any place I leave put everthing there back in other._
_15- note all this thing dakakeyi makesure you don't make any sound, a little sound wakes me up from sleep, so watch out._
_16- stop wasting time reading this as time is ticking_
_Sign OluwaTobi Tajudeen Adewale._
Da sauri tai hanyar bathroom dinshi rikeda list din, ahankali tabude kofa gudun karyay kara, kofofin gidan masu kudima dabanne baikoyi karan ba, bayin ta shiga ga bayin nan kal kal kallon list din ta shiga yi tana hadamai abubuwam daya fadi, tass sanan tagama tafito, ta shiga closet dinshi, wajen kayan work out taje tasanmenene work out tun a school, hakanan wasu set mai ruwan toka taga sun mata kyau shita ciro mai ta ijiye sanan taje bangaren boxer, boxers dinma duka sababbi ne, guda daya tadauka gajere taje ta ijiye sanan tadauko cream ta ijiye shima turaren tsoron fesawa tayi balle ta zabanmai hakan yasa kawai ta debi biyar randomly ta ijiye mai da deodorant dakuma body spray din sanan tadau dadduma tafita ahankali tamaida kofan tarufe sanan tabude kofa tafita daga dakin tasauka kasa da gudu dan duka duka bakwai saura minti uku, kitchen dinshi tayi bata tsaya kallon komi ba sabida kar time yakure mata tadau goran ta dauraye sanan tafito taje gaban water dispensa tacika mai goran da ruwa tafito ta ijiye a sama sanan takoma sama da gudu ahankali tabude kofan ta maida tarufe daidai bakwai na safe na clicking daidai kuma yana bude ido, karasowa gaban gadon tayi tai kneeling kanta akasa gabanta nawani irin mugun faduwa tana jira yatashi.
Tashi yayi ahankali zaune yana mika, sanan gently ya sauko da kafafunshi kasa batare daya fito da kanshi daga cikin labulen gadon ba, girgiza kafanshi for the first time bata luraba dan kanta nakasa akaro nabiyune ta lura dan alamun motsi tagani da sauri ta daga idanunta sama ta kallai gani tayi idanunshi lumshe kuma bai yaye labulen ba yana ciki, sake girgixa mata kafan dayayi yasa dawani irin sauri ta dauki bathroom dake wajen tasaka mai a kafafuwanshi dabasuyi kama da wanda aka taba takasu akasa ba sanan takoma inda take kanta nakasa, tashi tsaye yayi ahankali tareda bude idanunshi sanan ahankali yajuya yana tafiyan nan daidai cikeda gajiya kaman zai fadi yabude kofan bathroom ya shiga.
Tashi tayi itama tuna abinda yafadi mata ta tattare labulen gadon ta sakalesu inda ake sakawa, ta gyara gadon tsaf tareda shimfida hadaddun lallausan bargunan dake kan gadon da bata taba ganin irinsu, ta gyara decorations dasuke gefen side drawer tass, sanan tafita tadauko vacuum daga inda taga masu aikin jiya sun ajiye sun koya mata yanda ake amfani dashi tun jiyan ta jona ta share dakin da dama babu datti ko daya tass akasan sanan tafitar ta dawo ta sake kneeling a inta take, bude kofa yayi yafito dudda bata juyoba but saida kamshin sabulun wankan shi yacika mata hanci dakenan kaman turare yana kamshi combination na dry wood da citrus, jin yakara bude dakin closet yashiga yasa ta tashi tabude kofar bayin, chak ta tsaya ganin yanda yay messing bayin up kaman yaro karami, bathrobe da boxer daya cirene tagansu akasa, ga brush din dayay amfani dashi a inda tabarshi mirror wajen ya batashi da kumfan makilin kaman akanshi yake fesa kumfan, hadaddun rags dake shimfida akasan bayin ya jikasu da ruwa, toilet rolls najan kasa, ajiyan zuciya ta sauke ahankali tace "yarone wai wlh ko Sadiq dinmu bazaiyi wanan aikin ba" wani karamin basket da ak nuna mata jiya na kwashe kayanshi daya cire ta dauka ta tattare su ciki dan annuna mata mai wankin kayanshi da zata dinga bama kayan sanan ta shiga tattare bayin ta share madubin fess, tai mopping ta tsane bayin cikin 10min ta gyara bayin harda wankewa tasake yi sanan tafito dan ita inhar aikine baya mata wuya, dudda bata kalleshi ba but taga yana kan dadduma yana salla hakan yasa ta shiga closet dinshi tana rike da basket din kayan dattin shi, gani tayi ashe baiyi komi abayi ba, towels din duka daya cire ya wurgasu akasa, haka mayyukan daya shafa batare daya rufeba su ba ya jejjefar da marafen su akasa har zuba suke sabida bai kulle ba ya wurgan, turarukan kuwa wasu bama taga marafan su ba nan tashiga nemeneme takai kusan 20min tana aikin closet din sanan tai putting nashi back in shape tafito, ganinshi tayi zaune bakin kan gado yana saka sneakers na gudu data daukomai, daukekai tayi bata kalleshi ba tabude kofa tafita waje taje Guard din dake gaban dakinshi na ganinta da basket din kayanshi kafin ma tamusu magana suka amsa takoma ciki, daidai shima ya sauko kasa yana kokarin sake headphone dinshi a kunne yay wani irin kyau fuskanshi yadan kumburan bacci lips dinshi sunyi mugun pink, sai kamshi yake zubawa, batare daya kalleta ba yace "follow me with the bottle water" da sauri tai dinning ta dauki goran tabiyo shi dashi, yana jogging tana biyedashi abaya.
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍🏾M SHAKUR
_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.
_Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu_
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp
_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHUMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
EPISODE 2️⃣0️⃣
_FREE PAGE_
Harya kusan kaiwa gate binshi tayi abaya da gudunta sabida ta cimmai, cimmishi tayi suka fita tare tana binshi abaya sai haki take kafin sukai asalin main gate din gidan dazai fitar dasu daga gidan sarkin gabaki daya taji tana neman sumewa, nauyin water bottle din hannun nata kadaima ya isheta, tun tana binshi da sauri harta soma rage gudu ganin zata zube, sosai yamata nisa tanachan baya haryakai inda zaikai a jogging din sanan yadawo ya cimmata a inda take tana gudu da kyar hannu yamika mata batare daya kalleta ba hakan yasa ta mikamai ruwan da sauri bayan tabudemai, sha yayi sosai sanan yabata saikuma yacigaba da gudunshi, maida goran tayi tarufe tabishi kaman kirjinta zai fito daga jikinta ahaka sukakai gida, bangaren Maman shi ya shiga tana biyedashi abaya, lokacin 9 da minti biyar na safe, zama yayi gabaki dayanzu suna zaune dinning dukansu basu faracin abinci ba shi suke jira, zubewa Fatima tayi kasa alamun gaskiya shikuma Tobi ya janye headphone daga kunnenshi yacire tareda mikama Fatima batare daya kalleta ba sanan ya mika hannu alamun tabashi towel tabashi ya goge zufan dayakeyi fess sanan yatashi daga kujeran pecking Babanshi yayi yace "morning Dad" yama Mum dinshi dake kallonshi kaman zata cinyeshi yace "Good morning Mum" hararanshi tayi cikeda so tace "tell me ekaro, haba Tobi wai gudun yarenka kakeyi ne" komawa wajen zamanshi yayi batare daya kalli yayyin nashi ba yace "morning sis" ganin Babansu yasa suka amsashi a mutunce, coffee shi Mum tabashi sanan tadau plate daya tasamai two toast bread, fried sausage guda biyu, dakuma bake beans tana mikamai abin namata takaici tace "namiji daya kamata kai breakfast yanzu da strong amala ka wuni da karfi this ne this is your breakfast Tobi ko yayyinka mata basacin wanan" batare daya kallesu ba yace "bakiga yanda suke losing shape ba Mum, katin katin dasu sunmafi samarin su girma, niko aure zanyi bazan auri katuwar mace irinsu ba wlh, nafison mata kananu" narkamai muguyen harara sukayi ya dauke kai dudda iyayensu sunsan bai kyauta ba babu wanda yacemai uppan, Mum dinshi ya kalla yace "Mum put food for that boy" yanuna Fatima dahar lokacin ke kneeling akasa a falon, da sauri Taye tace "kataba ganin munci abinci tareda any worker gidan nan" batare daya kalleta ba yace "he is not just any worker, he is my Boy, Mummy" da sauri Maman shi tashiga zuba abinci kafin ran Tobi yabaci, hadaden fried rice tazuba mata da cikin da salad, dakuma shayi a kofi sanan takira Fatima dake kneeling awajen har lokacin tace "you" da sauri ta tashi tazo dinning din tazagaya ta wajen Mum, kasa kallon Mom tayi hannunta har rawa suke tamika ta karbi abincin sanan ahankali tace "thank you Ma" juyawa tayi takoma inda take Dami taja tsaki tamike tana korafi. "Sai Tobi yadinga cin karenshi babu babbaka akimai magana in mune ba'a kyalemu" "come back here" Mai Martaba yakirata ba wasa dawowa tayi ahankali taja kujeranta ta zauna yace "kin manta abinda nafadi jiya ko, Tobi is the King to be tun yanzu start getting use to anything he says happens, he says his errand boy should eat with us, he will eat with us, infact idan yacema yazo yazauna a dinning din yaci abinci damu zaizo, this is the strong last warning dazan bama dukanku duk randa an atom of disrespect yakara shiga between ku da Tobi saina mummunan bata muku rai" Mai Martaba yafadi babu wasa, Mum tace "thank you Honey, finally kafara gyarama yaranka zama" saida yacinye abincin shi tass sanan ya kalli Mai Martaba yace "Dad my phone i want to call Anty Ayo batazo jiyaba" da sauri Mum tace "kasan mai karamin ciki laulayi yataso mata ya sakan mata zazzabi takasa zuwa" shiru yayi duk yay wani irin hakan yasa Dad yace "common she will be fine" gyadamai kai yayi kawai sanan yatashi yawuce zai fita da sauri tabar abincin datakeci ta tashi tabishi da gudu duk suka bisu da kallo suna murmushi, flat dinshi yayi yabude kofa ya shiga tabishi ciki itama.
Zama yay akan daya daga cikin lumtsatsun kujerun falon yadau remote dake kan kujeran yana kokarin kunna TV yana girgixa mata kafa batare daya kalletaba zuwa tayi ahankali ta tsugunna gabanshi kwancemai takalmin tayi tacire mai tareda socks din, kanta nakasa tace "nahada ma ruwan wanka"? Shiru yayi bai amsataba, takai kusan 5min tana jiran abinda xaice amman baice kalaba hakan yasa ta dauki takalman da safan ta wuce sama harta fara hawa stairs cikin wata kwantacciyan murya yace "the water shouldn't be too hot, just mild" juyowa tayi ta kalleshi ganin idanunshi nakan abinda yakeyi yasa tawuce kawai ta tafi sama, maida takalman inda suke tayi bayan ta goge kasan da jikin da rag sanan tafito ta shiga bathroom ruwan wankan tahadamai tana kallon yanda ruwan ke tashi da bubbles gawani irin kamshi saitaji inama ace itane zatai irin wankan nan na yan gayu, wasu towels taciromai tasamai brush kamandai najiya sanan takoma closet dinshi ta tsaya tana kallo dudda bai bata work routine na rana ba but tai shiru ta tsaya tana lissafi, yaje gudun safe, yadawo yay breakfast, yanzu zaisake wanka idan yafito tunda ba fita zaiyiba dan taji Mummy shi na cemai saiyayi sati bai fita ba yahuta sosai agida ya murmure, hakan yasa taciromai wani plain white V neck t shirt talura duk t-shirts dinshi masu V neck ne, yanada white color abubuwa dayawa kaman white fav color nashi ne. Taciromai wani 3 qauter na wando dazaikaimai gwuiwa yanada fadi green common flag kaman na sojoji, da sabon boxer dakuma mayyuka da turare da wani indoors slippers da jikinshi na nan kaman bargo tsabagen laushe sanan tafito falo taje tazube akan rug gaban kujeran dayake kwance yana kallo ahankali tace "all set, you can go in and shower now Sir" baice mata komiba kanta nakasa yakusan bata 15min sanan yamike tsaye, hannunta ta shiga wasa dashi batasan mesa duk inya mike saita dinga jin kanta restless ba, anatse tace "akwai wani abu dakakeso namaka" wucewa yayi abinshi yafara hawa stairs batare dayama kalli inda takeba, kaman bazai amsa ba dan hartama cire rai saikuma taji yace "Anything" shiru tayi tana tunani menene anything to itadai ta shiga uku, gashi Head Guard yace karya sake yay laifi, tabata sama da minti biyar tana tunani saikuma tai tunani ai hala yafito kwallo zaizo ya kalla so basically he needs abu dazaisa aciki yayta ci dazai keeping nashi company hakan yasa tawuce babban kitchen dinshi da babu abinda babu aciki kaman kitchen din mai mata, katoton freezer dake kwance a kitchen din tabude, ganin kayan abinci ne da fruits aciki yasa ta ciro fruits, watermelon, kiwi, green apples da grapes saikuma strawberry data gani shima sai kallonshi take bata tabashan strawberry ba saidai tagani awaya ahoto