Showing 78001 words to 81000 words out of 150358 words

Chapter 27 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt

M Shakur   

07 Jan 2025

15389

Tobi ne dan tunda tabude kofa tafito yaji yatashi ya tsaya a sama ganin akan kujera taje ta zauna ba wani abu zatayiba, yana kallonta taketa maganganun nan ita kadai saikuma kuka tausayinta yakeji sosai, dago rinanun idanunta tayi ta kalleshi, shima ahankali yake kallonta asanyaye, cikin wani irin muryan kuka tace "my mum is late, my Dad said he's not my father, I am all alone in this world I don't have anybody Sir" tasake fashewa da kuka, hannunshi yakai yadaura kan fuskanta yace "shiii listen here, should I make you a promise" ahankali ta gyadamai kai, dan murmushi ya sakan mata sanan yasake sharce hawayen dasuka zubomata yace "I promise to be everything to you, I will take care of you, I will stand by you a ko'ina, zan maye gurbin komi you've lost, sanan i promise to be the family dabaki dashi, don't cry again, come here" yajawota jikinshi takara fashewa da kuka ta kankameshi bata taba sanin kirkin prince dinan yakai hakaba, sundade ahaka tare sanan tasake shi tana goge fuskanta, hannunta yakama yarike yace "promise me you will not cry again, promise me that, you cry too much u want to be admitted in the hospital again ne"? Girgizamai kai tayi hakan yasa yace "then promise me not to cry again Zaa......raaaaa" yakira sunanta ahankali yanadan elongating na sunan, ahankali tana share fuskanta tace "I will not cry again Sir" murmushi yadanyi yace "My name is OluwaTobi Tajudeen Adewale, call me that stop calling me Sir" shiru tayi kaman bazatai magana ba saikuma ahankali tace "I will call you Yaya Tobi or Ya Tobi" murya chan kasa yace "what is Yaya and Ya" ahankali batare data kalleshi ba tace "they all means brother, so will be calling you Brother Tobi" dan yatsine fuska yayi yace "uhmm nice kid sis" dan dagokai tayi ta kalleshi jin yakirata da Kid sis, saikuma ahankali tace "go and pray ana kiran salla Ya Tobi" dan jim yayi yana kallonta saikuma yatashi ahankali ya shiga bayin falon yadauro alwala yafita daga falon binshi tayida kallo hakanan saita sami kanta da murmushi, ahankali tace "thank you Prince".








_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.


_‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu_
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp


_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHUMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body_oils._
SIGN M SHAKUR






















💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫






_MASIFAFFIYAR KAUNA_






✍🏾M SHAKUR








EPISODE 4️⃣0️⃣






Wuraren 7 ya shigo gidan ahankali yabude kofa ya shiga ciki yana binta da kallon ganinta akan kujeran daya barta ta kwanta tana bacci sosai, ta lankwashe kafafuwanta sabida sanyin Ac, stairs yayi yay sama sai chan gashi yadawo rikeda bargo dakuma car key, ahankali ya karaso ya lulluba mata bargon harya tashi saikuma ya tsugunna ahankali yana kallonta kaman yanzu yafara ganinta, ahankali yakai yatsarshi yatattare nata gashin daya sauko kan fuskarta yana tunanin kaita saloon anjima idan yadawo daga gida, yabi idanunta dasukai kalan kuka sosai tsabagen kukan dataci this days sanan yamike tsaye ahankali yawuce yafita, saida ya tsaya yabama mai gadin sakon abincinta sanan yacemai yasamata ido sosai karya bari tafita idan wani abu yatashi yakirashi awaya sanan yafita zuwa gida.




Parking yayi yafito tareda daure fuska sabida kar wani ya tambayeshi kan Boy, flat dinshi yaje yay wanka ya sanyo 3quater da t-shirt yafito yazo flat dinsu duk suna zaune a dinning, iyayenshi dasuka tsareshi da ido ya kalla yadan daure fuska yace "morning Dad and Mum" sanan ya kalli yayyinshi yace morning tareda dauke kai, kafin yasake kallon Mamanshi yace "Mom am so hungry wlh give me food" zubamishi abincin tayi tace "inda kaje bakaci na dare bane" shiru yayi bai amsataba ya karbi abincin yafara ci kowama yafara cin abincin sosai, sunyi nisa acin abincin ya ijiye spoon dinshi ahankali yajuyo ya kalli Mai Martaba, ahankali yace "Dad" dagokai yayi ya kalleshi yace "yes Son" ahankali yace "there's something I want to understand Dad, inhar taimakon mutane zakayi why not kabasu kudin kawai kyauta maisa kake bada kudaden bashi"? Kallonshi Baban yayi sosai kaman yana kokarin gano wani abu tattare dashi hakan yasa yace "mesa kamin tambayan nan"? Dan murmushi yayi yace "toba kace am king to be ba, just a question out if curiosity" ijiye spoon shima Baban yayi yace "actually gadon abin nayi nima haka kakanka keyi kafin yarasu, kowani year akwai budgeted kudin danake fitarwa na taimakon alumma wanda za'a rabasu kashi hudu, North, South, West and East, ni am own shine ina cire kudin nabama Otun ne shine incharge of the work, kowani bangare that's kudu, gabas, yamma da arewa, munada lawyers dake representing garuruwan, Otun zai bama lawyers din kudin su bama duk wani maison bashi, zasu fadi ko shekara nawa sukeso subiya back without any interest, like anyway, but in ranan tayi basu mayarda kudin ba zamu kullesu ko subamu yaransu sumana labour idan ka kalli abin da kyau this is taimako, shi mutum ka dauki kudi dayawa kabashi he will become lazy but kacemai zai biya hakan zaisa they will work hard suyi business mai kyau dazai yielding musu profit kagane" gyadamai kai Tobi yayi yace "to idan mutum yatashi biyafa" anatse Dad yace "akwai account na biyan bashin wanda duk Otun ne ke incharge of it mutum kawai zai tura kudin back" zamu duba muyi confirming payment mubaka danka koda aranan kakeso, saisa ake mana addu'a kullum bama cutarda kowa" dan ajiyan zuciya Tobi yayi yace "Dad idan zakai kyauta kawai kayi, wanan maidamaka da kudin doesn't make any sense to me wlh" hararanshi Baban yayi yace "idan kazama sarki make ur own changes amman kabarni nai sarautata yanda naga dama" kwashewa da dariya yayinshi sukayi ji for the first time a history Dad yagama Tobi bakar magana, wani mugun kallo Babansu yamusu dayasa sukai tsit shikuma Tobi azuciye yatashi Dad nakiranshi "Tobi Tobi, Son" yawuce yafice abinshi.








Dakinshi ya shige ya zauna a falo yay jim yana tunani, sai kawai yadau wayarshi contact dinshi ya shiga yaciro number dayay saving da Ayoka, sanan ahankali ya danna unblock danyay blocking dinta, sanan yay dailing number ta yakara wayan a kunne. Ringing biyu ta dauka.
"OMG Besty its you" ahankali Tobi yace "Hi Ayoka" kaman zatai kuka cikeda shagwaba tace "why did you block me besty kanason nasami heart attack ne? Is your Mum ta kwantar min da hankali da yanzu hala ina hospital, are you missing me inzo muje cinema ko muje beach, please let's go out now na nunama friends dina how hot my boyfriend is" dan gajeren tsaki yaja kaman baison magana yace "I told you am not your boyfriend Ayoka" murmushi tayi sounding ko ajikinta tace "wlh you are na gama service zakagani bakasan maganan da akayi bane" dadan fada yace "can you just listen to me batare dakinyi magana boyfriend whatever ba" da sauri tace "okay love ina jinka" dan shiru yayi yana waswasin fadi mata saikuma yadan cije lips sanan yasaki yace "secret ne please I don't want anyone to know" da sauri tace "but kasan tun muna yara duk maitan Dami bata isa taji sirrin muba, I promise, pinky promise Baby" dan tsaki yaja saikuma ya shareta yace "ai you know about loan din da our Dads kebayarwa ko" dasauri tace "yes abinda idan an kawo yaran agidan mu ake saukesu kafin Dad ya rarrabasu" dan ijiyan zucya yayi yace "I need a favor" da sauri tace "what favor" ahankali yace "I need account number da ake biyan loan din back, da ace Dad dina ke handling d stuff dana samo dakaina but is your Dad am sure kuma suna gidansu" da sauri tace "but I don't know the account, kaima kasan I don't know anything about those stuff" "yes I know you don't I want you to find it for me" da sauri tace "a Dad's bedroom"? Ahankali yace "yes" ahankali cikeda tsoro tace "Tobi" shiru yamata bai amsata ba, saikuma tace "what do you need the account for ma at this first place, me ruwanmu da wayan nan yaran wulakantattun"? Anatse yace "will you help me yes or No" murmushi tayi tace "kaima dai kasan I can help you, I will always help you, banda haka in that whole house am the only person datasan password din bedroom din Dady, as per his only child da Allah yabashi yar gata kuma" tabe baki yayi yay shiru shida, tacigaba. "Zan maka aikin I will sneak in and get the account number for you but on one condition" da sauri yace "one condition" ahankali tace "yes in zakayi zan maka idan kuma bazakayi ba sai inga idan ka isa ka shiga bedroom din Dady kasamo abinda kake nema that's idanma kasa password din kenan, so are you ready nafada maka condition dina" shiru yayi nakusan 3min sanan yace "okay wats your condition" murya chan kasa tace "only if you agree to be my boyfriend, sanan zamu fadama kowa we are boyfriend and girlfriend, sanan xakazo gobe dasafe ka amsa kafin Dady yafita sabida na nunamai kai amatsayin boyfriend dina, inhar ka yanda yanzun nan Dady nafita zan shiga in bincika maka dakin ciki da bai na nemo maka acikin documents dinshi, do we have a deal yes or no" jin yay shiru yasa tasake maimaita tambayan tace "do you agree to become my boyfriend yes or no Besty"? Yadade yay shiru baison anything to do with her tunda tafara nuna tana sonshi but yanzu account number nan he needs it sosai whats there sef, hakan yasa ahankali yace "okay naji" da sauri tace "don't tell me okay naji, tell me okay Ayoka I take you as my girlfriend" kaman wanda baiso yay magana yace "okay i take you as my girlfriend Ayoka" ihun murna tayi har yanajin karan tsallen datakeyi tawaya tace "shikenan Baby saikazo goben, kuma daga yanzu u will be calling me baby, duk ranan da ka bata deal dinmu nima zan bata dan saina tona abinda kasani nayi, bye baby, tell me bye bye baby" yatsine fuska yayi irin na you know sanan yace "bye babe" tareda katse wayanshi yatashi yadau key yawuce yafita.






A compound din gidan yayi parking wajejen 3, sanan yawuce ciki bayan ya gaisa da mai gadin, yabude kofar flat din ya shiga daidai itama tajuya kai ta kalli kofan kaman daman jiranshi take, suna hada ido tasauke kanta kasa dasauri tanajan bakin gyalen dake kanta daya saimata jiya, tana sanye da red and black riga cikin wanda mai gadin yasayo yamata kyau sosai, jin shiru yasa tasake dago kanshi yana tsaye inda yake yana kallonta ahankali tace "good afternoon Si......" saikuma da sauri tace "Ya Tobi" wayanshi yaciro daga aljihu yace "get your shoes and meet me at the car" yawuce yafita tashi tayi tai sama tadauko takalmanta tasaka duktai wani iri, sanan tasauko tabude kofa tafito tana tafiya ahankali.


Ta mota yake kallonta yana zaune agaba, yana take tafiya ahankali tana kokarin jan gyalenta yarufe mata chest, yarinyar nada natsuwa batada iskanci irin na yaran garin nan dayasaba gani, harta karaso motan baisani ba saida tabude baya tashige sanan yasani tada motar yayi yafice, sanan yatafi da ita spa dayake zuwa, manager da kanta ta sauko kasa da aka gayamata shine yazo, Fatima yabata, anatse yace "arrange her from head to tea, how many hours zai daukeku"? Washe baki matar tayi takai hannunta tana taba fuskarta tace "she needs body polish, waxing, sauna bath, lip therapy, hair care, pedicure, manicure inshort everything" gyada musu kai yayi, yace "private room xaku sata, just finish go and get to work amata braiding this hair" dasauri manager tace "yes sir" sanan tasa aka wuce da ita, harsun has sama sanan tadan juyo ta kallai hada ido sukayi dan murmushi ya sakan mata sanan yawuce yabiya kudaden da aka chajeshi masu tsoka harya zauna a hadaddun kujerun dake reception din yadau news paper zai fara karantawa manager tazo tace "Sir who is this goddess daka kawo mana yau? My world I've never seen a beautiful girl like her before" batare daya kalleta ba yace "ask her" sanan yabude jaridan shi yafara karantawa, haka ya zauna wooo har isha'i salla kawai kefita dashi, sai wajajen nine yana zaune ya mike kafa kan hadaden table din wajen yana karatu kaman ance yadago kai, janye jaridan yayi kadan daga gaban fuskanshi, kanta na kasa yaga suna saukowa dudda darene bai hanashi ganin wani glowing da skin dinta keyiba barinma fuskanta wanan tamukewan datayi sabida kuka kaman sunyi tsafi sun cire, an mata kalaba da gashinta dasukai tsayi sosai bakin gashin ya kanannade sabida santsin gashinta, manager tarike gyalenta a hannu sabida tanaso tanunama Tobi yanda kitson yay kyau gashi basu mata parking ba suka saki gashin saura kadan yakai waist dinta, ganin sun kusan gama saukowa daga benen yasa yamaida jaridan da sauri kaman basu yake kalloba, har gabanshi takawo ta tace "Sir look yanda muka maida maka da baby, dan Allah ji gashinta, ji tsawon ahakafa bamu saka ko a single attachment me this girl is cute, da ana mata waxing kuka tadinga mana wlh batada dauriya, yanzun nan damuka gama komi muka maa massage zatafara bacci nace ta tashi kana jiranta tuntuni" dan janye jaridan yayi ya kalleta kanta nakasa tana wasa da yatsunta, bainuna komiba yace "give her the scraf" da sauri manager tabata gyalenta, sanan ya kalleta yace "let's go" yay gaba itakuma tana binshi abaya tana yana gyalenta akan kanta, bude bayan motan tayi ta shiga ta zauna sanan tarufo shikuma yashiga gaba yatada motar, saida suka danyi nisa a tafiya kaman daga sama asanyaye yace "is there anything you want"? Sosai takejin nauyi amman saita daure ahankali tace "hijab" baice mata komiba yaja motar har zuwa wani shago ya kashe ya shiga saigashi yafito rikeda leda yabude baya ya ijiye mata yarufe yakoma gaba yazauna yaja motan.




Wuraren 10 da rabi sukakai yay parking a tsakar gida yace "come down and go" bude motan tayi ta sauka ahankali sanan ta kalleshi ta glass din gaba inda yake zaune dayake kasa tace "thank you, May Allah bless you Ya Tobi" ko Allah yasan yaji addu'an nan har kasan ranshi, gyadamata kai yayi yace "take care" gyadamai kai tayi tawuce tana rikeda ledan a hannu tawuce, saida yaga tashiga ciki sanan yasauke ajiyan zuciya yabama mai gadi sako sanan yatafi gida.










_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.


_‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu_
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp


_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHUMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body_oils._
SIGN M SHAKUR
















💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫






_MASIFAFFIYAR KAUNA_






✍🏾M SHAKUR




EPISODE 4️⃣1️⃣
WASHEGARI!!
Wayarshi yatadashi daga baccin dayakeyi daukan wayan yayi yakai kunne batare dayay magana ba, muryan Ayoka yaji daga bangaren tace "I know daman baka tashi ba saisa nace lemme call you kai sauri kazo kamanta deal dinmune" katse wayan yayi ahankali ya jefar yasake komawa bacci sai chan kuma kaman wanda aka tsikara yabude ido da sauri, bathroom dinshi yatashi yashiga yay wanka sanan yafito yaje ya shirya cikin kananun kaya masu tsada designers, fitowa yayi yahau kan dadduma yay sallan safe yana idarwa yawuce closet yasake shiryawa ya feffesa turaruka sanan yabude drawer key motocinshi yadauki wani key mota daban yafito, ko kallon flat dinsu baiyiba yawuce ya shiga mota yatada yafita yabar gidan wajajen 8 saura.








Horn yayi agaban gidansu Otun, guards na gidan na ganinshi suka zube akasa suna gaisuwa da kirari dauke kanshi yayi shifa wanan abin baya burgeshi ko kadan sanan yaja motar ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login