Showing 9001 words to 12000 words out of 150358 words
Chapter 4 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
daga dakin yay hanyar fita waje batare daya kalli dumbannin mutanen dake GOPD ba, tun 4 nasafe ya shigo asibitin nan emergency baici komiba har yanzu yunwa yakeji sosai by 1 yakeso yatafi gida yahuta yay bacci, wajen parking space yakarasa yay wajen wata hadaddiyar Black suv bude motar yayi da key dinshi sanan yamika hannu yadauko wani haddedden moderate flask dake kan dayan sit din gaban mota, bude marfin flask din yayi da saurinshi sabida tsabaragen yunwan dayakeji yakai flask din bakinshi yana kwalkwalan coffee dake cikin flask din daya hada da asuba dazai fito, saida yay kusan rabin flask din sanan ya sauke daga bakinshi yana sauke ajiyan zuciyan gajiya, saida yadan huta sanan yadaga flask din zai kara komar dashi baki kaman ance ya kalli bangaren damashina ke parking ya hango wani mutumi dan magidanci dabai ganin fuskarshi da kyau zaune gaban wata mota a side dinshi rikeda folder a hannunshi yana share hawayen dake bin fuskarshi looking so confused and sad, jiyayi zuciyarshi ta tsinke dan haka Allah yayishi yanada tausayi sosai, kasa cigaba dashan coffee shi yayi dudda uban yunwan dayakeji, maida flask din yayi ya ijiye, yamaida kofan yarufe yamata key sanan yataka ahankali yana tafiya harya isa inda Baba yake zaune kanshi akasa yana share hawayen dake zubomai baima lurada wani yazoba dan hankalinshi yay nisa yana tunai. "is everthing okay Sir, mesa kazo nan kazauna kana kuka"? Wata zazzakan muryan da Baba yaji akanshi namai magana cikeda kamala hakan yasa yadago kanshi da sauri da idanunshi dasukai jajir yahada ido da Dr daya rubutamai maganin Zara, Dr na ganin Baba yaganeshi shima at a spot ai mutumin dazune Baban yarinyar dake emergency ward, ganin Baba yace "what is it Sir? Mesa kazonan kake kuka ina magungunan danace kasayo"? Dr yay tambayan yana kallon Baba yana kara nazarin yanayinshi, baki Baba yabude zaiyi magana saikuma wani irin takunkumin bakin ciki yakara tokaremai wuya wasu hawayen suka sake zubomai, kaman wanda notin kanshi ya kwance baisan lokacin daya kwaso yan chanjikan dasuka ragemai ba a aljihu yanuna ma Dr idanunshi sunyi jajir ga hawaye sun cika idanun kana ganinshi kasan he is pain yace "kagansu wanan ne kudin danake dashi gaba da baya, banda hanyan samun wasu, Zara'u na nachan kwance rai a hannun Allah an rubutamin maganinta nakasa saya sabida bandashi, bandashi, ina zansa raina? Asibitin gwamnati ma nakasa biya ba dole nazo nan na zauna ba likita" yanda yake maganan kaman ma wanda baya cikin hayyacinshi tsabagen damuwa yasa Dr yacigaba da tsayuwa a inda yake batare dayay motsi ba yay shiru yana kallonshi kawai, hawaye Baba yasake sharewa yace "Kaga Zara'u itace y'ata ta farko, tunda yarinyar nan tazo duniya bata tabajin dadi naba ni Mahaifinta, bana saya mata kaya, kaya irin nakowace yarinya budurwa datake tasowa, Zara'u bata tabamin korafi ba kokuma tace saina mata, yarinyar nan bata taba bude baki ta tambayeni abuba, kotamin korafi kotanunamin bacin rai, banmata kayan salla, bansiya mata takalmi, babu abinda nakema Zara'u sabida bandashi, yarinyar nan bata taba yimin kocemin Baba yimin kaza ba, yarinyar dake tausayin mahaifinta nake wahalarwa haka gashi yanzu ma datake rashin lpy nakasa mata komi, wlh ban cancanci zama mahaifint........" kafin Yakarasa maganan Dr ya tsugunna da sauri yakai hannunshi kan bakinshi hakan yasa Baba yay shiru yana kallon kyakkyawan fuskar Dr dake sanye da glasses, cikeda tausayi Dr yajanye hannunshi daga bakin Baba ganin yadan natsu yana kallonshi, hakanan yaji Baba ya mugun bashi tausayi, ahankali yace "Sir ba'a magana haka, Allah daya baka yarka yasan ka chanchanci zama mahaifinta ne saisa yabaka ita a matsayin y'a, sanan aganina godiya yakamata kama Allah daya baka y'a irin wanan wanda tun anan duniya take jinķanka, and just because bamu bama yaranmu abinda yakamata mubasu ba, or bamu wadatasu da kayan alatun duniya ba ba doesn't mean we are not good fathers to them, karka kara magana haka Sir, I know yarka na alfahari dakai, and stop crying, yanzu dai nawane kudin magungunan"? Ahankali Baba yace "8150 sukace" gyadamai kai Dr yayi sanan yamike tsaye yakai hannunshi bayan wandonshi wallet dinshi yaciro yabude yazaro wasu kudade yan dubu dubu dashi kanshi baisan yawansu ba ya tsugunna, hannun Baba yakama yasaka kudaden aciki yace "jeka sayo magungunan kazo mufarama yarka treatment ko" yay maganan yana sakinma Baba coolest smile dake comforting any kind of heart, wani natsuwa Baba yaji ya shigeshi tareda sake rike kudin da kyau yana kallon fuskan Dr ya nisa zai bude baki yay magana wayan Dr dake aljihun lab coat dinshi yahau ringing ciro wayan yayi yana mikewa tsaye yana gani inda ake kiranshi yatashi da sauri yajuyo ya kalli Baba yace "get magungunan now ka kawomin she's convulsing again" da gudu yajuya yabar wajen shima Baba sake damke kudin yay gam gam ya tattare su folder yatashi yay pharmacy harda gudun shi.
Da sauri yatura kofan yashiga dakin nurses kusan uku ke kanta suna kokarin tura mata wani abu abakinta sabida yanda ta taune hashenta kadan har yana jini daya daga cikinsu tace "wai where is her father da magungunan"? Karasawa inda suke Dr yayi yana kallon yanda bakinta ke jini yace "me aikinku? Ya akayi kuka bari tajima tongue dinta ciwo"? Yay maganan yana grabbing kumatunta da kyau ya karbi abin yasa abakinta sanan ya karbi alluran dasuke bashi yakara pushing a jijiyanta cikin sakan daya tadena convulsing, hakan yasa yace "are the test result not ready"? Bashi wata takarda sukayi hakan yasa ya karba ganin result dintane zai duba daidai lokacin Baba yashigo dakin da mugun saurinshi yana kallon Zara ganin jini abakinta yasa yabude baki zaiyi magana da sauri Dr ya karbi magungunan da folder daga hannunshi yana mikama nurses yace "Baba she is fine yanzu zamu fara treatment kaje waje kajiramu kaji" fita Baba yayi adimauce yarufe kofan dakin dawowa ciki Dr yayi yahada kayan yazo yamata fixing drip sanan yahada wani allura wanda shi a duwaiwai zai mata sanan yarufe yazo ya tsaya akanta, fuskanta yadan kalla wanda zai iya cewa kusan sai yanzu ne yakalleta da kyau yarinyar ko ta mugun kama da mahaifinta itama farace kall kaman shi, ahankali ya ijiye alluran sanan yakai hannayenshi yadaura kan hannunta yadan juyo da ita ahankali ta side, riganta yadan daga sama kadan idanunshi ne suka sauka akan farar fatar jikinta kaman na jaririya ga dan gashi kadan kadan sun kwanta sunyi lub, hannunshi yasake kaiwa yadan ja zaninta hade da pant dinta kadan sanan yashafa spirit kafin ahankali ya chaka mata alluran motsin dayaji tayi yasa yadan waigo ya kalli fuskarta gani yayi ta yatsine fuska cikin bacci, cire alluran yayi yamika ma nurse din ta karba tasa a bola, sanan yajuya yace "ku tsaya da ita I will be back in the next 15min" yafice daga dakin Baba na ganinshi yatashi yace "Dr yatake"? batare daya kalleshi ba yace "muje office dina" binshi Baba yayi har zuwa office dinshi zama yayi tareda nunama Baba kujera Baba ma yazauna yace "meke damunta Dr naga jini abakinta" dan murmushi yayi yace "wanan ba matsala bane taune hashenta tayi kadan, I called u ne danna fadamaka I don't think zamu sallami yarka yau, result yafito tana dauke da maleria da typhoid masu karfi wanda sune ma kesata wanan convulsion din, gakuma ciwon mara at least zamu iya riketa na kwana daya ko biyu haka" shiru Baba yayi yana kallonshi cikeda damuwa, murmushi Dr yayi yace "karka damu zanyi settling hospital bill din wanan kudin hannunka ka rike na abinci dawasu abu ko" shiru Baba yayi saikuma chan ya nisa yace "Ya sunanka likita" anatse yace "sunana Imam Naseer Marafa" girgixa kai Babba yayi cikeda gamsuwa, yace "kaidan aljanna ne Naseer, Allah yamaka albarka, Allah ya saka da alheri da taimako na dakayi, azamanin nan da wuya ake samin likitoci irinku, awanan zamin likita iyaka kabiya yay treating naka, idan baka biyaba babu ruwan shi, Allah yamaka abinda kakeso kaji Naseer" shiru yayi yana kallon Baba kafin ahankali yace "Ameen nagode sir" Tashi ahankali Baba yayi yace "bari nabaka wuri" gyadamai kai kawai yayi Baba yawuce yafita, bin bayan Baba yayi da kallo yay shiru kaman wanda ke tunani kafin ya fuzarda iska ahankali ya jingina da kujeranshi tareda lumshe ido dan yagaji sosai.
Bude kofanshi da akayi aka shigo yasa yabude ido kadan ya kalli kofar, wata female Doctor ce mace kyakkyawan gaske doguwa tana sanye da atampa golden da dige digen pink ajiki, ta yana kanta dawani pink gyale chiffon plain bakomi ajiki saikuma lab coat dinta fari kal yasha guga sai kamshi take bazawa wajen aljihun ta an rubuta Dr Zee ajiki, maida idanunshi yayi ya lumshe ganin itace, karasowa ciki tayi taja kujera tazauna tace "Dr Helper koma Dr Charity zankiraka am here i need help too pleaseDr" dan yatsine fuska yayi alamun he's not into her silly talk, murmushi tayi tace "okay joke apart Dr Imam, I just came in, namanta da stethoscope dina agida kuma idan HOD yaganni wlh zansha fada, please kindly aramin naka kaji kasan Helper is your second name right Dr nice" tai maganan tana kallonshi tana murmushi cikada tsokana, ahankali yabude idanunshi kadan yadan kalleta saikuma ya yatsine fuska yace "wai why are all this intern Doctors not serious haan"? Dan murmushi tayi, hakan yasa yadaure fuska yace "ina magana kina murmushi, alright go and find stethoscope awani wajen not here" da sauri cikin kara narkan da murya kaman zatai kuka tace "no fa, ni wlh badakai nake ba" ganin yaki kulata saima wayanshi daya ciro yana kunnawa yasa tace "kasandai idan HOD yakamani bani kadai zaiyi scolding bako dan ai yasani akasan kane" dagokai yayi ya kalleta baison surutu idan kuma akwai macen dayataba gani aduniyan nan datafi kowa surutu is this girl, baimasan mesa HOD su yasata under him ba, dan gajeren tsaki yaja strictly yace "tashi kidau stethoscope daga that drawer and get out of my office Zeenat" yay maganan yana mata pointing drawer dake facing su a other side of the office wall, tashi tayi ahankali tai wajen drawer tana kara nanata yanda yakira full name dinta yau, ahankali ta sanya hannayenta taja drawer tabude taciro wani sabon stethoscope mai kyau blue tadauka sanan tamaida drawer ta juyo ta kallai gani datayi yasake lumshe ido kaman mai bacci yasa murya chan kasa tace "thank you Dr Imam" sanan tadaga kafa tai hanyar kofa harta murda kofan zata fita sanan yace "Dr Zeenat" da sauri tajuyo tadan bude manyan idanunta da mamakinta jin yakirata, folder yamika mata yace "this my patient tana Emergency, monitor her, I've written everything anan idan time yayi push d injections ma left hand veins dinta, i repeat left hand, idan any complications arise give me a call, idan kuma condition dinta yay stabilising move her to ward, zanje gida yanzu under no condition should u leave his hospital saikinga dawowana" kaman zatai kuka da sauri tace "waimena maka daga zuwana zaka hadani da irin aikin nan, yanzu harsaika dawo zan tafi? Inada bridal shower dazanyi attending fa by 5pm" tai maganan tana batarai sosai, dauke kai yayi yashiga tattare kayanshi tana tsaye tana kunkuni, lab coat yacire yarage dagashi sai kananun kayan dake jikinshi yadau wayanshi da car key dawani folder yazo zai wuce ya watsa mata wani mugun kallo, hadiye maganan tayi tareda sunnar da kanta kasa dan jitayi yacika mata ido bazata iya kallonshi ko cigaba da korafin ba yawuce yafita yabarta tsaye anan, takai kusan 2min dukan kirjinta bai dawo daidai ba sanan tasamu tabude kofan tafita har lokacin kamshin shi takeji.*
💫 _DISASTROUS LOVE_💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍️M SHAKUR
_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
EPISODE 6️⃣
_FREE PAGE_
Fita yayi direct zuwa parking lot, motarshi yabude ya shiga yatadata yawuce yafita daga asibitin, agaban wani Baban gida a GRA yay horn ko sakan biyu ba'a dauka ba aka bude gate din yasa kan motar ya shiga ciki, packing yayi zai fito mai gadi daya rufe gate din yataho dagudu yace "angaida likita, Baban ka likita, Mamarka likita sannu ka da zuwa dan Alajin naira Alaji mai mutane nakowa" cikeda gajiya yasakamai key motarshi a hannu kaman zaiyi kuka yace "Ohhh i am not in for this your kirari Musa yau, ga key nan grab my things ka kawomin side dina and lock my car" yay maganan tareda juyawa yawuce abinshi, tsayawa Mai gadin yayi yarike kugu yakai yatsarshi daya kan kanshi yana tunani saikuma chan yanisa yace "wai ni da likita yaketamin yaren nan yadauka nima likitan ne yau, memawai yake nufi" "cha yayi ka kwashe kayan daya bari amota ka kaimai flat dinshi sanan karufemai mota" da sauri yajuya jin zazzakar murya na magana wata doguwar yarinya ce dabazata wuce 19 , 20ba, tana sanye da doguwan rigan atampa kanta a tsafe bama'a tajeba daga gani tsifa ake mata, harara mai gadin yaballa mata itama ballamai tayi tace "kazami kawai" da sauri yace "wlh saina hadaki da likita" gwalo tamai tajuya takoma flat dinsu shikuma ya shiga kwashe abinda akace ya kwashe sanan yawuce yay wani flat da shikadai ne daban agidan, sallama yayi tareda bude kofa yashiga ciki, falone hadadden gaske kal kal sai kamshi yake komi na dakin off whitene, shiga ciki yayi yana kalle kalle yace "dadina da likita akwai tsafta, kaga daki kaman nakara mai da yaji akai na ci tsabagen ban sha'awa" ijiye komi yayi kan centre table din sanna yawuce yafita yana kara waigen falon.
Sosai yabata lokaci sanan yafito yana sanye dawani short H&H 3quater milk color, yasanya wata black plain t-shirt, wanan karan babu glasses akan idanunshi hakan saiya kara bayyanar da kyawun kwayan idanunshi dasuke nan farare kal kwayan idon kuma bakake kirin, silipas yasaka sanan yabude kofa yafice, Baban flat din gidan ya shiga, wasu yan matane su uku ne a falon suna zaune suna kallo, suna ganinshi kowacce ta natsu atare suka gaidashi "Ya Imam good afternoon welcome" gyadamusu kai kawai yayi yace "how come banga ku fara shirin islamiyya ba" karaman cikinsu mai 19yrs din wacce ake kira da Rayyana ce tace "Ya today is Thursday fa" gyadakai yayi yace "oh okay, where's Ammi"? Kafinma subashi amsa sukaji murya datadan manyanta ance "anya akwai randa Imam zai iya dawowa gidan nan bai tambayi maman shi ba, ai kaga abinda yasa nafiji dakai kansu wa'è" tanuna babban cikin yara matan mai suna Rahma tace "su yaran Babansu ne" dariya yayi daidai ta sauko ya rungumeta hannunta takai kan cikinshi tace "zokaci abinci oya oya, cikin nan babu abinci cikinshi" dining takaishi tazubamai abinci a plate sosai yaci abincin yay nak sanan yafara mata hira, aduniyan nan Ammi kadai yake hirada ita kaganshi awani waje zaka dauka bai magana ko dariya.
Yatsine fuska yayi yace "Amma wlh nagaji da aiki at this government hospital, narasa maisa Dad baiso nai aiki a hospital dinshi" murmushi Ammi tayi tace "ai duk Dr dabai aiki a federal government hospital ba baida experience, watarana zakaga abinda yasa Babanka choose that 4 you son, banda haka is just the matter of time ko" yatsine fuska yayi yatashi yamika hannu yadau cup din fresh juice yace "Ammi bari naje nadan kwanta, by 5 kitadani pls, 6 zan koma clinic" binshi tayi da kallo yawuce falo, kannin nashi ya kalla yanda suka natsu suke kallon zeeworld yace " kunyi salla"? Kasa amsashi sukayi saidai kowannensu yashiga tashi ahankali gudun karya makesu sukai stairs da gudu, girgixa kai kawai yayi yawuce yafita daga flat din zuwa nashi.
****
Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai tanadan yatsine fuska ganin haka yasa da sauri Baba dake zaune kan kujera gabanta yakai hannunshi kan kumatunta dakeda wani irin laushi kaman na jariri ya shafa taredakai fuskarshi yana leken idanunta datake kokarin budewa yace "Zara'una, Fatima Zara bude idanunki nine Babankine, ganinan taredake" ahankali take bude idanunta jin muryan Baba sama sama saikuma tabude idanun tass tadaurasu akan fuskan mahaifinta tanajin wani irin ciwon kai amman bakaman nadazu ba (safe). Jin hayaniya sama sama yasa taware idanunta duka da kyau ta kalli inda dake, karfe tagani da ledan ruwa kafin tabi igiyan da kallo taga yana hannunta sanan ta waiga tana kalle kalle ganin suna wani babban daki dake dauke da gadajen marasa lafiya guda goma side dinta biyar opposit dinta ma biyar, yanda take kalle kalle yasa Baba yace "kina asibiti ne an kwantar dake" juyowa tayi ta kalli Baba kafin tayi magana Dr Zee data gama duba patient din kusada gadon Fatima ne takaro fuskarta cikeda annuri tana kallon Fatima data bude ido tace "ahhh yar gatan Baban ta kin tashi"? Dayake Zee akwai surutu ta kalli Baba tace "Baba Zara'unka ta farka ka barni nahuta yanzu, kasa naduba maka ita ko baccin lafiya take dazu yafi sau dari" sanan ta kalli Fatima tace "Zara bara infada miki wani abu Babanki nasonki sosai sosai da ace haka iyayen kowa ke sonsu haka da yara basu wahala aduniyan nan ba daduk munji dadi" dan murmushi tayi dudda ciwon kan dake cinta murmushi yasa dimples dinta suka lotsa sosai dasauri tace "auuuuu Baba yarinyar ka nada mugun kyau jibi wani cute dimples dasuka bayyana akumatunta dudda batada lafiya, Baba kuyan wani garine dan Allah"? Tai maganan tareda juyawa taja kujeran next bed dake gaban na Zara takawo gaban gadonsu kusada Baba zata zauna dantaji labari taji andaka mata tsawa. "What do you think you are doing Dr Zee"? Ba Zee kadai ba har Baba, Fatima dama duka yan ward din saida suka dagokai duk suka waigo, Dr Imam ne, yana sanye da black cover, black trouser, sky blue short sleeve t-shirt daya bayyana muscles dinshi manya