Showing 21001 words to 24000 words out of 150358 words

Chapter 8 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt

M Shakur   

07 Jan 2025

15366

bari naje na dauro alwala nai salla gwara ke aurenki da gata for now Allah ya yafemiki" murmushi tayi saikuma tamata gwalo irineh din jedai kiyi, Maryam tafice daga dakin tana dariya tace "dadin abin nimadai nakusan zuwa nawa hutun sallan" samin kanta tayi da tunanin maganganun Maryam saikuma tai maza ta kawarda zancen daga zuciyanta, ranan wuni tayi tareda Maryam har Magrib itama Abida batai kukaba dan tasami tuwo taci takoshi tai nak sai wasa take abinta sunama Maman su Maryam barna adaki itada kannin Maryam, koda takoma gida taga Baba na nan baifita ba suna hira shida Mama ta gaidasu Mama ta dauki Abida itakuma tawuce daki.








Washegari Asabar batabar Baba yaje ko'ina ba bamata barshi ya zauna shi kadaiba sabida batason yay tunanin abin, sai wajajen 9 nasafe suka fita ita dashi sukai kasuwa tare suka sayo kayan gwanjo riguna masu kyau kala biyar dogayen wanduna jean burguza burguza kala biyar, sai kito sabo da cambas na gwanjo guda daya, da ganamasgo da fatar kwaikwadon kan Bald cap, da fatan kunne da silkin dokin dakomima sanan suka dawo gida wajajen karfe daya suka shiga uwardakan su da kayan bata bari Baba yaje mallaci ba sukai salla adaki already yara duk sun dawo gida since abincin rana sukaci suka koma aiki, saida sukaci abincin da Fatima takawo musu sanan Mama ta kalleshi tace "lokaci yayi kira yarka muyi maganar anan uwar dakana" gyadamata kai yayi abin tausayi muryanshi har wata yar dishewa tayi ya kwalamata kira. "Za.....Zara, Zara'u, Zara" dag daki ta amsa da "na'am Baba" fitowa tayi tazo ta tsaya agaban dakin batare data shigoba ahankali yace "shigo" sallama tayi ta shiga dakin tasami waje tabakin kofan ta zauna akasa tace "gani Baba" shiru yayi yana kallonta duka duka yaushe yarinyar nan taji sauki dahar zai iya mata wanan maganan ganin yakasa magana sai kallon yarinyar yake kaman yauya fara ganinta yasa Mama ta kalli yarinyar tace "Fatima ayanda mahaifinki yawahala dake aduniyan nan inhar kika kasa rufamai asiri awanan bakin yanayi dayake ciki wlh sai Allah yay mummunan ykamaki, tun kina yar shekaru biyu mutumin nan yake wahala danya sami kudi yaciyar dake" Mama tai shiru tana kallon Fatiman dataga bata gane komiba kan zancen datake fadi, Mama tace "lokacin dakika gama Js3, zaki shiga SS1 wato shekaru uku kenan dasuka wuce lokacin muna wanan tsohon gidan damuke ada, Babanki fatara ta isheshi baida hanyan samin kudi yasakaki a school gashi har anfara first term kina zaune damu agida, wata kawata mai suna Razika tare muka taso tai aure mijinta Lawyer ne amman karamin lawyer yana kiranta da Madam hakan yasa sunan yabita, muna cemata madam, akwai wasu lauyoyi da mijinta kema aiki, suna taimakama musulmai ta hanyar basu bashi kona miliyan nawa kakeso kekona biliyan nema zasu baki sanan babu interest, ayanda suka baki kudinsu ahaka zaki mayarmusu dashi batare dakin kara musu ko ficika ba, su kalan tasu yanayin taimakon kenan, sanan idan kika karba keda kanki zaki fadi ko shekara nawa, wata nawa koma dai yaushe kikeso ki biyasu kudinsu bak sharadin dayane duk randa kika fadi zaki biya back ranan zaki biya, idan ranan tazo baki dashi akwai abu biyu kodai su kulleka agidan yari kokuma kabada danka namiji babba yaje yamusu aiki zasuyi calculating sufadi maka albashin danka misali suce alabashin yaronka dubu dari duk wata to haka yaron zaiyi aiki harna watananin dazai daukeka kudin dasukebin ubanka yakare, but duk randa uban yasami kudin zai iya kiransu yabasu adawo maka da danka cikin koshin lafiya, danaji wanan labari mai kyau dan tunda nake arayuwata ban tabajin wanan kalan taimakon alheri hakaba, aduniyan nan yanzu ko kawarka tabaka aron kudi saita cemiki idan kin juya zaki dawo mata dashi ki kara mata wani abu akai, amman wanan kam ga makudan kudi ko nawa kakeso sanan kaida kanka zaka fadi ranan dazaka biyasu back babu ko anini asaman kudin da gudu nadawo na sanarda mahaifinki duk wanan bayanin dana miki nidashi muka shirya na kaishi wajen mijin madam Oga Abdu, yamana hanya dan irin kudin nan sai kanada hanya kanada kafa, yamana hanya aka saka sunanshi cikin masu neman bashi akace za'a nemeshi l, bayan kwana bakwai aka kira babanki aka dauki information dinshi, Mijin Madam ya tsayama Babanki amatsayin guarantor na Babanki kuma witness na babanki dan bansan kowa yasani asan bashi mukaci, aka kirga miliyan uku cash yan sababbin dubu dubu aka bama babanki yadawo da miliyan uku cash a hannu gida, kafin yadawo bayan anbashi kudin yarikesu a hannu aka tambayeshi yaushe zai biyasu instead yace shekara goma ko shekara ishirin ma bayaga miliyan ukuba sai kawai yafurta shekara uku shima kaman wawa yadawo gida yake gayamin shekara uku yace kinga fadan dana mishi saikuma na share muka biyamiki kudin makaranta kika fara ss1, kanenki ma haka, muka chanza gida, yasai machine ya gayaramana daki yasai mana katifu kujeru da komidai dakika gani na wanan dakin ahaka kudi suka kare wanda har yau dadan ragowan chanjin muke rayuwa yanzu haka gobe ne ranan biyan bashi ko bada d'a Fatima ko akulleshi, ke yarinya ce Fatima mai basira ilimi dakuma fikra kinsan Habib yay karanta daza'a kaishi aikatau, Habib baidama hankali balle ya tsare kanshi saisa ubanki ya yanke shawaran kezaikai amman zamu maidake namiji" tunda Mama tafara maganan kanta akasa sai alokacin ta dago kanta ta kalli Mama shima Baba ita ya kalla sabida shairin dayaji tamai, wani mugun kallo tama Fatima tace "kobazaki rufama mahaifin naki asiri bane butulu? Dakuma nace maidake namiji ba ina nufin nane miki tsuliya ko yanke miki mama nake magana ba a'a zadai mu boye hallitunkine, ga kayan damuka siyomiki nan na maza" tanuna mata ganamasgon sanan tace "ke kinsan bantaba miki karya ba, inhar baki yardaba kulle ubanki za'ayi kuma kinsan mahaifinki baida kowa dazai iya biyamai miliyan ukun nan, saidai agana mishi azaba agidan yari karshenta ma akashe shi achan, kafin yay signing duk angayamai sharuddan nan kuma ya yarda ya amsa, idan yanzu suka tafi dake aikatau din zai dage da nema Oga Abdu yamin alkawari zai samomai aiki dudda baiyi makaranta sosai ba zamu dage nima zan fara sana'a cikin wata biyu ko uku mubiya mu madawo dake, zaki iya hakuri kiyi rayuwa namiji ki boye macen ki aciki na watanni dabasufi uku ba dan rufama wanan mahaifin naki daya miki komi asiri? Mahaifinki dake wahala dake tun kina yar tatsitsiya ya raineki shi kadai mutuminnan, yay achaba, yay faskare, yay leburanci duk sabida ke, yanzu lokaci yayi dazaki nuna mishi baiyi haihuwan banzaba kema yar halak ce zaki iya"? Ahankali ta kalli Baba dataga kanshi akasa dan hakanan yaji ayau yana kunyar yarshi bai chanchanci zama mahaifinta ba, tuna tun tana yarinya yanda yake wahala da ita tayi da wanan rashin lafiyan datayi, dakuma yanda yakeda hawan jini, aduniyan nan da'a kulle mahaifinta gwara an kulleta so dubu, da mahaifinta ya tozarta aduniyan nan gwara ta to tozarta sau dubu, da'aci mutuncin Abban ta gwara acinci nata, da ubanta yamutu gwara ita ta mutu, da Baba yasha wahala gwara tasha wahala. Cikin fushi Mama tace "kinmin shiru" ahankali takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata tace "Mama babu abinda bazan iyama Abbana ba koma menene aduniyan nan, zanje zanyi aikatau din koda Baba bai sami kudiba zanyi aikin koma na tsawon shekara nawane dazai dauka bashin yakare, Baba kadena damuwa kaji karka fara ciwo" tai maganan ahankali tana kallon Baba dayaji jikinshi yadawo kaman kankara, wani hadadden murmushi Mama tayi tace "kaga yarinya yar albarka maison mahaifinta, duk diyar data rufama iyayenta asiri Allah zai rufa mata itama, cikin dare zan tadake na shiryaki anjima zamuyi kitso, dau kayan gwanjon kije ki wanke kinji ki shanya su bushe yauko mekikeso ninezan dafamiki dakaina yar albarka, me zakici"? Murmushi ta kakalo ta girgiza kanta tace "bakomi" cikeda farinciki Mama tace "ai ina saina saimiki tsiren dare yau" daukan ganamasgon tayi tafita dashi kayan tacire tadau omo ta tafi makwarara wanki, Mama ta kalli Baba dahar lokacin kanshi akasa tace "dalla me haka sokake tadauka akwai wani abu akasa ne iyye saki ranka jor mutuwa zatayi komene nifa banson haka, tashi kahau gado muyi baccin rana" tashi yayi yahau gado haka dan dolenshi tasashi yay bacci.




Wanke kayan tayi tass tana kallonsu itace yanzu zatasa wanan kayan mazan wandunan ma kaman sun mata tsawo dayawa, komawa tayi daki ta zauna, itakuma Mama saida ta tabbatar Baba yay bacci sanan tafito tace "xomuyi kitson" babu musgunawa haka Mama ta zauna ta zuba mata zane yan kanana masu kyau gashi har tsakiyan bayanta data gama ta tupke bakin gashin tace "cikin dare zamusa hulan fatan, nasiya miki always dayawa zan saka miki a kasan jakan duk wata karki bari kowa yasan kinayi kitafi da magungunan ciwon mara karki sake kibari asirinki yatonu dan kashe babanki za'ayi kinga yanda baida lafiya hawan jini yamai raga raga" kaman ba Maman data sabada itaba yau tsabagen dadi zama tayi tana koyama Fatima duk yanda zatayi harda koyamata muryan dazata dinga yi da kalan tafiya dakomima ranan bata bari tai girki ba ita tayi.










Cikin dare Mama tashigo ta tadata ahankali gudun karsu tada yara fitowa falo sukayi Mama ta zaunar da ita, tasanya mata bald cap dinan bayan ta zuba gum da ake sa bald din dashi ta shigar da gashinta tass ciki abin yabame bam gashi tasayo daidai kalanta fari sabida farace, kan yay kato amman ba chan chan ba, sanan tasamata fatar daya rufe hujinn kunnenta shima, cikedajin dadi Mama tace "tashi ki kalli kanki a madubi" ahankali ta tashi taje ta tsaya gaban madubin falonsu tana kallon kanta badadan atampan dake jikinta ba zaka rantse namiji ce ita, ahankali tadaura hannunta ta shafa saikon kannata hawaye taji zasu zubomata hango Baba datayi ta madubi yafito ya tsaya abakin kofa ya rungume hannunshi yana kallonta yasa tahadiye kukan tajuyo tareda murmushi tace "Mama yay kyau nayi kaman Habib ko" dan dariya Mama tayi tamika mata kallabinta tace "ungo daura karki bari su Habib suga kan, da sassafe gobe zan kadasu hadda karfe tara zaku tafi keda Babanki jekiyi kwanciyarki" wucewa tayi ta shige dakinsu itakuma Mama ta watsamai harara tace "wuce ciki" ciki yayi ba musu, daren cikinsu babu wanda ya runtsa ita Mama farin ciki yahanata Bacci zata rabu da ķaya Allah yayi fatanta Allah sa nan gaba agane mace ce asirinta yatonu su kasheta tahuta gaba daya dan ta tsani yarinyar nan, Baba kuma damuwa ainun yasan yacuci yarshi sosai, guilt yahanashi ya runtsa, itakuma Fatima kuka tayi sosai na tausayin Babanta yanzu bazata gansu ba sainan da wata uku, tana tausayin Babanta sosai tana addu'a Allah yabashi aikin yi sabida karyaje yasake karbo wani bashi dazai sakashi a matsala irin wanan.




Tun karfe biyar Mama ta tashi tadaura girki tana gamawa ta tadasu Habib tamusu wanka, kowa yafito yay wanka bakwai daidai ta kadasu babu yanda sukaso suka tafi haddan tun kafin 8, tacema Fatima taje tai wanka wanka tafitayi hakan yabata daman balbale Baba da masifa kan yasaki ranshi, hakuri yabata sanan ta barshi Fatima nafitowa daga wanka Mama tabita dakinsu.






Yau duk yanda takejin kunya saida Mama taganin mata nono, silkin doki Mama ta dauka da akama igiya ta bakunan guda biyu tace "kullum wanan zaki dinga daure nonon ki dashi sabida kar agansu" nannada mata tayi sanan ta daure tamau harsaida tai yar kara sabida azaba takasa tsayuwa da kyau, Mama tace "ahaka zaki rufama baban naki asiri tsaya da kyau jor" tsayawa tayi da kyau da kyar Mama tace "sannu duk idan zakiyi bacci kidinga kwancewa kadan" sanan tabata singileti tasaka sanan takawo rigan mazan navy blue shirt mai gajeren hannu tasaka Mama ta kulla boturin ba laifi nonon sundan boye sabida rigan dama burgujeje ne baka ganinsu sanan tasaka Jean din daya mata yawa mama ta nannade kafan suka kama kwankwason jeans din da igiya, sanan Mama tabata kamvas tasaka, Mama takoma baya ta kalleta batada banbanci da namiji kaman irin yaran nan maza da yanzu suka fara balaga dinan, kawai kyaune da ita sosai ga pink lips na bala'i which is normal daman sunsan babanta kakkyawa ne jini fulani da buzu ce yarinyar, ran Mama shar ta kwalama Baba kira tace "zokaga diyarka" shigowa dakin yayi shima ya shirya kallo daya yamata yadauke kai yawuce yafita, Mama tace "yanzu saka hijabi sabida kar yan gidanku su gane sai kunyi nisa sosai saiku cire babanki ya karba yaboye" hijabinta tasaka har kasa, Mama tahada mata jakanta fess saikuma tabata jakan goyon makarantan Habib tazuba mata abinci a flask tasa mata cinyan kaza da biskit guda biyu, da ruwan gora dakuma lakasera guda daya, karba tayi tana godiya, Mama ta kalli Baba daya zauna tace "tashi kutafi takwas da rabi" tashi yayi yawuce yafita Mama bata damuba tadau jakan tarike suka fito ta kwalama yan gidan kira tace "Fatima zataje hutu wajen Baabarta" sallama suka mata Maman Dady tabata 200 suka mata rakiya har waje, Baba yajuyo yana kallonsu agaban machin tasamai gana masgon itakuma tahau baya tana rikeda jakan Baba yatada machine din suka tafi.






Tafiya mai nisa sosai sukayi kasancewa hotel din dazasu da nisa dan hanya fita daga kano ne, sunyi tafiya mai mugun nisa sanan yay parking akan hanya ya sauka itama ta sauka hannunta yarike suka shiga wani uncompleted building dake kan hanyar har lokacin yakasaa kallonta, suna shiga ta kallai ahankali tace "Baba hijabin ko"? Da sauri ya gyada matakai yana juyamata baya, ahankali tacire hijabin tarike a hannu tana kallon bayanshi tasan yadamu hakan yasa ahankali tazagaya ta gabanshi ta kalleshi gani tayi idanunshi sunyi jajir kaman wuta, ahankali tace "Baba menene?" Kaman jira yake saukar da guiwowinshi yayi kasa ya rike hannuwanta biyu fuskarshi yadaura kan kafafunta baitaba kuka ko hawaye gaban yaranshi ba amman wanan karan yakasa daurewa saiga hawaye sharrr da sauri ta zube akasa itama ganin fuskarshi da hawaye yana kuka yasa tafashe da kuka sosai zatai magana yadaura hannunshi kan bakinta cikin wata irin murya mai rauni sosai yace "Fatimatul Zara'u kiyafeni, ki gafarceni, ki yafema mahaifinki, tunda na haifeki baki tabajin dadina aduniyan nanba, niba uba nagari bane, jibi abinda nasa kika zama, namaidake namiji sabida kawai na rufama kaina asiri, Fatima na cutardake dayawa aduniyan nan, dan Allah kiyafemin, kiyafema Babanki" wani irin kuka takeyi tashiga girgizamai kai tace "Baba kaine uba nagari dana sani aduniyan nan, da ace akwai wata rayuwa bayan wanan still kai zan zaba kazamto mahaifina Baba, kaizan saba danni kaina nasan I am so lucky da Allah yabani kai amatsayin ubana, Baba dan Allah kayakuri kadena kuka, bakamin komiba kaji, koma kamin nayafe maka duniya walahira nima kayafemin Baba" kamota kawai yayi yarungumeta tafashe da kuka sosai ajikinshi ta kankameshi dan yasa taji wani iri yanda taga Babanta nakuka, sun dade sosai ahaka sanan tace "Baba tashi mutafi zamuyi latti" tana maganan wayanshi na ringing sakinta yayi yana duba wayan yaga Oga Abdul ne bai daukaba ya maida aljihu yatashi tareda karban hijabin ya share mata fuska sanan ya ijiye hijabin awajen suka fito yahau machine itama tahau yatada suka shiga titi, tunda tai wayau bata taba fita ba hijabi ba ballema har ba dan
Kwali yau itace iska ke daka yana ratsa tundaga kanta, kunnuwanta da wuyanta haka, haka suka karasa hotel din mai suna Prestigious, yana shiga yaga Oga Abdul yaci suit sai kallon agogon dake daure a hannunshi yake, yana ganinsu yataho dagudu murya chan kasa yace "kayi latti sosai sokake kasamu a amtsala" ya kalli Fateema yace "good, from now sunanki Khalid understood" gyadamai kai tayi, yace "any question dasuka miki answer them da turenci, sukaga u are educated zasu yanka miki albashi mai yawa nan da nan agama biyan bashin babanki" tasake gyadamai kai, ya shiga gabansu da saurin shi yace "let's go" jikinshi har rawa yake hakan yasa taji gabanta na dukan uku uku, shiga hotel din sukayi sukai upstairs, wani babban hall suka shiga ga security guards gardawa aciki, hall ne da aka jera kujeru hadaddun gaske, ga maza manya magidanta amman irin talakawan nan haka kusan su 100+, ga yara samari maza agefe dabazasu wuce sa'oninta ba zuwa yan 22yrs suma zaune kan kujeru adayan bangaren kusan su 63 ko morethan ma, saikan hadadden stage din da akai decorating da flowers aka zuba wasu arnayen kujeru wasu hadaddun manya manyan lawyers ne da baristoci sunci suit suna rubuce rubuce ga laptops agaban su, da printers, kallon Baba Oga Abdul yayi yace "kujirani anan lemme talk to them nazo dan ankira sunanka yafi sau uku" stage din yayi zuwa wajen wani babban Barrister dan tsoho nema dukawa yayi yamai magana a kunne sanan yadawo yaje wajensu Baba kujera yanuna musu yace "kazauna za'a kiraku" zama Baba yayi yana rikeda hannun Fatima itama ta zauna a kujeran kusada shi, saishima Oga Abdul yazauna kusada Baba yace "yanzu nan police suka tafi dawani mutumi thank God kayi tunani mai kyau da....." "Muhammad Alhasan Muhammad" shiru Oga Abdul yayi jin ankira Baba, faduwa gaban Baba yayi haka itama Fatima dan yanzu saitaji tanajin tsoro sosai dan ga dukkan alamu wanan babban organization ne baba yaci kudinsu duk azatonta tazaci is just a small something, hannun Fatima yarike sukai stage, cikeda girmamawa ya gaida lawyoyin da duk suka zubamai ido suna kallon yanda danshi yay kama dashi, yace "yallabai bangama hada kudin ba amman ga......" kafin yagama maganan Barrister ya kalli Fatima yana gyara glasses din idanunshi yace "young Man akwai turenci" gyadamai Fatima tayi ahankali, yace "whats your name" gyara muryanta tayi ba yabo ba fallasa dudda muryam baiyi kaman na namiji ba hakama baiyi kaman na mace ba tace "ahhhm Khalid Muhammad" ajiyan zuciya Oga Abdul ya sauke, Barrister yace "how old are you"? Anatse tace "i am 19yrs old" documenting sukayi sanan yace "what level are you in school" ahankali tace "I just write waec this year" gyadamai kai yayi yace "what are you good at Khalid? What can you do what are your skills?" Shiru tayi saikuma ta kalli Baba taga kanshi na kasa sanan takalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login