Showing 108001 words to 111000 words out of 150358 words
Chapter 37 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
dawani kayan baccin a leda tamikama Fatima tace "ungo kema Mum dinki ta aikomiki da sabo" murmushi tayi ahankali sanan takarba tace "thank you" Granny tace "kina gama komi ki kashe wuta ki kwanta" gyadama Granny kai tayi ahankali, Granny tace "saida safen ku" atare suka mata saida safe, sanan tawuce bayi ta tahada ruwa tamata wanka da hadadden shower cream din dake bayin sanan suka fito ta shiryata cikin kayan baccinta ta kwantar da ita akan gado taja bargo tarufa mata ahankali tace "nima bari naje nayi" bayin tawuce tai nata wankan da ruwan zafi sosai tana karajin dadin jikinta sanan tadauro alwala tafito daga bathroom din tana kallon Amna dataga tai bacci, dan murmushi tasaki taje tabude kayan baccin, normal pj ne dogon wando da riga mai kamada t-shirt amman gajeren hannu yanad taushi sosai, hijabin dake kan sallayan tai tahau tai nafila sanan ta tashi ta linke dadduman takarasa takashe wutan saiga hasken wayanta dakuma ringing atare hakan yasa ta kalli screen din wayan dataga an rubuta Imam ajiki.
_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp
_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHuMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
✍🏾 M SHAKUR
EPISODE 5️⃣7️⃣
Saida gabanta yafadi dasauri takarasa gudun kar wayan yatada Amna tazare wayan daga chargy tama rasa mezatayi kawai tadaiga tai picking call din taga alamun yana kirga mata secs, ahankali takai wayan kunnenta tai hannunta nabari jin shiru yasa tacire wayan ta kalla ganin har lokacin call din nanan yasa takara kai wayan kunnenta ahankali tace "h......hello" tai maganan tana tashi ta kwanta akan gado ahankali tanajan bargo tana rufe kafanta, dan lumshe ido yayi yana gyara zama akujeranshi na office dan night yake, ahankali yace "Fatima" murya chan kasa kaman mai tsoron magana tace "uhm" saikuma tai shiru jin yayi shiru yasa ahankali tace "ina yini" ahankali shima yace "ya hanya? Kukai lafiya"? Murya chan kasa tace "lafiya lau" saikuma suka sakeyin shiru for so long hartana ciro wayan daga kunnenta ganin still call din is on yasa murya chan kasa tace "Thank you" ahankali taji yasauke ajiyan zuciya yace "for"? Alamun tambaya dan yanaso yasatai magana, only magana ne zaisa tasaki jikinta ta manta d past life dinta, murya chan ciki kaman tana tsoronshi tace "for bringing me to Baaba" tai shiru saikuma ahankali kaman tana shakkan fadi tace "and for giving me a family" murmushi yayi dahar saida taji sautin murmushin yace "you are welcome Fatima" suka sakeyin shiru saikuma chan yace "kinga Baffa na, da Mum da Amna" murya chan kasa tace "eh" saikuma chan tace "sunada kirki" dan murmushi yayi yace "ina Amna"? Ahankali tace "gatanan" murmushi yasakeyi yace "I guess kinyi sabon kawa kenan, saikin gaji da magana" dan murmushi kadan tayi dayasa yaji dadi dan yaji sound din murmushin, ahankali yace "take care, jeki kwanta" kaman yana ganinta ta gyadamaikai sanan ahankali tace "nagode Ya Imam" lumshe idanu yayi sanan yabude su ahankali tareda katse wayan.
Janye wayan tayi daga kunenta ta ijiyeshi agefenta tajuya takife akatifa sabida hasken, sanan tai shiru tareda lumshe ido. "Ya To....bi" tafadi amugun hankali saikawai hawaye taji ya gangaromata daga idanu, tuna last ganinshi datayi jiyane sama sama yayi butu butu ya lalace kaman bashiba sama sama taga yana kuka yana jijjigata daganan batakara sanin inda kanta yakeba tadai tashi taga kanta a kano. Kife kanta tayi a filo tana kuka dabazama ta iya tantance namiye ba she is happy Allah yafitarda ita daga kangin wahalan nan nagidansu Tobi, yanzu she's back Allah yahadata da masu sonta but wani bangare na zuciyanta na wishing takoma gidan badan komiba saidan kawai taje taga Tobi, ayanda take ayanzu har cikin ranta jitake shikadai kawai zatagani taji she's fully happy. Kasa hakuri tayi tai kuka sosai sanan bacci yay nasaran kwaceta.
Karfe biyar daidai ringing wayar ya tadata harsaida ta firgita dan bata saba da wayaba, bama ta taba wayaba, daukan wayan tayi ganin Dr Imam ne yasa takara a kunnenta ahankali, cikin a very calm and light voice yace "tashi kiyi salla, lokaci yayi" murya chan kasa tace "uhm" sanan yakatse wayan, ijiye wayan tayi ta tashi ahankali tareda kunna wuta ta kalli Amna yanda yarinyar ke diban bacci abinta tai lakur a bargo sanan tawuce tashiga brush tayi da komi tadauro alwala tafito daidai ana bude kofan dakinta Granny ce ganin tana fitowa daga bayi yasa tace "kin tashi Diyar kirki" gyadama Granny kai tayi, Granny dake rikeda da charbi tace "ok" xata juya tafita saikuma tadawo tace "namanta ban fadamiki ba banda tsarki da ruwan sanyi, ga bayi nan akwai ruwan zafi muddin akwai wuta kome kikayi kidinga tsarki da ruwan zafi kinji" ahankali tace "to" sanan takalli Amna dake baccinta sanan tawuce tafita tarufo mata kofa, hawa kan dadduma tayi tai rakatanil fajiri sanan tai sallan asubahi data idar tai azkar tai karatu sanan tashiga addiua Allah yacire mata kunci da damuwan datake ji aranta, wajajen 6:30 tagama komi tacire hijabi tafito tana sanye da kayan baccin dogon wando da riga peace sunmata kyau kanta nacikin hula tafito, kitchen din falon tashiga tadauko tsintsiya da paka tazo tabi falon nan tamai hadadden gyara sanan tabishi da mopping, showglass na turaren daks falon tabude tadauko turare da burner datagani ta kunna turaren sanan takashe komi datai amfani dashi tawuce kitchen saida tafara gyra kitchen din dabaiyi datti ba sanan tashiga store tana kalle kallen abinda zata dafa, wake tafara debowa ta wankesu tass ta jika aruwa sanan tadauko Irish tasami waje ta zauna tashiga ferewa kana ganinta kasan ba yarinya me kiwuya bace saida tagama sanan ta yayyanka, ta tashi tawuce tanika waken da attarugu da albasa a blender tasa ruwa kadan sabida karyay ruwa, tana gamawa tajuye a bowl sanan tasa mai aruwa tazuba Irish din itakuma takoma gefe tashiga bubbuga kosan, tanayin haka tana tashi idan Irish yasoyu ta kwashe tazuba a hadadden kula, bude kofan kitchen din akayi chak Granny ta tsaya tana kallon yanda tazauna kan wata yar karaman turmin dake kitchen din tana bubbuga kosai, salati tayi tace "oh ni yarsu waya saki aiki haka Zara keda yakamata ki koma bacci" murmushi tayi tace "dan Allah Granny karki hanani nizan dunga girki" dan jim Granny tayi saikuma tace "ai shikinen" tashigo kitchen din tace "ai bakyayi uban aikin nan ke kadai ba, mezan tayaki"? Make kafada tayi tace "ni wlh kitafi" yanda tai maganan ashagwabe yasa granny tai dariya tace "to tunda ankoreni nida kitchen dina natafi, wanan abinci dayawa yake zan hana mamanki girki duk anan zasuzo ayi breakfast din" tawuce tafita tana murmushi, kafin nine tagama komi ga hadadden kosai bushashe, ga Irish da egg sos lafiyayye, saikuma kunun tamba wanda shikadai tagani yasa tayi saikuma ruwan shayi lafiyayye dayaji kayan kamshi tajera komi a dinning ta ijiye plates cups dakomi sanan tawuce ciki Granny namata sannu da aiki tace "yi sauri kiyi wanka kifito muyi kari yanzun nan su Mamanki zasu shigo" shiga dakin tayi ta tarar da Amna kan dadduma tana salla hakan yasa ta wuce bayi tana watso ruwa tasaka wani black second gown wanda Rayyana tabata sabo sanan tafice ganin Amna bataciki, a dinning dukta samesu har kasa ta tsugunna tagaida Mum da Dad duk suka amsanata da fara'a Mum tace "wanan hadadden breakfast haka da kyar fa nadaure nakosa naci wlh" murmushi tayi akunyace kanta akasa tace "mezan zuba miki Mum da Dady" duk murmushi sukayi Mum tace "a'a zauna abinki lemme serve ni" zubama mijinta kosan tayi da kunun danshi yakeso, itakuma tazubama Granny kosan da Irish tazuba musu duka sukahau ci shiru kakeji, Granny dai takasa hakura ta kalleta tace "Zara wayakoya miki girki haka"? Murmushi tayi tace "tun ina karama nakeyi" gyadakai duk sukayi Mum tace "diyartawa ta isa aure Granny" awani irin kunyace da gudu tatashi tai ciki duk suna dariya Granny tace "yooo kujimin y'a daga maganan aure to bazakiyin bane" Dady ya kalli Mum dake dariya yace "kinga yanzu kin hanata cin abincin ta" da sauri Mum tace "oya small Madam zokibi Anty ki da abincinta" tashi Amna tayi Mum tahada mata abincinta a tray Amna ta dauka tawuce ciki duk sukai dariya suka cigaba da breakfast dinsu, tass suka cinye kosan Irish ne kawai yarage sanan Dad yatashi yace "natafi office Sweet Mum, saikun dawo karkuyi dare by 4 ya zamto kuna gida" sanan yaciro bandir din kudi yan wrap na 1k sababbi guda shidda ya mikama Maman tashi yace "kumata siyayya harda na hostel" Granny tace "ga Mamanta nan ni kana bani I inme dasu ita tasan meza'a saya ai" harcikin ranta Mum kejin dadin yanda Granny kemata kara sanan ahankali tasa hannu ta karbi kudin tace "Allah amfana Dady" dukowa yayi yamata peck agoshi yace "bye wife" Granny ta harareshi batare datai magana ba dariya sukayi dagashi har Mum din sanan yace "kicema Amna natafi tunda tamanta dani, yau bazataje hadda ba" da sauri Granny tace "saidai gobe dukanmu zamu fita yau" baice komiba yawuce yatafi, Mum da kanta ta kwashw kayan abincin tashiga kai kitchen daidai lokacin Zara tafito kanta akasa ta karbe na hannun Mum tawuce dasu kitchen Mum tacema Granny baritaje ta shirya ta tafi da Amna danta shiryata itakuma Zara tagama wanke wanken sanan tatafi daki.
_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp
_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHuMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
✍🏾M SHAKUR
_Erotic Ideas group na matan aure zalla ne, group ne damuke program guda HUDU aduk sati, ranakun sune ALHAMIS, JUMMA'A ASABAR da LAHADI._
_Duk ranan Alhamis munayin program mai suna MARRIAGE LIFESTYLE, wato ZAMANTAKEWAN AURE, inda nakema mata lectures kan yanda ake zama da miji dakuma dabarun zama da miji, ranan jumma'a kuma muna program din damuke kirada TALK & HEAL wato yi magana ka warke, inda matan aure zasu gayamana matsalolin dasuke fuskanta agidajen mazajen su, zasu iya turamin ta pc idan basuson asansu nisainai forwarding group mu taimaka musu da shawarwari dakuma dabarun dazasubi su magance wanan matsalolin, sai ranan asabar shine ranan LECTURES, inda zan dauki darasi dake dauke da dombin ilimi abu wanda ya dace mata su iya dangane da aurensu, mu koya musu ayi magana akai sosai, sai ranan Lahadi zamuyi lectures akan ilimin daya danganci yanda zaki gamsar da mijinki sanan ki gamsar da kanki, kisaka mijinki ihu agado yana kururuwa yana sambatu, mukoyar dake yanda zakiyi spicing up sexlife dinki, and yanda zaki dinga rayuwa da mijinki kullum kaman sababbin aure._
_Idan kinason shiga wanan group din zaki turo 2000 to 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din, wata daya ne group din, idan kinason ki cigaba da zama duk wata dubu dayane 1500 ne subscription, sababbin zuwa kuma new member zakiyi register is 2k ne, don karin bayani zaki iya tuntubata a number ta 07012181461_
M Shakur ❤️
EPISODE 5️⃣8️⃣ & 5️⃣9️⃣
Shopping sukaje mata mai suna shopping ba muna shopping ba, sun saimata tsadaddun kaya kowani atampa ko lace ko material zasu saimata saisun sayamata gyalenshi da takalmi da jakanshi, jaka irin na yan mata ba manya manyan nan ba hadaddun gaske, gyaluluwan ma na yan mata medium itadai binsu da ido take Mum da Grandma ganin basu siyamata hijabai ba, manyan akwatuna suka saimata na kayanta na lv, sanan akaje bangaren undies aka saimata bras size dinta da pant da kayan bacci but irin decent kayan baccin nan dazaka saima yarka mace yawanci masu dogayen wanduna, saikuma masu short wanduna iya guwiwa da gowns, saikuma suka sainata abaya kala biyar awajen UMNA ABAYA, hadaddu sanan suka gama shopping kayan sawa, saikuma akaje bangaren school materials hadadden school bag na goyo, math mathset, calculator, jakan byro da pencil, sanan suka saimata mattress size na gadon makaranta, buckets plate spoon babu abinda basu saimata ma har jeep dinsu yakasa kwasa saida suka hada dawata motar haya dasukai shatta, sanan Mum ta tsaya tasai musu ice cream itada Amna da some other pastries ko saloon din barinshi akayi dan 3 tayi suka tafi gida, aka sauke komi gateman na kwasansu zuwa bangaren Granny, duk suka tafi ciki sukai salla sanan saiga Mum tashigo bangaren Granny, Granny kadaice a falo tanajan charbi Mum tace "Granny ga telan nan zuwa" ko gama fadi baiyiba taji ana sallama mai gadi zai fadi bako yazo tafita tace "ashigo dashi" shigodashi akayi har side din Granny, sanan Granny ta kwalama Zara kira, Auwal Tela shine maima gidansu dinki baya wasa dasu dan suna biyanshi biya na haukama saisa dazaran Mum takrashi yake zuwa, Zara tanunamai tace "Auwal y'ata nakeso ka dingama kaya, nasan kayan dayawa bazaka iya gamasuda wuriba but please kayi dayawa this week sabida makaranta zata tafi idan kagama sauran saika kawo suma" da sauri yace "to Hajiya" Mum tanunamai Zara tace "aunata, kowani kaya kamai style din daya kamata idan riga da skirt ne kokuma doguwan riga kawai kafitomin da yarinya" dasauri yace "angama hajiya" tape dinshi yafito dashi daga aljihu sanan yazo inda Fatima take ya shiga aunata yana rubutawa a book saida yagama tass sanan Mum tace "kawomai kayan Zara" fitoda manya manyan jakunkunan tayi one by one guda biyu dake cikeda kaya Auwal ya karba, Mum kuma tabashi 100k tace "kafara" har kasa yayi yana godiya yace "nagode Hajiya, sai anjiman ku" yawuce yafita yana murna sosai, Zaara kuma itama ahankali ta tsugunna gaban Mum da Granny dake zaune kujera daya tace "Granny, Mum, nagode dakomi Allah yasaka da alkhairi" kanta Mum tashafa tace "kidena min godiya, idan Babanki dai yadawo kije ki godemai".
Ance wayansu bala'u nafaruwa dakaine idan akwai alkhairin dazai faru dakai, yanzu Fatima take ganin ashe zata taba haduwa da mutane dake sonta haka, Mum tamaida Fatima kaman yarta kuma bawai sone dan taga Granny ba kodaya sone kawai Allah yadaura mata sabida taga yarinyar nada natsuwa gason aiki barinma girki, saisa duk rand zatai girkin yan gayu zata aika tazo suyo tare dan taga yanda zatayi Granny kuma bakaramin jin dadi tayiba, tuni Auwallu tela yakawo mata dinkunanta about kala 15 agoge, da Mum tasa tagwada sun mata cip cip dadas ajiki takusan sumarda Auwalu dakudi yakara mata alkawari nanda next week za'a gama duka.
Abangaren Imam kullum saiya kirata dare da safe yatadata tai salla, dudda bawani magana takemaiba but yakan tambayeta abu, Amna nason Zara ko abin kaman magic itama Xara nason yarinyar sosai, Kaka dai hankalinta kwance yanzu kawai Ibrahima suke jirada admission letter ta.
Karfe biyar yau Dady yashigo gidan parking yayi yafito, bangaren mamarshi yawuce direct, Granny yasamu a falo da matarshi suna hira ganinshi yasa sukai shiru da hiran dasuke Granny tace "kadawo Maza" akan kujeran datake yazauna sanan yabude file din hannunshi yaciro wani takarda da aka rubuta admission letter akai sanan yamikama Granny yace "amshi Grandma saiku shirya mata komi, ranan gobe da yamma zamu kaita makaranta sabida ranan Monday dasafe tanada class, anbata admission na national diploma a Health Information Management, sune suke managing all hospital record, suna coding and indexing, suna statistics da sauran su, idan tagama ND zata iya amfani da result din tai applying direct entry tashiga university idan kuma batason course din xata iya next year tasake jamb, but course din nada kyau shita samu" da sauri Granny tace "yo ai babu course din banza aduniyan nan, barinma bangaren lafiya data samu, Allah maka albarka Ibrahima Allah sa kagama da duniya lafiya" tai maganan tana bama