Showing 12001 words to 15000 words out of 150358 words
Chapter 5 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
manya, idanun nan nashi sanye da fararen glasses, gashin sajenshi sunyi lub lub sai uban kamshi yake zubawa hannunshi rikeda lab coat bairiga yasakaba yana kallonta babu wasa ko daya akan idanunshi, tsit kakejin dakin kaman ba'ai hallitta awajen ba, ahankali tahadiye miyan dataji yabushi abakinta dakyar ta iya dauke idanunta akanshi ta kalli agogo 6 na yamma daidai maisa batai tunanin lokacin dawowan shi yayiba taketa surutu, kasa magana tayi ta tsaya awajen chak, nan kakejin kus kus awajen masu jinya na daman ta ishemu sai shegen surutu ga Oganta nan ai yashigo, wasu na kus kus suna su basu taba ganin likita mai surutu hakaba wasu na ai kaman yar makaranta ce batariga tazama likitan bama, jin kus kus din dayan ward sukeyi yasa yahadiye fushinshi dan baiso ya disgata as it is yanzu ma was so embarrassing balle kuma yamata fada hakan yasa yace "go and wait 4 me in my office" da sauri ta gyadamai kai ta tako har zuwa inda yake abakin kofa tawuce tabi ta gefenshi tafice.
Yadan dauki kusan 1min sanan yakaraso ciki yawuce gadon Fatima inda yaga Zeena ta tsaya alamun anan take, yana karasawa kafinma yay magana Baba yabashi hannu yace "barka da zuwa likita" "ina yini Baba yamai jiki ta tashi"? Da sauri Baba ya kalleta ganin idanunta a lumshe yakira sunanta yace "Zara'u tashi bude idanunki Dr yazo dubaki" adan hankali Dr Imam yace "barshi tukunna sai Nurses sun mata wanka an chanza mata kaya taci abinci sanan zanzo naduba ta, Nurse" yakira biyu daga cikin nurses din ward din yamusu magana da yaren da Baba bayaji sanan yawuce yafita, tadata sukayi cuka cire karin ruwan, kasa tsayuwa tayi hakan yasa suka gunguro wheelchair.
Sosai take cije lips kaman zatai kuka sabida yanda takejin azababben ciwon mara har suka kaita bayin, daya daga cikinsu ne tadawo tace "ina kayanta Baba" da sauri yanuna musu yar karaman jakan daya sawo mata kaya, dauka tayi tawuce bayin da taimakonsu tana bala'in jin kunya suka mata wanka da ruwan dumi suka gyarata suka saka mata wani sabon pant da pad, wani aikin sai nurses all hail to our hospitals nurses, you people rock, Allah yabiyaku ladan aikin dakukeyi Ameen!!!.
_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
Wani doguwan bakin riga taga Baba yasayo nata babu gayu ajiki kana gani kasan mai araha ce amman tai kyau sosai, sai wani pink hula shima mai kyau daya kara haska fuskarta, sai kallon rigan take da idanunta dasuke juya mata, dawo da ita sukayi suka dagata suka sata akan gado shikuma Baba yabata shayin daya kadamata kasa karba tayi hakan yasa yace "sannu kinji" gyadamai kai tayi ahankali tanajin kuka, kaimata shayin yayi baki tadan kurbi kadan ko kadan bakinta bayamata dadi sai kallonsu suke yan ward din ana mamakin yanda Babanta ke dawainiya da ita, ba mamanta ba, wasu na halan batada mahaifiya ce daman gashi tai kama da Baban nata kaman yay kaki yatofar, gasu kyawawa kaman bayan Nigeria ba. Sosai tasha tea sanan tace ya isheta ijiyewa yayi sanan yace "indomie da kwai fa nasayo miki" dan yasan tanason indomie sosai, girgizamai kai tayi ahankali tace "zan kwanta Baba" da sauri yace "a'a bari kihuta kadan saiki kwanta likita ma zaizo yadubaki sanan za'a maidamiki da karin ruwan" gyadamai kai tayi kawai, ganin batajin dadi yasa yadau pilon gadon yasa ya jinginar da ita, dan murmushi tamai dan taji dadi shima murmushi yamata, ahankali tace "Baba yaushe kasayomin wanan rigan? Ina hijabi na"? Ahankali yace "dazu nasayo miki gashi tamiki kyau, kibar hijabin likita yasa aka ciremiki baga hula akanki nanba, kiji sauki tukunna" gyadamai kai tayi tana kokarin lumshe ido gabanta ya yanke yafadi da saida tadan zabura ta tashi daga jikin filon ta dafa kirjinta da sauri Baba yace "menene amai kikeji"? Yay maganan yana rike hannun data daura akirji zatai magana sukaji mutum akansu da sauri ta daga kanta da manyan shanyayyun idanunta dake cikeda zazzabi suka hada ido likitan daya dakama wanan macen likitan tsawane saidai yanzu yasa lab coat, kaman yanda take kallonshi haka shima yake kallon kwayar idanunta, Baba dake tsaye kusada itane yace "Likita barka da zuwa" batare daya janye idanunshi ba yace "barkada yamma Baba" yay magana yana tura hannu cikin aljihu yaciro wata yar touch light mai kama da byro yadan taka zuwa gaban gadon, jitayi kirjinta yacigaba da faduwa sosai da sauri ta janye idanunta ta saukesu akasa tareda sa hannu takama rigan jikinta tawajajen cinya ta rikegam, ahankali yajanye nashi idanun shima ya kalli Baba yace "Baba kadan bamu wuri zamu dubata" da sauri Baba yace "to" zaro manyan idanunta tayi dasauri kwalla yataru a idanun tabi Baba da kallo harya wuce yabar wajen nurse din dake tareda shine rikeda tray din injections tace "ba cinyeki zamuyi ba yanzun nan muna gamawa zai dawo kinji" gyadamata kai tayi ahankali idanunta na shining sabida kwallan daya cikashi, batare daya kalli nurse dinba yace "ja labule" jan labulen daya zagaye gadonta tayi na both side dana gaban gadon hakan yasa babu wani na cikin ward dazai iya ganinsu, ahankali yakai hannunshi zai kama habarta da sauri taja kanta baya, dan dariya nurse din tayi tace "matsoraciya" wani kallo yama nurse din hakan yasa tai shiru tana hade hannayenta biyu alamun sorry sir, juyoda kanshi yayi yasake zubama Fatima shanyayyun idanunshi yakai hannunshi for the second time ahankali zai kama habarta komar da kanta baya tasakeyi shar hawayen kwayar idonta na dama ya zubo na haggun shima yacika fam yana shirin zubowa, da yatsa ta nuna nurse din tace "k....ki.....ra....min Baba dan Allah" sai alokacin Nurse din tasake magana tace "toki tsaya Dr yadubaki bazai daukemu 2min ba sai Babanki yazo" bayan hannunta takai ta share hawayen sanan ta saukar da hannun tasake kama jikin riganta kanta akasa, ahankali for the third time yakai hannunshi yakama habarta yadago da kanta sukai eye to eye, hawayen kwayar idanun haggunta ne suka zubo sharrr sukabi kumatuntu sukai wuya.
_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128*_
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
_WANAN LITTAFIN IS 500 IDAN KINASO KIBIYA SAINA SAKI A GROUP, HAR YANZU INA FREE PAGE, 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK_
_FOR BUSINESS PROMOTION KO ADVERT CHAT ME UP ON WATSAPP 07012181461_
✍️M SHAKUR
_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
EPISODE 7️⃣
_FREE PAGE_
Toculan hannunshi ya kunna yana kallonta still, ahankali yabude bakinshi kaman wanda baiso yabude softly yace "stop crying" gyadamai fuskarta dake hannunshi tayi yana kallonta tahadiye kukan gabanta na faduwa sosai, haska duka idanunta biyu yayi sanan yasaki habarta yace "meke miki ciwo yanzu"? Kasa jure kallon dayake mata tayi tasake saukar da kanta kasa murya chan kasa tace "kaina" "damene kuma"? Dagokai tayi ta kallai saikuma tasake sauke kanta kasa takasa magana, karban folder hannun nurse din yayi sanan yace "raise her gown cover her legs with the bedsheet" sanan yajuya musu baya yana rubuce rubuce abinshi acikin folder ta. Fashewa tayi da kuka ganin yanda Nurse din ta kwaye mata riga ga namiji awurin, riganta har saman cikinta, saitaja bargon gadon tarufe mata cinyoyinta har zuwa kasan maranta, tundaga cikinta har maranta abude sanan tajuyo tace "angama Dr" ahankali yajuyo yamika mata folder yana kallon cikin nata dayay lakur kaman batacin abinci sai maranta dayadan kumburo, handglove yasaka sanan yakai hannunshi yataba maran yakalli fuskanta motsi yaga tayi tareda runtse udamunta gam alamun tanajin zafi, ahankali yace "zafi"? Murya chan ciki dake rawa sosai danduk a birkice take jin namiji nataba mata ciki tace "eh" dagowa yayi yadauki kwalaben allurai 3 dake tray injection da nurse din takawo ya fasa ya zuko alluran a syringe guda biyu da karami da babba sanan yadaga alluran sama yana saitawa kaman ance tabude idanunta tabude alluran data gani yasa tawani irin tsandara ihu. "Babaaaaa! Baba wlh naji sauki kazo mutafi gida ni kar amin allura" da sauri yajuyo ya kalleta kwaye zanin da aka lullube ta dashi tayi tawani zabura zata sauka hannu daya yasa yariketa dan faduwa zatayi tana tashi yamikama nurse din alluran, kokarin kwace kanta tayi tafashe da kuka sosai tace "wlh wlh naji sauki ku kiramin Baba mutafi Allah kuwan, inkanama Allah karkamin alluran nan dan Allah Doctor, dan Allah dan Allah" ayanda take kuka take rokonshi he could feel her fear tundaga heart dinta and is not a good condition ama patient allura haka, da hannu daya yariketa yakai hannunshi daya kan bakinshi yana kallonta yace "shiiiiiiii inbakiso namiki alluran kiyi shiru bake kadai bane a ward dinan ba am I clear"? Gyadamai kai tayi tana wani irin nishi tana neme nemen alluran taga batagani ba, hakanan saiyaji tana tunamai Rayyana haka take itama batason allura, juyawa yayi ruwan goran daya gani kan kantarsu yadauka yamika mata yace "sha ruwa and calm down" yabude mata goran tareda bata karba tayi takai baki tana kalle kalle kurba tayi kadan tabashi da idanu yama nurse alamu taje ta bayanta, ahankali yace "ya isheki"? Gyadamai kai tayi yace "to kwanta" yanda yake mata maganan sosoft ysata natsu, kwanciya tayi ahankali yaja zani yarufa mata kafa batare daya kalleta ba, hannunshi yamika ya karbi allura daya yace " ki kalli bakina kome nafadi kifadamin test zanmiki okay inaso nagane daga wani lobe ciwon kanki ke zuwa" gyadamai kai tayi, ahankali yake mata wasu alamu da baki yakai alluran yamata daya gabaki daya batasani ba dan haka Allah yayishi baida zafin hannu ko digi, yamata dayanma, murya chan kasa yace "mena fadi"? Ahankali tace "banjiba" murmushi nurse tayi tace "cewa yayi yagama miki alluran" tanuna mata empty syringe din, da sauri takalli syringe din saikuma ta kalleshi abinma mamaki yabata, danharara yasakin mata yace "katuwa mai tsoron allura" ahankali tasaki murmushi dan yanda yace katuwar was a bit funny, da sauri yadauke kai yakama hannunta yamaida mata da karin ruwan sanan yawuce yafita daga wajen aka yaye labulen nata ya shiga duba sauran patient din da Zeena bata dubaba tai shiru tana binshi da kallo tanajin ciwukan datakeji ajikinta na sauka kadan kadan tana mamakin inda Baba yaje saikuma tai tunani yatafi salla, juyowa Dr imam yayi yakalleta kaman ance ta kalli gadon dayake hada ido sukayi da saurinta ta dauke kai gabanta nafaduwa kawai saima ta lumshe ido.
Wuraren 10:30 nadare yagama komi zai tafi, fitowa yayi rikeda jakan laptop dinshi a hannu, hanyar ward dinsu Fatima yayi, awajen kofan ward din ya tsaya yana kallon ciki batare dasun lurada shiba danbai bude kofaba, yanabi bed by bed yana kallo haryakai gadon Fatima, zaune ya ganta Baba yasa filo abayanta yana rike da plate da indomie keciki da soyayyan kwai yana ganin plate din yagane namai shayin gaban hospital dinsu ne, indomie Baba yadeba da cokali zaikai bakinta, makemai kafada tayi tadan turo baki idanunta dake cikeda ciwo sukadan juya ahankali tace "ni Baba nakoshi" da sauri Baba yace "yakuri ci wanan shine na karshe, aini bansan akwai ciwon dazakiyi ki tsani indomie kiba, oya ci ci ci Zara'una" yakai cokalin bakinta yana mata murmushi, washe cute white teeth dinta tayi zata bude baki tai magana Baba yasamata indomie aciki dariya tahauyi tana taunawa shima Baba yahau dariya yace "yaushe aka haifeki yarinya bagashinan kinci ba" batarai tayi tana taunawa saikuma tahau dariya ahankali dan bata da karfi.
Ahankali yasaki dan murmushi yana kallonsu yana tunani who ever says money shine happiness karyane, happiness kauna ce, just look at this father and daughter gwanin ban sha'awa. Kaman ance Baba yajuyo yaga Dr Imam tsaye da hannu Dr Imam yamishi alamu dayazo batare da Fatima ta gansu ba, tashi yayi ya ijiye plate din yace "ina zuwa Zara'u" hanyar kofa Baba yayi hakan yasa ta kalli kofan hada ido sukayi da Dr Imam da sauri ta dauke kai, abakin kofa Baba yasameshi yabashi hannu suka fara tafiya sukai hanyar waje Dr yace "Baba daman i wanted to see you kafin natafi ne, akwai abinda nakeson na tambayeka" da sauri Baba yace "menene likita"? Dan jim yayi kaman wanda baison yin maganan saichan yace "Baba naga tabon duka, fresh shaidan bulala ajikin Zara'u, waye yamata wanan dukan Baba?"
_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_
Shiru Baba yayi yakasa cewa komi yama kasa cigaba da tafiya hakan yasa shima Dr ya tsaya kaman mai nazarin shi saichan ya nisa yace "Baba shirun dakamin ya tabbatar da kasan wanda yamata dukan kenan wanda nina tabbata bakai bane, ayanda naga kakeson yarka nasan bakaine zaka mata wanan dukan ba, Baba yarinyar nan bama wanan dukan bane na farkon dukan da aka mata ba dan jikinta da tabo dayawa, koma waye ke dukanta Baba hakkinka ne amatsayin ka na mahaifinta ka kareta, ka tsareta, mace ce tanada rauni sosai, abu kankani zai iyasa rayuwar ya mace yabaci dan haka dole ka kula, idanma rashin ji take bada duka zaku gyarata ba ai" ahankali Baba yace "bantaba ganin salahar yarinya mai biyayya irin Fatima ba, ko kadan batada rashin ji sai dumbin biyayya da girmama nagaba da ita" Shiru Dr Imam yayi yana kallon Baba ahankali yace "mahaifiyarta ke dukanta"? Girgizamai kai Baba yayi yace "batada mahaifiya" shiru Dr yayi saima yakasa magana, ganin haka yasa Baba yace "ni fulanin Maiduguri ne, mahaifiyarta buzuwar Maiduguri ce amman dukanmu dagani har mahaifiyarta rainon kauyene muba yan burni bane, a kauye mukai aure muka kuma tare cikin dangi da yan uwa da abokan arziki harta haifamin diyata Fatiman nan dakake gani ayau, bazan manta ba, lokacin Fatima nayar shekara biyu da watanni zan fita kiwo da safe tahau kuka zata bini, haka takemin and muddin tabini tosaina siya mata plantain chips da ake saidawa a bakin gari nadawo da ita gida sanan zata barni nafita kiwo, haka na dauketa nace bari naje nasaimata wanan plantains chips dinan abakin express sabida tanason abin sosai, kauyenmu nakan express road ne na zuwa asalin cikin garin Maiduguri, kuma masu saidawa anan bakin titin kake ganinsu (hawkers) na dauketa namata makawuya da nufin innaje nasayo mata mukoma nafita kiwo, muna fita bakin titi nakira mai plantain zan siya mata, na karba daya nasa mata a hannu nasa hannu zan ciro kudi a aljihu nabashi bangama cirowa ba mukaji wani irin kara da girgizan kasa dabansan lokacin dana dauki Fatima data rusa ihuba na kankame ajikina, kafin kasani naga ana ihu ana gudu, ga hayaki wuta natashi daga cikin dajin dana fito...." yadanyi shiru tareda lumshe ido, yanda Baba yay shiru yasa yagane end of the story, ahankali cikin wata murya dazai nuna asalin damuwa yace "Allah ya jikansu" ajiyan zuciya Baba ya sauke yace "Ameen, hadadden bomb yan boko haram sukai amfani dashi suka tada kauyenmu tass wai warning sukama gwamnati, dagani sai Fatima muka rayu a kauyen mu gabaki daya dasu bomb din yatashi dan safiya ne basuriga sun fita ba, nida Fatima mun wahala aduniyar nan, neme neman aiki, kwadago, da leburanci shine yakawoni nan Kano, inda nasami wata baiwar Allah matar nada kirki sosai tabani machine ina express tana tayani rainon Fatima dan tanason Fatima sosai matar Fatima ke kirada Baaba, yaranta duk suna waje, da aikin danake nasamu nahadu da wata budurwa dake saida mana da abinci a tasharmu na yan achaba Rukkaya, naji ina sonta namata bayanin kaina tace taji tanaso na, nadauki Fatima na kaimata tanason Fatima sosai, Fatima na yar shekara biyar mukai aure, Hajiya tabamu yarmu tabarmin machine din cewa zasubar Kano, ranan Fatima tai kuka amman ta hakura, a kasan waje take zama bata cika dawowa Nigeria ba, amman duk intazo Fatima na zuwa wajenta" ahankali yace "step Mum din Fatima tamata dukan nan"? Gyadama Dr kai yayi ahankali saikuma yace "da farko dana aure Ruka tana bala'in son Fatima sosai, dayake bata haihu dawuri saida mukai kusan shekaru biyu Fatima na shekara bakwai ta haifi Habib to daganan kaman asiri son datake ma Fatima yakoma ki, kodan taga son danakema Fatima mai karfine oho, bawai bansan sauran yarana bane a'a kawai dai son Fatima dabanne araina, sabida tun tana yar yarinya take wahala bata taso gidan gatan uwa ba kona kakanni duksun rasu, ina matukar tausayama Fatima, yanda kuma nake sonta haka Fatima take sona, ko ciwon kai yakamani yarinyar nan saikaga kaman zata haukace sabida damuwa, ina iyakan kokarina wajen kareta, ni kaina bansan da dukan ba sai dazu danaje gurin aikinsu d'ana Habib a samin iska a machine yake gayamin ai dukan da Mama ta mata yatada mata da ciwo" Ajiyan zuciya kawai Dr Imam yasauke sosai yaji Baba yabashi tausayi ainun, ahankali yamikama Baba hannu yace "Baba ka koma wurinta saida safe, gobe idan nazo taji sauki zan sallameku saita cigaba dashan magani, ka kulada ita" gyadamai kai Baba yayi Dr yawuce yatafi yabar Baba anan tsaye, Baba yadade tsaye awajen yana wani irin dogon tunani, da