Showing 6001 words to 9000 words out of 150358 words
Chapter 3 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
yadauke hannunshi yace "innalillahi Ya Faty bakida lpy in tada Baba"? Girgizamai kai tayi, cikin muryanta da ba'aji sosai tace "dagani na zauna" hannunta datake mikamai yakama yadagata ta zauna da kyar tana share hawaye tana cizan baki, sosai yaji tabashi tausayi, yanason Ya Faty kaman ba gobe dan tamafi kulada su kan uwarda tahaifesu, tun suna yara itane komi nasu, duk in yanajin yunwa saidai in Ya Faty batada kudi amman saita bashi yaje yasai wani abin, idan basuda lpy, Mama nafita kome sukeso saita dafa musu suna gamawa su wanke tukunya ta yanda Mama bazata saniba, ganin yanda hawaye yakasa dena zuba daga idanunta yasa yakoma kusada ita ya zauna kanshi ya daura kan hannunta yafashe da kuka ahankali gudun kar ajisu murya chan kasa yace "Ya Faty kiyakuri kinji Allah na sama yana kallo wata rana sai labari, Mama batada kirki kuma batason ki amman kinga duk ranan dana girma zan daukeki daga gidan nan nasai miki wani gida nasai miki mota nasa police nace musu karsu bari Mama ta shigo balle ta dakeki kota saki kuka, I promise idan na girma ko maganan banza babu wanda ya isa yafada miki kinji, kidena kuka, bari na girma kiga abinda zai faru kidena kuka" yay maganan yana share hawayen dake zubomata, danne kukan tayi takai hannunta ta sharemai hawayen shi shima tana murmushi tace "ninasan kanina soja ne, Habib dina, nasan idan Habib ya girma ko kallon banza babu wanda ya isa yamin, Habib dina sojana toko tubambale mayen abinci" dariya yahauyi kaman bashine ke kukaba, murmushi tamai tace "jeka koma baccin ka kaji" da sauri yace "kinji sauki"? Gyadamai kai tayi alamun eh, tashi yayi yawuce ya kwanta awajen shi yace "dazaran yacigaba ki kirani kinji" Tom ta amsashi ahankali, kwanciya yayi tareda kashe toculan, sai alokacin taji ashema hiranshi rahama ne agareta wani mahaukacin ciwone yakamata dayasa taji kaman zata kurma ihu amman ta daure tarasa inda zata saka kanta taji dadi, har aka kira asubahi idanunta biyu, har aka tashi tanaji Baba yabude kofa yafita yadawo amman takasa koda motsi.
**
_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_
Wuraren shida nasafe Habib yaji wani irin nishi da sauri yabude ido ganin gari yay haske yasa ya kalli katifar ta da sauri ganin Ya Faty kwance tana wani irin nishi kaman wacce ake fizgema numfashi yasa yawani irin kwala ihu. "Ya Faty!!!" yatashi da gudu yay kanta, ganin jini akan gadonta yabaci jikinta yabaci Ya Faty dabaka ganinta babu hijabi amman wanan karin zaninta wuri guda, yar under skirt dinta baki iya cinyan ta ne kadai yarage ga fararen cinyoyinta sun baci da blood yasa Habib ya kwalama Mama kira. "Mama! Mama! Baba! Babaaa!!" dawani irin sauri Abba yadiro daga gado dagashi har Maman suka fito jin yanda Habib ke kwala musu kira, Abba ne yariga shigo dakin Mama biyeda shi, kafinma Abba yay magana ganin Fatima yasa yay kanta da sauri yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, maiya sameta Habib? Ke Zara'u, Zara'una Baba"? Gabaki dayama batasan inda kanta yakeba daukanta Baba yayi yasata ajikinshi yana jijjigata yace "ke Zara'u, kallen, nine nine meke damunki"? Cikin kuka Habib yace "tun cikin dare naji kukanta, jikinta yay zafi tahanani tadaku ni bansan meke mata ciwo ba" dagokai da sauri Baba yayi ya kalli Ruka dake tsaye inda take yace "Ruka huramin wuta kisa ruwa tai wanka mutafi asibiti" hararan shi tayi tace "ai hala kasayo itace ne" da sauri yace "to saman mini awajen makota dan Allah" tsaki tayi tace "kaima kasan abinda banyi kenan rokon makota saidai ni suzo suyi maula wajena, Um ni kaga tafiyata ku karata" tawuce tasakin musu labule tai gaba abinta, rasama abinda zaiyi yayi ganin haka yasa Habib yace "bari naje wajen Maman dadi" "yauwa Habib" da sauri Habib yatashi yafita bucket yadauka yay kitchen din gidansu wajen wata mata dake kitchen yaje direct cikeda tashin hankali yace "Maman Dady dan Allah ki tsammana ruwa Ya Faty batada lpy wanka zatayi mutafi asibiti" da sauri Maman Dady tazuba mai aroba tace "ayyah Allah bata lpy" karban ruwan zafin yayi yaje bakin rijiya ya sirka ruwan yadauka yakai bayi sanan yadawo daki, lokacin daya shigo yaga har lokacin tana jikin Baba daidai tabude ido, ahankali Baba yace "meke miki ciwo Zara'u"? Murya chan kasa tace "ciki da kai" Habib daya tsaya kansu yace "Baba nakai ruwan bayi" ahankali Baba yace "zaki iya tashi tsaye ki chanza kaya"? Gyadamai kai tayi tashiga kokarin tashi da taimakon Baba da Habib tamike tsaye, zani Baba yanemo mata yasamata a hannu yace "cire kayan ki daura wanan saiki kirani zomu fita mubata wuri Habib" fita sukayi shida Habib dakin Mama ya shiga yasame ta zaune tana bama Abida nono, cikeda damuwa yace "dan Allah zoki taimakawa yarinyar nan tai wanka kinga suma taketayi Ruka" wani kallo tamai tace "gaskiya kayakuri amman bazan iyaba kuje chan ku karata" jin karan fadin abu timm yasa dagudu daga Baba har Habib sukai dakin itane tazube akasa asume tacire kayan amman bata gama daura zanin da kyau bama. "innalillahi wa innailaihi raji'un kawomin ruwa Habibu" Baba yay maganan yana daukanta yana gyaramata daurin zanin tareda fitoda ita falo, daidai Habib nakawo ruwa, shafa mata a fuska yayi ta farfado kaman zai mata kuka yace "sannu kinji, Habib biyoni da soson wanka" tama kasa tafiya daukanta Baba yayi har zuwa bakin bayi yama rude yarasa yanda zaiyi kallonta yayi yace "zaki iya wanka"? Gyadamai kai tayi idanunta dabasa buduwa da kyau, da sauri Habib yace "Baba wlh bazata iyaba kartaje tafadi tasume abayi" hayaniyan su da Maman Dady taji yasa tafito daga kitchen ta zagayo hakanan tanason Fatima sabida natsuwa da kunya da girmama na gaba da ita, tana kallon jikin mahaifinta yanda yabaci da jini tagane meke damunta tace "assha sannu Fateema, kawota nan Baban Habib bari natayaku" da sauri Baba yamika mata Fatyma, karbanta tayi ta shigar da ita bayi babu ko karfi daya ajikinta, sanan ta turo kofan tsayawa Baba da Habib sukayi suna jiransu, basu wani dadeba Maman Dady tafito da ita tace "dauketa Baban Habib zata iya zubewa Allah yasawake" da sauri Baba yadauketa yace "nagode Allah ya sakada alkhairi" wucewa da ita Baba yayi shikuma Habib yadauki bucket da so so Maman Dady tabisu da kallo bakaramin tausayin Fatyma takeji ba, daga ita har Mahaifin nata da aka gamada shi, bata shiga harkan Maman su sabida wlh zata iya mata dukan tsiya kan fatyma dan arayuwanta ta tsani zalunci, tadade tana tunani saikuma kawai tawuce ta shiga dakinta, always ta dauko tasaka a leda dawasu sababbin pant da mijinta yasayo mata na jegon Dady dabatai amfani dasuba dan sunmata kadan, kullewa tayi a bakar leda, sanan tafito tai sallama gaban dakinsu fitowa Habib yayi bashi tayi tace "gashi kabama Baban ka yabama Fatima" karba yayi yakoma ciki itakuma tawuce abinta.
Baba na kokarin zaunar da ita kan gadonsu Habib, Habib ya shigo ya mikamai ledan da Maman Dady tabashi tace "Maman Dady tace kabama Ya Faty" karba Baba yayi yabude ganin me aciki yasa yabata yace "kin iya amfani dashi Zara'u"? Gyadamai kai tayi idanunta na kukkullewa dan bata gani sosai, barinta Baba yayi akan gado yaje wajen kayanta yadauko mata wani atampan na riga da zani bakida da ruwan toka sanan yadau sabon hijabin da Maryam tabata dayagani saman kayanta ya ijiye mata komi gefenta yace "lallaba ki saka kayan kinji bari nahado miki shayi nazo" fita sukayi shida Habib yawuce uwardakan su ko kallon Ruka baiyiba yay wajen kayan shayi yadeba yazuba a kofi sanan yazuba ruwa ya yagi buredi yafito tsayawa abakin kofan yayi yace "kin gama Zara? Zara" yasake kiranta shirun dayaji yasa ya kutsakai ya shiga dakin ganinta yayi tasa pant din da pad ajikinta, tasaka riga amman takasa jan zip din ta kwanta akan gadon tana wani irin rawan sanyi kaman wacce zata mutu, rasama mezaiyi Baba yayi yace "innalillahi Zara'u karkimin haka kinji" dagata yayi jikinta kaman wuta yahada zip din yaja sanan yadau zanin dagakan gado ya daura mata sanan yazauna akan gado yana kwalama Habib dake falo kira. "kawomin shayin Habib" shigowa Habib yayi da shayin ya karba yace "sha tea kadan kidan samu karfi saimu tafi asibiti ko" girgiza mai kai tayi tareda sakinmai kuka ahankali da muryanta dabaya fita tace "Baba ni kasayo min magani allura za'amin a asibiti" murmushi yamata yace "sha shayin to mugani tukunna inkinsha da kyau sai na sayo miki magani" kai shayin bakinta yayi ta kurbi kadan ko idasa hadiyeshi bataiba sai amai bata kasan dakin tayi da aman da babu abinci aciki, tashi Baba yayi yace "bari na chanza kaya mutafi zauna da ita Habib" zama kusada ita Habib yayi yadau hijabinta yasaka mata shi karan kanshi saida tace "kai wanan hibajin mai hulan nan yamiki kyau sosai" daki Baba ya shiga ya chanza kaya yadau key machine dinshi sanan yajuyo ya kalli Mama yace "bari nakaita asibiti" yan dubu biyun dake aljihun wandon shi yaciro yakalla sanan yatura a aljihu sanan yawuce yafita ya gungura machine dinshi zuwa waje lokacin 8 dayan mintoci nasafe sanan yadawo ciki, dagata yayi Habib yakawo mata silifas dinta tasaka Baba yariketa tana ta karkarwa da kyar suka fita waje saida yafara daurata kan machine din sanan yahau yatada suka tafi General.
Ahankali yake gudu da ita jin yanda jikinta ke bari, saisa sukai kusan 30min kafin sukai, parking yayi inda ake parking ya sauko ahankali sanan yakamata ya saukoda ita yana tattare ta gudun karta fadi yace "sannu Zara'una, muje" riketa yayi suna tafiya ahankali tana binshi ahankali dishi dishi take ganin gabanta daidai sun shiga ciki dip tadena ganin komi daga sama sama taji muryan Babanta na ihu "ataimakamin ataimakamin jama'a".
_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_
Dawani irin gudu nurses suka gungunro wani gado aka karbeta daga hannun Baba suka dagata sauka daurata akan gadon akai ciki da ita, wani babban examination room suka shiga da ita Baba zai bisu aka hanashi shiga sanan daya daga cikin nurses din tafito tashiga wani consultation room saigata tafito tareda wani Dr dabazai wuce 35yrs ba yana sanye da farin glasses a idanunshi wuyanshi sanye da stethoscope, wajen aljihun Lab coat dinshi ta gaban rigan anrubuta Dr Imam, da sauri sauri gudu gudu suke tafiya daidai zasu shiga dakin Baba yarike hannunshi gam hakan yasa yajuyo tareda tsayawa ya kalli Baba yakuma kalli hannunshi da Baba yarike irin lafiya, kaman wanda yazare dakin Baba yanuna mishi cikin wata irin raunanniyar murya yace "likita y'ata ce acikin dakin, dan Allah kataimaka mata kar wani abu ya saman mini Zara'una likita" wani calm smile Dr yayi tareda karbe hannunshi daga hannun Baba yakama kafadar Baba ya zaunar da Baba kan kujeran dake wajen yace "abinda nakeso dakai Baba shine ka kwantar da hankalin ka kazauna anan kama yarka addu'a, abangarena kuma namaka alkawari zanyi duk abinda zan iya naga na ceto rayuw........." bai karasa maganan ba wata nurse tafito tace "Dr come she's convulsing" da sauri yay ciki yana yana kallon Baba yace "just stay here" da gudu ya shiga dakin ya karbi handglove din da wata nurse ke mikamai yana sakawa a hannu yana kallon patient din sanan yace "ya za'ayi tana convulsing bazaku cire mata wanan hijabin ba, ku cire mata and someone should on the AC" yafada ba wasa sanan yakarasa inda take bayan yagama saka hand glove din, ahankali yakai hannunshi yajuyo da ita, tareda karban wani kalan spoon da nurse kebashi yakama kumatunta ya matste bakinta yabude yasa cokalin abakinta gudun karta taune harshenta, zafin dayaji ajikinta saida yabashi tsoro, sanan ya karbi alluran dayasa abashi yakama hannunta yanemo jijiyanta yamata allura, ko minti daya ba'a daukaba tadena convulsing yay stabilising nata, yasake saka wani sabon alluran ya debo jininta awani a syringe din yabama wata nurse yace to the lab" sanan ya kalli wata nurse yace "send in the father" fita tayi bata jimaba suka shigo tareda Baba hakan yasa sauran nurses din suka fita shikuma yadauki wani paper da byro ya kalli Baba dayaga yaje ya tsaya akan Fatima yana kallonta yace "ya sunan yarka Baba"? batare daya kalleshi har lokacin idanunshi nakan Fatima yace "sunanta Fatima Zarah Muhammad" gyadama Baba kai yayi bayan yarubuta yace "meya sameta, meka damunta, tamaka complain wani abu namata ciwone"? Ajiyan zuciya ya sauke yace "ni jiya narabu da ita lpy kafin natafi aiki, nadawo gida wajajen goma sunyi bacci, saida safen nan kaninta yakirani nazo naganta babu lafiya, ciwon cikine na al'ada dakuma ciwon kai" rubutawa yayi sanan yace "daman haka yake mata"? Gyadamai kai Baba yayi yace "eh haka yake mata amman kusan watananni biyu dasuka wuce ko ciwon kai batayiba sai wanan watan kuma, sumanta kusan uku agida, kome taci sai amai, batada karfi ko kadan, tun dare babu aiki sai kuka" sake rubuce rubuce yayi sanan ya ijiye takardan yadauko wata paper yay rubuce rubuce sanan yamikama Baba yace "yanzu dai kafara zuwa kasayo wayan nan magungunan a pharmacy kafin result din test dinta yafito mufara treatment yanzu kawai stabilising condition dinta nayi ba'a mata komiba tukunna sai kaje kabiya kudin kati da folder abaka ka kawomin anan da magungunan."
_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani* dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals
💫 _DISASTROUS LOVE_💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
✍️M SHAKUR
EPISODE 5️⃣
_FREE PAGE_
Karban takardan Baba yayi kaman mara lafiya yajuya yana tafiya ahankali yafita daga dakin yay reception, tsayawa awajen yan kati yayi yabude kati da folder, folder dubu daya, karamin kati kuma dari uku yarage duka kudin saura dari bakwai, bai karayaba yarike komi a hannunshi yawuce Pharmacy ya tsaya gaban kanta tareda mika musu takardan da Dr yabashi, gani yayi anciro gorunan ruwa, allurai daban daban dawasu magunguna ankawo gaban table anyi wani tabe tabe a computer sanan aka fitomai da wata yar takarda, namijin wajen ya mikamai yace "Baba ga takardan biyan kudi je chan wajen account kabiya kudin saika dawo mana da takardan biyan kudin saika amshi magungunan katafi" karban takardan yayi ya kalli kudin dake rubuce awajen dubu takwas da naira Dari da talatin wani irin mugun faduwa gabanshi yayi ahankali yajuyo ya kalli saurayin dahar ya juya yakoma wajen zamanshi, dan gyara muryanshi dayaji ta shakemai yayi yace "Yallabai jimana" tasowa saurayin yayi yazo yace "gani Baba" cikeda damuwa Baba yace "kaga y'ata ce ba lpy, rai a hannun Allah, duka duka yanzu chanjin hannuna basufi dari shida ba, nace kozaka bani abubuwan nafara kaima likita afara mata treatment, inyaso kafin mubar nan wajen saina biya kudin daga baya yanzu dai afara bata taimakon gaggawa" dan murmushi pharmacist din yayi yace "Baba kenan, kayakuri Baba bama haka awanan asibitin" yanamai maganan yashiga attending to wasu mutane dasukazo wajen siyan magani, gajiya da tsayuwa Baba yayi awajen kafin ahankali yadaga kafafuwan shi dayaji sunmai nauyi sosai yawuce yafita, ahankali yake tafiya haryakai wajen parking space, sabida kar mutane su ganshi yasa ya zaga ta gaban motoci yazauna kan dakalin wajen yay shiru yana kallon folder da katin daya bude mata ga sunanta ajiki baro baro, Fatima Zara'u Muhammad, yarinyar nan tun tana yarinya wahala take yanzu gashi tana ciwo baida kudin kulada ita, jiya da yafita neman kudi yaje babu wanda yasani dayabashi kudi koda sisine, Rukayya ko yasan ko Mutuwa Zara'u zatayi bazata taba cire kudin ta tabada ba, dudda yasan itama ba lallai yasamu irin wanan huge kudin a hannunta ba amman bazai rasa yarsu dubu dubu biyuba, toya fita yay bara ne? Ya tambayi kanshi, but ayanda duniya ta chanza babu wanda zai ganshi yanzu haka ya yarda yabashi kudi yayi tsaf tsaf dashi gayar shaddar shine tsaf tsaf ne za'a yarda abashi taimako, jiyayi wasu hawaye masu shegen zafi sun zubomai yakai hannu ya share amman suka kasa dena zuba hakan yasa kawai ya barsu suka slcigaba d kwarara.
Agogon hannunshi kirar iwatch dake daure a wrist dinshi ya kalla about 25min kenan Baban Patient dinan bai dawoba, dagakai yayi ya kalli yarinyar ganin har yanzu she is stable bacci take yasa yadauki stethoscope dinshi yarataya awuya ya kalli nurse din dake wajen yace "stay with her, idan her Dad yakawo magungunan call me, idan ta tashi call me" yana maganan yajuya yafita