Showing 18001 words to 21000 words out of 150358 words
Chapter 7 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt
bakin gado tana fifita Abida datai bacci da mafici dan babu wuta tayi kyau sosai taci gayu tasa atamfarta mai kyau harda sarka awuya kaman wacce taje biki wanda abune dayasan bata sabayiba, zama yayi kusada ita tareda washe baki yace "wanan kwalliyan fa ni akamawa ne"? Wani banzan kallo ta jefeshi dashi sanan tace "kai asuwa, ni kaga dan Allah kabarni damuwan dake kaina daban Baban Habib" binta yayi da kallo yay shiru, dan yatsine fuska tayi saikuma ta nisa tace "uhm gwara ma nagaya maka, daga gidan Madam nake" yanda ya kalleta da sauri tareda sake natsuwa yasa ta gyadamai kai tace "gwarama kai salatin da kyau kaji, kirana tayi awaya tace nazo, nashirya naje nasameta tace min yaya ake ciki taji mijinta da mutanen nan namagana awaya ranan lahadi jibi kenan dan yau ai Jumma'a zasuzo, wai ya mun shirya mun gama hada kudin nace mata ko asi bakada shi balle chasi" wani gumi Baba yashare ahankali yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, wlh inda nasan haka abin nan zai kasance daban karba ba dukkece kika sani awanan ukuban" wani irin zaremai ido tayi tace "nice mene kace"? Kasa maimaita maganan yayi daya kalli kwayan idanunta saikuma ya saukar da murya ahankali yace "kiyakuri badake nakeba" kwafa tayi tace "Allah yasoka wlh dasaika raina kanka wlh mtswww" taja tsaki, ahankali yadafa kanshi saikuma ya buga tagumi saikuma ya kalleta cikeda damuwa yace "yaya zanyi yanzu Ruka kifadamin abinyi"? Shiru tayi tana kallonshi saikuma ta nisa tace "Mijin Madam yariga ya sanarda mu duk wasu ka'idoji da sharuddai na wanan lamarin ko kaje still maganardai itace zai sake maimaita maka, amman dudda haka yanzu katashi kaje kai wanka ka chanza kayan nan kasa wanan giznar danasa kasaya, ka feshe kanka da turare katafi chan sakateria office dinshi kasame shi kaje kuyi magana mai kyau, yafada maka idan dawata hanya dazakabi kome yagaya maka kadawo kasanar dani daga A zuwa Z sabida nasan yanda zamu bulloma lamarin daganan in lokacin Jumma'a yayi saika wuce kadawo gida karka biya ko'ina kadai jini ko" gyadamata kai yayi ta tashi tace "bari naje naduba ruwan dake murhu inyay sanyi kayi wanka da ruwan sanyi dan gaskiya sabida kai bazan hura wuta naci gayun nanba" tawuce tafita yabita da kallo yaji zafin yanda take gasamai magana amman yakasa cemata kala, kayan yacire yasa jallabiya yabi bayanta takaimai ruwan tadawo daki.
Fitowa yayi yadawo daki ya shirya tsaf yay mugun kyau kaganshi zaka dauka wani alhajine harda fesamai turare sanan tace "saura ka kalli wata mace" dan dariya yayi yaja hancinta yace "inada mace har mace irinki mezanyi da wata Ruka Baban Habib sai Maman Habib" murmushi tayi cikeda sonshi tace "nidai wuce katafi" tai maganan tana bashi key machine dinshi ta tasashi agaba har waje dudda yaso yama Fatima sallama dan taga yanda yake kallon dakin but bata bashi damaba haka yaja machine yatafi, murmushi tace "kwanaki kadan yarage kurabu" tawuce takoma daki, hijabi ta dauka tasaka sanan tafito ta shiga dakinsu Fatima, akwance ta ganta tana bacci, da kafa tasa ta hambareta da sauri ta farka harara ta balla mata tace "tashi kifita falo kizauna kimin gadin Abida tana bacci nikuma zan fita, in yarana sun dawo daga boko ki basu abincin dana dafa yana kula" gyadamata kai tayi ahankali Mama taja tsaki tawuce tafice daga gidan.
Wuraren goma Baba yakai sakateria yana kaiwa gate yay parking mai gadi yace "wajen Oga Abdul kazo ko" dasauri Baba yace "eh" ciki mai gadi yayi saigashi yadawo yace "yace kashiga" wucewa ciki Baba yayi yay knocking gaban wani dan madaidaicin office daga ciki aka amsashi "shigo Malam Muhammad" bude kofa Baba yayi ya shiga wani mutumi ne yana sanye da suit zaune akan kujera daga ganinshi kasan ba bahaushe bane banufe ne ya fadada murmushin kan fuskarshi yace "barka da zuwa Malam Muhammad" yamikama Baba hannu suka gaisa sosai sanan yakoma ya zauna yanuna ma Baba waje shima ya zauna sanan yace "ya ake ciki mutumina kahadama mutanen nan kudinsu kuwa"? Da sauri Baba ya girgiza kai anatse yace "saisa na shirya nazo wajenka Oga Abdu naga kana mutunci da mutanen nan saisa nazo ka taimakeni kadubi iyalina ka nemamin alfarma awajensu dan Allah, su dan karamin kwanaki zan biya wlh, ka taimakamin" hmmmm Oga Abdul ya fuzarda iska sanan ya kalli Baba yace "Malam Muhammad kasandai kai mutumina ne ko kuma tsakanina dakai babu boye boye, babu karya kowani abu, maganan gaskiya shine mutanen nan basusan menene alfarma ba wlh, saisa suke cewa mutum dakanshi yafadi yaushe zai biya back kuma duk ranan daya fadi ranan zai biya ko yabi sharadin daya yarda akai dazai ari kudin, mutumina idan baka da kudin nan bakada hanyar samu ka biyasu, kawai kabi sharadin inba hakaba kasan sauran" shiru Baba yayi gabanshi nafaduwa sosai yama kasa magana hakan yasa Oga Abdul yace "kaima ka tafka kuskure anbaka makudan kudi haka dazasu chanza maka rayuwa ko gonace tunda daman shine sana'ar daka iya dakaje kayi amman bakayi ba kaje ka wulakantar da kudaden nan, kasai machine da sauran su kana washagali bakasan rana irin tayau zatazo ba gashinan idanunka sunyi ja" yay maganan cikin dan fushi dan Madam tagayamai abinda yayi da kudin ya chanza matarshi kayan daki da gida, ganin Baba yakasa magana saikuma yabashi tausayi hakan yasa yakai hannunshi yasaukar da hannun Baba daga kan kuncinshi dayay tagumi dashi yace "kaga abokina bashi kaci ba kisan kai kayiba, kowa nacin bashi, abinda nakeso dakai kabasu dan naka kawai, d'ana yaje yay aikatau dasu, wanan sirri ne dabana fadima kowa, nima naci bashinsu nakasa biya dana yaje, basa wahalar da yaro, ba cuta ba cutarwa yaro yay aikinshi duk wata ana biyanshi a matsayin biyan bashinka, yarona yadawo na ganshi yamafi sanda yake gidana akarkashin kulawata kyau wallahi, kawai kabasu inbadai so kake adaureka agidan yari ba dan trust me mutanen nan sune hukuma gabaki daya wlh bazaka iyaja dasuba kokai waye I know what am saying, kawai ka shirya ranan lahadi by 9 tamaka a wanan hotel din dasuke sauka in sunzo katafi dayaronka kabasu baki alekum agabanka zasuyi documenting yaron sugaya maka salary shi dakuma aiki watanni ko shekarun dazai musu, kaikuma saika dage da nema kafin lokacin kahada kudin katura musu adawo maka da danka cikin lumana kaji ko" gyadamai kai kawai Baba yayi, nan Oga Abdul yacigaba da bashi shawarwari sanan wuraren daya suka fita tare zuwa sallan jumma'a daganan yawuto gida.
Da sallama yashigo falon Fatima yagani tana share falon dayay kaca kacha da abinci alamun yara sunci abinci, da sauri yace "inasu Habib da Sadiq dasukaci abincin suke dakike shara"? Mama ce tafito daga dakinta ranta abace tace "sun koma wajen aiki, Habib yatafi gareji, Sadiq na shagon dinkinsu, Ibrahim na wajen kafinta kagako tunda itace agida bata zuwa wajen aiki aisaitai sharan, wuce mutafi daki" tanunamai hanyar uwardaka, wucewa yayi itakuma ta watsama Fatima data cigaba da shara abinta harara sanan tashige dakin nasu, zaune taga Baba kan gado yacire riganshi yarataye a kofar sip yarage dagashi sai farar shimi da dogon wandon shaddan ya zauna, washemai baki Mama tayi tace "musamman nahada maka kunun aya mijin Ruka" tai maganan tana tafiya wajen wata yar karaman fridge dake uwardakan tabude taciro katuwar goran kunan Aya tadaura a tray da kopi tazo ta ijiye kan dadduman data shimfida a kasan uwar dakan sanan ta dauko kulan abincinshi takawo tazauna akan dadduman ta kallai tace "sauko" saukowa yayi ahankali tabude kula tana kokarin zubamai shinkafan data dafa yace "ina Abida?" "Uhm wanan rigimamman tana dakin su Habib tana bacci" janshi da hira tadinga yi yacinye abincin tass yasha kunun ayan dayay dadi sosai sama da rabin gora ya kalleta yace "ke bakisha kunan ayan ba dukni na shanye" dan dariya tayi tace "wanan nakane special namaka ninasha nawa tareda yaranmu dazu, shanye kaji" daga goran yayi ya tsiyaye ragowan wanda yarage a cup yakai baki ya shanye tass wani irin murmushi tayi tace "haka nakeso yallabai, baka bani labari ba yakukayi da mijin Madam"? Danjim yayi for a moment harya manta saikuma yanzu yaji damuwan shi tadawo danya fall yanda yakasa magana yasa tace "ba gudu baja dabaya ko"? Gyadamata kai yayi ahankali, murya chan kasa tace "yanzu da gaske ranan lahadi Habib zaka dauka kaje kayi biyan bashi dashi"? Kallonta yayi yace "toya kikeso nayi eh Ruka? Kudinnan kinma finici aciki, kuma banda haka Oga Abdu yacemin basa cutarda yara ko kadan shima danshi yataba zuwa aikatau din daya dawo saima wani kara bulbul yayi, basaina bada Habib ba inyaso saina dage da neman kudi bada jimawa ba nasamu nahada nakai adawo dashi koya kikace" wani kallon raini tamai tace "kana haukane Baban Habib ko kanka yatabu ne dakake cewa zaka basu d'ana Habib"? Baki yabude zaiyi magana tawani dakamai tsawa tace "kamin shiru bance kai magana ba" hadiye maganan dazaiyi yayi kaman an daure bakinshi yana kallonta kaman d'a da Uwarshi.
Shiru tayi sanan ta kwalama Fatima kira."ke Zara'u" da sauri Fatima tafito daga dakinta tayi bakin kofarsu batare data daga labule ba ta tsaya awaje cikeda girmamawa tace "gani Mama" cikeda batarai da masifa tace "dau Abida ki goya ki tafi gidan kawarki Maryam karku dawo yanzu" abin bakaramin mamaki yabata ba yanda Mama da kanta tace tafita taje wajen Maryam, washe baki tayi cikeda jin dadi tace "tom nagode Mama" da sauri tajuya, Mama tace "saura inji kinbiya wani wajen jaka kawai mai kama da zabiyar dila" bata damuba ta goya Abida tasaka hijabi tafito tace "muntafi Mama" tsaki Mama taja bata bata amsaba tace "jamin kofar falo" jan kofar tayi, sanan Mama tajuyo ta kalli Baba ta gyara zama tace "dagani sai kai saikuma mahalliccinmu ne adakin nan Baban Habib, kalle ni nan ka kara ni dai Rukkaya matarka ko ana hamaza hamata wlh wlh, billahilazimu bazantaba bari kakai d'ana yaro karami dan shekara goma sha 12 chan wani garine ko kasane ohon musu aikatau ba da sunan biyan bashi ba kaji na rantse maka kuma kasan halina sarai basai anbaka labari ba" gyadamata kai Baba yayi kaman wani yaronta yace "shikenan abar zancen Habib zan samesu jibin nagaya musu bandashi inyaso dukma yanda zasuyi sai suyi" da sauri tace "hauka kake? So kake su kulleka? Ni zaka jama abin fadi aduniya ana ganina da daraja aji labarin an kullemin miji dama dukkudin damuke wasshagale dashi na bashi ne, karma kasake kayi tunanin nan kana jina ko" gyadamata kai yayi ahankali yace "toya kikeso muyi"? Wani hadadden makirin murmushi ta sakinmai takai hannu ta tabashi tace "yanzu kai magana mai kyau my handsome miji na dan baiwa shege gakadai talaka bako sisi amman Allah yamaka bindi" tanuna wajen wandonshi, yanda take murmushi yasa shima yasaki murmushi kaman wawa, daure fuska tayi tace "zancen kai Habib bashi, zancen a kulleka sabida baka da kudin biyan su babushi shima, kaga yarinyar nan data fita" tanunamai kofa da sauri ya kalli kofa dan baigane metake fadiba yace "wace yarinya"? Daure fuska tamau tayi tace "yarka Fatima Zara'unka da ita zakai biyan bashin nan Baban Habib"!!!!
_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 07010439656 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫
_MASIFAFFIYAR KAUNA_
_NAKUSAN GAMA FREE PAGES, IF YOU WANT THIS NOVEL IS JUST 500, SEND 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK, SEND EVIDENCE OF PAYMENT TO MY WATSAPP NUMBER 07012181461 THANK YOU_
✍🏾 M SHAKUR
_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._
EPISODE 🔟 &1️⃣1️⃣
_FREE PAGE_
Dawani irin sauri Baba ya kalleta yanda gabanshi yafadi har ita saida tagani, itama kureshi tai da ido kur tayi irin da magana ne amman yakasa furta uppan saima ya sunnar da kanshi kasa, wani takadirin murmushi tayi tace "aina zaci zakace wani abune" tadanyi shiru tace "Fatima itace yarinya babban damukeda shi maidan hankali kuma yarinyar nan zata iya komi tarufa maka asiri, ta mallaki hankalin kanta shekaranta sha tara duk inda muka kaita hankalinmu akwance sabida musan zata kare kanta" ahankali kaman wanda ke tsoron magana yace "Ruka mutanen nan kin manta sharadinne yaro namiji kadai suke karba basu karban mace" dan dariya tayi tace "ance maka ni dakikiyace irinka hmmmm" tadan girgixa kai sanan tace "inada plan, hadaddiyar plan" ahankali bakinshi har rawa yake yace "wani irin plan?" Murmushi tayi tace "zamu komar da ita namijii"!!!! Zuru zuru yayi yana kallonta kaman sauna ta gyadamai kai tace "zamu komarda ita namiji ta hanyar boye duka hallitun mace da Allah yamata Madam cema tabani shawaran nan dan itama tasan Habib yay karami ga Habib ba wayau, inada wasu kudi dubu goma zan ara maka gobe zan shiga kasuwa, zan sayo silkin doki dashi zamu kulle mata kirji wanan manyan maman datake dashi dauresu zamuyi tamau, kanta ko nida kaina yauzan zauna namata zane yan kanana zan sayo Bald cap (hulan fata na kwaiwaido) zan zauna nasaka matashi da gam, sanan zan sayo kayan maza riguma da wando na gwanjo burguza burguza dakuma Ghana masgo, hujin kunenta akwai wata yar fata dazan like awajen baza'a taba gane antaba huji awajenba saikuma takalmi kito, da kambas, wanan maganan dagani sai kai da madam da mijinta, duk wanda yatambayi Faty zakace tayi tafiya ta tafi wajen Baabarta na Abuja hatta su Habib bazasu sani ba kanajina" gyadamata kai yayi kaman maraya, hararan shi tayi tace "duk duniyan nan bakada mace mai sonka maikuma rufamaka asiri irina dan haka kadinga godemin, kuma bayau zaka sanarda Fatima ba sai gobe sanan agabana za'ai komi kanajina ko" gyadamata kai yasakeyi kaman maraya yakasa magana yakuma rasa abinda yasa yakasa magana, murmushi tayi har cikin ranta ganin yanda maganin sabon wajen da Madam ta kaita yay aiki sama dana tsohon datake amfani dashi da, murmushi tayi tabudemai hannayenta tace "zonan mijina" da saurinshi da rarrafe yashiga jikinta ta rungumeshi tana shafamai baya tace "inhar kanajin maganata kanamin biyayya bakada matsala wlh, komenene zan tsayamaka aduniyan nan, duk rashin kudinka ina sonka, ni bankibama kai zamanka agidaba nina dinga fita nema dan wlh banson mata na kallemin kai kafin wata ta kyatsa amin wuff dakai dole na tsaya tsayin daka aranka, dan kyakkyawan bafulatanina" ta shiga sarrafa shi wai ance duk wayan namiji yashiga hannun mace jariri yake dawowa, shida kecikin damuwa dayake rikakkiyar yar tasha ya aura tuni ta mantar dashi tana tsotse shi saigashi yafara ihu suka shiga cin juna yau harda ihauce ihauce barinma shi dayajita yau daban saida ta taushemI baki sabida ihun yasoma yawa sai sama Madam albarka take yanda taga lokaci daya Baban Habib ya susuce mata ba ita tabarshi ba sai wuraren karfe biyar daga ita harshi sun galabaita da kyar ta sauka ta zura hijabi tayi tsakar gida tana taku dai dai madam tafito yar gatan mijinta tawuce takaimai ruwa bayi sukuma suna gulman su Kullum yana gindin mace an maidashi sauna sai yanda akai dashi.
*********
"Kewai mesa yar kauyece Zara"? Cewan Maryam da tundazu suke hira da Zara datazo tana bata labarin rashin lafiyan datayi just this two days, Abida kuma nachan dakin Maman su Maryam tanacin tuwon da aka dafa tana wasa.
Hararanta Fatima tayi tace "ni wlh ko kallonshi nayi sai gabana yayta faduwa" wani irin dariya Maryam tashigayi tafada kan yar yaloluwan katifarta tana daga kafa, daure fuska Fatima tayi tace "me haka wanan dariyan fa"? Da sauri Maryam ta tashi ta zauna tace "ke wlh sonshi kike" da sauri Fatima ta zaro idanu cikeda wani irin mugun mamaki gyadamata kai Maryam tayi cikeda jinjinawa tace "eh ke matsalata dake baki karance karancen littatafan soyayyane dakin gane menake fadi, kinsan ko ance duk namijin dazaka gani gabanka yayta fadi shine zaka aura ko shine mijinka" wani irin kallonta Fatima take kaman tasami TV, Maryam tace "kuma shima wlh sonki yake, har yana barin aikin dayakeyi yazo yatareki dankarki fadi kice kaza kaza, ina gayamiki sonki yake kawai dai bai sami ta hanyar dazai fadimiki baneba kawai, kuma zakigani nan....." da sauri Fatima ta tareta tace "ni mubar maganan dan Allah banmaso wlh meneke dashi da irin wanan mutumin zaiso mace kaman ni ke kinganshi ne kuwa? Hanyar jirgi daban hanyar mota ma daban abar maganan" tashi Maryam tayi tace "anbarta