Showing 54001 words to 57000 words out of 150358 words

Chapter 19 - DISASTROUS LOVE (Azababbiyar Soyayya) Book Complete by M Shakur.txt

M Shakur   

07 Jan 2025

15383

creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan nUmber 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._












💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫






_MASIFAFFIYAR KAUNA_








✍🏾M SHAKUR






EPISODE 2️⃣7️⃣ & 2️⃣8️⃣
Wanka yayi ya chanza kaya yafito daga ciki, tundaga stairs yake kallonta ganin yanda rigan jikinta yabaci da da pepper soup din tana zaune a inda yabarta tabude idanun da ayanzu sun dena mata zafin saidai kawai yana yana kaman cobweb dasukasa idanun sukai mata wani irin, tunda taji tafiyarshi tadago kanta ta kalli ta saitin datakejin tafiyan shi, kan kujeran datake zaune yasami gu a gefe yazauna ahankali yace "you are hungry right, you haven't eaten" kasa amsashi tayi ta saukar da kanta kasa ahankali hadadden kamshin dayakeyi na ratsa hancinshi, doorbell dayay kara alamun an danna yasa ya kalli kofan yabada izinin ashigo, wasu guards suka shigo da warmers da plate hadaddun gaske aka kawo wajen, ijiye abinci akayi agabansu, yasa suka zubamai sanan yasa suka zubama Boy, ya karbi nata yadaura mata a hannu yace "eat" sanan yabasu izini dasu fita.




Lafiyayyen farin rice ne da stew dayaji namomi zako zako, spoon din tadauka tadebi first spoon of rice din takai bakinta da kyar tahadiye saikuma tahau bude baki tana hura iska tana kokarin danne yajin but ina takasa, yajin is something else da sauri ya kalleta yanda takeyi yas yace "is it pepprish?" Gyadamai kai tayi da sauri idanunta natara ruwa again sabida tsabagen yaji, ruwa yadauka yabude yabata takarba tareda kafawa abaki da sauri tana kwalkwala, sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta ganin tana neman shanye ruwan goran sanan ta ijiye, da spoon din yaga rana ture stew din saman abincin gefe sanan tafaracin rice din hakanan tanayi tana shan ruwa hartadanci sosai sanan ta ijye shikuma har lokacin yanacin nashi ahankali yana kallon ball abinci dan in dasabo yasaba cin abinci dayaji tunda aka haifeshi.




Saida yaji ankira la'asar sanan yakawo glass din yabide yakama hannunta yabata yace "saka muga" sakawa tayi ahankali ta kalleshi, ga mamakinta saitaga tana ganinshi amman kadan ba clear ba yafi babu da dazu bata gani ko kadan, da sauri yace "can you see me" gyadamai kai tayi tace "yes but small" ajiyan zuciya yayi da saida taji karanta yazauna kusada ita looking so relieved, ahankali tace "sir I want to go to my room and shower nacire kayan nan" da sauri ya kwalama guard kira, na bakin kofanshi ne suka shigo yace "sukai yaron dakinshi" tafiya dashi sukayi yabisu da kallo sanan yawuce sama yaje yay alwala yay zuhur da asir sanan yakoma ya kwanta sai bacci.




Itama wanka tayi tsaf sanan tadawo dakinta ta kulle tai salla tadade akan dadduma tana addu'an Allah ya tsareta yakareta sanan yabama Baba kudi yazo yacireta tagaji da gidanan nan yautaga azaba iya azaba, tagama tasake tofe kanta da addu'a sanan ta tashi tabude kofa takoma ta kwanta bata koma dakinba kuma bai aiko akirata ba saidai ya aikomata da magungunan ta sanan da biscuits da chocolate din dayasainata.






**************
WASHEGARI!!
Wuraren karfe shidda wani bakin mutumi dake sanye da farin zani kaman yadin likafani yadaurashi yamaidashi kaman wando da riga saidai shoulder shi daya abude da akai wasu irin zane da farin fenti ketahowa cikin fadan yana tafiya yana buga wata sandar hannunshi na karfe, kunenshi na sanye da wasu irin dankunnaye na cowries, hakama hannayenshi yay warwaro da cowries din, kafafunshi ma haka, sanan sandar karfen dayake rikeda shi duk cowries dinne akai dakesa abin yana kara idan yana tafiya yana kara, tundaga nesa duk guard din palace din dazai ganshi zubewa suke suna kwasan gaisuwa yay hanyar fada, da sauri fadawan dake tsare gaban fadan suka budemai kofa ya shiga ciki ya zauna a tsakiyan fadan akasa, fadawan suka shigo suka zube dan gaidashi, cikin harshen yarensu yace "akiramin Oba dakuma Otun yanzun nan" davmsauri fadawan sukace angama, wasu suka fita sukai cikin gida wasu kuma suka fita dan zuwa kiran Waziri agidanshi da baida nisa sosai da nasu.




Waziri yafara isowa wuraren bakwai, saiga Sarki dan saida ya tsaya yay wanka sanan yazo ya shigo falon da Waziri ke zaune kan kujeranshi shikuma mutumin har lokacin yana kasa bai zauna akan daya daga cikin kujerun dake fadanba, Mai Martaba yashigo yakarasa kan kujeranshi ya zauna Otun na gaidashi, sanan Waziri yabada izini guards su fita suka fice aka rufo musu kofa yarage su kadaine afalon.




Anatse cikeda girmamawa Waziri ya kalli mutumin cikin yanayi na tashin hankali yace "Ooluwo (Chief priest) meya kawoka fada da sassafe haka? Kamana aike muzo lpy"? Shiru mutumin daya kirada Ooluwo yayi wato bokan gidan sarautan Chief priest kenan, saikuma yarufe idanuwanshi yana wasu irin surkulle da basaji sunadai ganin bakinshi na motsi sanan yabude idanunshi ya kalli Oba da Otun yace "banson natada ma jama'an wanan fadan hankali ne saisa dakai da Mai Martaba kadai nakira" sanan yasakeyin shiru kafin ya shiga Koro bayani.
"Iya sanina tun zamanin forefathers din wanan gidan sarautan, tun lokacin kakana na uku, wanda ya taka matsayin Chief priest din wanan fadan daya buge duk wani boka maiji dakanshi a Nigeria da kewaye gabaki daya, boka mai amana wanda yay rayuwanshi yagama yana serving kakanninka" yanuna Oba sanan yace "dukanku nan kunsan prophecy da kakana na uku yagani tun a zamanin, annunamai cewa duk randa wanan gidan sarautan zai dauki y'a mace a matsayin yar aiki agidan nan, wanan gidan sarautan, inhar mace zata saka kafarta ta shigo gidanan da sunan aiki to destiny gidan sarautan nan zai chanza gabaki daya, tun awanan zamanin kakana na uku awanan lokacin yasa aka dena dauka masu aiki mata daga ranan dayaga wahayin har zuwa rana irintayau da nasan ko mace daya babu agidan nan da sunan aiki, baku dauka mata amatsayin mai muku aiki kwata kwata" anatse Otun dat was looking confuse yace "kuma tundaga lokacin, har aka nada abokina Sarkina a matsayin sarki har rana irin tayau bamu dauki mace a matsayin yar aiki ba tunda abune damukaga tun iyayemu basuyi ba balle mu, wanan ai rule ne ma nagidan sarautan nan datake ashimfide, tundaga kan fadawa, guards, cooks, masu shara, gardeners, securities, masu wanke wanke dakomima daka sani na wanan gidan maza muke dauka, hatta nani masu mana rainon yaran mu tun suna yara maza ne, certified maza dasukai karatu kan zama nani, Bokanmu hatta gidana babu dan aiki kodaya mace balle ma gidan sarautan nan gabaki daya, meke faruwane? Meke shirin faruwane tsoro yacikamana zukatan mu dagani har Sarkina, ataimaka awarware mana zaren" wasu yan maganganu bokan yafadi dabasu gane meyake nufiba, sanan yay kaman ya sallame salla saikuma yajuyo ya kallesu yace "jiya naga vision da daddare" duk kallonshi suke yay shiru, sanan ya sauke yar ijiyan zuciya yace "naga vision cewa wani gagarumin abu na gabda faruwa awanan gidan, masarautan nan dazai chanza destiny gidan nan gabaki daya, makiyanka da makiyan gidan sarautan nan zasu maka dariya, zasu maka dariya zaka dawo abin magana awanan, gidan sarautan nan zai shiga bakin koya zakubi Nigeria gabaki daya, babu abinda banyi ba anki warwaremin vision din nakasa gane takamaimen menene zai farun"? Kana ganin idanun Oba da Otun kasan suna cikin damuwa sunma kasa magana, hakan yasa yadaga musu hannu yace "ku kwantar da hankalinku" Cowries din wuyanshi ya cire ya yar atsakiyan dakin yay wasu maganganu tareda taba tsakiyan sarkan yace "nunamin komi ke madubin tsafi" gani sukayi tsakiyan cowries din yakoma kaman madubi saidai tsakiyan yay bakin kirin basa iya ganin komi ciki, Chief Priest ya kallesu yace "tun jiya abinda yake nunamini kenan, wanan abun babba ne, babban gaske, babu wanda bazai girgiza ba koma menene abin ba, yan adawan masarautan nan na wasu gari da baku zaman lafiya dasu zasu muku dariya akai, kun tabbatar babu mace agidan nan sabida insan ko sabida macen nan wahayin kakana na uku ke shirin tabbata"? Da sauri Otun yace "har abada babu mace agidan nan, mata bamasa neman aiki agidan nan sabifa sunsan bazamu basu ba sunsan bama abayarwa, duka factories dinmu, companies, gonaki, gidan kaji gidan kifi da duk wasu kafofin kasuwanci damukeda shi a lagos dinan kaf da kewaye maza ne ma'aikatan mu, hatta lawyers dinmu maza ne, likitocin mu mazane, masu mana wanki maza ne, yanayin rayuwan muma babu mata ciki banda yaran da muka haifa mata tota ina mata zasuzo"? Jinjina kai Chief priest yayi cikeda gamsuwa da bayanin Otu yace "yace na yarda dakai, daman nasake tambaya ne dan insake tabbatarwa idan ma akwai sharadin biyune wanda Kakana na uku yafadi a lokacin, aka kama macen koku kasheta ya zamto batada rai gabaki daya hakan zaisa kaddaran yaki faruwa dan wacce kaddaran zata faru ta sanariyarta ta mutu kokuma ku kaita nesa chan nesa da wanan masarautan tayanda bazata taba iya dawowa gidan masarautan nanba har abada! yanzu inaso zaku siyo bakin akuya guda bakwai, ayayyanka atafasa naman aci batare da an soyaba, zanje nacigaba da duba koyaya ake ciki kubani nanda kwana bakwai zanyi communicating the Gods of the night" yatashi yafice batare dayajira cewansu ba.












Kallonshi Oba yayi hakama Otun kallonshi yayi, Otun yace "tayayama zasu dauki mace a matsayin yar aiki wanan ba abu mai faruwa bane bama har abada, so bashi alayi bamashi cikin layine ko kadan, ka hararo wani abin mekake tunani"? Dan jimm sarki yayi saikuma ya kalli Otun shima cikeda shirin damuwa yace "abu daya na hango OluwaTobi" da sauri Otun yace "OluwaTobi kuma"? Gyadamai kai sarki yayi yace "Tobi kadaine nasan za'a iya tabamin dazai chanza kaddaran gidan nan, jikina yabani wasu nason kawoma d'ana hari anaso akashe shi sabida masarautan nan ya zamto baida magaji, daman kwanan nan inata mafarkin shi koyau haka saida nayi mafarkin shi, bana ganin komi amafarkin saidai naga Tobi na da inaga tunda ya girma ban taba ganin kukanshiba inga yana kuka amafarkin yanace min please Dad, please Dad, those are the only words dayake gayamin" da sauri Otun yasaki salati arude yace "to mesa baka gayama Ooluwo wanan ba kai shiru harya tafi" girgiza kai yayi yace "inaso afara nunamai vision din yay clear tukunna" ajiyan zuciya Otun yayi yace "to yanzu yazamuyi" shiru shima sarki yayi yace "Tobi is very stubborn bayason security bayason guards su bishi ko'ina, gashi yafita kallon kwallo da daddare har 12 yaron nan yake kaiwa bai dawoba inta kiranshi yaki wani zubin ma kashe wayanshi yake, but everything will change, companyshi ma danakeso yafara zuwa yana aiki bazaije ko, bazai kara fita ba har sai munji me muke ciki, inason u should call the police department inaso abani SSS gida biyar ma Tobi sudinga guarding nashi har anan cikin gida, I can't trust anyone da yarona Otun, Tobi is my whole entire life that stubborn boy dakake gani haka, sanan match din dayake cewa yanada shi a Saudi he's going back next month babu inda zaije" ahankali Otun yace "ananne fa zakuhau sama ku fado kasa da Tobi" da sauri Oba yace "i am ready for that, I won't risk his life for komi idanma yaga dama yay fushi dani for that month duka zamu shirya, and one day zai bude bakinshi yay thanking dina for protecting him, and I don't want anybody har mutanen fada suji maganan nan, thank God bayacin abincin kowa banda na mahaifiyar shi danace shima routine na abincin shi is going to change, just get the SS, talk to them kafada musu mahimmacin aikin and pay them konawa sukeso cus inaso sukaremin d'ana" gyadamai kai Otun yayi yace "angama Sarkina" ahankali yace "tashi katafi, kataho dasu ku sameni anan fada" tashi yayi sanan yaduka yace "nabarka lpy" yawuce yafita daga fadan shikuma Otun dukyabi yadamu, kasa hakura yayi yatashi ya shiga cikin gida, har flat din Tobi.






Ahankali yake taka stairs yana kara karema dakin kallo har zuwa bedroom dinshi yabude kofa ya shiga, ganin dakin yay so mercy ga gadon so dirty ba'a gyaraba, tsayawa yayi yabi dakin da kallo daidai Tobi yabude kofa yafito yana daureda towel waist dakuma karami asaman kanshi yana tsane kitson dake kanshi sai wani irin mayen kamshi yake na sabulun wankanshi, ganin Babanshi yasami gefen gadonshi yazauna yasa ya tsaya looking at his father surprisingly, saikuma yace "Hey Dad, what brought you to my room this early morning"? Hararan shi yayi yace "shiga closet kadauko cream dinka kazo nan" yanda yafadi hakan yayi ya shiga yadauko man shafawanshi yafito yazo zama yayi kusada baban nashi akan gado, Dad yakarbe man daga hannunshi sanan yakai hannunshi yacire towel din kanshi, yana tsanemai gashin da kitson yace "wanan drade din ai ya tsufa ko yaushe zakaje a tsafe agyara kan amaka sabo"? Murmushi yayi yakai hannunshi yaja daya daga kitso ya sauko ta wajen idanunshi ya kalla yace "sai Boy ya warke zamuje tare muyi" murmushi Babanshi yayi daidai yagama sharemai jikin yabude man ya shiga shafamai yace "kasan menene nazo fadama, and I don't want you to argue for once Tobi quietly listen to your father okay" turo baki yayi yace "ainasan just like that bazakazo dakina da sassafe hakaba Dad, kaida bakason anama tashina da wuri" kafanshi yakama ya daura akan cinyanshi yana shafama feet dinshi mai yace "kaga anjima kadan za'a kawomaka security guards bama na nan palace ba daga police department za'a kawosu, they will protect you 2/4/7, duk wanda zai shigo nan side din naka saisun dubashi, duk inda zaka they will accompany you, they will be your shadow daga yau kaji Son" tunda yafara maganan yadaure fuska ranshi yamugun baci, fuskanshi Dad yashafa yace "I am sorry okay, thank God ma bakada any friends, and bazaka fitaba from now har zuwa seven days, idan u wants company nida kaina zan sa adauko maka besty ka Ayoka tazo nan kusha firanku tatafi daga baya" da sauri yace "ni ban cemaka inason ganin wata Ayoka ba, whats with this nadena fita nobody should visit ne dakuma securities ne ko police dazaka zubamin agaban flat, what's with all of that?" Ahankali cikeda lallashi yace "zan fadamaka all in due time just comply now Kaji Tobi" kallon Babanshi yayi trying to understand something a face dinshi yace "Dad you know i hate all this over protectiveness naka ko, I hate it, Dad I just wanna be me, saisa banson zama gidan nan, I want to go out there live on my terms people should see me for who I am, people should realize my potentials batare da influence nakuba, Dad I am strong look at me, you think har yanzu am not man enough to protect myself"? Da sauri Baban yace "ni bance hakaba" da sauri yace "but that's what you mean now dakake daukomin wasu police suyi guiding dina saikace yaro, Dad you always make me feel less of a man, and is affecting me kullum ganina nake karamin yaro sabida haka kuke kirana alhalin I am not one, my mate a North sunada about 8kids amman nine ake dauko wasu maza da maybe I am even stronger than me su tsare ni" yay maganan sounding so angry dan har karshen zuciyan shi he hates that sometimes yanama wishing dabai foto ta gidan sarautan ba, he don't live life yanda yakamata, har abokanai ba'a wani bari yayi, dayayama yasamu suka bari yafara buga ball din, cikida lallashi yace "duka duka nawa suke, su yan North suna aure dawuri both mazansu da matansu al'adansuce, kai duka duka nawa kake, yaushe kafara girma? I got married at the age of 40, so please allow me to take care of you, naxo fadamaka dakaina ne sabida karka gansu kaji haushi, karkuma yazo xaka fita su hanaka just stay here, idan kanaso nakira maka Ayoka zan kira" cikin fushi yatashi yace "ni karka kiramin kowa tom" yafada closet dinshi ya maida kofan yabuga Babanshi nabinshi da kallo, girgxa kai kawai yayi sabida yasan halinshi Tobi yadauko tsaf shiyama ubanshi rashinjin dayamafi na Tobi, tashi yayi yafice ya tura cleaners su gyaramai dakin dan yasan sabida rashin idon yaronshi ne yasa dakin yakeda datti.








Saida yay salla sanan yafito, flat dinsu yaje for breakfast, dukansu suna dinning harda Dami dake zaune fuskanta ya kumbura harda idanunta suna jiranshi yazo, kujera yaja yazauna yace "good morning Mum" "good morning son" tai maganan tana bashi plate din breakfast dinshi karba yay ya ijiye gabanshi batare daya kalli su Dami ba, kaman daga sama yaji Dami tadafashi ahankali adan tsorace ma hakan yasa yadaga kanshi yajuyo ya kalleta babu alamun wasa akan fuskanshi. Murya chan kasa tace "Tobi sorry about what I did yesterday" daukekai yayi yace "nizaki cema sorry or wanda kika maida makaho"? Sake danne zuciyanta tayi sabida gayama su Mum datayi zatai making peace dashi tace "zanje nabashi hakuri nagama breakfast, zaka rakani dan Allah muje tare sabida kagani" "go alone" yafadi batare daya kalleta ba, da sauri babansu yace "haba kai mesa bakason zaman lpy, yayarka naso ku shirya kuma bazaka rakata ba" dan jim yayi saikuma yace "ok" yacigaba da cin abincin sukuma duk sukai murmushi harda su Taye.






Saida suka gama breakfast din tass, sanan Dad ya kalleshi ganin shitake jira yace "tashi kuje" sanna yacema daya daga cikin guards din dake cikin masu tsayuwa agaban falo yace "kaisu bangaren yan aiki" sanan yatashi, itama Dami ta tashi tareda karban wani Baban Ted fari mai kyau da Taye kebata, karba tayi ta rungume tana tafiya ahankali tana biyedashi tana sanye da short daya tsayamata a cinya da farin singlet mai kyau na mata batare datasa bra ba, kanta sanye bone straight wig, tanada kyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login