Showing 1 words to 3000 words out of 96407 words

Chapter 1 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3599

1 & 2 🦋🦋FANSAR MACE🦋🦋

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_______da sunan Allah me rahama me jin kai.

Book one

1 & 2

A cikin tafiyar rayuwa, ba mu da ikon tsallake ƙaddara mai kyau ko mara kyau, domin komai yana gudana ne bisa rubutun Ubangiji. Idan Allah Ya ƙaddara alheri, babu mai hana shi isa gare mu; haka idan ya ƙaddara jarabawa, babu mafita sai hakuri da dogaro gare Shi. Kyakkyawar nasara da cin jarrabawa ba ta samuwa sai ta hanyar juriya, imani da tawakkali. Jarabawa hanya ce ta gwaji, kuma cin nasara a kanta alamar kusanci da rahamar Allah ne. Don haka, kaɗan ne daga cikin bayin Allah ke samun ikon cinye waɗannan jarrabawa, ba saboda ƙwazo ko wayo ba, sai dai saboda falala da so daga ubangiji.

Fansar mace labari ne me ɗauke da darususuka me tarın yawa. tare da zalunci da cin amana da aka tafka me munin gaske. A ɓari daya kuwa, soyayya ce me zafi wanda ta dalilin fansa yake neman rugujewa,ku biyu ni a cikin wannan littafi da yazo da salo na daban dan jin yanda zata kaya,shin zalunci yana tasiri?ko kuma soyayya ze rinjayi fansa?. Ku kasance dani Mrs Isham dan jin yanda zata kaya.

WAIWAYE (mafarin labari)

PROGRESS RADIO TV GOMBE

Wannan Doctor da ya shahara a duniya domin baiwa da kwarewarsa akan aikinsa ne zaune akan kujera,tare da daya daka cikin ma'aikatan progress Radio wanda ze gabatar da hira da shi,kyakyawan mutum wanda a kalla ze kai shekaru hamsin da uku a duniya. duk da ya manyanta amma babu alamar tsufa a tare dashi. Chocolate color ne yana sanye da manyan kaya farare. fuskarsa ɗauke da murmushi kallo daya zaka masa ka gane kamilallen mutum ne me daraja da dattako.

Presenter da ze gabatar da shirin ne ya fara magana

“Assalamualaykum masu sauraro! kuna tare da Progress radio gombe akan meter casa’in da bakwai da digo uku FM. da fatan zaku kasance da mu domin yau muna tare da babban bakon da ku ka kasance kuna begen son kasancewa dashi a wannan gidan radio na mu domin yin hira dashi,wannan bako namu bakowa bane face DOCTOR SAGIR LELEWAL. Ku kasance dani Dahiru Muhammad wanda zan gabatar da wannan shiri me suna bakon mu a yau. Muna yi maka barka da zuwa wannan gida radio namu. sannan muna godiya da amsa goron gayyatarmu da kayi. Dr. Sagir muna so ka sanar damu takaitaccen tarihinka”

Murmushi Dr. Sagir Lelewal yayi yana me gyara zaman glass din idonsa ya ce “Assalamualaykum musulman duniya Ina yi wa kowa barka da wannan lokaci. Sunana Sagir Mohammed Lelewal wanda aka fi sani da Dr. Sagir Lelewal ni haifaffen dan jahan Gombe ne a karamar hukumar kumo. Iyayena Fulani ne usul, wanda suka bada rayuwar su ga kiyo da noma in da haka nida yan uwa na muka taso muka tarar. Duk da kauyen mu makaranta daya ce kuma primary ce anan nayi karatuna daga aji daya zuwa aji shida. Bayan na kammala mataki na farko na tafi birni gurin kawuna domin ci gaba da karatuna inda har Allah ya bani daman gun karatun likitanci,bayan na gama degree na tafi ƙasan India na yi masters dina a can na zama cikekken medical doctor. inda na dawo ƙasata garina na samu aiki a babban asibitin gombe wato federal medical center (FMC) in da har na kawo matakin Medical director (MD) wannan shine kaɗan daga cikin tarihina.”

Mai gabatarwa Dahiru Muhammad ya ce “Masha Allah. Allah ya yi wa rayuwa albarka. Dr. Sagir duk da ni na san kana da aure amma nasan masu sauraro zasu so su ji daga bakin ka domin kuwa waka a bakin me ita yafi dadi…”

“Ina da aure,matata daya da yarana uku maza biyu da kuma mace daya.”

“Masha Allah masu saurara fatan kuna tare da mu domin jin wannan hira. Dr. Sagir ka kawo ci gaba sosai a wannan jaha na gombe inda ka taimakawa talakawa da dama wajen samun magani da kuma tiyata kyauta,inda a hakane ka sace zuciyoyin al’umma maza da mata manya da yara kowa yana kaunar ka saboda yanda ka ke taimakon al’umma. Shin menene dalilinka na batar da dukiyanka me yawa wajen taimako wanda yanzu a cikin manyan masu kudi ba kowa ne ke da zuciyar taimako irin naka ba.”

Gwauron numfashi Dr. Sagir Lelewal ya sauke “tabbas akwai dalili me karfi wanda kullum in na tuna se na zubar da hawaye. A lokacin da na tafi birni domin yin sakandari na,Ina jss two mahaifina ya kamu da cutar daji. wanda a turance ake kiransa da cancer. aka kawo sa nan cikin gombe domin yin jinya a nan ne likitoci suka sanar da mu yana matakin karshe inde ana son ceto rayuwarsa dole se an masa tiyata. Ba tiyatar bane matsala kudin da zaa yi tiyatar ne, wanda ko da ace zaa haɗa kudin shanayensa Kaf tofa bazasu kai kudin nan ba. Mun yi kuka sosai muna ji muna gani a gaban idon mu mahaifin mu ya mutu ta dalilin rashin kudin tiyata da na magunguna. Wannan dalilin ne yasa na ɗaukarwa kai na alkawari zan zama likita sannan in share hawayen talakan da basu da karfin nemawa kan su lafiya.kuma Alhmdullh Allah yana bani nasara akan burina.”

“Allahu Akbar Allah yajikansa da rahama.”

“Ameen ameen”

FEDERAL LO-COST

a ƙerarren gidan Dr. Sagir lelewal wani ƙaramin yaro ne da baze wuce shekara goma sha daya ba,yake gudu hannun sa riƙe da remote yana gudu yana dariya tare da waiwayan bayan sa yana faɗn

“ ALISHA Darling ba zaki iya kama ni ba”

Wata kyakyawar budurwa ce take bin sa da gudu, doguwace balaifi chocolate color tana kama da Dr. Sagir Lelewal sosai. A kalla zata kai shekara goma 18. kyakyawa ce makura ta kasance siririya bata da jiki sam duk inda kuke tunanin kyau na black beauty Alisha ta wuce nan tana da kyau na fitan hankali.tana sanye da wandon jeans pencil da vest.

“Aryan ka tsaya ka bani remote din man,baka ga Ina kallon hiran da ake yi da Papa bane?” Ta faɗa tana bin sa amma Aryan yaƙi tsayawa se gudu yake yi yana wasa da hankalinta. Maman su da take zaune a falo ne ta miƙe tana

“Nikam Alisha da Aryan lafiyan ku kuwa? Gaba daya kun cika gidan nan da ihu”

Cikin magana irin na su na sangartattun ƴaƴa tace “Mommah shine fa Ina kallon hiran da ake yi da Papa yaron nan yazo ya canza min channel tare da ɗaukan remote din ya gudu”

Ta yi maganar kamar zata yi kuka. Yanda take magana daki-daki cikin nutsuwa da tura baki zaka fahimci shagwababbiyace ta gidan gaba sannan kuma miskila.

Girgiza kai Mommah ta yi tace “Sorry Alisha darling. Na san halin Aryan da tsokana kyale sa zo mu zauna anan mu kalla kin ji ko? Rabu dashi kai kuma sena yi seizing din Ps3 game din ka in ka sake shiga mata daki tunda ta faɗa maka countless time bata so amma ka ƙi ji”

Riƙe hannun Mommah tayi tana faɗin “is okay Mommah Kyale sa nasan baze ƙara ba, ko Aryan dina ?”

Gyada kai yay saying “yes Alisha darling I promise you I won’t do it again “

“Good boy “ ta faɗa tana karɓan remote din a hannun sa. Muryan Dr. Sagir suka ji a Tv yana amsa tambayoyin da ake masa yasa Alisha da Aryan suka yi tsalle a tare suna

“Yeahhhhhh ga papa ga papa”

“Tom duk ku zauna mu kalla a nan tare. Na san yayan ku Zaid yana can bedroom dinsa yana kallo shima.”

Zama suka yi Alisha na kwanciya a jikin Mommah suna ci gaba da kallon su.

Bayan kaman 30 minutes a time din an kammala shirin bakon mu a yau suna tsumayin jiran dawuwan mahaifinsu Zaid ya fito daga bedroom dinsa,hannun sa riƙe da goran ruwa fuskarsa ɗauke da murmushi kyakyawan matashi ne da akalla ze kai shekaru ashirin da daya zuwa da biyu. duka yara ukun suna matukar kama da juna sosai daga kalar fatar su har kamannin su komai daya.

“Oh my God…. Gaskiya papa jarumi ne. I love the way he answers all the questions smoothly omo papa ya haɗu ah swear “ ya faɗa yana zama a kujeran da su Alisha suke zaune.

Tana kwanto da kanta a kafaɗarsa ta ce “Wallahi kuwa “ suna haka kuwa suka ji an buɗe gate sun san ba kowa bane face Dr. Sagir Lelewal. da gudu duk yaran suka fita a falon fitowansu yayi dede da fitowar doctor daga motar rungumesa suka yi suna faɗin “Oyoyo papa” dariya yayi yana

“God when? Yaran nan zaku karya ni Allah ya nu na min ranan da dukkan ku zaku san kun girma,most especially you Zaid. You always behave like your younger siblings “

Dariya Zaid yayi yace “papa please duka ma yaushe na kai twenty years din. Am still a kid guy”

Marin wasa ya masa a keya “ au ni ne guy din Kenan ?”

“Papa today nasan ka kara fans sosai,wallahi hiran ku ya yi dadi sosai kamar kar ya ƙare.”

Cewar Alisha tana rungumesa again.

“Thank you darling oyah mu je ciki saboda am so tired and hungry “

“Papa nima yunwa nake ji kai na ke jira ka dawo mu ci abinci tare."

Zare idanu Zaid and Alisha suka yi suna kallon Aryan da yayi magana a tare suka furta “wallahi papa he’s lying dazun ya gama cin abinci plate biyu”

Riƙe hannun Aryan yayi ya ce “ban yarda da ku ba. Nasan auta na baze min karya ba”

Ciki suka shiga suna ta masa surutu shi kuma yana biye musu yana dariya. Dr. Sagir Lelewal yana da kyakyawan alaka da shakuwa me karfi da iyalansa he is so friendly. Shi da matar sa Hajiya Hannatu suna matukar son ƴaƴan su sosai, haka suma yaran suna son iyayensu sosai. Komai suke nema a rayuwar nan ana yi musu shi. Zaid shine babban ɗan su yana university of Gombe (GSU) yana 200 level a yayinda Alisha ta gama secondary school one week ago tayi jamb tana jira ya fito ta nemi admission a GSU itama. Se kuma ɗan autansu wato Aryan yana primary five suna shirye-shiryen zana jarabawa. Duk da yanda yake nunawa yaransa so da kauna hakan be hanasa basu ingantaccen tarbiyya ba.suna da ilimin addini uwa uba sun san darajan dan adam,duk da uban su yana da kudi hakan be sa sun ɗauki kan su sun fi wasu ba musamman Alisha ba kowa bane yasan ita din ƴar Dr Sagir Lelewal bace. saboda tana jin dadin kasantuwarta a cikin yara marasa karfi duk da bata da kawaye sosai. Iya yan ajinsu ne suka san complete name din ta. Ko a social media handle din ta da suna Alisha darling kawai take using. Ba kaman Zaid ba da yake TikTok da instagram ba,kowa ya san shi ya san kuma shi jinin Dr Sagir Lelewal ne.

Abinci me aikinsu ta jera musu suna ci suna hira gwanin burgewa.

“Wayyyo na manta shaf yau muna da lectures 3 to 4Pm. Mommah,papa bye se na dawo “ ya faɗa yana ɗaukan kofin tea ya nufi falo. akan table ya ɗauki car key din shi ya na kokarin fita Mommah ta ce

“Zaid yanzu haka zaka tafi makarantan babu handout balle jaka?”

Yana tafiya yace “Duk suna cikin motana byeeeee na tafi se na dawo”

Girgiza kai kawai suka yi suka ci gaba da cin abincin su.

Bayan sun gama ne Doctor ya dubeta “darling result din jamb din ku be fito bane har yanzu ?”

“Yes papa nima shi nake jira. Ina son please papa ka tura ni Kano in yi karatu acan wallahi na gaji da Gomben nan is so boring “ ta Karashe maganar tana yatsina fuska.

Murmushi irin na su na manya suka yi ya dubi Mommah yace “bana gaya miki ba,small chance in Alisha darling ta samu tsaf zata gudu ta bar mu a nan gombe ba ruwanta.”

“I see yarinya zata tafi wani gari yin karatu ta bar iyayenta anan” cewar Mommah

Tura baki ta yi tana ajiye phone din hannunta “Fineeeeeee…… na ji na hakura da zuwa Kano karatu,tunda duk time din da nayi magana se kun kawo excuses bana son zama da ku blablablablaaaaaa”

Dariya suka yi har da Aryan ,jawo ta jikinsa yayi yana faɗin “nooo darling bawai muna hanaki freedoms din ki bane. Kawai akwai abinda jikina yake bani ze faru nan gaba ne shisa ko da yaushe bana so kiyi nesa damu. Na miki alkawari hutun first semester da za ku samu in de da rai na da lafiya zan kwashe ku duka mu tafi Hutu Dubai I promise you “

“Wowww papa dagaske? Wallahi na yarda I love you so much papana “

“Love you too darling “

Mommah kallon su kawai take tana murmushi kafin ta ce “oyah guys time din ku ya kare da papa yanzu time din Mommah ne. Duk ku tafi bedroom din ku”

Miƙewa suka yi Aryan yace “ nooo Mommah this is unfair, I really want to spend the whole day with papa”

“Me too kawai Mommah wayo ta mana” cewar Alisha. Sake baki Mommah tayi Tana kallon su kafin ta jinjina kai

“Okaayyy naji ku zo ku zauna amma ku sani yau No phone for you Alisha. and for you Aryan Noo Ps game. Duk ku zauna maza ni bari in baku guri “ ta faɗa tana miƙewa ai a saba’in suka bar falon jin zaa hana su waya da game. Dariya tayi tana zama shima dariya yayi yana

“These children are so funny Allah ya raya min ku”

“Ameen papa… hiran yau was so excited. Allah ya ƙaro dubun nasarori ya kuma kare min kai daga Sharrin masu sharri”

“Ameen my wife”

Yana rufe bakin sa wayar sa ya soma ringing yana duba wa yaga sunan ‘Doctor Jamal’

ɗaga wa yayi shuru yayı yana sauraransa

“Okay “ kawai ya furta ya ajiye wayar yana furzar da iska.

Kallon sa Mommah ta yi “meyafaru papa?”

“I don’t know yet kawai yace min akwai important meeting a asibiti yanzu. kuma har da ƴan siyasa sanın kan ki ne kwata-kwata bana son haɗa hanya da wayannan mutanen shima Dr Jamal ban san meye haɗin sa da yan siyasa ba.”

Cikin kwantar da murya tace “kuma yanzu din zaka tafi ?”

“Ya zan yi to tunda sun ce meeting din is very important “

“Shikenan to Allah yasa mu ji alkairi”

Dama already ya yi wanka ya sauya kaya driver kawai ya ɗauka suka nufi FMC.

Ko da ya isa dakin taro da manyan doctors suke gabatar da meeting ya shiga domin Dr Jamal yace masa a ciki suke. Yana shiga ya tarar da manyan doctors guda uku har da Dr Jamal din se manyan yan Siyasa guda hudu. Suna zaune zama yayi fuskansa ba yabo ba fallasa.

“Barkan ku de”

“Yawwa barka da isowa Dr Sagir Lelewal “ cewar daya daga cikin manyan yan siyasan da suke zaune saboda shine babban su,kallo daya ya masa ya gane sa bakowa bane face Hon. Modibbo Ɗan gaske,a gefen sa kuma akwai Hon. Hashim zakewa tare da Chairman Habibu Katanga,se na karshe da ya kasance Christian ne shi me suna Chukuemeka Peter.

“Shin zan iya sanın dalilin da ya sa aka kirani?” Yayı tambayar yana kallon Dr Jamal,cikin shakkan sa Dr Jamal ya soma magana yana carkewa domin ya san wanene Dr Sagir Lelewal

“Dr dama wani opportunity ne suka zo mana dashi me gwabi wanda duk zamu amfana dashi daga mu har su. Wannan harkallan zaa raba komai 50-50% ne wanda a kalla kowa ze samu sama da million dari biyu (200 millions)” tsare Dr Jamal da ido kawai ya yi yana sauraransa bawai dan ya fahimci inda zancen sa ya dosa ba.

“Se de har yanzu ban gane inda wannan zance naka ya nufa ba Dr. wani irin harkalla ne wannan da zamu samu kudi sama da 200 millions?”

Ya tambayesa ba tare da ya cire idonsa akan sa ba

Gagara magana yayi saboda yaga irin kallon da Dr Sagir Lelewal ke bin sa dashi.

Gyara zaman sa yayi cike da izza da iko yace “ nasan kasan wanene ni ba se na sake gabatar maka da kaina ba”

“Kwarai na san ka Hon. Modibbo Ɗan gaske “ Dr ya faɗa yana kwantar da bayansa a kujerar da yake zaune.

Jinjina kai Hon. Ɗan gaske yayi ya ce “good. Abinda Dr Jamal ya gagara faɗa maka ni zan maka bayani dalla-dalla yanda zaka gane.

Wata biyu da suka wuce Dr William babban likita daga kasan Amerika ya shigo Nigeria domin akwai abinda yake son gwadawa inda ya same ni ya min bayani kuma na fahimcesa sosai.

Sun haɗa sabon kwayoyin magunguna na ciwon kai,ciwon ciki da kuma zazzabi kuma suna son su gwadasa suga ya yanayın aikin magungunan yake. wannan dalilin ya taho Africa domin haɗa hannu da manyan mutane irin mu domin gwada wayannan magungunan akan mutane. Kuma bama wannan kaɗai ba ya yi mana tayin naira billion darı dari. Tabbas wannan harkalla ce me kyau wanda duk zamu ji dadin sa. Sanın kana da al’umma da suka yarda dakai sannan suke son ka ne yasa mu ka ga haɗa hannu da kai ze taimaka mana matuka.”

Tunda Hon. Ɗan gaske ya fara magana Dr ya zuba masa ido ya gagara ɗauke idon sa akan sa, he can’t believe what his ears just heard. Mamaki ne ya rufe sa da yasa ko magana ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login