Showing 93001 words to 96000 words out of 96407 words
Chapter 32 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
/>
Dariya Alisha da Zainab suka yi jin abinda ta faɗa Alisha ta girgiza kai
“Ameera Allah ya shirye ki”
Ko da time din karyawa yayi saboda ita yau baa yi breakfast a dinning ba,Adda da su Yusra a falon Adda aka yi breakfast su Maryam kuma a part din su.
Haydar yana office din sa gaban sa System yana aiki da shi ya cire suit na saman ya rataye a kujera farar rigar ya bari se necktie,hankalinsa duk yana kan system din dan tunda ya zo ya zauna system din ke gabansa saboda akwai abu me muhimmanci da yake aiki akai,wayarsa se haske yake kawuwa yana ɗauke wa amma da yake aiki yasha masa kai be bi kan wayarsa ba,vibration da wayar ke yi ne ya ishe sa hakan yasa ya zare glass din idon sa yana kwantar da bayansa a jikin kujera me juyawa trying to relax for some time,kiran da ya kuma shigowa ne yasa shi jan siririn tsuka yana kai hannunsa ya ɗau wayar,da mamaki ɗauke kan fuskarsa yake kallon his phone screen ganin irin uban tarın missed calls din da aka mishi ga kuma texts na mutane daban-daban. Da sauri ya shiga call logs din sa dan abun ya ba sa mamaki sosai baa taɓa tara mai irin wannan missed calls me shegen yawa ba
5 missed calls din Ɗan gaske ya gani,sai 2 missed call na Adda,Alisha 2 missed calls,ga kuma su Sadeeq da sun masa missed calls ya fi ashirin ban da wayanda suka kasance mutanen gun aiki da de sauran su. Message ya shiga nan ya ga Adda texts him da
“Ka dawo gida akwai matsala “
Dam ya ji gaban sa ya faɗi ,a take ya roƙi Allah yasa ba wani mummunar abu bane ya faru ake neman sa haka ruwa a jallo,yana zaune yana wannan tunani Kenan kiran Sadeeq ya shigo ɗagawa yayi yana sawa a handsfree tare da rage volume.
“Man ina ka shiga haka mun maka missed calls bila adadın ina ka ajiye wayarka haka?”
“Ina aiki ne ban san an tara min wayannan calls din ba se yanzu nagani,Dude fatan komai lafiya yanda ake nemana scared me a bit “
Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke wanda ya sake jefa Haydar a ruɗu kafin, ya ce
“Haydar,is your brother Sameer”
“Meye ne ya faru da Sameer din?”
A bangaren Sadeeq ya furta
“Na ga alama ba ka ma san abinda yake faruwa ba kana can a office din ka busy with your work, ka hau media ka ga abinda ke faruwa,zamu yi waya anjuma”
Yayi hanging call din.
Facebook ya hau abinda ya fara cin karo dashi shocked him to death. ya kasa gasgata abinda ya ke gani,Sameer ne zaune ga mata sun zagaye sa babu kayan kirki daga su se pant da bra gaban su kayan maye ne su shisha,giya, da kuma cocaine,yan mata biyu zaune akan cinyarsa yana kissing din dayar,dayar kuma yana shafata kamar me shafa mata mai.
“Innalillahi wainnailaihi rajuun,Sameer burinka ya cika na son zubarwa Ahalin Ɗan gaske mutunci, you finally succeed”
Yayi maganar dakyar a ƙasan makoshi tsabar takaici da bakin ciki, wayarsa da car key ya dauka kadai ya bar office din ya shiga motar ya nufi gida.
Gudun da ya yi ne ya kawo sa gida a less than 10 minutes,yana shiga falo ya same su ilahirinsu zaune sun yi carko-carko,Sameer da Ɗan gaske idanun su sun yi ja more especially Sameer jikin sa rawa kawai yake yi. Adda kam tagumi kawai ta buga ta zubawa Sameer ido idonta ko kyaftawa ba yayi, su kuwa su Yusrah sun yi jugum duk fuskokin su dauke da matukar damuwa har da Alisha da tayi jugum itama innocent face dinta dauke da damuwa. Maryam na rike da Aryan tana shafa mai baya.
Shigowa falon Haydar yayi yana bin sa da kallon takaici, a kausashe ya furta
“Burinka ya cika ko? Na ce burinka ya cika ko Sameer? se da ka yi abinda ka zubar wa da gidan nan mutunci, na sha fada maka wannna halin ka ze taba mutuncin gidan mu amma for once ba ka taɓa ɗaukan magana ta ba, gani ka ke kamar ina takura maka ne kuma ban kai in gaya maka gaskiya ba saboda ni ƙanin ka ne duba yanzu abinda ka janyo,yanzu in an tashi haka zaa dinga kwantance ana gidan Honorable Modibbo Ɗan gaske ne,kuma akwai Detective chief superintendent a gidan amma ya je yana aikata abinda ya gadama,da wannan zaa dinga kwatancen gidan mu Sameer, haka zamu zama abun dariya a idanun mutane kar ka manta da hakan.
Ka zubar da na ka mutuncin tare da namu har da na ƙananan ƙannen mu mata,are you satisfied now? Faɗa min hankalin ka ya kwanta yanzu?”
Ya faɗa yana isowa gabansa rai a matukar ɓace yana maganar ma yawun bakin sa ɗaci suka koma mai.
Miƙewa tsaye Sameer yay yana “ Haydar you need to believe me? Wallahi this is an old video,I’m a changed person now ko Maryam za ka iya tambaya,na dena komai, tunda na shiga neman takara you can even ask Father shi ya ba ni shawarar in zubar da komai in rungumi siyasa in ba haka ba zaa samu matsala. Ban san ya aka yi aka samu wannan video ba, ban san aina,waye yayi sa ba, believe me “
Tabbas shima in ze ba da shaida ze iya cewa tunda Sameer ya sako maganar siyasa a gabansa ya sauya sosai,saboda yana tsoron yayi abinda ze taɓa mai zaben sa,ya dena shaye-shaye,ya dena bin mata saboda kullum suna government house,ya dena hayaniya da Maryam. Ba ya ma gidan balle ya samu saɓani da kowa. Amma fa in su sun san da wannan ai mutane ba ruwan su da wannan kuma ba su isa su hana kowa judging ba.
“You see ? Abinda ake gudu Kenan shisa ɗan uwanka ya ke so ka gyara abubuwan da ka ke yi, yanzu wa gari ya waya? Na sha faɗa maka... Son kar ka yi abinda ze ruguza maka wannan siyasar ta ka,amma se da ka yi hakan hankalin ka ya kwanta, ga shi an sauke lasisin takaranka,kana ji kana gani kujeranka ya kuɓuce maka zaa ɗauka ne a bawa abokin takaranka”
Ɗan gaske ya faɗa yana karkaɗa kafa rai a bace.
Girgiza kai yayi “da gaske an sauke maka lasisinka? Mtsssw dama wannan abun an yi sa ne intentionally saboda a lalata maka zaɓe”
Cewar Haydar yana rike kugu, ya ji haushin lasisin Sameer da aka sauke sosai, be ji dadi ba at least sabods zaɓen Sameer ya fara sauyawa.
Sameer da kamar ze yi kuka yana jin zafi da ƙuna a ƙarƙashin zuciyarsa, ya ce “ Wallahi Haydar duk wanda na samu da sa hannun sa a fitowar wannan video se na ga bayan sa, Zaɓen nan na sha wahala na kashe makudan kudadena saboda a zabe ni. Kawai daga karshe a rusa min komai wallahi se na ɗau mummunar mataki akan duk wanda na Kama da sa hannun sa a wannan abun da aka min. Wannan alkawari na ne. An bata min suna yanda ko a nan gaba bazan iya neman wani kujerar ba,ina da burin zama dan siyasa kamar Baba amma ka ga abinda aka min an taba min carrier na, they ruined my image bazan taba yafe wannan abun ba,zan fara bincike daga nan har karshen numfashi na”
Ya fada da murya me cike da daci a zuciyarsa,dafa kafadarsa Haydar yayi
“İn sha Allah duk wanda ya aikata wannan abun se ya shiga hannu zan taimaka maka wajen lalubo wanda ya daura video “
Daura hannun sa yayi akan na Haydar hawayen takaici da bakin ciki suna kokarin zubowa daga idanunsa amma da yake kansa a kasa babu wanda ya lura da haka
“Thanks bro” ya fada haka yana wucewa Part din sa.
Duk bayan sa suka bi da kallo suna ji babu dadi a ran su,Adda ta dubi Dan gaske
“Yallabai an ya ba abokan gaban ka bane suka sako wannan ahali a gaba ? İn ba haka ba meye haka? Farko video Meenal? Na biyu aka maka shune har gida aka zo aka kama ka,yanzu kuma Sameer? Ka duba yanda ya nutsu duk saboda wannan siyasar ya gyara dabi’unsa saboda kujeran nan,amma ka duba lokaci daya aka lalata masa komai, anya baa yi wa gidan nan baki ba kuwa? Ni gaskiya bana son wani mummunar abu ya kara faruwa, yakamata a yi saukan Qur’ani a kore duk wani mugun ido da mugun baki, a samu a yi auren Alisha da Haydar lafiya”
“Kar ki damu babu abinda ze faru ni Modibbo na fi karfin su” ya fada yana mikewa shima ya nufi part din sa.
“Haydar ka yi wani abu akai in ba haka ba video nan haka ze yi ta yawo”
Cewar Adda tana kallan sa
“İn sha Allah “ haura part din sa shima yayi dan yana bukatar shan maganin ciwon kai.
A haka aka yi kwana uku video Sameer na yawo a media ya zamana ko fita baya son yi ya koma so silent yana shirya yanda ze dau mummunar mataki akan wanda ya watsa video nan,ya sa yaran sa yan daba suna masa bincike amma har yanzu shuru ba labari . Duk da Haydar yayi magana da wasu influencer da suka yi sharing video a page din su kuma yasa sun goge, amma video se kara trending yake musamman a TikTok da Instagram.
Yau saura kwana biyu biki zuwa yanzu Haydar ya dauki Hutu a gun aiki yau ma shi yakai Alisha da su Yusrah Saloon kuma ya dawo da su bayan an kammala.
Bayan sun dawo ne tana dakinta tana shan maganinta kiran Mujahid ya shigo dagawa tayi ta kara a kunne
“Amarya “
“Uhmm neman magana zaa kira wannan ko me Mujahid?” sai da yai dariya me sauti kafin ya ce
“Eh to kusan haka,dama Zaid ne ya ce yana son magana dake,ga shi nan”
Tayi mamaki jin wai Zaid na son magana da ita amma akan me, ta ɗauka ai ya ɗauki fushi me zafi da ita amma ga shi yana nemanta
“Ykk” kadai ya faɗa cikin shan kamshi
“Ina lafiya. Kai fa!?"
A taƙaice ya furta “doesn’t matter, Daren jiya mun yi magana sosai da Mujahid, kuma ya fahimtar dani dalilin da yasa ki ke son yin wannan aure kuma na fahimta,but you have to promise me babu abinda za ki bari ya shiga tsakanin ki da Haydar,saboda bana fatan mu haɗa iri da wayannan la’anannnun mutane”
Murmushi me sanyi ta sake tana jin farin ciki ya dabaibayeta, finally ɗan uwanta ya goya mata baya akan plan dinta.
“Thank you so much Ya Zaid dina I love you so much, na maka alkawari babu komai da ze shiga tsakanina da Haydar.”
“Darling I missed you so badly. I don’t care da wannan auren, I just want to see my lil sister, yaushe za ki zo?”
Waro ido ta yi ta san wanann ba me yuwa bane “ Ya Zaid fitowa na ze yi matukar wahala”
“Saboda wannan auren ne ki ke so ki ce bazan gan ki ba ko me?”
Dafe goshi ta yi tana jin rigimar Zaid, ta san yanzu se ya ƙara cewa ze yi wani fushin
Cikin kwantar da murya ta ce “Ko kaɗan ba haka nake nufi ba, ka dena sa wannan auren a ranka, ba shi da muhimmanci a guri na, dashi da babu shi duk daya ne. Kuma dole ka ga lil sis din ka. I’ll make a plan yanda ku za ku zo gidan ba wanda ze gane ku,daga yau zuwa gobe zan ga abinda zan yi”
“Okay I trust you “
Murmushi tayi bayan sun gama wayan. yanzu hankalin ta ya fi kwanciya tunda Zaid ya amince.
Adda ne da wata mata suka shigo dakin suka same ta
“Ƴar albarka,, ɗazun kun yi magana da Yusrah ko? Dan ta same ni ta na ce min wai dayan setin akwatunan lefenki bana zamanı bane ba lallai ki so su ba,yanzu ban wayar ki in ba ki number manager company fashion trolley and more suna da akwatuna masu kyau se kiyi magana dasu su kawo mana gobe tunda jibi ne daurin aure, in ha so sai su ɗauki wayancan din”
Wani irin dadi ne ya mamayeta kamar ta daga hannu ta gode wa Allah a gaban su saboda tana zaune mafita ya zo ya same ta har inda take. Wayar ta ba ta, Adda ta sa mata number tare da faɗin
“Ki kira su fa ? Gobe su zo su kawo miki sabbi se su tafi da wayancan din kin ji”
“To Adda nagode “
“Yawwa “
Suka fita,suna fita kuwa ta kira Mujahid ta faɗa musu yanda suka yi da Adda yanzu.
Washe gari ana gobe ɗaurin aure aka kira kwararriyar me yin dayis ta zo around 10:00 na safe ta ranɗaga mata mayen dayis hannu da kafa dayis bakaramin kyau yayi ba kamar a lashe.
Zuwa karfe biyu ya bushe Maryam ta taimaka mata ta wanke,dama a falon downstairs ake lallen so gaba daya su matan da su Adda da kowa suna downstairs ba kowa a part din Adda kowa na ƙasa. Bayan an wanke mata ne ta haura sama ta shiga dakin ta tayi wanka.
Around 3:30 wasu samari biyu suka shigo gidan aka yi directing din su har zuwa main falo inda kowa yake suna sanye da riga green iri daya kansu da facing cap fuskar su kuma sun rufe da nose mask.
Suna riƙe da akwatuna na zamani masu matukar kyau,cikin girmamawa suka gaishe su, Adda ta ce
“Yawwa kun kawo akwatin ko, to ku haura upstairs kofan farko nan ne bangare na se ku ajiye akwatunan a parlor, sannun ku”
Kai suka gyada sannan suka haura saman kamar yanda ta musu kwatance suka shiga.
Sameer ya fito daga wanka ya gama shiryawa ze fita Kenan Hajja Hauwa ta kirasa ta ce ya haɗa ta da Adda za su yi waya ta kira layinta baya shiga, to ya ce sannan ya nufi part din Adda ko da ya shiga be ga kowa a falon ba, se akwatuna da ya gani a zube,hanyar dakinta ya nufa se kuma ya ga kofar dakin Alisha a wangale, isa bakin kofar yayi ya tsaya yana leke baya son ta gan sa dan ya ganta tsaye a bakin window ta juya masa baya kanta ba dankwali tana sanye da doguwar riga mara nauyi.
Har ze shiga kuma ya dakata saboda magana da ya ji tana yi ita kaɗai
“Ban taɓa ɗaukan alkawari ban cıka ba, in na ce zan aikata abu to tabbas se na aikata, Sameer Ɗan gaske ya azabtar dani yanzu na fara ɗaukan fansa na akan sa, lokacin da zaɓen sa ya ruguje ba ƙaramin dadi na ji ba, yana ta haushin neman wanda ya watsa video sa da yayi sanadiyyar taɓa zaɓensa, be san yana zaune a gida daya da wacce ta saka aka watsa video ba, be san da cewa ni ce nan na sa aka fitar da video da ya ja ya rasa zaɓen sa ba, kuma burina ya cika na yi abinda nayi alkawari mutumin da be iya ruling din gidan sa ba taya ze iya ruling din al’umma gidahumi mara tunani”
Ta ƙare maganar tana dariya
Wani irin bugawa da tafarfasa zuciyar Sameer ya hau yi, jikin sa ya soma rawa haka hannun sa ya kasa riƙe kansa kai tsaye ya shiga dakin na ta idon sa akan ta.
“Dama ke ce ki ka watsa video na Alisha? Menene na miki da za ki ruguza min abu mafi muhimmanci a gare ni? Lallai da na san ke ki ka yi haka da na jima da kashe ki,dama ku ƴaƴan talakawan nan babu abinda ku ka iya se bakin ciki da hassada, tabbas yau se kin san ni wanene. zan samu Haydar in faɗa masa ke din sam ba macen aure bace, kuma in aka Kore ki in sanya yarana ƴan daba su yi miki fata-fata.”
Lumshe ido tayi iskan dake shigowa a window yana sauka akan kyakyawar fuskarta dake dauke da murmushi, ta juyo gare sa a hankali tana harɗe hannunta a kirji ta zuba masa dangerous eyes din ta babu tsoro ko fargaba a tare da ita take kallon sa,tana tuna abinda ya aikata mata.
“Ban so kai ne ka zo a layi ba. Nayi niyyar kai da mahaifinka ku zo a ƙarshe, amma tun da ƙaddara yasa dole kai za ka bi bayan abokan cin musheku bamatsala. Kana maganar za ka fita ka je ka samu Haydar ka faɗa masa meye???”
Ta tambayesa tana ɗaura hannunta a setin kunnenta alamun tana son ya sake nanata abinda ya faɗa.
Yanda take kallon sa da sakar mai murmushi really shocked him .yayi zaton in ya nuna ya ji abinda take faɗa jikin ta ze hau kerma ta tsorata amma se ya ga saɓanin haka.
A ƙule ya ce “sai na faɗawa Haydar sam ke ba matar aure bace”
Tafi ta yi masa tana dariyar renin hankali “ Kuma kana tunanin za ka bar wannan dakin ne?”
“Me ki ke nufi ?”
Kallon bayansa ta yi tana “Mujahid ku taimaka ku rufe mana dakin”
Jin sunan na miji da ta kira ne kuma tana kallon bayansa ya sa a sukwane ya juya bayan, nan ya ga tsayayyun samari masu ji da jini suna tsaye a bayansa fuskar su da face mask sun harɗe hannu a kirji suna kallon sa suma, kofar Mujahid ya rufe kirif ya murza key.
Tsoro ne ya kamasa ya haɗiye wani yawu dakyar? babban tashin hankalin ma babu kowa a upstairs kowa na ƙasa babu wanda ze san abinda ke faruwa.
Dawo da duban sa kan ta ya yi murya na rawa ya ce “wacece ke? Nace ku din su waye ? Me ku ka zo nema a gidan mu?”
Ɗaure fuska ta yi duk wannan murmushin ya gushe. Zaid da Mujahid suka dawo kusa