Showing 21001 words to 24000 words out of 96407 words

Chapter 8 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3624

tuntsire da dariya. Shi de ido ya zuba musu yana jan siririn tsaki saboda yasan dalilin da yasa suke masa wannan kallon da dariya.

Auwal ne soma magana “Maza ka gan ka kuwa? Gaba daya a firgice ka ke,a firgice kuma a razane” Wani dariyar suka sake tuntsirewa dashi suna tafawa. Shi de girgiza kai kawai ya yi be ce dasu komai ba domin in da sabo ya saba da wannan iskancin na su tunda suka yi aure suka sa rayuwar sa a gaba, haka zasu zo office din sa su yi ta masa shakiyanci.

“ Wallahi Haydar ka gaggauta yin aure ko zaka samu nutsuwa dube ka dan Allah duk wanda ya gan ka yanzu ya san kana cikin tension “ wannan lokacin Sadeeq ne yayi magana.

Shi de kallo kawai yake bin su dashi “Dole duk wanda ya gan ni ya san ina cikin tension mana tunda binciken da nake yi yana kokarin tsotsemin ruwan kai”

Yayi maganar yana kwantar da bayansa a kujera

“To yanzu da a ce ka yi aure cikin sauki za ka dinga solving din case din ka, amma har yanzu kana nan a tuzuru ya zaa yi basirarka baze soma toshewa ba ai kawai Alhaji ka yi aure “

Duban Sadeeq da yai maganar yayi “wai dan Allah me yasa ku ka sako ni a gaba ne kam? Shikenan saboda kun yi aure se aka ce muku ni lokacin yin nawa auren ya yi? abeg you guys should let me breathe in peace “

“Mu fa gaskiya mu ke faɗa maka, amma tunda baka so a bar maganar se mun sake zuwa zaa yi sa yanzu ya ka ke ya Adda”

“Lafiya lau Auwal. Gaba daya ina cikin busy ne yan kwanakin nan shisa ko ta kan ku bana bi”

With a serious face suke kallon sa saboda sun hango damuwa da bakon yanayin da ya kasa ɓoyuwa a tattare dashi

Sadeeq ne ya gyara zamar sa yana mayar da dukkan hankalin sa gaba daya akan Haydar cikin sassauta murya ya ce “wacece ita? Faɗa mana wacece ita?”

Daga Auwal har Haydar kallon sa suka yi in a confused way,Haydar ne ya soma duba bayan sa kamar me neman wani abu ya ce “kai da waye ka ke yi? ”

Wurga mai goran ruwan hannun sa da ya shigo dashi yayi “Ban son iskanci da wa nake kuwa da ya wuce kai, Haydar wannan damuwar da ka ke ciki ba iya na stress din aiki bane definitely there’s a girl behind it,kar ka min karya daga kallon cikin kwayar idanun ka na fahimci haka”

Se da ya kalle su na tsawon minti daya batare da ya ce komai ba sannan ya sa hannu yana shafa kansa,ganin haka da suka yi be musa ba ya tabbatar musu da tabbas maganar Sadeeq gaskiya ne.

Furzar da iska yayi yana sauke numfashi a hankali “Yarinya ce ƙarama da ta rasa kowa na ta a kananun shekaru,ina tausayinta sosai. Can you imagine yarinyar nan aiki take yi kamar babbar mace? kallo daya za ka mata ka fahimci she is not use to it ”

“Amma ka na son ta ne da yasa hakan ya dameka?” Auwal ya wurga masa tambaya

“No no no Auwal! babu wani zancen soyayya kawai tausayinta nake ji,besides ai ba se dole kana son mutum ne za ka ji tausayin sa ba. The gurl is so innocent in na ga tana aikin wahala har raina bana jin dadin haka, saboda na san da ace daya daga cikin kanne na ne bazan taɓa bari su yi ba”

Dafa kafaɗarsa Sadeeq yayi yana tapping “Abokina in har kana tausayinta har haka why not kawai ka aureta?”

Kallon bakwai saura ya masa kafin yace “Damn it… Sadeeq are you okay? Yarinyar da ban jima da sanin ta ba zaka ce in aure ta,maybe tana da wanda take so besides ni bana fatan in yi auren da babu soyayyah a cikin sa. Kawai tausayin ta nake ji bayan haka kuma babu komai”

Taɓe baki yayi yace “shikenan kai ka sani,a juri zuwa rafi wata rana tulo se ya fashe.wata rana da kan ka za ka ce min ka faɗa soyayya da ita”

Kallon sa shi de kawai yake yana tunanin meye yake damun Sadeeq da wayannan maganganun,ganin in suka ci gaba da zama a haka to fa zasu ta jero masa tambayoyi ne Kamar wasu yan jarida. hakan yasa ya ɗauki car key din sa da files din da yake bukata ya nufi hanyar barin office din yana me cewa “to in kun gama shakiyancin na ku se ku fito min a office nide na yi gida”

Dariya suka yi Auwal yace “ au mu zaka tafi ka bari a office din ka? To ai baka isa ba malam kawai ka tsaya mu yi sallah sannan kowa ya wuce gidan sa mu masu mata”

Ya san neman sa da magana yake yi yasa be ko juyo ba balle ya amsa shi ya fice su kuma su ka bi bayan sa.

A can gida kuwa baƙi kaff an watse an bar maryam da su Adda kowa na sashin sa,Alisha kam tana naɗe bisa kan gado se su Ameera ne suke tare da ita.

Parking din motar sa yayi a farfajiyar gidan yana kokarin fitowa yaga an wangale gate motoci uku suka shigo, ya fahimci Dangaske ne da Sameer suka dawo gida. Ɗaukan abubuwansa ya yi ya fito daga cikin motar yana kokarin wucewa tamkar be hango su ba kenan ya ji muryar Ɗan gaske

“Aliyu Haydar”cak ya tsaya yana me jin haushin kan sa akan rashin dawuwa da wuri da be yi ba, domin da ya dawo da wuri yau sam baze bari ya haɗu da Ɗan gaske ba. saboda ya san se ya masa tambaya dangane da binciken mutuwar amininsa zakewa.

Shi da Sameer suka iso wajen sa “Baba barka da dawuwa”

Fuska a haɗe yace “aha… wato in na lura ni da kai wasan mage da ɓera muka fara a cikin gidan nan? Yau kwana uku kenan kana ɓuya ka ƙi mu haɗu dan kar in tambayeka ya case din da ka ke yi yake tafiya right?”

Sosa kunnensa yai bece komai ba yana kalle-kalle kamar be ji abinda ya faɗa ba.

“Aliyu Haydar? Ba ka ji ina maka magana bane?” Ɗan gaske ya faɗa yana duban Haydar din da kyau.

“Baba na ji ka kawai ban san amsan da zan baka bane,wannan binciken da nake yi bawai abu ne na gaggawa ba dole ina bukatar lokaci domin in haɗa duk wasu information da na samu a tsanake, aman kai kullum se ka ta maimaita min magana daya shisa kawai nake ɓoye maka”

Dariya irin na su na manya Ɗan gaske ya hau yi yana dafo kafaɗar Haydar suka soma tafiya kamar wasu abokai se da ya tsagaita dariyar kana ya ce “ abinda yasa zaka ga ina damunka ba komai bane face na ji shuru, daga kai har commissioner ba mu ji komai daga gare ku ba,kai da mu ke gida daya ai ya dace ka tsaya ka min bayani ko ba haka ba Sameer?” Yayi tambayar yana juyo ɓarin da Sameer yake.

“Hakane Baba “yai maganar yana yin gaba ya bar su a baya.

A haka suka shigo cikin falo bayan Haydar ya sanar dashi nan ba da jimawa ba ze gama binciken kuma ya faɗa masa hakan ne dan ya samu ya bar sa ya huta da yawan tambayoyin nan na sa.

Sama ya haura har ze nufi bangarensa se ya tuna da ita hakan yasa ya fasa shiga nasa ya shiga na Adda yana me shiga dakin da ta ke,can ƙasan maƙoshi ya yi sallama yana shigowa kan sa tsaye. tana zaune a bakin gado ta ga shigowarsa amma ta ƙi amsa masa saboda yanda ya yi sallaman can cikin maƙoshi kamar an masa dole wanda in mutum bawai ya kasa kunne ba tofa baze taɓa jin sa ba.

Zura hannayensa yai cikin aljihun wandon jeans din da yake sanye dashi yana jingina rabin jikinsa a jikin kofa ya tsura mata ido, yanda ya ga ko ɗago kai bata yi ba tamkar bata san da wanzuwarsa ba ya ba sa mamaki domin ko kaffara ba ze yi ba in ya ce ta san da shigowarsa

“Alisha..”

Se a sannan ne ta ɗago wayannan mayun idanunta ta ɗaura su akan sa da shima ita din yake kallo “Naam barka da dawuwa uncle Haydar” girgiza kai ya yi domin ɗan sanin da ya mata ya gane akwai ta da izza,wanda ba kowa ne ze fahimci hakan ba se me lura.

Rage murya yayi ya ce “barkan ki ya kafar ta ki ?”

Kallon kafar ta yi “Dasauki “

Be kuma cewa komai ba ya shigo yana isa inda take ya dubi kafan nata da ta ajiye sa akan pillow “in sha Allah nan da kwana biyu zuwa uku ze warke ki kiyaye kar ruwa ya taɓa sa”

“İn sha Allah zan kiyaye“ tayi maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa. Shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai.

Satan kallonsa ta yi jin sa shuru bece komai ba ta ga ya tafi duniyar tunani,wani tunani tayi sannan ta yi gyaran murya da siririryar muryarta

“Uncle Haydar tunanin me ka ke yi haka?”

“Bakomai me ki ka gani?” Yayi tambayar yana miƙewa tsaye da niyar tafiya

“Uhmm naga kamar ka faɗa duniyar tunani ne. shin ko akwai abinda yake damunka,” cikin zolaya ya kankance idanunsa akan ta “ko zaki min maganin damuwar tawa? “ ganin yanda ya zuba mata sexy eyes din sa ne yasa ta saurin janye idanun ta akan sa jin irin amsar da ya bata

Cikin kame-kame ta ce “sorry for asking “ ta ci gaba da wasa da hannun hijab din jikinta,ganin kamar bata ji dadin amsar da ya bata bane yasa shi sakin murmushi. domin shi cikin zolaya ya faɗi haka kuma ba da wata manufa ba amma ya ga kamar ita tayi wa maganar sa wata fahimta

“Alisha wani bincike nake yi da har yanzu na gagara kawo karshen sa if you can include me in your prayers I’ll really appreciate “

Dariya tayi a cikin ranta jin abinda ya faɗa dangane da binciken da yake yi a fili kuma cike da kulawa ta ce “in sha Allah uncle” sallama ya mata ya fita bin bayan sa da Kallo tayi yanda yake tafiya take kallo har ya ɓacewa ganin ta.

“Hmmmm Haydar Modibbo Ɗan gaske ai cases din da suke zuwa nan gaba da za ka yi binciken su Allah ya musu yawa a ciki kuwa har da wanda ka ke kira baba”

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

13 & 14_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

13 & 14



Tun daga wannan rana Alisha ta ci gaba da rayuwa a gidan Ɗan gaske. kuma har izuwa yanzu be san da baƙuwar fuska a gidan ba,haka Sameer dan Alisha kullum tana daki, saboda kafanta ba ta fita ko zuwa bakin kofa daga dakin ta se dakinta,sede Adda da su Zainab suna shiga gurin ta. haka maryam ma ta na leƙota su ɗan taɓa hira.yau ya kama kwananta hudu cif a gidan kuma kafanta ya warke saboda bata da ƙyan jiki ko kaɗan, ciwo na saurin warkewa in ta ji,sannan ba ta wasa da magungunan da Haydar ya kawo mata saboda yanda take Allah-Allah kafar ya warke domin ta fara tsara shirinta na gaba. yau saura Kwana uku date din da ta rubutawa chukuemeka Peter su cika hakan yasa ta matsu ta warke. Yau da safe da ta farka ta ji akwai bukatar da ta je can gida dubo Inna. Wanka ta yi,ta sa abayar dake cikin kayayyakin dasu Ameera suka kawo mata a cikin akwati. Hula ta sanya akan ta sannan ta fara tunanin ta ya za ta yi ta fice a gidan nan,ina tasan zata ce musu zata he, gaba daya lissafinta ya toshe se faman safa da marwa kawai take a dakin ta rasa yanda za tayi.

Maryam da fitowarta daga wanka kenan ta hango Sameer zaune cikin kujerun da suke falon su yana kallon waya, ya mayar da hankalin sa da imanin sa gaba daya akan wayar hakan yasa tunanin ta ya bata daya cikin biyu ko waya yake yi ko kuma de video call,kasancewar ya ba ta baya yasa sam be san da zuwanta ba,ko da ta iso abinda ta gani a wayansa yasa taji jiri na kokarin zubar da ita a ƙasa cikin ƙanƙanin lokaci hawaye ya soma wanke mata fuska domin kuwa kama sa tayi yana video call da daya daga cikin yan matan sa yarinyar tsirara haihuwar uwarta babu komai jikinta tana nuna masa jikinta tare da yin wasu irin abubuwa marasa Kyan gani.

Cikin fushi ta sa hannu ta fisge wayar ba tayi tunanin komai ba ta bugasa da bango yayi raga-raga. A zabure ya tashi yana kallon yanda wayarsa ya tashi a aiki domin bazata sake moruwa ba. a fusace yake kallonta ransa in ya yi dubu ya ɓaci idanunsa har wani shigewa ciki suka yi tsabar bacin rai

A tsawace yace “Maryam ke wace iriyar dakikiyar macece?wannan wani irin dabbanci ne zaki fasa min waya ko da kudin ki na siya?”

Itama cikin ɗaga murya kamar yanda ya ɗaga mata ta mayar masa da “kai ne zancewa kai wani irin dakikin mutum ne? Wanda be san darajar aure ba, saboda rashin mutunci har yakai a falo na ka zo kana wayar batsa da wata tsinanniya karuwa. Wallahi Sameer na yi danasanin aurenka, nayi danasani ban taɓa sanın kai jahili mara tarbiya bane se da na fara rayuwa da kai” Wani irin lafiyayyen mari ya ɗauketa dashi kafin ta gama dawuwa hayyacinta ya zare belt din wandonsa ya hau kanta da duka kamar wanda Allah ya aikosa,Maryam da yake itama ba baya ba wajen zafin zuciya da ta ga yana kokarin kashe ta da duka ta rarumo jug din glass ta buga masa akai da se da ya sanya Kara yana ja baya ita kuma tana haki tana kuka gaba daya muryoyin su ya cika part din

Tana kuka da haki tace “Wallahi nagaji, baze yu ka mayar dani jakarka ba yau ko ni ko kai ne ko ka kashe ni ko kuma ni in kashe ka shege ka fasa “ta faɗa tana ɗaukan kofin glass ta riƙe a hannunta tana kuka

Adda da fitowar su kenan da su Ameera za su je dinning domin ɗaukan breakfast suka ji hayaniyar dake tashi a part din Sameer, hakan yasa Adda ta gane faɗa suke yi da sauri suka nufi part din. itama Alisha da ta ji hayaniya yayi yawa yasa ta nufi part din. isan su part din yayi dede da ɗaga hannu da Sameer yayi ze watsa mata mari Adda ta yi saurin faɗin

“Kar ka kuskura ka ɗaura hannun ka akan ta Sameer in ba haka ba ranka ze yi matukar ɓaci” kallon ta yayi yana watsa mata mugun kallo kamar wanda ya ga sa'ar sa cikin raini ya ce “ke kuma a wa da za ki shigo min part har ki sa baki a abinda ya shafeni da iyalina?”

Da zallar al’ajabi Alisha take kallon Sameer jin yanda ya gasawa Adda magana kamar wanda yake magana da saa ko na ƙasa dashi,ba ta taɓa tunanin fitsarar sa ya kai nan ba tasan Adda kishiyar mahaifiyarsa ce, amma tayi tunanin yanda Haydar yake girmama Hajja Hauwa haka yake a bangaren shima Sameer ashe sam baya ganin girman Adda.

Adda da duk sun saba da halin sa ne ta shigo tana riƙo maryam da ta ke kuka ga shatin tafin hannunsa kwance a saman fuskanta

“Meyasa baka da Imani ne Sameer yau ko sati daya baa yi da suna ba yarinyar nan bata da ƙwari amma da yake kai zalunci shine a gaban ka har ka iya sa ƙatin hannayenka a jikinta.”

“Dallah malama ki kwashi ruɓaɓɓun kafafunki ki fice min a falo kar ki sake shigowa inda nake in kuma ba haka ba wlh duk abinda ya biyo baya ke ki ka jama kan ki “

Adda da yanzu ranta yayi kololuwa gurin ɓaci ne ta ta haɗiye wani yawu me ɗaci “yooo to ko ni ma za ka dake ni ne fitsararre?ko za ka dake ni ne nace?”

Cikin hayayyaƙowa kamar ze kai mata duka yace “ai se de ba ki yi abin dukan ba,ki ka yi abin duka wallahi tsaf za ki daku din munafukar banza da wofi, an gaya miki ban san duk wani makircin da ki ke kimtsawa a gidan nan bane? A fuska kamar ta Allah aikin banza aikin wofi. Ki yi takatsantsan dani a gidan nan wallahi dan in ki ka ci gaba da shiga gonata to tabbas se na miki abinda mijinki baze so ba”

“Chabb dijam” wanann shine abinda Alisha ta iya faɗa a ranta mamaki da al’ajabi ya hanata ko kwakkwaran motsi. Ameera ce ta fita a falon da gudu domin yanda Sameer yake magana yana nuna Adda da yatsa yana matsota tsaf ze iya cewa ze doke ta dan ba hankali ne dashi ba. Da gudu ta faɗa falon Haydar ta same sa yana ɗaura agogo a hannunsa ganin yanda ta shigo masa falo ko sallama babu ne yasa shi dubanta da alamar tambaya

“Uncle Haydar wallahi ya Sameer ga shi can yana yunkurin dukan Adda saboda ta hanasa dukan anty maryam” ai be ko tsaya ya gama sauraranta ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login