Showing 24001 words to 27000 words out of 96407 words

Chapter 9 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3607

ya fita a dakin a harzuke yana jin wani ɓacin rai na taso masa idanunsa har basa ganin hanya dakyau. kirjinsa na bugawa fat-fat-fat domin an taɓo abinda ba ze iya Kawar da ido ba saboda da a taɓa masa Adda gwara a yi duk uwar uban da zaa yi,in kana son ganin zazzakwaran ɓacin ran Haydar to a taɓa Adda nan ne yake juyawa ya koma asalin Aliyu gadangansa sarkin fushi da zuciya.

Yana shiga part din ya soma tattare hannun rigarsa sama yana tafiya ne kawai be san inda yake wurga kafafunsa ba muradinsa shine ya sauke hannunsa akan Sameer kawai. hakan yasa yana shigowa falon ko lura da ita be yi akan hanyarsa ba ya bugeta da se da ta kusan faɗuwa dakyar ta samu ta tsaya akan kafafunta ta dubesa a mamakance. Yana isa ya kai masa naushi me kyau a fuska. Sameer be gama dawuwa dede ba Haydar ya hau shi da muguwar duka kamar shine babba akan sa,duka yake masa yana zazzaginsa muryarsa na sarkewa tsaban bacin rai wasu maganganun be ma san me yake faɗa ba jikinsa karkarwa kawai yake.

Duk yanda Adda take ihun kiran sunan Haydar kan ya rabu da Sameer amma a banza,be ko kalli inda take ba balle ya yi abinda tace dakyar ta iya shiga tsakanin su tana yi wa Haydar faɗa

“Baka da hankali ne haydar ? Sameer kam ba yayanka bane?”

A zuciye ya ce “ni ba yayana bane,matukar ze ce ze dinga mi ki fitsara to wallahi zan illata sa a gidan nan,akan ki zan iya kashe mutum “ya faɗa yana huci kamar zaki.

“Ai dama saboda an ga uwata bata gidan nan shine yasa ake yi min duk abinda a ka gadama amma duk se na yi maganin ku daya bayan daya “ ya yi maganar yana fita fuuuu a falon ya barsu tsaye.

Sosai Alisha ta yi mamaki da lamarin Haydar bata taɓa tunanin haka yake da zuciya da fushi ba. kallon yanda jikin sa yake rawa kawai take yi,Duba da yanda ya kasance mutum me matukar saukin kai da kuma hakuri da kulawa tare da tausayi babu wanda ze yi tunanin yana da zuciya irin haka amma da yake hausawa sunce a guji fushin me hakuri saboda fushin su sam bashida kyau.

“Hmmm lallai ka ci sunan ka Aliyu Haydar domin duk masu wannan suna an yi amanna suna da zafin zuciya” ta faɗa a zuciyarta tana jiniina kai.

Ruwan sanyi Ameera ta miƙowa Adda ta ba sa dakyar Adda ta samu ya zauna ta basa kofin ruwan ya sha kafin ya soma sauke ajiyar zuciya me zafi.

“Dan Allah duk abinda Sameer ze yi a gidan nan Haydar dan Allah ka dena biye masa,ka san yanda mahaifinka yake son Sameer baya son abinda ze taɓa sa… ko ba ma wannan ba Sameer ɗan uwanka ne na jini duk mun san halinsa “

Sosai ta ke yi masa magana cikin rarrashi dan ta san wanene Haydar abu baya wuce wa ta dadi a gun sa musamman in abun yakai kololuwa wajen ɓata masa rai hakan yasa take ta tausansa saboda ya sauko kafin Ɗan gaske ya neme su

“Adda ai shi ba mahaukaci bane da duk sanda ya tafka kuskure se a ce kar a biye sa,yanzu maryam yaushe-yaushe ta haihu da har ze zage yana dukanta? Ko kuma ke saar sa ce da ze tsaya yana mayar miki magana har yana nu na ki da hannu?”

Yana faɗin haka ya miƙe ze fice a dakin idon sa ya sauka akan ta tana tsaye rakuɓe a jikin kofa, tunawa yayi lokacin da ya shigo ita ya buge ya wuce hakan yasa ya ce “sorry “ ya bar dakin duk bayan sa suka bi da kallo.

Adda hakuri tabawa maryam game da abinda ya faru tare da sanar da ita komai lokaci ne wata rana in ance ya sa hannu ya daketa baze yi haka ba.

Tunda ta zo gidan se yau ta sauko ƙasa falo ganin goge-gogen da yan aikin gidan suka yi be gogu sosai bane yasa ta ɗauki towel ta soma gogewa,cikin gaggawa Ɗan gaske ya buƙaci ganin maryam,Sameer,Adda tare da Haydar a babban falo bayan duk sun hallara ne ya soma magana

“Yanzu ni ku ke so ku mayar mutumin banza a cikin garin nan kenan? kowa gidan sa shuru babu hatsaniya amma banda gidana,kai Haydar akan meye yasa za ka sa hannu ka daki ɗan uwanka? “

“Baba kokarin dukan Adda fa ya….” Katsesa yayi ta hanyar ɗaga mai hannu yana

“Yi min shuru,ai duk ya sanar min abinda ya faru, da ka ke cewa yana kokarin dukan Hajiya Zuwaira din ya daketa din ne?na ce ya daketa? To kar in sake jin ka ɗaura hannun ka akan sa ko da wasa, in kuma ba haka ba se na yi mumunar saɓa maka”

Rai a ɓace ganin yau ma ya goyi bayan Sameer kamar ko yaushe “ Baba matukar kasan duk sanda za ka buƙaci ganin mu, kuma kasan bayan rashin gaskiya zaka bi to dan Allah kar ka sake kirana ka ɗauki matakinka kawai yanda ka so…… duk yanda Sameer yake cin mutuncin maryam ko kuma yi wa Adda rashin kunya baka taɓa tsawatar masa ba,ko da yaushe nu na wa kowa ka ke duk abinda yake yi akan dede ne.. yanzu let say Ameera ce ko kuma Zainab ko kuma de yusra ce Allah ya haɗata da miji kamar Sameer ya zaka ji ƴarka a ce mijinta ya mayar da ita jakarsa? duk abubuwan da yake yi ina iya kokarina wajen ganin na kauda ido na akai amma yanzu kam wallahi mun kulla kafar wando daya dashi in de ba ze riƙe girmansa yasan shine babba ba to kuma ni zan taimaka masa in mayar dashi kan matsayinsa.”

Ɗan gaske be nu na ɓacin rai ko kuma mamaki da yanda Haydar yake yi masa magana ba dan inda sabo ya saba,Haydar kaff cikin yaransa shine baya jin tsoransa, baya shakkan mayar masa magana a duk sanda ya so,duk maganar da ya zo masa baya tunanin furta masa shi,tun yana yaro yayi kokarin tankwarasa amma taurin kai ne dashi haka yana ji yana gani Haydar ya ta so cikin rashin tsoron sa da rashin Jin maganar sa,wannan dalilin yasa ya gane Haydar shine jarabawarsa. Duk da yanda kowa ke yabon halin sa amma shi sam ya gaza ganin kyawawan dabi’un Haydar din saboda shi gani yake kawai Haydar rena sa yayi da yakai ga baya tsoron sa.

Ita de Alisha goge-gogen da yakasa ƙarewa take ta yi yau, dramar da take gani a wannan gida ya shocking din ta,lamarin gidan Ɗan gaske ya bata mamaki, kowa da dabi’arsa ko wa da irin ta shi matsalar daga ɗan shaye-shaye makashi,se kuma me baƙar zuciya mara ganin girman ubansa. Daga uba da ƴaƴan kowa da nasa matsalar. Tana aiki amma kunnanta yana kan su.

Cikin son naɗe taburman borin kunya ya dubi maryam ya soma bata hakuri sannan ya tursasa Sameer ya bawa maryam da Adda hakuri,dan ya san in ba haka ya yi ba to Haydar ze iya ɗaukan gaba dashi daga nan har shekara dari.

Buɗe baki yayi ze kuma magana ya hango ta tana goge TV stand,sosai ya zuba mata ido yana mata kallon kurilla ko ze tuna inda ya santa amma ya kasa hakan yasa shi kasa hakuri ya ce “ke kuma baiwar Allah daga ina? Ko kuma Hajiya Zuwaira sabuwar me aiki ki ka kawo”

Kallon direction din da Hon Ɗan gaske ya kalla duk suka yi domin babu wanda ya san tana aiki a gurin.

Adda da ya tambaya ne ta amsa mai “ah ah ba me aiki bace ƴar cikin dangina ce sunanta Alisha kasancewarta marainiya yasa nace ta dawo gidan nan ta zauna tare damu kawai”

“Ohh to to to babu laifi Allah ya ji kan su”

Duk suka amsa da ameen.

“Aliyu Haydar”

Ɗago kansa yai da yaji yana sara masa saboda bacin ran da ya shiga ya saukar masa da matsanancin ciwon kai hakan yasa be iya amsa shi ba se kallon sa kawai ya yi

“Nayi maka maganar aure har nagaji,tunda har ba ka da zaɓi to na gama yanke hukunci zan haɗaka aure Da Meenal yar wajen abokina Habibu Katanga saboda ta sanar da ubanta cewa kai take so”

Adda tagumi kawai ta yi tana jin ikon Allah saboda sanin halin Ɗan gaske in yana magana baa iya sa a ce masa waye-waye ba Haydar din ne ma yake iya mayar masa da magana duk gidan,amma tayi mamaki da ta ji wai Ɗan gaske da bakin sa yake cewa ze haɗa Haydar aure da Meenal yarinyar da sam ba tarbiya ne da ita ba.

Girgiza kai ya hau yi alamar baze yu ba “Baba nifa bana bukatar a yi min auren da ba soyayya a cikin sa. na fi son se na samu yarinyar da nake so take sona sannan in yi aure sannan Meenal din da ka ke magana yarinyar da Kaf Gombe kowa ya san irin hau din ta.”

Daka masa tsawa yayi dan zuwa yanzu ya gaji da rashin ɗa’an da Haydar yake masa domin ya lura shi kaɗai ya rena

“Kar in sake ji ka aibatata ka ji na faɗa maka. Tun kana yaro ka ke yin abinda ka gadama dede da sau daya ba ka taɓa bin raayina ba,da farko na ce ka shiga art class ka nu na min commercial ka ke so haka na hakura na Kyale ka duk dan ka ji dadi,ka gama secondary nace ka tafi England domin karanta yanda zaka zama politician saboda ka gaje ni nan ma ka bujire main, bayan ka je ka karanci criminology nan ma ban ɗau mataki akan hakan ba. ka dawo Nigeria nace ka shiga harkata ta siyasa ka nuna min kai ka fi karfin zama ɗan siyasa haka ka je ka zama jami’in bincike. Duk abubuwan da ka ke yi bawai ina so bane ina jin ciwo a duk sanda nace kayi ka ƙi yi. Amma ban taɓa nu na maka fushi na ba. To ko da mutuwa za ka yi wannan karon se ka bi zaɓi na,domin kuwa aure kai da Meenal babu fashi ka ji na faɗa maka shashasha kawai…nan da kwana biyu zata zo gidan tayi spending holidays din ta saboda ku dedeta junan ku”

Kowa a falo tsit yana jin yanda Ɗan gaske ke zazzagawa Haydar faɗa,a kasalance ya miƙe yana zura hannayensa cikin aljihu ya ce

“Baba ni de ba ni za ka aura wa wancan yarinyar ba,kuma a duk sanda na ji zuciyata tana son wata mace to zan kawo maka maganar aure kai tsaye” yana faɗar yaka ya sa kai ya wuce yana me nufan bangarensa.

Karkaɗa kafa kawai yake yi yana jin zafin Haydar amma duk yanda yakai da yin fushi dashi baya iya ɗaukan mataki a kansa. Sallaman kowa yai duk suka watse.

Suna barin falon itama ta haura sama tana nufan falon Maryam saboda kukan Aryan da ta ji yana tashi tayi tunanin maryam ta shiga wanka ne yasa yake ta tsala wannan kukan.ga mamakinta tana shiga ta samu maryam riƙe da Aryan yana kuka itama tana kuka,a hankali ta zauna kusa da ita tana karɓansa a hannun ta tare da soma jijjigasa ai kuwa shuru yayi yana tsotsan hannu.

“Anty maryam ki yi hakuri komai yai farko ze yi karshe,kin ga yanzu jego ki ke yi in kına shiga damuwa ze shafi Aryan “ tayi maganar muryarta a hankali cikin tsigar lallashi

Share hawayen ta tayi da tissue sannan tace “Alisha nayi danasanin auren Sameer yafi sau million. Yau shekaran mu uku da aure dashi amma izuwa wannan rana ban san menene dadin aure ba,kullum cikin faɗa mu ke dashi ba akan komai ba kuma face ƴan barikin ƴan matan sa da yake tare dasu….tun ina ganin with time ze dena amma ko da yaushe se gaba gaba yake. Haka ze kwanta akan gadon mu na sunnah yana zina da mace a waya wani time din in bana nan har kawo su gida yake yi.. ba iya nan matsalar ya tsaya ba Sameer yana shaye-shaye na wuce tunani,duk sanda ya bugu se ya zo yai ta dukana. Mahaifin sa be taɓa tsawatar masa ba,Hajja Hauwa ma da itace ta haifesa ya renata balle kuma Adda da yake mata ganin matar uban sa… Duk gidan nan Haydar ne kaɗai yake iya taka masa burki.. lokacin da ya sakeni da ƙaramin ciki Hajja Hauwa ce ta bukaci indawo gidan ta in ya so in na haihu se in koma garin mu saboda ni ƴar Bauchi ce amma ki duba yanzu na dawo gidan sa babu abinda ya sauya munanan ɗabi’un sa babu ko daya da ya canzu “

Sosai ta ji babu dadi a ranta jin irin zaman auren da maryam take da Sameer wannan yasa ta ƙara tsanansa ta kuduri niyar yin maganin sa akan munanar abubuwan da yake yi.

“Kiyi hakuri in sha Allah lokaci na zuwa da za ki dena zubar da hawayen ki akan sa,Allah ze saka miki. Amma nayi mamaki ganin Uncle Haydar a irin yanayin da na gansa yau nayi tunanin shi babu ruwansa ashe na masa fahimta ne ta baibai”

Waro idanu maryam tayi waje ta na me riƙo hannun Alisha “waya faɗa miki ? A gaskiya har yau ba ki san wanene Uncle Haydar ba, Alisha shi din mutum ne na musamman. in nace na musamman ina nufin musamman,he is not like his father and brother,domin kuwa duk inda ki ke neman mutum me saukin kai,kulawa,tausayi,hakuri,daraja ɗan adam,faɗar gaskiya,ilimin addini da na boko,sanin mutuncin mace to Haydar shine ze zo na daya. mutum ne da be ɗauki rayuwar nan da zafi ba sam bayi da girman kai,wallahi namiji irin uncle Haydar shine mafarkin ko wace mace. Domin duk macen da ta same sa a matsayin miji to tabbas ta kasance me matukar saa a rayuwa, domin za ta yi rayuwa dashi ne tamkar sarauniya. Amma fa akwai zuciya,idan ran sa ya ɓaci rikiɗewa yake ya koma tamkar ba shi ba,sannan abu baya wuce wa ta dadi a gurin sa, saboda irin zuciyarsa wannan kuma da ita aka haifesa. Sannan wani abu dangane da Haydar be iya so ba in yana son abu yana so ne da dukka zuciya da ruhinsa sannan in ya tsani abu to tsana ce me zafi”

Jinjina kai tayi bayan ta gama jin jawabi akan sa cikin son sake sanin wani abun ta ce “ To amman menene ya sa ya rena mahaifinsa har haka? “

Taɓe baki Maryam ta yi “ Maybe Allah ne ya kamasa ta hanyar yin amfani da Haydar, Haydar mutumin kirki ne se de fa in yana gaban Baban su za ki sha mamaki in ki ka ga yanda yake masa magana kai tsaye se kin ji kina tantama akan sa. Kuma wallahi iya mahaifinsa ne yake yi wa haka. Sam Allah be ɗiga masa tsoro ko shakar sa ba, Hajja Hauwa de ta ce Allah ne ya Kama Baba shisa ya haifi Haydar domin ya ji zafin yanda mutane suke ji”

Nan ma ta jinjina kai ta kuma yi tana faɗawa duniyar tunani wato in ta fahimta Haydar ne kaɗai yake iya challenging din Ɗan gaske a cikin gidan nan.lallai kam wannan gida gidan drama ne.

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

15 & 16_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

15 & 16



Shigowa falon Adda ta yi, ta samu suna hira ganin ta da suka yi ne yasa duk suka ja bakin su suka yi shuru,murmushi tayi ganin su zaune Alisha riƙe da Aryan da yayi bacci,”Ashe kuna nman? “ hannun ta riƙe da ƙaramin tray jug ne a saman tray din, se kofi da ƙaramin spoon da curve sugar,a gefe guda kuma magani ne.

“Eh Adda” Alisha ta amsa ta

“Ko za ki miƙawa Uncle din ku coffee din nan ?”

Miƙawa Maryam Aryan din ta yi sannan ta karɓi tray din Adda tayi mata kwatancen part din na sa ta fita.

Tana cikin tafiya kawai ta ga mutum kwatsam a gabanta ya karkace a jikin balcony ya tare mata hanya yana bin ta da wani mayen kallo tamkar Kuran da ya ga nama. Baya ta matsa saboda yanda yake kokarin taɓa jikinta. yanda ya tsayar da idonsa tsam akanta, haka itama ta kure sa da ido tana bin sa da kallon tsana, tana tuna daren da ya rabata da abu mafi daraja ,tana tuna yanda ya yi mata fyade cikin rashin imani be duba ƙananun shekarunta ba,ihu da kukan Aryan ya soma dawuwar mata aka wanda hakan yasa kanta ya fara juyawa har ya iso gabanta yana riƙo hijab din ta bata sanı ba saboda kwakwalwarta take son komawa gidan jiya a take.

“Yan mata yaushe ki ka zo gidan nan “yayi maganar kamar tsohon maye yana wani kashe mata murya tare da shinshinan hijab din ta

“Dan Allah na roƙe ka kar ka yiwa ƴar ƙamarar yarinyata komai. dan Allah ku rabu da ita” muryar Dr Sagir kenan lokacin da yake bawa Sameer hakuri kan ya rabu da Alisha shine yake ta dawo mata kwakwalwa nan take jikinta ya dau kerma bata san lokacin da ta ɗauki jug din hot coffee na Haydar ta watsa masa a jiki tare da wurgi da jug din ƙasa nan take ya fashe saboda glass ne,ja baya yayi daga kusa da ita yana jin raɗaɗin coffee din a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login