Showing 48001 words to 51000 words out of 96407 words
Chapter 17 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
yanzu ta nemi sa ta rasa cire yatsan yayi da ga bakin sa
“Har yanzu kina jin zafin ?”
Bata iya buɗe bakin ta ba se kawai kai da ta gyada.
“Ki dinga kiyayewa please, da kin min magana na ciro miki shi ai”
Fuska a marairaice ta ce “bakomai Uncle is not that deep”
Wayar ya ɗauka ya kunna ya sa mata sim da cover ya miƙa mata, ta mai godiya ta yunkura za ta ɗauki tray din da ta zo dashi, da sauri ya ce “ Noo Alisha ,ki tafi kawai zan kira a zo a ɗauka”
“Uncle ka bari in ɗauka zan iya”
“Akwai ciwo a ɗan yatsan ki,ki bari kin ji “
Kai ta gyada sannan ta fice a falon. komawa yai inda ya bar wayarsa ya duba ga mamakin sa se ganin Auwal da Sadeeq yayi har yanzu suna video call din alamar duk abinda ya faru sun ji.
“DCS Aliyu Haydar Ɗan gaske “
Cewar Sadeeq yana masa wani kallo me cike da shakiyanci shi kuma Auwal yana dariya
“Wannan kiran fa?” Ya tambaye sa
“So ashe akwai mace a falon na ka time din da mu ke waya amma tsaban ka kware wajen zurfin ciki bamu sani ba se da abu ya same ta? ”
Murmushi ne ya suɓuce mai batare da ya ce komai ba dan be san me ze cewa Sadeeq din ba. Ganin ya musu shuru ne yana sakar musu murmushi yasa su tabbatar da zargin su,wannan Karon Auwal ne ya furta
“Mutumina ka shiga hannu fa,faɗa mana wacece haka? wata ƴar sa'ar ce?”
“Guys is not what you all think,Alisha ce fa ta ɗan ji rauni ne and I helped her is there anything wrong with that?”
“Wacece Alisha to ita kuma ina ka samo ta ?”
“Oh my God Sadeeq meyasa kafiya kwakwafi da yawa ne kam? Ita ce yarinyar da kwanaki na baku labari “
A tare suka ce “Auu yarinyar da ka ke tausayi?” Suna faɗn haka kuma duk suka tuntsure da dariya
“Allah ya shirye ku gaskiya” ya faɗa yana kwantar da bayansa a jikin kujerar da yake zaune.
“To ai gaskiya muka faɗa, kai fa da bakin ka kwanaki kace mana ba son ta ka ke yi ba,kawai tausayi take baka”
Cewar Auwal
“Hmmm… har yanzu am not fully sure I have feelings for her ba,na san de ina jin ta na daban a zuciyana. Duk sanda nake tare da ita ba na iya janye idanu na akan ta.. Wallahi yarinyar ta dabance komai na ta ya na burgeni “
In ban da blushing babu abinda Auwal da Sadeeq suke yi shi yake maganar amma su ke jin shauki da farin ciki, domin yanzu sun yarda abokinsu fa ya faɗa tarkon soyayya da yayi masa kamu lokaci daya.
“Gaskiya zan so ganin wannan yarinyar “
Sadeeq ya faɗa yana murmushi
Auwal yace “ba kai kaɗai ba,hatta ni ina son ganin wace yarinya ce ta yi saurin zurma abokin mu ya kamu da son ta da gaggawa hDhaka
“ ku fa kuna da saurin yanke hukunci,na faɗa muku har yanzu ban tabbatar da ko san ta nake ko akasin haka,amma har kun kai mu conclusion “ yai maganar yana girgiza kai.
“Haydar….! Kana jina?”
Shima in a serious tone kamar yanda ya kira sunan sa ya ce “ina jin ka Sadeeq”
Sadeeq ya ɗaura da “ Kar ka tsaya kana yaudaran kan ka Haydar,kai kan ka kasan kana son ta, kar ka tsaya wasa ka bi abinda zuciyar ka ya faɗa maka. İn har de ka yarda da hankali da dabi’an ta why not ka aure ta ? Wallahi Haydar daga iya kwayan idanun ka ina hango yanda ka kamu da so. Mu abun farin ciki ne a gurin mu domin kuwa tun tasowan mu ba mu taɓa jin kace yau ga yarinyar da ka ke so ba,imfact ba ka ma magana akan ƴan mata se de mu muyi ta shiriritar mu,amma tun ranar da ka fara magana akan yarinyar nan na fahimci akwai wani abu a karkashin zuciyarka,why not ka bawa zuciyar taka abinda yake nema?”
Furzar da iska yayi yana me lumshe idanunsa yana jin wani ɓari na zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri bakomai ne ya jawo hakan ba face maganganun Sadeeq. tabbas izuwa yanzu ya yarda da duk wani abubuwan da abokin nasa yake faɗa saboda ya san waye Sadeeq asalin Romeo ne a soyayya, yayi soyayyah da dama kafin yayi sure. ko kwanan ka daya da faɗawa soyayyah batare da ka faɗa masa ba kallon ka kawai in yayi se ya gane hakan.
Ganin yanda ya lumshe idanun sa ne ya sa su sakin murmushi kana Auwal ya samu daman cewa “ Tun ranar da ka fara mana maganar ta nima na gane akwai abinda ka ke ji dangane da its, sai de kai ka yi kuru kace wai tausayi ne kawai,Dama inde kana son mutum dole za ka dinga jin tausayin sa,nuna masa kulawa,yawan tunanin sa a ko da yaushe,ko da yaushe za ka ji kana bukatar kasancewa kusa da wannan mutumin har yakai ga in baka gan sa ba gaba daya ka rasa mutsuwarka. Shin Faɗa min ba ka jin haka dangane da ita?”
Shuru ne ya biyo bayan maganar da Auwal yayi sun zuba mai ido ganin har yanzu be buɗe idanun nasa ba,suna son su ji amsar da ze ba su.
“Duk abinda ka lissafo ina jin hakan “ cewar Haydar yana ware idanun sa akan fuskokin su a screen din wayar sa.
“Then don’t waste your time aboki na,ka mayar da ita mallakin ka” Sadeeq ya faɗa masa cikin karfafa masa guiwa. murmushi yayi yana gyada musu kai. A haka suka yi sallama yana me jin wani farin ciki a tare da shi,miƙewa yai ya fice a dakin sa domin zuwa ya samu Ɗan gaske dangane da hukuncin da ya yanke.
Da sallama ya shiga part din Ɗan gaske ya same sa hakimce akan kujera yana waya wanda daga gani za ka fahimci waya ce me muhimmanci. duk da ba ya jin me ake faɗa amma ya fahimci hakan duba da yanda ko samun amsa gaisuwarsa Ɗan gaske be yi ba hakan ya sa shi ya samu ya zauna kusa dashi yana me jiran sa ya kammala.
Se yanzu ya ji Ɗan gaske ya yi magana “in sha Allah zaa yi hakan. Dama na jima da yin tunanin hakan amma tunda ka ga hakan yafi babu matsala ƴarka ai ƴata ce, kamar yanda Haydar yake ɗa a gurinka.. se de wani hanzari ba gudu ba mu bari a yi burial din Peter tukuna in ya so se a yi baikon na su ina ga hakan ze fi kar mutane su fara kananun maganganu “ tun da ya ji ya ambaci baiko ya gane da Chairman Habibu Katanga yake waya.amma maganar baiko da ya ji ya ambata ne be gane komai akai ba domin shi mantawa ma yake da kashin Meenal a gidan.
Gama wayar yayi yana dariya ya ce “Aliyu kana jina da surkin ka ko?ya matsu a yi muku baiko kai ɗa Meenal,yanzu de rana ita yau in sha Allah zaa sa muku rana “
Hade fuska yayi kamar ba shi ne ya ke murmushi ɗazun ba, duk wani walwalarsa se da ya ɗauke.
“Baba bana son yarinyar can bana son ta,ina da wacce nake so kuma abinda ya sa na zo gurin ka kenan dan in sanar dakai na samu macen da nake so. Ku ajiye maganar aure na da ita dan bazan taɓa auren mace irin Meenal ba “
Murmushi irin na su na manya Ɗan gaske ya yi “ İs too late my son. Lokaci ya rigada ya ƙure. Kasan de bana canza magana ko? To ko kana so ko ba ka so se ka auri Meenal in ba haka ba kuma in tsine maka saboda ba ka min biyayya “
Da hanzari ya ɗago kai ya kalle sa jin Kalmar tsinuwa da ya ji ya ambata,da tsananin mamaki yake kallon sa “Baba akan wannan auren ne ka ke ikirarin tsine min?”
“Kwarai kuwa domin na sha yin hakuri da kai tun tasowar ka kake yin abinda ka gadama ban taɓa tursasaka ba, amma wallahi akan wannan auren da ka ke kokarin bijiremin za mu samu babban matsala da kai,ka ji na faɗa ma.”
Wani sabon tsanan Meenal ne ya sake darsuwa a ransa domin komai ya ke faruwa yanzu ita ce sila, danne ɓacin ransa yayi amma idanun sa sai da suka nuna ya ce “Ina da macen da nake so,kuma ina burin aurenta “
“Za ka auri ko wacce mace a duniyar nan ne bayan auren ka da Meenal Katanga. Bayan bikin ku za ka iya ƙara auren I support your decision,amma a yanzu kam ba za ka maida ni mutumin banza a idon duniya ba. Dole ko me ze je ya dawo Meenal zaka fara aura ta zama uwar gidanka.”
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
27 & 28_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
27 & 28
A tsarin rayuwarsa sam babu tsarin auren mata biyu,amma ya ze yi in de yana son auren zaɓin ransa dole ya bi abinda Ɗan gaske ya faɗa, saboda a wannan karon be ga alamun ze samu sassauci daga garesa ba tunda ya rigada ya rantse to yasan babu abinda ze sa shi janye kalamansa,fuskansa babu walwala haka ya tashi ya fice a part din ya nufi nasa bangaren,gaba daya ransa babu dadi, taya za'a yi a ce wai matashi dashi amma ze auri mata biyu. Baya son haɗata da kowa so yake ya aure ta ya nuna mata gata,ya zame mata uwa da uban da ta rasa a rayuwa, ya ba ta dukkan farin ciki na rayuwa,yana son ya mayar da ita Gimbiya me ƴanci,amma yanzu dukkannin shirin sa na rayuwar farin ciki da yake son yi da ita yana neman rushewa.
Zuciyar sa ne ya tambayesa “to shin ma tana sanka?kana ganin za ta yarda ta aure ka bayan ka auri Meenal?”
Cike da kwarin guiwa ya gyada kai a fili ya furta “Za ta so ni kamar yanda nima na so ta in sha Allah “
Yana tsaka da nemawa kan sa mafita Adda ta shigo ta samu guri ta zauna daf dashi tana ɗaura hannu kan kafaɗarsa,kallon ta yayi batare da ya ce da ita komai ba.
“Tunanin me ka ke yi haka ?”
“Babu komai Adda” ya faɗa mata dan bayasan ta fahimci yana cikin damuwa batare da yasan ta rigada ta san akwai abinda ke damun sa ba.
Cikin tsantsan soyayya irin na uwa ta ke duban sa cikin tausasan murya ta ce
“Nasan abinda Baban ku ya faɗa maka ne ya sanya ka cikin damuwa,kar ka ɗaga hankali,Ka yi addua, Kane mi zaɓin ubangiji in auren wannan yarinyar alkairi ne Allah ya yasa, in kuma ba alkairi bane Allah ya rusa komai. Kasan de babu abinda ya fi ƙarfin addua ko?”
Tabbas mahaifiya rahama ce shigowanta kaɗai yasa shi ya ji damuwar da yake ciki ya soma raguwa, ga kuma dadaddan maganganun da take faɗa masa, ji yayi tamkar an zuba masa kankara akan kirjinsa tsaban yanda yayı sanyi ba kamar ɗazun da yake jin zuciyar sa na tafarfasa ba. Kwanciya yayi akan gadon ya yi matashi da cinyarta.
Hannunta ta ɗaura akan sa tana shafawa “bayan wannan maganar auren kana da wani matsala ne?”
Lumshe idanun sa yayı yana sakin sanyayyan murmushi jin tambayar da ta yi masa duk da be yi tunanin za ta kuma yi masa wata tambayar ba.
Murya ƙasa-ƙasa kamar me jin bacci ya furta “Adda na samu yarinyar da nake so amma Baba ya kasa tsayawa ya fahimce ni, ƙarshe ma se cewa yayi in ma akwai wacce nake son aure to se bayan na auri Meenal se in aure ta. Ban taɓa jin sha'awar yin mata biyu ba tunda nake,ina son in kasance miji me kamanta adalci amma ta ya zan aikata hakan bayan ni mace daya nake so? bazan taɓa iya yin adalci a tsakanin Meenal da wacce nake so ba. Ina tsoron Allah ya kamani da laifin rashin adalci a tsakanin su domin dole ne in fifita wacce nake so”
Da mamaki kwance kan fuskarta take kallan fuskar ɗan nata mafi soyuwa a gare ta,a gaba daya shekarun da ya mallaki hankalin sa ko a cikin wasa be taɓa ce mata yau ga yarinyar da yake so ko take burgesa ba,amma yau wai Haydar ne da bakin sa yake cewa ya samu macen da yake so,dole tayi mamaki ga kuma farin cikin jin haka da ta yi. cikin zolaya ta matso da bakinta daf kunnensa ta masa raɗa da
“Inyeeeh!! wacece haka ta saci zuciyar yallabai Haydar?”
Be yi niyar dariya ba amma yallabai da ta kirasa dashi ne yasaka shi sakin dariya me sauti kaɗan, dama duk sanda ta ke son tsokanar sa haka take ce mai yallabai.
Cike da shaukin da yake ciki na farin ciki ya ce “ Za ki san ta nan ba da jimawa ba Adda. kuma zaki yi matukar alfahari da zaɓi na”
Ta san ko da ta tsawaita tambaya ba amsa za ta samu ba gwara ta kyalesa yanda yace za ta sanı din shi da kansa ze faɗa mata kamar yanda yanzu ma ya sanar mata akwai wacce yake so din.
“Ina fatan matar da za ka aura ta kawo canji a cikin wannan gida namu,domin ni na gaza, na gaza daidaita kan wannan ahali. Tunda Hajja Hauwa ta gagara nima na sare,muna rayuwa ne kamar ba ahali daya ba,bama cin abinci a tare a kujeran cin abinci na ahali,mahaifin ku bashi da lokacin iyalansa se na siyasarsa,kullum cikin aiki yake kowa na harkokinsa, shida ɗansa sam basu da lokacin kowa. Allah yasa a samu sanadiyyar daidaituwar komai a wannan gida” tayi maganar fuskanta ɗauke da ɗan damuwa,kansa na kan cinyar ta ya riƙo hannun ta cikin sonta yace
“İn sha Allah komai ze daidai kamar yanda ki ke fata”
Tana murmushi ta ce “Allah yasa hakan ya kasance, ya batun binciken da ka ke yi? Ka samo me aikata hakan!? ”
"Ah ah Adda har yanzu,amma yana daf da shiga hannu kuskure kwalli daya kawai ze yi ya faɗa tarkona. Yana tunanin shi me wayo ne in ya yi kisa yana goge hujja. Ni Baba ne ma na ga kamar mutuwar Peter be dame sa ba”
“Hmmm Baban na ku ai kafi kowa sanın halin sa,ko abu ya damesa ba ganewa zaka yi ba, Allah ya baka saa akan wannan binciken naka. Ka samu ka huta”
Ta faɗa tana mayar mai da kansa kan pillow ita kuma ta fita. Yana kwance kawai ya miƙe kamar wanda aka tsikarawa allura,dakin da ya ware yake binciken sa ya shiga. Wani album ya buɗe ya ɗauki hoton Hashim Zakewa ya manna a jikin board ya caka wani jan allura akai,sannan ya manna hoton Peter a gaba da na Zakewan ya koma baya yana me harɗe a kirji ya tsurawa hotunan ido.
“Da farko Hashim zakewa,se kuma Peter wayanda kuma sun kasance abokai ne,wani dalili ne ze sa wannan ɓoyayyen makashin ya bibiye su har ya kashe su? Tabbas akwai ƙullalliya, akwai abinda ba daidai ba,ba ze tsaya a iya Peter ba ze yi wani kisan nan gaba amma to waye next target na sa?waye,waye,”
Ya faɗa da karfi yana shafa kansa tare da riƙe habarsa yana tunani.
“A cikin wayannan abokai huɗu, biyu sun mutu, saura biyu,Baba da Katanga”
Ya faɗa a hankali,yana ware idanunsa tabbas tunanin sa da hasashensa sun faɗa mai gaskiya, amma abinda ya ɗaure mai kai menene haɗin makashin da wayannan abokai huɗu har yake bin su daya bayan daya yana shekewa?. Manna hoton katanga yayi kafin ya sa na Ɗan gaske a ƙarshe ya tsaya yana kura musu ido.
“Tabbas abinda na yi tunani gaskiya ne, wannan makashin yanzu harin sa na gaba akan Katanga ne daga nan kuma se Baba,amma bazan ba ka damar haka ba. Za ka shigo hannuna nan ba da jimawa ba,zan tabbatar da ba ka ƙara yin wani kisan ba,zan baza jami’an tsaro ko ta ina da zasu ba su kariya. Bazan ba ri sun san rayuwar su yana hatsari ba,daga yanzu har lokacin da zan gama bincikena zan yi komai cikin sirri”
Washe gari ta farka da ciwon mara ta san period din ta ne ya zo, magani ta ke bukata amma ba ta jin za ta iya fita a dakin da take, saboda yanda yake mukurkusanta ga shi tun safiya Allah be wurgo mata su Ameera ba gashi har karfe tara yanzu.
Tana daga kwance taja tsaki yafi sau dari domin izuwa yanzu jan tsaki ya gama zama dabi’arta, akan ƙaramin abu se ta ja tsaki sau babu adadi saɓanin da ba haka take ba,wayar da Haydar ya bata ne da tun da ta shigo dakin ta daren jiya da ta baro gurin sa ta wurga wayar kan gado gefe da ita bata sake bi ta kan wayar ba se yanzu da ta ji wayar na ringing ita tama manta da an bata waya. Haka kawai ta ji ringing din ma da yake yi yana ɓata mata rai yasa ta kuma jan tsaki ganin kiran ze katse ta jawo wayar. kallon baƙuwar number dake kiran tayi ta yi jim tana kallon number abinda yasa ta tsaya ganin number shine ya kasance special number very easy and simple har ta haddace