Showing 42001 words to 45000 words out of 96407 words
Chapter 15 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
ba amma ya san kashe sa suke da niya ga shi a halin da yake ciki baze iya aikata komai ba.
Buɗe boot yai ya jawo driver da ya sumar ya kaisa ƙasan bishiya ya kwantar ya dawo, igiyar da ta zo dashi a jakanta ne ta miƙa masa. motar ya shiga ya ɗaure Peter hannu da kafa kamar wani gagarumin ɓarawo. Duba time tayi ta ga 15 minutes ne kaɗai ya rage musu, hakan yasa ta isa window motar da glass din ya kasance a sauke fuskarta ɗauke da kawataccen murmushi me nuni da tsantsan farin ciki ta dube sa kamar yanda shima ita yake kallo yana hawaye.
“Na san kana ta tunanin menene yasa muka maka haka, kuma mu su waye. Sunana Alisha Sagir Lelewal. Ni ce yarinyar da ku ka tarwatsawa komai. Allah ya sa ina da dogon kwana na rayu na dawo da wutar fansa da kai da duk sauran abokan cin mushenka da daidai zan gama da ku. Na fara da zakewa yanzu kuma kai. Saduwar alkairi Peter” idanunsa tuni suka kaɗa suka yi jaa numfashin sa ya fara fisgewa tsantsan tashin hankali da ya shiga sakamakon jin abinda ta faɗa,murmushin ta har yanzu be gushe ba hannu ta miƙa, Mujahid ya bata gum,liƙe masa baki tayi sannan ta bar gurin tana dariyar mugunta da ya fito da sahihin kyawu da ubangiji ya yi mata. Motar mujahid ya shiga ya kunnasa tare da seta hancin motar izuwa wannan ƙaton kwarin motar ta soma tafiya, shi kuma ya fito a ciki ya koma gefen ta ya tsaya tare da harɗe hannu a kirji kamar yanda itama tayi suka zubawa motar ido suna ganin yanda yake tafiya towards kwarin a hankali har ya faɗa ciki. Ƙaran faɗuwar motar suka ji kafin wuta ya kama, kallon juna suka yi sannan suka sake murmushi a lokaci guda.
“Ya je su haɗu da zakewa a can sai su tattauna “ cewar mujahid yana dariya itama dariyar tayi kasa-kasa ta ce “Daya bayan daya se sun karbi hukuncin abinda suka shuka . Mujahid yau ne motar ku ze tashi yakamata mu bar gurin nan tun kafin mutane su ankare” ya yarda da abinda ta ce hakan yasa ya ɗauko mata mask din ta da ta cire a ƙasa ya bata, ta sanya nan ta sake komawa sak na miji suka yi tafiyar su suka bar driver kwance ƙasan bishiya be ma san a duniyar da yake ba.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
23 & 24_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
23 & 24
A babban dajin nan kuwa motocin yan sanda ne ya zagaye ko ina, ga an ke waye gurin saboda ƴan jaridu da suke ta yunkurin isa gurin domin ɗaukan rohoto amma yan sanda sun hana su. ACP da sauran jami’ai suna tsaye a bakin wannan ramin suna ganin yanda motar katafila take kokarin jawo motar da ya yi hatsarin. Motar katafilan ne yake kokarin ciro motar Peter da ya ƙone kurmus a cikin ƙaton ramin. Motar ƴan sanda ne guda biyu suka kutso cikin dajin, suka yi packing inda sauran motoccin suke.buɗe masa kofa wani police yayi ya fito, yana sanye cikin shiga ta farar riga me doguwar hannu da wando coffee color yayi stucking kyakyawar fuskarsa na manne da farin glass yayi kyau sosai , sede fuskarsa sam babu walwala yana saukowa polisawan suka hau sara masa hannu. kawai ya ɗaga musu yana yin gaba iso shi inspecter yai yana sara mai tare da cewa “Sir ana kokarin ciro motar a ramin ,domin jami’an mu baze yu su shiga ciki ba saboda ramin yana da zurfi dole se motar katafila “
Se da ya ɗan karanci gurin na wasu dakiku kafin ya dubi inspecter “babu wani shaida gani da ido da aka samu? Babu wanda ya ga abinda ya faru ?”
“Gaskiya babu domin ko mutumin da ya fara sanar da mu hayakin wutar ya gani yana fitowa a cikin ramin shine ya leka ya ga mota ce ke ci da wuta. Se de kuma akwai driver shi chairman Peter din da muka same sa a sume a jikin bishiya “
Dawo da hankalin sa yai kansa jin abinda ya faɗa “yana ina?” ƙasan bishiyar da driver ke zaune ya takure gu daya suka isa, kallo daya za ka masa ka fahimic tsoro da tashin hankali shimfiɗe a fuskarsa ,saboda yanda zufa ke tsatstsafowa ta gefen goshinsa da wuyan sa ga idanunsa da suka yi ja suka kadɗ. Sunkuyawa yayi a gaban sa yana masa kallon kurilla kafin ya zare glass din fuskansa.
Da tausssan muryar sa da yake a dakile yau, ya ce “uban gidanka ya yi hasari ya aka yi Kai ka tsira bata re da samun rauni ba? Ko de da sa hannunka a abinda ya faru?” Ya masa tambayar yana tsare sa da idanun sa me birkita mutum, Kai ya hau girgizawa “ah swear to you bani da saniyar abinda ya faru kawai farka wa na yi na gan ni a nan sannan ga kuma police a kaina. “
Taɓe baki yai “ to kenan motar ne ya wurgoka karkashin bishiya se ya gangara da Peter cikin rami?” Ya sake wurga mai tambaya me zafi da yasa shi gyara zama “hey Jesus Christ! Ta ya zan aikata haka? Oga na ne fa! I never had bad intentions towards him,mutumin kirki ne yana kyautata min I will never do such a thing.”
Ɗaura hannun sa yay a kafadar Kingsley ganin duk ya daburce “ka nutsu ka min bayani,saboda Kai ne kawai shaidan gani da ido. Da bayanan ka za mu samu hujja da mu ke bukata. Try to calm yourself and tell me everything you know okay?” Gyada kai yayi kafin yace “sir na san de akwai wani matashin da…”
“Sir an fito da motar kuma gawan Peter yana cikin motar” cewar daya daga cikin ƴan sandan dake gurin. wannan maganar ne ya dakatar da Kingsley ƙarasa statement din sa. Ba tare da ya sake bin takansa ba ya miƙe ya nufi inda aka fito da motar . face mask ya sanyawa fuskarsa ya tsaya daga gefe yana ganin yanda ake kokarin ɓalle murfin motar har Allah yasa ya buɗu. Gawan Peter da ya kone kurmus ne suka gani cikin motar kwarangwal dinsa ɗaure tamau kamar yanda suka ɗaure sa. Kwarangwal din babu kyan gani in aka ce maka wannan shahararren ɗan siyasan ne haka bazaka yarda ba. Fito da gawar suka yi a yanda yake suka sanyasa cikin ambulance domin wucewa dashi asibiti a yi masa abinda ya dace a mikasa mortuary . Sawa ya yi a bincika masa motar bayan an bincika baa samu komai ba.
“Yallabai duba da yanda mu ka samu gawar Peter hakan ya sake tabbatar da kashe sa aka yi. bayan an ɗaure sa an kuma firgitasa kafin a ka kashe sa aka kuma tura motar nasa izuwa wannan kwarin “ cewar inspecter da ke tsaye tare da Haydar. Girgiza Kai yai yana shafa kwantaccen sajen sa
“Be mutu ba lokacin da motar ya faɗa rami. Makashin da ya aikata hakan yana son Peter ya ɗanɗani azaba da raɗaɗi me zafi kafin mutuwa. Tabbas da ran sa wuta ya cinye sa kuma saboda yana a ɗaure yasa be yi kokarin taimakawa kan sa ba. Lallai ko ma wanene wannan mashekin yana da kwarewa sosai wajen ganawa mutane azaba. amma ko ma wanene haka wata rana ze shiga hannu na se ya ɗanɗana guɗar sa…..” sosai ya jinjinawa basira da Haydar yake dashi.
“Amma to yallabai in har makashin nan ze iya cire driver Peter a motar to me ze sa har ya iya kashe Peter ? Na fi tunanin daya daga cikin abokan hamayyan su ne”
Da fa kafaɗarsa yai, ya zuba masa sexy eyes din sa “Ka sanı ba'a taɓa aikata abu babu manufa. A yanda hasashe na ya bani wannan makashin sumar da driver Peter ya yi sannan yayi amfani da damar sa wajen ganin ya ɗauko sa har ya aikata masa haka. Sannan be bar wannan dajin ba seda ya tabbatar da Peter ya soma shan azaba. Idan ka yi la'akari da sawun takun takalmin nan dake kusa da kafa na za ka gane an tsaya a gurin har na tsawon mintuna biyar zuwa goma kafin aka tafi, hakan na nufin se da ko ma wanene ya tabbatar da ya idda nufin sa”
Kallon sawun takalmin yai tabbas abinda Haydar ya faɗa gaskiya ne domin yashin gurin na da laushi hakan yasa shatin takalmin ya nitse cikin ƙasa kaɗan. Wanda ana samun hakan ne a lokacin da mutum ya tsaya na tsawon lokaci me tsayi a kan yashi me laushi .
“Ko ma wanene wannan makashin se da ya shirya tsaf kafin farmakan Peter. hakan yana nuni da tun daga gida aka bibiyi driver sa inda har ya ci sa'a ya sumar da driver shi kuma yayi amfani da damar sa. Ina me tabbatar maka da bazan bari ka sake wani kisan ba zan kamaka wannan alkawarina ne. Ku ɗauki hoton sawun kafan a bincika wani kamfani ne suke buga irin wayannan takalman.” ya gama maganar yana mayar da glass din idon sa, motar ya shiga aka yi driving din sa zuwa police station. In da gawar Peter kuwa tini an wuce dashi mortuary .
Knocking ya yi a office din commissioner izinin shigowa ya ba shi sannan ya shigo ya same sa tsaye ya goya hannun sa baya kana ganin fuskansa za ka fahimci ransa a ɓace yake, sara ma sa yayi.
“Detective chief superintendent Haydar am not happy with you ko kaɗan. Yau satı biyu kenan da mutuwa zakewa, amma har yanzu ba ka kawo min bayani ko daya ba. Ga shi yau an sake kashe daya daga cikin manyan mutane a gombe. Na yarda dakai da yakinin with just a few days zaka kawo min sakamakon binciken ka amma shuru. am so disappointed in you Haydar. Gaskiya kana ɓata min lokaci shisa na tugeka daga wannan gudanar da binciken zan ɗaura wani domin na ga you’re actually not ready “ yana ƙame, tsayuwarsu na jami’an tsaro. ya na sauraran duk abinda yake faɗa seda ya tabbatar da ya gama magana kafin ya ce
“Yallabai commisioner I do understand you,na fahimce yanda ka ke a ƙagare cikin son jin bayanai daga wajena. Duk yanda ranka yakai ga ɓaci ina me tabbatar ma ka be kai nawa ba, saboda wannan shine bincike na farko da ya wahalar dani ya kwashe ni kwanaki ban iya gano komai ko da da hujja kwara daya ban iya samowa ba saboda makashin is very clever, amma ya manta da cewa duk wayo da basirarsa hukuman ƴan sanda sun ƙere sa. Dama daya kawai nake bukata a gunka,dama daya kacal sir. ni kuma na maka alkawari se na gurfanar maka da wannan takadirin makashin a gabanka in ban yi haka ba ni ba ɗan Moddibbo Ɗan gaske bane. One chance sir”
Sauke numfashi commissioner yayi yana jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan Haydar “Zan baka wata damar saboda har yanzu ina ji a jikina kai ne za ka kawo karshen wannan makashin. Kar ka yi wasa da wannan damar da na baka Haydar “ya yi maganar yana nuna sa, gyada mai kai yayi yana kuma sara masa da karfi.
“Zaka iya tafiya Allah yabada saa”
“Ameen “ ya faɗa ya fice a office din.
“Hello Mujahid shin ya ake ciki kun tafi din ne ko har yanzu ? Hankalina ya gaza Kwanciya kuma ba ze taɓa Kwanciya ba har se na ji kun bar Gombe. saboda any moment za'a iya sa curfew domin soma binciken mutuwar sa “ta yi maganar cikin sauri-sauri tana faman safa da marwa a tsakiyar falon inna, gaba daya bata cikin nutsuwarta gani take kamar za'a iya Kama Mujahid din.
Sautin murmushin sa ta ji ta wayan “Alisha darling ki kwantar da hankalin ki babu abinda ze faru da mu da izinin ubangiji kin ji ko” kamar Wanda yake gabanta ta hau girgiza mai kai
“Noo Mujahid hankalina ya gaza Kwanciya please ka sanar dani how’s it going?”
“Shikenan to tunda kin matsu bari in sanar dake, da farko de na ɗauki shatan motar Gombe line kuma har mun fita a gombe mun nufi hanyar Kano domin a nan ne jirgin mu ze tashi daren yau in sha Allah. “
Wani irin siririyar ajiyar zuciya ta sauke da yasa se da ta samu guri ta zauna tana sakin murmushi “Alhamdulillah se yanzu na ji na samu nutsuwa,you’re really a smart person Mujahid. Allah ya kai ku lafiya ya kuma dawo daku lafiya “
A bangarensa shima murmushin kawai yake sakewa “ameen ameen lovely sis dan Allah ki kula min da kan ki. Sannan kuma yakamata ki koma gidan Ɗan gaske kar su fara zargin ki “
Wani killer smile ta yi tana aura kafarta daya kan daya “ba za su taɓa yin hakan ba ai. ba zan kuma ba su damar gano komai dangane da ni ba. Zan koma musu a salo na daban yanda zasu sake jiki dani ni kuma in ɗauki fansata yanda nake so. Se na tarwatsa Ɗan gaske ya koma wulakantaccen da bashi da komai kafin ya mutu. Se na ɗauke murmushi akan fuskar wannan ahali na sa, zan nu na masa shi da ɗansa fansar mace yafi ko wani fansa zafin ɗauka.”
“Ina bayan ki Alisha darling darı bisa dari”
Ya faɗa mata hakan cikin Kara karfafa mata guiwa.
A haka suka gama wayan ta shiga bedroom din ta tayi wanka ta shirya ta sanya doguwar hijab har ƙasa ruwan hanta. Dakin inna ta shiga ta mata sallama domin tayi niyar komawa gidan Ɗan gaske sosai ta mata addua kafin ta bar gidan.
Ko da me napep ya sauke ta a gaban gidan biyan sa kudin sa tayi sannan ta yi knocking a gate. leko kai me gadi ya yi yana ganin ita ce ya buɗe mata suka gaisa ta wuce ta shiga ciki. Kan ta tsaye babu wani fargaba ko tsoro ta shiga main falon na su domin ta gama shirya duk wasu maganganun da za ta faɗa musu.
“Assalamualaykum…..” Ameera,Zainab ,Yusra da suke zaune a falo ne suka jiyo muryarta hakan yasa su waigowa suna kallon ta cike da mamaki har ta iso kusa dasu ta zauna suna bin ta ne da ido kawai.
Zainab ce ta soma faɗin “Alisha ina ki ka shiga haka? Kin tayar mana da hankali sosai mu ka dinga neman ki. Musamman uncle Haydar hankalin sa ya fi na kowa tashi “
Tana kokarin buɗe bakin ta ta bata amsa Ameera tayi caraf ta tari numfashin ta “yes tell us Alisha where have you been all this time da mu ke neman ki? ” shuru tayi tana sunkuyar da kanta ƙasa ta soma wasa da yatsunta,ganin hakan ne yasa Yusra fahimtar she’s nervous hakan yasa ta girgiza kai tana kallon su
“Gaba daya kun ruɗa yarinyar nan da tambayoyin ku da wanne ku ke so ta fara ba ku amsa? Ko amsa sallamanta ba ku yi ba se tambayoyi kamar abun tashin hankali”
“Sis mu na mata wayannan tambayoyin ne saboda we really cared about her mun matukar damuwa da ita shisa mu ka kasa yin shuru”
Satan kallon Ameera da tayi magana yanzu Alisha tayi tana hango asalin gaskiyar abinda ta faɗa a kwayar idon ta.
Yusra ta kuma ce “na sanı nima ai na damu da ita, amma this is not how you guys supposed to react.”
Maryam da Adda da suke kitchen ne suke jiyo surutunsu ya yi yawa yasa suka fito turus suka tsaya ganin Alisha zaune a kujera mazaunin mutum daya.
“Wacece nake gani haka kamar Alisha “cewar Adda da tana maganar ne a yayinda take ƙarasawa inda take.
“Ina yini Adda”
Ta gaisheta a gajarce
“Lafiya Alisha. ina ne ki ka shiga duk kin tayar mana da hankali “
Se da ta saki murmushi a ranta ganin yanda duk hankalin su ya tashi da yanda suka damu da ita ta ce
“Dan Allah ku yi hakuri na san hankalin ku ya tashi sosai musamman da ba ku san inda na shiga ba,Kawu na ne ya gan ni a San Hussain super market shine ya kirani ya dinga min masifa ya wuce dani gidan sa. yau kuma ya koroni wai ya sake gani na a kusa dashi ”
“Allah sarki ai sai da mu ka yi tunanin haka muka ce ko kina gidan kawun ki to ai da sauki sosai” cewar maryam
“Masha Allah sannu ko ki je dakin ki yanzu za'a kawo miki abinci” Adda ta faɗa tana shafa kanta,kai ta gyada cikin sanyin jiki ta nufi bangaren Adda tana jiyo su suna magana akan wai kawun nan nata baya kyautawa.
“Wallahi Adda Alisha tausayi take bani sosai,kina ganin ta za ki gane akwai damu a tattare da ita”
Numfashi Adda ta sauke ta zauna “Hmmm Zainab ai maraici ba wasa bane,abun ya haɗu ya mata yawa ga rashin iyaye ga danginta da suka ƙi su kula da ita. Yarinya ƙarama amma suna kokarin su ga sun lalata mata rayuwa”
Kallon Adda da ta gama magana, Maryam ta yi “ta ci gaba da zaman ta anan har ran da Allah ze sa su karɓeta ko kuma tayi aure abun ta”
“Yoo ai dama Alisha kam yanzu ta zama ƴata, na gaya mata ta dinga ɗaukan kanta kamar ƴar gida "
Haka