Showing 81001 words to 84000 words out of 96407 words

Chapter 28 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3636



Zama ta yi ta na masa godiya gaisawa suka yi cikin girmamawa. shima Haydar din yana zama kusa da ita.

“Gaskiya ne Ango tun kafin ka shiga daga ciki har ka fara hasken angonci” cewar Auwal yana kunshe dariyar sa

Kallon ba ka da hankali ya masa dan ya ga za su fara mai abinda suka saba a gaban Alisha da ta yi shuru a inda ta ke zaune,cikin canza magana ya ce

“Ba na son iskanci Auwal,mun zo gwaji ne ku mana in samu in mayar da Madam gida”

“Awwwwwwn” Auwal da Sadeeq suka ce, kafin suka saka dariya me karfi da ya sa Haydar watsa musu harara ko ta kan sa ba su bi ba suka tafa,su ka sake haɗa baki wajen cewa

“She is like a sister to me “ dariya suka kuma sawa bayan sun faɗi hakan.

Wani mugun kallo ya bi su dashi dan ya san tsokanar sa suke da abinda ya taɓa ce musu lokacin da suka ce mai ya auri Alisha, shi kuma ya ce musu ba wai son ta ya ke ba tausayinta yake ji,she was like a sister to him, shine yanzu suke amfani dashi suna mai dariya.

“Allah in ku ka ɓata min rai zan tafi wani asibitin a yi mana ba ɓata lokaci”

Ya faɗa yana yunkurin miƙewa da sauri Sadeeq ya riƙo sa yana kunshe dariyar sa

“Allah ya ba ka hakuri Angon satı biyu, dawo ka zauna ai baza mu bari ka ɗauki amarya ka kai ta ko ina ba mu na nan”

Buge hannunsa yayi yana “ naga lamarin na ku akwai renin wayo ne ai”

Duban Alisha Sadeeq yai yana “Amarya ki sa ba ki please “

Murmushi kawai tayi ,ta ɗan dubi Haydar. su na haɗa ido ta sa mayafinta ta rufe fuskarta.

Dariya shi da friends din nasa suka yi ganin yanda ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Sosai suke yi wa abokin nasu farin cikin samun mace da ya ke so, me hankali da nutsuwa, ga kunya ga ta yarinya ƙarama. sun san Haydar ze ji dadin zama da ita saboda hankalinta.

Auwal ne ya ɗibi jininsu ya tafi dashi lab bayan one hour ya dawo hannun sa riƙe da results guda biyu ya miƙawa Haydar. ko da ya duba nan ya ga result din sa da na ta everything was perfect dukkansu AA ne, godiya ya musu,sannan su ka mu su sallama suna ta tsokanar shi haka suka fita a office din. Ganin tana tafiya kamar ta gaji ne yasa ya riƙo hannun ta suka ci gaba daya tafiya, mutane sai kallan su suke yi saboda yanda suka yi kyau da kuma dacewa da juna abun baa cewa komai, duk wanda ya gan su sai ya ji sun burgesa musamman yanda suke jerawa a tare hannun su sarke cikin na juna,kowa ya ɗauka irin sabbin ma’aurata ne.

Khalil da ya fito daga office din wani doctor, yana tafiya hannun sa riƙe da car key din sa. ya je gun doctor ne karɓan magungunan Alhaji Jabir Lelewal,dama yau satın sa biyu a gombe kuma yau ze koma saboda ya gama signing contract din titin da ya kawosa shine ya shigo gun doctor Abban nasu ya karɓa mai magungunan sa ze fita kenan ya hango su suna nufosa,cak ya tsaya guri daya gaban sa na faɗuwa,sosai ya zuba mata ido kurr dan san tabbatar da ita ce ko ba ita bace, amma ita din de ya ke gani coming towards him.

Alisha da su ke tafiya tare da Haydar ne kamar an ce ta kalli gabanta ta na ɗagowa kuwa su ka haɗa ido da Khalil,wani irin rararas kirjinta ya bada sauti.

“Ya Khalil kuma? Me ya shigo yi a gombe” ta tambayi kanta ta na riƙe hannun Haydar gam da sai da ya juyo ya kalle ta

“Black Queen are you okay?”

Kai ta gyada mai batare da ta nuna masa wani alaman tana cikin firgici na kallon Khalil da tayi tsaye a gaban su ba,shi kuwa hannu yasa yana goge idonsa dan tabbatarwa kan sa gizo ne ko kuma mafarkin ido biyu yake yi,tana ganin haka ta cewa Haydar su sauya hanya ba tare da ya kawo komai a ransa ba suka canza hanya. sauke ajiyar zuciya ta yi ganin sun fita a ward din gaba daya.

Bayan ya gama goge idon sa ne ya ɗago, sai de me? Wayam babu Alisha da ya gama gani yanzu. sosai ya sha mamaki ganin ba ta a gun da ya ganta tare da wani gaye tsaye,zagaye ya fara yi a cikin ward yana dube-dube amma babu ita ko alamar ta babu a gurin,da sauri ya fita a cikin ward ya nufi parking lot, yana isa motar Haydar ya bar cikin asibitin, kasancewar be gan su a cikin motar bane yasa be yi zaton suna a ciki ba.

Wani irin kerma jikinsa ya ɗauka a take ya ji wani irin zazzabi me zafi ya sauko masa, dakyar ya taka izuwa inda motar sa yake ya shiga, ko iya rufo motar be yi ba ya kifa kan sa a stirring yana hango ta a cikin idanun sa. tabbas ya san bawai gizo bane ko mafarki ba,,,Alisha ya gani ido da ido amma me hakan yake nufi.

Muryar sa na rawa ya furta “Alisha darling “

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

41 & 42_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

41 & 42

Su na tafiya hankalin ta gaba daya ba ya jikinta, tunanin ta kawai yanda haɗuwarta da Khalil ya kasance ne, ba ta so hakan ba sam, da ta san za ta fita har ta haɗu da daya daga cikin cousins dinta to tabbas da ta sanya niqab ko face mask,amma Allah ya rigada ya ƙaddara sai fa sun haɗu din,fahimtan ta tafi duniyar tunani ya sa ya dube ta yana

“Are you okay?”

A sanyaye ta ce “yes Uncle,am just nervous “

Dubanta yayi da kyau ya furta “nervous about what?”

Baki ta ɗan tura kaɗan,sai kuma ta ɗaga ido ta kalle sa shima kallon na ta yayi, ya ɗage mata giransa daya alamar yana jin ta

“Kai ba ka sani bane? In mace za ta yi aure tana jin fargaba,sannan ina kewan iyayena na so a ce suna raye zan yi aure” ta faɗa ta na ɗukar da kanta ƙasa hawaye na cikowa idonta,gefen titi ya je yayi packing motar sa ya kashe,ya juyo gare ta.

Haɓarta ya ɗago ya zuba wa fuskarta ido “Alisha”

Maimakon ta amsa kiran sunan ta da yayi sai ta ɗago idanunta da suka tara ruwan kwalla ciki ta kalle sa dasu.

Sarƙewa idanun su yayi da na juna, kokarin janye na ta idon take amma ya ƙi ba ta damar hakan,so ta ke ta janye idon ta saboda ba ko yaushe take juran haɗa ido dashi ba.

“Trust me duk inda iyayen ki su ke suna farin ciki da kuma alfahari dake,na yi miki alkawari ba za ki taɓa kukan rashin su ba. zan maye mi ki gurbinsu matukar ina raye”

Lumshe idanun ta yi hawaye suka gangaro a hankali akan fuskanta. wani irin mugun kewansu ne ya lulluɓeta, ta na jin wani abu na tokare mata zuciya wanda za ta iya kiransa da kunci,tayi kewan su ta yi tsananin kewar lokutan da su ka ɗiba tare. Rawa tsakar zuciyarta ya fara nan ta fara gyada kai ta buɗe idanunta ta kalle sa dasu murya na rawa

Ta ce “uncle ina bukatar yin kuka,zuciyata zafi. Ina kewan ahali na. Ina kewan su sosai,ina son yin kuka”

Cike da tsananin tausayinta ya gyada mata kai tare da jawo ta jikinsa yana tapping bayanta ya ji ta fashe da kukan da ya taɓa masa zuciya ya ji kamar ya ta ya ta yin kukan,sosai ya ke shafa bayanta, yana jin yanda ta riƙe gaban rigarsa gam tana kuka ga zuciyarta da mugun bugawa.

“Shisssssh is okay My Queeen” ya faɗa ya na sake mannata a cikin jikinsa, kanta manne a faffadar kirjinsa,sautin kukanta har tsakiyar kansa yake ji. Kusan mintuna biyar ta ɗiba tana kuka sam be yi kokarin hanata ba,saboda in mutum ya faɗa da bakin sa yana bukatar da yayı kuka to abu na cin sa a zuciya ne,kar ka yi yunkurin hana sa yin kukan da ya furta yana son yi,ka bar sa yayı kukan,ta hanyar yin kukan ne ze samu relief,ɗagota yayi a jikinsa yana kallon face na ta da manyan idanunta suka yi ja fuskarta ya jike da ruwan hawaye,hannu yasa ya goge mata hawayen tare da hura mata iska a fuskan,ya matso daf da ita sosai fuskar su na daf da gogan na juna,tsinin hancin su na kokarin haɗuwa,murya cikin raɗa ya furta

“ Kukan ya isa haka Queen. ka da kan ki ya fara ciwo, na san yanzu kin ji sassauci a cikin zuciyar ki”

Tunda ya soma magana ta tsurawa pink lips din sa idanu tana ganin yanda yake motsa su kamar wanda yake tsoron motsa su,yanda numfashin sa yake sauka akan fuskanta ne yasa ta lumshe idanu tana jin bugun zuciyarta na sake tsananta.

A hankali ta matso da na ta face din inda hancin su da goshinsa ya samu daman haɗewa guri daya suna gogayya ta ɗaura soft lips dinta akan nasa ta sumbata, idanunta are still closed,Haydar knew she is not aware of what she’s doing,she just want to calm herself down that’s why she find his lips so attractive da ya kai da ta yi kissing nashi.

Harɓata ya riƙo with just two fingers ya zubawa innocent face na ta ido, kafin ya manna mata kiss a kumatu,saukan kiss din da ta ji ne yasa ta saurin ware idanunta tana me dawuwa hayyacinta, baya ta ja ta koma gurin zamanta tana runtse ido tuna abinda tayi.

Furzar da iska yayi a bakin sa ya tayar da motar suka soma tafiya batare da dayan su ya kuma cewa komai ba,wayarta dake cinyarta ne ya soma ƙara da ya sa firgit da buɗe idanunta a tare shi da ita suka kalli wayar,number da babu sunana ne yayi appear a gaban screen din,ta ƙasan ido ta kalle sa ta ga ya maida hankali kan hanya yasa ta ɗaga,gudun kar ta shiga zargine yasa ta ɗaga wayar ta sa a kunne tana matse gurin rage volume.

A bangaren inna da ta kira ne ta ce “Alisha in da hali ki bar duk abinda ki ke yi ki gaggauta zuwa gida akwai matsala”

“To” kawai ta fada ta katse kiran tana tunanin wannan irin kira da inna ta mata na meye? meke faruwa, dan a tsawon zaman su ba ta taɓa mata irin wannan kira na gaggawa ba, hakan ya tabbatar mata da akwai matsala babba.

Kwantar da jikinta tayi a kujera tana lumshe idanunta da suka ɗan kumburo hankalinta gaba daya ya karkata ya koma kan gida.

“Are you okay?”

“Yeah Alhamdulillah” ta faɗa a gajarce.

Ko da suka isa gida bedroom dinta ta shiga bayan ta shiga gun Adda ta sanar mata da dawuwar su,kwanciya tayi tana tunanin abubuwan da suka faru yau daga fitan su harma dawuwansu gida.

Missed call din Inna da ta sake gani ne yasa ta miƙe zaune tana kafe wayar da ido,tana tunanin yanda za ta samu ta fita.

Suna zaune a falo suna hira suka hango shigowansa. yanda ya ke tafiya kaɗai ya isar musu da sakon bayi da lafiya Duk kallon sa suke yi suna jiran ya iso falon,ko da ya shigo kai tsaye gaban Alhaji Jabir ya nufa ya duƙa a gabansa ya dube sa da idanun sa da suka rine,amma be ce komai ba. cike da kulawa Abba ya ɗaura hannun sa a wuyan Khalil ya ji yanda jikin sa ya ɗau zafi rau

“Subhanallahi Khalil me yake damun ka haka? Ba ka jin dadi ne?”

A maimakon ya bawa Abba amsar tambayar da ya masa sai girgiza kai yayi yana duban fuskan mahaifin nasa.

Ganin ya ƙi cewa komai ne yasa Umma cewa “Khalil ba ka ji Abban ku yana tambayar ka bane ? Me ke damunka?”

Dawo da duban sa kan ta yayi dakyar, ya yi na mijin kokari wajen buɗe bakin sa, ya ce

“Umma na gan ta,ido da ido na ganta yau Umma,Wallahi ba ta mutu ba tana nan a raye”

Da mamaki su ke kallon junan su jin maganar da ya faɗa wanda sam ba su fahimci inda ta dosa ba.

Kallon Ummah Abba yayi kafin ya kalli Khalil dake duƙe a gaban sa kamar me neman gafara,ya ce

“Khalil akan wa ka ke magana? Wacece take raye ba ta mutu din ba?”

Sai da yayi gathering courage saboda yanda kansa ke sarawa, ga masassara na nuƙurƙusan shi

Ya furta

“Alisha,yau na ga Fav cousin a hospital ita da wani gaye yana riƙe mata da hannu,ido da ido mu ka ga juna amma kafin in tattaro duk wata nutsuwata sa ban ganta ba kuma”

Tirkashi! Khalil ya zo mu su da babban magana da ya ja suke masa kallon bashi da hankali ta ya zaa yi ace wanda ya mutu ya dawo?hakan ba me yuwa bane. it’s either me kama da Alisha ya gani ko kuma de gizo ta yi masa.

Kowa baki sa ke suke kallon sa kamar baƙon halitta,Abba ne ya jinjina kai yana, faɗin

“Khalil wannan wani irin magana ne? Tunda ka ke ka taɓa ji ko ganin wanda ya mutu ya dawo? Maybe zazzaɓin da ka ke yi ne yasa ka ke imagining things”

Duk sun yarda da maganar Abba,Umma ma ta ce

“Kwarai kuwa Abban ku ya faɗi gaskiya,wanda ya mutu ba ya taɓa dawuwa Khalil,sai de ko me kama da Alisha darling ka gani”

“Exactly “ cewar Najib

Ganin duk ba su yarda dashi bane yasa ya riƙo hannun Abba

“Wallah tallahi Abba ku yarda da ni, na yi maka imanı da Allah Alisha na gani yau,ina cikin hayyacina kuma lafiya ta kalau. A lokacin da mu ka haɗa ido da ita na hango tsoro a cikin idanunta,tsoron ganin da ta min,sai kuma ta wayance kamar ba ta san ni ba. Tabbas Alisha ce kamanninta, kwayar idanunta komai da komai wallahi ku yarda da ni it’s her “

Zuwa yanzu lamarin Khalil ya gama ɗaure mu su kai, wannan babban zance da ya zo dashi ya dulmiyasu a duhu,su de sun san baa taɓa yin haka ba,ba kuma su taɓa jin labarin haka ba,amma yanda Khalil ya dage ya ke son tabbatar mu su da iya gaskiyar su ya ɗaure musu kai, tabbas Khalil ba ya daga cikin mutanen da su ke yin karya ko kuma fadar abinda ze dasa shakku a zukata,mutum ne me faɗar gaskiya da kuma yin aiki dashi,ba ya taɓa yaɗa jita-jita ko abinda ya san be tabbatar ba. Sanın wannan halayen na sa ne yasa maganar sa ya tsaya musu a rai.

“Khalil ka kwantar da hankalin ka bawai ba mu yarda da kai bane,maganar da ka zo da ita din ne me girman gaske,Ze iya yuwa me kama da Alisha ka gani ko kuma de….”

Katse Abba yayi da “Abba ni na san ba karya na ke faɗa mu ku ba,naganta da idanu na. Za ku ce na faɗa mu ku? za ku tabbatar da Alisha darling ta na wannan duniyar,my little sister is still alive “yana ƙare maganar sa ya miƙe tare da ajiyewa Abba dake bin sa da ido maganin sa sannan ya nufi bedroom din sa,duk bayan sa suka bi da kallo.

“Abban su shin ka yarda da maganar Khalil? Ni de hankali na sam be kwanta ba,Alisha fa tana cikin gidan ranan da abun ya faru saboda na yi waya da mamanta,da ba ta nan ai za ta ce main bata gida. Ina tunanin zafin zazzaɓi ne ya taɓa sa”

Sauke ajiyar zuciya Abba ya yi cikin sanyin murya, ya furta

“ Kar ki sha mamaki wata me matukar kama da ita ya gani da yasa duk ya bi ya daburce haka”.

Haka su ka bar lamarin dan wannan abinda ya zo dashi ba abu ne da hankali ze ɗauka ba.

Har za ta wuce ta hango Ameera a kitchen hakan yasa ta yi wani tunani,kitchen din ta shiga ta tsaya daga bakin kofa

“Ameera”

Jin an kira ta ne yasa ta juyo tana ganin Alisha ce ta ɗauki plate din da ta jera snacks a ciki ta nufota tana kai daya baki ta soma taunawa

Baki cike da snack ta ce “Amarsu ya aka yi ne? Sai ina?”

Murmushi ta yi ta ce “dan Allah ko da kin ji Adda na nemana ki ce mata na je bakin Junction yanzu zan dawo,akwai abinda nake son siya ne”

Kai ta gyada mata tana “amma kar ki jima kin ga yamma ya fara yi”

“In sha Allah “ ta faɗa tana wucewa,ta yi wannan dabaran ne dan kar a zo a yi ta nemanta baa san inda ta je ba,amma yanzu da ta sanar da Ameera ko an fara neman ta za ta ce ta faɗa mata za ta je ta dawo. Dan bazata iya rufe ido akan kiran Inna ba,ba ta san wani dalili bane yasa ta ke mata wannan kira na gaggawa ba. Hankalin ta ya tashi.

Napep ta tara ta sanar mai inda ze kai ta,30 minutes ne ya ɗauke su kafin suka isa kofar gidan. ta miƙa mai kudi sannan ta tura ƙaramar kofar ta shiga,a tsakar gida ta iske İnna dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login