Showing 12001 words to 15000 words out of 96407 words
Chapter 5 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
idanun sa a kan commissioner yayi “ aikina ba yi da haɗi da alakar mahaifina da mamacin. Abinda na sani shine zan nemo me laifin da ya aikata kisan kai.” ya faɗa yana miƙewa tsaye.
“Am so proud of you Haydar Allah ya bada saa” sara masa yayi ya fita. Kai tsaye motar sa ya nufa ya shiga,sannan kai tsaye ya wuce Gona devision . yana shiga ƴan sanda suka fara sara masa
Gently ya furta “Shin an samu wani bayani dangane da kisan mamacin?” Wani ɗan sanda ne yace “No sir har yanzu”
“Okay ina bukatar mai gadin gidan Hashim zakewa a station “
Zaro wayarsa daga aljihu yayi saboda ƙarar da yaji yana yi “hello Adda na” da yake haka yake kiranta da Adda, bama shi kaɗai ba,kowa haka yake kiran ta da Adda.
“Haydar kana Ina ? Matar Sameer ta haihu ta haifi namiji”
Kayitacciyar murmushi ya saki “Masha Allah gaskiya na yi murna in sha Allah ko zuwa dare zan zo ganin baby boy”
Bayan an kawo Mai gadin ne aka kai sa investigation room. Zama yayi yana fuskantar me gadin
“Kai ne ka ke gadi a gidan Hashim zakewa ?”
“Kwarai ni ne”
Haydar yace “bani labari ya wannan daren ya kasance”
“Bayan su Alhaji sun shiga sun kwanta, kamar kullum da na saba se na duba ko Ina na cikin gidan sannan in rufe gidan. karfe daya nake shiga in kwanta,karfe biyu da rabi na ji ana buga min kofa nayi tunanin Alhaji ne hakan yasa ban kawo komai araina ba na buɗe. Ina buɗewa naga wani mutum a gabana sanye da bakaƙen kaya fuskarsa na sanye da mask domin idanunsa kawai nake iya gani. kafin in an kara ya buga min abu akaina farkawan da zan yi na ganni a tsakar gida an min ɗaurin goro,sannan ga kuma matar yallabai itama an ɗaureta an manne mata bakin ta da game, jaririnta na kwance a ƙasa yana ta tsala ihu. Se ga makashin ya fito da Alhaji shima ya masa ɗaurin goro.yana jawo igiyar da ya ɗauresa dashi kamar wanda ke jan Kayan wanki. Wani irin wuka da tunda nake ban taɓa ganin sa ba wannan makashin ya fito dashi. Sokawa Alhaji ya yi a ciki da kuma kirji daga karshe kuma ya masa yankan rago wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wannan shine iya abinda na sani”
Duk abinda yake faɗa Haydar na rubutawa bayan ya gama magana ne ya dubesa “shin zaka iya kwantanta min yanda kirar jikin makashin yake?”
“Ehh to a gaskiya de siriri ne bashi da jiki yana da ɗan tsayi ba sosai ba. Sannan yana da kaifaffan idanuwa wanda babu tsoro a cikin su a tsaye suke a bushe.Wannan ne iya abinda na sani”
“Da yake yi masa wannan azabar be yi magana ko kuma faɗar dalilin sa na yin kisan ba”
Girgiza Kai me gadi yayi
“Gaskiya ban ji ya yi ko tari ba,komai yake yi cikin nutsuwa yake yi “
Jinjina kai ya yi “mun gode in muna bukatar wani abu zamu nemeka “ Haydar ya faɗa yana miƙewa ya ɗauki files din ya fita. Gidan su dake Tudun wadan Sarki ya nufa.
Kannensa mata ya samu a falo suna hira Ameera da Zainab suna ganin sa suka ce “barka da dawuwa uncle Haydar”
“Barka dai ku ba ku je gidan haihuwan bane?”
“Eh Adda ne tace se ta dawo zamu je”
“Okay “
Bangarensa ya nufa yana kokarin shiga ya hango kofan falon Sameer a buɗe, hakan yasa ya fasa shiga nasa bangaren ya nufi na Sameer din. ko da shigansa samun sa ya yi yana aikata zina da wata a tsakiyar falon sa. Runtse idanu yayi
“Sameer iskancin na ka yanzu har ya kai ka dinga kawo mana matan banza gidan mu na sunna kana aikata zina da su?”
Da sauri ya tashi a kan yarinyar yana tureta gefe tare da ɗaura towel
“Haydar kai wani irin dakiki ne da zaka shigo min bangarena ba tare da neman izinina ba?”
Kallon takaici kawai yake bin sa dashi kafin ya kalli yarinyar “ke kuma dan uban ki zo ki wuce ki bar gidan nan kafin in sauya miki kamanni shashasha kawai” ganin yanda Haydar ke watsa mata mugun kallo ne yasa ba shiri ta sanya kayanta ta wawuri jakanta ta fice da gudu.
Kallon sa yayi yaga hankalin sa kwance ko kunya be ji ba “wallahi ko da ni ce a matsayin maryam bazan taɓa zama da mazinaci irin ka ba Sameer,domin kuwa wata rana zaka iya sawa yarinyar mutane cuta. Dube ka dan Allah ko kunya baka ji a gaban kannenka ka ke kawo matan banza ka wuce ta gaban su. Ya zaa yi bazasu rai na ka ba? Kaji tsoron Allah Sameer. ka mayar da kan ka mazinaci ɗan shaye-shaye kai abin be maka yawa ba dan Allah? ko Ina se bata mana suna ka ke tirrr da wannan halin na ka”
Rai a bace Sameer ya miƙe “how dare you Haydar,, yaushe ka zo duniyar ma da har zaka tsaya a gabana kana faɗa min banzayen maganganu? Wait ban hana ka ma shiga rayuwa ta ba? Ko ciki daya muka fito ne?”
“Na ji uwar mu ba daya ba,amma uban mu daya ka ga kuwa ko mutuwa zaka yi se na faɗa maka gaskiya. Sannan da ka ke maganar ka girme ni me yawan shekarun suka tsinana maka? Ko kana aiki da su ne mutumin banza kawai”
Yana gama magana ya fice masa a falo ya nufi nasa yana jin zafi a ran sa domin kuwa ya tsani dabi’ar yayan na sa. amma ya ze yi Sameer mutum ne da baa faɗa masa gaskiya yanzu se ya fara tsanar ka,bugu da ƙari mahaifin su Ɗan gaske shine yake ɗaure masa gindi shisa yake sheka ayarsa yanda yake so.
Wanka ya yi sannan ya gangaro falo ya ci abinci suna hira da kannen sa.
Bayan la’asar su Adda sun shirya zasu tafi “nikam Hajja Hauwa baza ku mayar da yarinyar nan gurin iyayenta ba? Danginta kila suna can suna nemanta.”
“Eh in sha Allah yau zata koma “
Alisha dake tsaye a bakin kofar su ta kasa kunne tana jin abinda suke faɗa ne,
ta ce “ai na zo Kenan tunda na san ku din su waye ba zan taɓa rabuwa daku ba har se na gama aiki na” tana gama magana ta nufi dakin da take ta zauna domin ta ji alamun kamar fitowa zaa yi.
“Yawwa ke kuwa ba ki gaya min a wani anguwa ki ke ba ga yamma ya yi yakamata a mayar dake gida”
Cewar Hajja Hauwa da ta shigo dakin tana tsayuwa jikin wardrobe
“Dan Allah baiwar Allah ki taimake ni wallahi ni marainiyace banida kowa,ki taimaka ki bani mafaka ko aiki in dinga miki ni ko baki biyani ba bakomai inde zan samu mafaka da ci da sha asirina ze rufu dan girman Allah ki taimaka min “
Sosai jikin Hajja hauwa ya yi sanyi domin kuwa ita din macece me matukar tausayi abinda Alisha ta faɗa mata ya matukar kashe mata jiki
“Allah sarki kin ban tausayi sosai,shikenan tunda haka ki ka ce zan ɗauke ki aiki abinda zaki dinga min shine wanke-wanke da shara kawai, kuma ai bazeyu in danne miki hakkin ki ba dole na zan dinga biyan ki. Ni de abunda nake so ki kasance me gaskiya da riƙo da amana. Sannan ki saki jiki ki dena wannan takurewa guri dayan dan Allah kema yanzu yar gıda ce. Ina da yarinya kamar ki sunan ta Yusra. Yawwa in kin samu sauki se ki fara aiki sannan ga Kayan sawa nan baki da matsala “
“Nagode hajiya na gode sosai Allah yabiyaki bani da bakin da zan iya gode miki sede in miki addua”
Murmushi tayi “ bakomai,sannan kidena ce min hajiya sunana Hajja Hauwa dashi kowa ke kira na”
“To Hajja Hauwa “
Murmushin samun nasara tayi bayan fitar Hajja hauwa “yanzu aka fara wasan,zan shiga jikin ku yanda zaku yi danasanin sani na daga karshe“
Wanka da alwala tayi ta saka doguwar riga tare da dogon hijabi ta shimfida sallaya ta gabatar da sallah mangriba. Fitowa tayi a dakin ta shiga kitchen ta haɗa kwanukan wanke-wanke guri guda a sink ta duba morning fresh da zata yi wanke wanken amma bata gani ba hakan yasa ta nufi dakin Hajja Hauwa.
Da sanyayyan muryar ta ta yi sallama “ Assalamualaykum “
A tare Hajja Hauwa da maryam suka amsa mata
“Barkan ku de ya jariri “
Murmushi Maryam ta yi “lafiya lau Alisha ko?”
Dam ta ji gabanta ya faɗi jin yanda ta kira sunan ta kamar ta santa, satan kallon ta ta gefen ido ta yi bata ce komai ba.
“Hajja Hauwa haka yar aikin ta ki take da kunya ?” Cewar Maryam tana dariya
Itama Hajja Hauwan dariya ta yi “ Ahh ba laifi akwai kunya kam ga rashin son magana “
“Am.. Hajja Hauwa na zo tambayarki Ina morning fresh yake zan wanke kwanukan da aka ɓata"
“Ah ah ke da baki gama warkewa ba ki bari ki samu lafiya tukuna se ki fara aikin,zuwa anjuma zan yi wanke wanken “
Marairaicewa tayi “Ayyah Hajja Hauwa ki yi hakuri in yi naji sauki ai”
“Ba fa zaki yi ba Alisha in na tashi zan wanke su”
Maryam dake sauraransu ne ta ce “Hajja Hauwa kin gaji da yawa tunda tace zata yi ki bar ta tayi din mana”
“Yawwa Anty Maryam “ cewar Alisha
“Shikenan ai tunda kun fi ni da baki” ɗan murmushi suka yi ɗauko mata tayi ta bata
“Nagode “ ta faɗa tana fita
Tafiya take yi kan ta a ƙasa ji tayi ta bugi mutum har se da morning fresh din ya faɗi. da sauri ta sunkuya ta sa hannu tana kokarin ɗauka hannun sa ya riga nata taɓa roban.
A tare suka ɗago suka kalle juna “sorry ban lura dake bane” ya faɗa yana mika mata roban, karɓa kawai tayi ta miƙe tsaye kafin shima ya miƙen,yana kare mata kallo a ransa yana tambayar kan sa to Hajja Hauwa kuma ina ta samo wannan yarinyar. Ganin bata ce masa komai bane yasa ya motsa da niyar raba gefenta ya wuce hakan yayi dede da ita ma zata wuce din nan suka sake cin wani karon amma wannan karon kafaɗarsa ne ya gogi nata kafaɗar.
“Wai kai malam baka gani ne dan Allah ?” Ta faɗa tana tsuke fuska. da mamaki yake kallon ta ganin yanda tayi magana cike da tsiwa ga ta de a zahiri so innocent babu wanda ze yi tunanin yanda take da innocent face zata yi tsiwa haka.
“Wuta sarkin zafi Allah ya baki hakuri “ya faɗa yana harɗe hannun sa a kirji. Bata kulasa ba ta yi wucewarta ta shiga kitchen da kallo ya bita kafin ya girgiza kai
“Yara sa'an kannenka amma sun iya rashin kunya Allah ya kyauta “ ya faɗa yana shiga bedroom din Hajja Hauwa.
Cikin nutsuwa take wanke kwanukan har ta gama ta soma jera su a kitchen ware.
“Wai in ji Hajja Hauwa ki sa min Fura “ batare da ta ko waigo ba ta ce “ban san inda yake ba”
Yana tsaye a bakin kofa ya ji abinda ta faɗa hakan yasa ya shigo ya ɗauki kofi da spoon a cikin wayanda ta wanke, ya buɗe fridge ya fito da kindirmon dake cikin ƙaton galon ya soma kokarin zuba wa amma ya kasa saboda be iya ba. cikin tsautsayi nonon ya fara zubewa hakan ya yi dede da shigowanta
“Ah ah Haydar kai kuma yana ga kana sa nonon da kan ka? Ga shi baka iya ba kana ta zubarwa” da sauri ta juyo jin muryar Hajja Hauwa sanın laifin ta ne yasa tayi saurin cewa
“Laifi na ne,ya ce in sa mishi ni kuma ban san inda yake ba” ta yi maganar tana sunkuyawa gabansa ta karɓi kofin ta zuba masa sannan ta rufe gallan din.
“Ka yi hakuri” ya ji ta faɗa a sanyaye.
“Ai shi Haydar be iya ɗibawa ba,in ki ka sa shi ɗiba ma sede ya zubar dashi,ga shi yana son fura da nono sosai”
Cewar Hajja hauwa da ta dibo fura tana marmasawa ta zuba cikin cup din mikewa yayi tsaye yana wanko hannunsa.
Suna tsaye Hajja hauwa na dama masa fura ita kuma Alisha tana ganin yanda take yi
“Hajja hauwa aina ki ka samo wannan?” Yayi maganar ƙasa-ƙasa
“ sabuwar me aiki na yi “
“Wannan din?” Ya tambaya yana kallon ta haɗe fuska ta yi kamar bata san maganar ta suke ba
Shide mamaki ya cika sa domin kuwa Alisha duk wanda ya ganta yasan batayi kama da masu aiki ba,batayi kama da wacce wahala ya nu na a fatar ta ba.
“Alisha”
Da sauri ta sake fuskarta tana “Naam Hajja hauwa”
“Wannan shine Haydar ɗan kishiyata ƙanın Sameer ”
Satan kallon sa ta yi ta ga ita yake kallo abinda yasa ya kalleta din kuma ganin yanda expression na fuskarta ya sauya lokacin da ta ji shi ƙanın Sameer ne amma ya kasa gane me yasa yanayinta ya sauya lokaci guda.
“Ohh nagane barkan ka Haydar”
“Barka dai Alisha “
Nodding kawai tayi ta ci gaba da jera kwanuka,Hajja hauwa na basa furan ta fice
Bin bayan Hajja Hauwan shima yay se da ta tabbatar da duk sun fita ta ajiye plate din hannunta riƙe setin zuciyarta ta yi da taji yana mata zafi
“Sameer Ɗan gaske,Hon Modibbo Ɗan gaske ku ne silar shiga maraicina ba zan taɓa yafe muku ba… Haydar kenan shima jinin Ɗangaske ne? Dukkan su bazan bar su ba”
Tayi maganar a hankali har time din tana riƙe da setin zuciyarta
Wani murya ta ji a jikinta na faɗin
“Ah ah Alisha fansar ki iya mutanen da suka zalunce ki ne,kar ki shigar da wayanda ba su san komai ba,ke de ki shiga jikinsu yanda zaki samu biyan bukatar ki sannan ki bar gidan”
Gyada kai tayi tana sakin murmushi “Zan yi komai domin ɗaukan fansa ta”
Tana gama maganar ta gyara kitchen din ta yi mopping sannan ta je falo ta same sa zaune kamar bata san da mutum a falon ba ta hau gyare-gyare.
Maryam ce ta fito falon riƙe da jaririnta ta zauna suka fara hira da Haydar
“Uncle Haydar am ya aiki? Hajja Hauwa ta sanar dani kai ne ka ke binciken mutuwar Hashim zakewa. Allah ya toni asirin makashin nan”
Tana goge-goge amma hankalin ta da kunnuwanta yana garesu tana jiyo su jin abinda maryam ta faɗa ne yasa ta sake ƙare masa kallo tabbas se yanzu ta fahimci ya yi yanayı da jami’i.
Aranta ta furta “ɗan sanda ne shi kenan? Lallai Yakamata in bi a hankali domin alamu sun nu na yana da matukar basira. Dole in kwantar da wuya domin tserewa zargi”
“Maryam kin san Hashim abokin Baba ne, kuma duk halin su daya hakan yasa na tsani alakar baba da zakewa. Saboda kafin ya mutu na fara bincike akan sa kawai de ya mutu ne amma wallahi wayanda ya zalunta mutumin nan suna da yawa. na yi niyyar doka tayi aiki akansa a gurfanan da shi a gaban kotu. Se ga shi an kashe sa. Ko tantama bana yi daya daga cikin wayanda ya zalunta ne suka yi masa wannan kisan. Kawai commissioner ya ɗaura ni akan binciken nan ne in ba haka ba babu abinda ze sa in bi ta kan case din sa”
“Hmmm Allah ya kyauta. Dama mutumin nan kana ganin sa ka san ze yi rashin imani”
Cewar maryam
Juya maganganunsa ta dinga yi tabbas ko da iya kallon fuskarsa zaka fahimci Haydar is a very good person yanzu da ta ji wayannan maganganun da suke yi da Maryam ta fahimci shi de ya fito a jinin Ɗan gaske ne amma sam hali be zo daya ba. Halin sa ya fita daban be ɗauko halin ɗan uwansa Sameer ba balle na mahaifinsa Ɗan gaske.
Yana karɓan jaririn a hannunta yace “Sameer ya zo ne? ”
Girgiza kai ta yi “be zo ba,kuma be kira ni ba,Haydar bazan boye maka ba na gaji da zama da shi,baze taɓa sauyawa ba neman mata da shaye-shaye ya mayar dashi bakomai ba”
Cike da tausayinta ya ce “kiyi hakuri maryam,wata rana se labari ina me tabbatar miki akwai ranar da ze zo ya nemi yafiyarki “
“Hmmm Uncle Haydar kenan” kawai ta faɗa
“Sannu da aiki Alisha “
Ɗan murmushi ta saki “Yawwa sannu anty Maryam “
Dubanta yayi yaga mopping din dinning area take ya kalli maryam yana miƙa mata jaririn “ni zan tafi zan je gidan Hashim zakewa ƙarasa bincike,ki cewa Hajja Hauwa se gobe zan dawo”
“Laaa yanzu uncle Haydar bazaka shiga ciki ka mata sallama ba,yanzu in ta fito ta samu ka tafi masifa zata yi ta yi”
Dariya ya yi “ni de na tafi” ya fice a falon
Se mun hadu ranan Monday in sha Allah,kamar yanda ku ka sanı bana posting a weekend 🥰🥰
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
9 & 10_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi, to Kar ku yi ƙasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin nawa 08166018849 Mrs isham domin a tallata muku hajar ku.❤️😊
9 & 10
Washe