Showing 39001 words to 42000 words out of 96407 words

Chapter 14 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3608

ka. Ni da kai soon zamu yi aure, dan haka duk wata mace da ka ke da alaka da ita it will be good to end it “

Kalmar da ta faɗa na yana son Alisha ne ya dinga masa yawo a tsakar ka wanda har yasa sauran zantukan na ta duk be ji su ba, kalmar ya tsaya masa a rai sosai da yaji yana bukatar kaɗaicewa domin ya yi tunani,hakan yasa ya kalle ta jiki a sanyaye ya ce “Meenal yanzu ina cikin mood da nake son kasancewa ni kaɗai ki je bedroom din ki gobe zamu yi magana”

“Amma Haydar ka san de…” katseta yai ta hanyar faɗin “ki je mana. na ce za mu yi magana gobe kar ki sa in sauya ra'ayi na” ba ta da zaɓin da ya wuce ta tafi din ,dan in ta ƙi yin yanda yace har ta tunzura shi tofa ba hankalin sa zata samu ba hakan yasa ta fice fuuuu kamar iska.

Tun da ya ke be taɓa jin akwai kalmar da aka faɗe sa ya tsaya mai a rai ba kamar wannan,ya kasa gasgata hakan sam ya ƙi aminta da abinda zuciyar sa yake faɗa mai,shi ya san babu soyayyarta a cikin zuciyarsa tausayi ne kawai.

“She’s like a sister to me,tausayin ta kawai nake ji shine kawai “ ya tabbatar wa kan sa. Wanka ya shiga ya fito ɗaure da towel a kugunsa, murɗaɗen jikinsa me ɗaukan hankali ruwa na kwance akai se da ya sa towel ya goge fatar jikinsa sannan ya shirya saboda ze je office ɗaukan wasu files da ya manta dasu yana da bukatar yin aiki akan su kafin gobe Monday. Ya yi kyau sosai cikin shiga na wandon jeans da riga t-shirt se baza kamshi yake ga chocolate color skin nashi sai ɗaukan ido yake waya da key ya ɗauka ya fita.

KUMO local government

Gidan Alhaji Jabir Lelewal tun daga mashigar falo za ka jiyo hayaniya na tashi, Alhaji Jabir Lelewal shi da matar sa na zaune da ƴaƴan sa maza biyu ƴan mata biyu suna zaune sun yi jugum sun zubawa Alhaji Mustapha Lelewal ido yana ta zazzaga masifa. Dogon numfashi Alhaji Jabir ya ja cikin sanyin hali irin na shi ya ce

“Amma de yaya ka san de babu wani ƙadaran Sagiru a gurina ko? saboda tare dakai muka je wannan gida ba wai takaddun dukiyarsa ba hatta shi ka ga yanda ya koma toka shi da iyalansa, balle wani banza dukiya da duk yanda muke son su a nan duniya zamu tafi mu bar su. Ai yakamata wannan abinda ya faru da ɗan uwan mu wanda ya kasance ƙani a gare mu ya zamo mana darasi. Amma yau shekara guda kenan da faruwn wannan abu kusan kullum sai ka zo gidana ka ɗaga min hankali ni da iyalaina haba dan Allah.”

Muguwar kallo yake bin sa dashi kana ya ce

“wannan kai ta shafa kai ne kasan kutunkutun munafurcin da ku ka kulla kai da lawyer Sagir, in ba haka ba ai an san mu din danginsa ne tunda babu magadansa ai mu ne zamu ci gadon sa,ga filaye ga gidaje ga gidan mansa dake by pass Lelewal,ga gidan abincinsa duk wai bamu isa mu mallake su ba saboda babu takardunsu. Hauka ne abun? mu da ɗan uwan mu a ce za'a mana iya ka da dukiyarsa. to wallahi Jabir tun wuri ka je ka samu wancan tsinannen lawyer ya ɗauki hakkin ɗan uwan mu ya bamu “yana kai karshen maganar sa ya fita fuuu su de da kallo suka bi sa. Girgiza kai kawai Alhaji Jabir yayi yana Allah ya kyauta, ya rasa ɗan uwan sa wani irin son abin duniya ne dashi.

Babban ɗansa ɗan shekara ashirin da bakwai me matukar kama da Zaid ne ya ce “Abba to me yasa ka hana lawyer a bawa su uncle gadon Uncle Sagir ?”

Kallon ɗan na sa ya yi yace “ Haba Khalil sai ka ce ba ka san halin Uncle din ku ba? Yanda lawyer ya sanar dashi kan cewa babu shaidun da ze sa a bamu wannan ƙadarorin haka nima ya sanar min,Allah ya sani wlh wannan dukiya ta Sagir sam bata gaba na tunda nima de dukiyar nan ina dashi. A bar ni in ji da kewan ɗan uwana man, amma Alhaji ya sanı a gaba haba dun Allah”

“Ka yi hakuri Abban su komai ze wuce,ai shi yana tunanin kai ka hana komai bayan ba haka abin yake ba. Wallahi ni kaina ina kewar su matuka. in na tuna mun yi waya da Hajiya Hannatu Ana gobe za su rasu sai in ji jiki na ya yi sanyi sosai duniyar nan ba komai ba ce,amma wayanda ba su san hakan bane suke faɗa akan ta Allah de yasa mu dace “ Duk suka amsa da ameen,daya daga cikin yan matan da suka kasance sa’annin Alisha kallo daya za ka musu ka gane yan biyu ne sai de ba sa kama sosai, ta ce “Umma ni da Imaan mun yi waya da Alisha har da Aryan da dare ashe bazamu sake ganin su ba”

“Hmmm Ilhaam rayuwar kenan in da suka tafi mu ma wata rana za mu je Allah ya sa de mu dace” cewar me bin Khalil me suna Najib.

Alhaji Jabir da yayi shuru yana jin ƴaƴan nasa suna magana akan yan uwan su inda shima yake tuna ƙanın sa yake yi Sagir. sun ta so cikin so da kaunar juna komai tare suke yi sai de sun samu banbancin raayi. wannan doctor wannan kuma engineer. kuma shi Alhaji Jabir ya fi son rayuwar kumo , saɓanin Dr Sagir da yake rayuwa shi da iyalansa a cikin Gombe duk da haka babu abinda ya sauya cikin alakar su suna kawo musu ziyara sosai,haka suma suna kai musu. mutuwar ɗan uwansa ya taɓa sa sosai duk da ya kasance mutum me sanyi amma sanyin nasa ya ninku ,saɓanin babban yayansu wato Alhaji Mustapha Lelewal da sam mutuwar be damesa kamar son mallakar dukiyar da Dr Sagir ya bari. Dama shi tun asali yana da son abun duniya duk da yana da kudi shima amma san kudin sa ya wuce misali.

Shurun da ta ga yayi ne yasa ta faɗin

“Abban su tunanin me ka ke yi haka? dan Allah kar ka sanyawa kan ka tunani da yawa har ka kamu da ciwo,ka ga yanzu ma likita yace in baa kiyaye ba jininka ze hau. babu abinda Sagir da iyalansa suke bukata a wajen mu sama da addua mu”

Gyada kai yayi yana sauke numfashi “Fatima wato Ina mamakin mutane wallahi abinda Alhaji yake yi ko bare ne baze yi haka ba. Ɗan uwan mu ne fa ya mutu,ɗan ƙaramin ƙanın mu da muka nunawa gata lokacin kuruciya amma yanzu saboda kayan kyalekyalen duniya ya manta da hakan hmmm. Ni wlh ko da a ce zaa ɗauki dukiyar Sagiru a bani to be wuce in yi masa sadakatu jariya dashi ba, zan gına masallaci in haƙi rijiya da kuma taimakon talakawa ladan ya isa kabarin su. Kaicon Alhaji kaico “ ya karishe maganar cike da tsantsan bakin ciki,kallon yaran ta yi “Imaan da Ilhaam ku tafi dakin ku,kuma haka khalil da Najib”

A tare duk suka nufi dakunan su domin bawa iyayen na su guri,dakin sa ya shiga ya rufe ya kafe inda babban hotonta yake kamar zata yi magana tsabar yanda hoton yayi kyau ya yi clear kamar ka kira ta ta amsa da ido.

A hankali ya nufa inda hoton yake ya tsaya yana kallon ta na tsawon mintuna kafin hawaye suka fara gangarowa a idanun sa

“Yau shekara daya kenan da mutuwar ki Alisha darling amma na gagara cire ki a raina,na gagara manta ki. Na gama tsara mana rayuwar farin cikin da zamu yi mu da ƴaƴan da za mu haifa, sai ga shi tun kafin in kai ga bayyana miki soyayyata kin tafi kin barni a wannan duniyar. Bana jin zan iya rayuwa da wata ƴa mace in ba ke ba,Ke ce macen da na fara so a rayuwata ta ya ya ne zan iya mancewa dake a duniya ta ke din komai dina ce” jin alamun ana yunkurin shigo masa daki ne yasa ya share hawayen fuskansa sannan ya koma ya zauna. shigowa Najib ya yi ya zauna kusa da ɗan uwan nasa kallo daya ya masa ya fahimci yayi hawaye sakamakon yanda gashin idanunsa da suka kasance dogaye suka mammanne da junan su

“Ya Khalil shin har yanzu ashe ba ka manta da Alisha darling ba? Yakamatu ka manta da komai ka ga de yanda su Abba suke ta ma ka maganar aure alhalin kai ba ka da ko budurwa “

Duban sa yai kamar ze ce wani abu kuma se yayi shuru,fahimtar hakan ne ya sa Najib cewa “dan Allah ka manta komai babu abinda Alisha darling da su uncle suke bukata a gare mu kamar addua”

Cike da damuwa ya ce “in sha Allah nagode ka samu ka je dakin ka ka kwanta dare yayi nima yanzu zan kwanta”

Miƙewa yai yana me masa se da safe.

10:30Pm tana zaune gaban table gabanta system ne da littatafai dakin duhu saboda kashe wutar da tayi se candle da ta kunna shi ya bada damar haska kyakyawar fuskanta da gashinta da ta warware ya zubo gaba yana rufe mata fuskan ita kuma tana sa hannu tana kwashe su tare da mayar dasu baya, amma duk da haka sake zubowa suke yi,fuskan ta babu yabo babu fallasa manyan idanunta suna kafe akan system din ta tayi focusing akan abinda take yi,wayarta ne ya yi ringing tana dubawa ta ga sunan Mujahid, ɗaga wa tayi batare da tayi magana ba tayi shuru kawai alamun shine yake magana ita kuma ta kasa kunne tana sauraransa se da ya gama kana ta ce

“wow gobe ze dawo kenan? Shikenan kafin karfe biyun de mu yi waya ” tana faɗin haka ta katse kiran ta ajiye wayar sannan ta yi serching Chairman Chukwuemeka Peter and his family,bayanan sa ne rututu ta ga ya watso mata. hoton sa ta gani da yaran sa yan shekara goma zuwa sha biyu guda uku,se shi da matar sa. Tabe baki tayi ganin bayida manyan yara,dan ita ta fi son suna da manyan ƴaƴa yanda za su ji zafi kamar yanda suma suka ji wannan zafin. Fita a shafinsa tayi ta shiga shafin Habibu katanga wanda shine next target din ta. Ba ita ta tashi a gurin nan ba se karfe daya saura ta miƙe ta shiga toilet. wanka tayi ta yi shirin bacci,koda ta kwanta baccin be zo mata ba saboda tunani da ta ringa yi har karfe biyu kafin ya sace ta bata sani ba.

Ko da rana ya fara fitowa inna ta ji ta shuru bata fito ba hakan yasa ta shiga dakin nan ta iske ta tana bacci hakan ya tabbatar mata da Alisha ba ta samu bacci ba jiya da dare,duban agogo tayi ta ga karfe sha daya saura shiga tayi tana “rana ya yi yarinyata ki tashi kin ji” kai kawai ta gyada mata sannan ta shiga toilet tayi wanka da brush sallah kam ta rigada da tayi tun asuba. fitowar ta bata ga inna a dakin ba, wayar ta ta duba nan ta ga tarın missed call din Mujahid waya suka yi yake sanar mata yanzu ze fito.

“All the best “ ta furta sannan ta ajiye wayar tana murmushi. Baƙar leda ta ɗauko a cikin wardrobe dinta ta sa almakashi ta buɗe sa, kaya ne suit na maza baƙaƙe a ciki, sanya su tayi sannan ta sanya wani fuska irin na maza, babu wanda ya isa ya ganta ya ce wannan macece saboda suit din da ta sanya oversize ne ya boye duk wani halittan surarta, sai ma kumburata nan take ta tashi daga Alisha ta koma wani namijin daban saboda mask din maza da ta sanyawa fuskarta da kanta. Ƙarewa kan ta kallo tayi a mirror ta yi sannan ta buɗe maajiyar kayan aikinta sannan ta ɗauko wukan da take ji dashi sannan da wani dogon igiya me karfi ta sanya su cikin wata yar jaka ta riƙe. Takalmi cover shoe ta sanya sannan ta fesa wani Turare me karfi da ya kasance turaren maza. A karo na biyu ta kuma kallon kan ta a jikin mirror yanda ta ɓatar da kamanta ne ya sanyata sakin murmushi tana shafa sajen dake fuskarta na mask din.

Fita a gidan ta yi batare da ta sanarwa inna dake kitchen tana haɗa mata abin karyawa ba.kan ta tsaye take tafiya sanın babu wanda ze yi zargin wannan ba namiji bane har ta tari ɗan sahu ta sanar dashi inda ze kai ta.

A gidan Hon. chukuemeka Peter kuwa daya daga cikin amintattun driver sa ne ya ɗauki haɗaɗiyar motar ya fita domin ɗauko uban gidan nasa a airport a lawanti. yana cikin tafiya harya haura mill uku ya ga wani matashi yana tare sa da kamar ba ze tsaya ba se kuma ya tsaya yana “Kai ya aka yi ne”

Se da ya matso kusa da motar sannan ya ce “dan Allah zan je Lawanti ne ko za ka min lift?”

“Okay shigo nima can zan yi” yana riƙe da jakan makaranta ya shigo ya zauna gaban motar driver ya ja motar suka ci gaba da tafiya se da ya ga an zo tsakiyar daji in da babu kowa sannan ya dubi driver ya ce “dan Allah ko za ka tsaya, fitsari ya matse ni wallahi “

Ran sa be so ba dan baya son abinda ze sa ran Peter ya ɓaci amma haka ya tsaya yana “kar ka ɓata min lokaci” murmushi yayi ya fita yana zagayawa ta bangaren driver ya ce “na ce ba” yana juyowa ya fesa masa wani turare ba tare da ɓata lokaci ba ya suma. Se da ya tabbatar da babu kowa a gurin sannan ya sauya kayansa izuwa kayan driver, ya kuma ɗauki driver ya sanya sa cikin boot ya rufe motar ya shiga yana sauke gwauron numfashi kana yace “am doing this for you abokina Zaid” kiran waya yayi ya ce

“Plan A mission successfull” da gudu ya fisgi motar ya nufi airport ko da ya je ya tarar da Peter da be jima da saukowa daga Jirgi ba tsaye kana ganin sa zaka fahimci ransa ɓace yake ko da yay parking fitowa yai cike da biyayya ya nufosa yana ɗan duƙawa tare da kokarinsa na karɓan jakan Peter din dakatar dashi ya yi

“Kai yaro ya haka,ina Kingsley yake? Ya na gan ka da mota ta?” Ya wurgo masa tambayoyi a tare.

“Sir! Oga Kingsley ne ya aiko ni saboda yana kokarin zuwa nan shine ya samu rauni, to shine ya roƙe ni in zo in ɗauko ka. ya ƙara dacewa in ba ka hakuri. Ni brother sa ne” duba da yanda yake kallon sa za ka tabbatar da maganganunsa ba su wani gamshesa ba. Wurga mai jakan yai ya shiga bayan motar yana me hakimcewa.

“Da sauki ai tunda ka yarda kuma har ka shiga” ya faɗa a hankali kafin ya shiga mazaunin driver ya soma driving, suna fitowa bakin AirPort din wani na miji ya tare su cikin shiga na suit be damu da abinda Peter ze ce ba ya tsaya gaban wannan mutumin

“Ɗan uwa ina zaka je?”

Da tsantsan mamaki Peter yake kallon sa kafin ya ce “kai mahaukaci ne? A motar na zaka tsaya kana kokarin ragewa wani hanya you’re very stupid my friend dallah ja motar mu tafi “ ko a jikin sa da yanda yake mai magana a tsawace ya ce

“Saboda motar ka ce sai aka ce ba z'ayi taimako ba Kenan? Ku fa ƴan siyasan nan renin wayon ku ya yi yawa kuna ɗaukan kan ku kunfi kowa mtsssw “

Mamaki,al’aljabi lokaci daya suka kama Peter ya zubawa so called driver nashi ido har be san lokacin da mutumin da ya nemi ragin hanya ya shigo motar ba.

Tafiya suka yi babu me magana kowa yayi gum se a lokacin da mujahid ya canza hanya sannan ne Peter ce wa “ya kuma na ga ka biyo ta wannan dajin mu da zamu shiga cikin Gombe? ”

Babu wanda ya amsa shi ya ci gaba da tafiya hankalinsa kwance.

Ganin ya share sa ne yasa shi sake faɗin “dakai fa na ke magana “nan ma shuru duk su biyun suka masa kamar ba su san yana magana ba. Nan ne jikin sa ya ba sa wayannan mutanen akwai abinda suke shirya masa,a tsorace ya zaro wayarsa ze yi kira mutumin da suka wa lift yana kallon duk movement din shi ta mirror, juyowa yayi ya kwace wayar nasa sannan ya shaka masa wani abu a hanci da ya kashe masa jiki ga shi nan de idanun sa biyu amma jikinsa ya mutu murus ko yatsarsa baze taɓa iya motsawa ba. Se bin su da kallo da yake yi. fakin motar yayi a tsakiyar dajin da babu kowa se kananan dabbobi ga gaba da su kuma babban kwari ne ( rami ) me matukar girma da zurfi.

“Alisha darling mun iso shin me za'a masa “ murmushi na mijin da aka kira Alisha yai ta zare mask din fuskarta nan take yalwaltaccen sumanta suka zuba fuskarta da gadon bayanta.

Ɗan ƙaramin ribbon ta ɗaure gashin kafin ta buɗe baki ta ce “Duk abinda za mu yi mu na da mintuna talatin ne kacal Mujahid. A da na yi tunanin yi masa abinda na yi wa Hashim Zakewa amma shi wannan ina son mutuwar sa yafi na zakewa muni. Ina son yayi mummunar mutuwa ya ji azabar da ake ji in aka kona mutum da ran sa”

Jinjina kai yai sannan suka fito a motar suka bar sa se zare ido yake domin yanzu ya gama gane abinda suke nufi dashi duk da be san su din su waye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login