Showing 66001 words to 69000 words out of 96407 words
Chapter 23 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
jijjiga da ganin wannan video dan tabbas ta ga fitan Meenal yau kuma tabbas da wannan kayan a jikinta ta fita ashe abinda za ta je aikatawa kenan.
“To a gaskiya an zo gaɓar da ba zan bari yallabai ya cuceka ba,da farko ana ta maganar auren ka da yarinyar nan bance komai ba saboda ina tunanin in ku ka yi aure za ta shiryu,sede ba haka bane wannan yarinyar babu alamun hakan a ranta.”
Adda ta faɗa rai a ɓace sosai tana miƙewa tsaye ta bar Part din nata,bin bayanta Haydar yayi dan ya san bangaren Ɗan gaske za ta je,haka su Yusrah da Maryam duk suka bi bayanta.
Ita daya ta rage a falon zaune duk sun watse sun barta daya bayan daya,bazata iya bin su ba balle ta ji me suka tattauna akai ba saboda matsala ce ta su ta ahali.
Murmushi ta sake tana haurawa kan kujera ta zauna ta soma danna wayarta,the same video da aka turawa Haydar ita ma aka tura mata buɗewa tayi murmushin kan fuskar ta na sake faɗaɗa.
A babban haɗaɗɗiyar falon Ɗan gaske kuwa duk suna zaune kowa yayi shuru suna jiran su ji me ze ce,shi kuwa yana zaune hakimce akan kujera hannunsa riƙe da wayar Haydar yana kallon video.
“Ungo nan Zainabu ba sa wayarsa” ya faɗa yana miƙa mata wayar.
Fuskar sa babu yabo babu fallasa ya dubi Haydar ya ce
“Dakatar da wannan aure ze kawo mana saɓani ni da abokina,amma hakan baze sanya ni in tauye maka hakkinka ba. Na san dama ba san ta ka ke yi ba ka amince da wannan auren ne saboda biyayya Allah ya maka albarka.”
Yanda ya amince da dakatar da auren cikin ruwan sanyi ba ƙaramin mamaki ya bawa kowa ba,saboda yanda suke da Katanga ,sun yi zaton se an kai ruwa rana akan maganar amma cikin mamakin su ya amince within a minutes.
Cikin samun kwanciyar hankali Haydar ya furta “nagode sosai Baba”
Yana karkaɗa kafa ya dube sa da kyau “dakata mana bawan Allah ai bawai ka gode ba,dole ka fito da matar aure a yanzun nan tunda ita wannan din Allah be yi matar ka bace.. dan yanzu zan kira Katanga in shaida masa komai”
Shafa sajen fuskarsa yay yana kallon kyakyawar fuskarta na masa gizo a ido
“Baba wacce nake so a gidan nan ta ke”
Da ga Adda,Ɗan gaske da su Yusrah da kallan mamaki suke bin sa jin abinda ya faɗa, yanzu a gefe daya kuma suna tambayan kan su wace yarinya ce a gidan nan wacce yake so bayan kuma duk su yan matan gidan kannensa ne kuma yan uwan sa na jini
Cikin zurfafa tunani Yusrah ta ɗago kai a sukwane ta kalle sa domin wani tunani ne da ya faɗo mata a rai ya girgiza ta hakan yasa ta cewa
“ Duk gidan nan mutum daya ce bare a cikin mu,hakan yana nufin Uncle Haydar kana magana akan Alisha ne?”
Sai da ya lumshe idanun sa kana ya iya furta “Kwarai Yusrah! Alisha ita ce yarinyar da na ke so kuma na ke burin aure “ ya juya ga Ɗan gaske
“Baba ita ce wacce na maka magana akai “
Adda ta yi mamaki duk zaman su a gidan ace babu wanda ya taɓa sanın Haydar da Alisha akwai wani abu a tsakanin su,har cikin zuciyarta ta yi farin ciki domin yanda ta ɗauki Alisha a cikin ranta ya wuce misali, ta san ta yi dacen surka natsatstsiya me tarbiyya da girmama manya. Ba iya Adda ba hatta su Yusrah da Maryam wannan abu ya mu su dadi, dan da Haydar ya auro musu Meenal gwara ya auri Alisha da suka san ba ta da matsala ga hankali.
“Ita Alisha kun yi maganar aure da ita ne Haydar?”
Adda ta tambaya tana kallan sa
Girgiza kai yayi “Hasalima ban ji ma da sanar da ita ina son ta ba,kuma ta ƙi amincewa saboda ta san aure zan yi “
Ya sanar da su yanda su ka yi da Alisha,babu Wanda ya ga laifin ta domin koma waye tunanin makomar sa ze yi a irin wannan situation din.
Muryar Ɗan gaske su ka tsinkayo yana fadin
“Nikam ita ce yarinyar da ta taimake ni din nan ko?”
Ameera ce ta yi saurin cewa “ehh Baba ita ce”
Jinjina kai yay yana tuno wannan ranan a idanun sa. yana tuna ba domin Allah ya wullo masa ita ba da yanzu ba wannan zancen ake yi ba,he will forever remembered her kindness towards him.
“In de wannan yarinyar ce ai ba laifi akwai hankali ga hali na taimako,tunda yar dagin mahaifiyar ka ce da sauki. Ku kira min Meenal sannan da ita Alishan.”
Su biyu suka miƙe Zainab da Ameera, bayan kaman 5 minutes suka dawo tare da Meenal da kuma ita Alisha.
Yanda ta ga su Yusrah zaune akan carpet haka itama ta zauna a kasa, while Meenal ta zauna kan kujera tana kaudi ita ga amarya
“Hi uncle” ta faɗa tana ɗagawa Ɗan gaske hannu,kai kawai ya girgiza thinking of where to start
“Meenal” ya kira sunan ta a cikin tsiga na rashin wasa ko sakin fuska,ganin face din sa yau babu walwala kamar yanda ta saba ganin sa ne yasa ta dan maida hankalin ta gare sa
“Yes Uncle”
Se da ya dubi Haydar ya ga hankalin sa na ga wayar sa sannan ya soma magana
“Tsakanin ki da Allah kina san Haydar?”
Wani murmushi ne ya suɓuto mata ta kalli inda Haydar din yake da zama sannan ta yi rolling idanunta
“Yeah Sosaima kuwa uncle, words can’t even express how much love I have for him “
“To se de Haydar ya nu na shi baya son ki kuma ba ya bukatar auren ki. kuma yana da dalili me karfin gaske wanda nima na amince da janye batun wannan aure shine dede”
Kamar wata sakara haka ta kafe Ɗan gaske da idanu tana kallo kamar de yau ta soma ganin sa kirjinta wani irin duka yake yi kamar ze faso waje,a take hawaye ya soma wanke mata farar fuskar ta.
“Nooooo Unlce please not this time,ba yanzu ba da auren yake saura kwana biyu kar ka juya min baya uncle Modibbo kai ka min alkawari za ka aura min Haydar ko ta halin ƙa-ƙa,kasan yanda nake tsananin san shi “ ta yi maganar cikin muryar kuka
Ɗan gaske “Nasani Meenal. na san ni na miki alkawarin auren sa,amma ya zo da shaida me kwari,amma ki gani da kan ki se ki yanke hukunci.”
Alama yayi wa Maryam da ido nan ta karɓi wayar Haydar da ko ɗago kan sa be yi ba ta miƙawa Meenal. nan ta ga video hankalin ta ba ƙaramin tashi yayi ba,tambayar kan ta take yi ta yaya hakan ya kasance?duk barikin da ta gama yi video ta ko sau daya be taɓa fita ba se yanzu da take gaf da yin aure?wanda ma ba ta yarda ta aikata komai da shi ba kawai romance ne da abinda bazaa rasa ba shine aka samu wani azzalumin ya mata wannan video dan ya tarwatsa mata aure.ta san ba kowa ne ya aikata haka ba face friends din ta, ta san akwai masu yawa da suke bakin ciki da auren da zata yi da most handsome guy da ya kasance burin ko Wace ƴa mace.
Se da ya tabbatar da ta gama kallan video sannan ya ce “wannan shine hujjan sa,ban yi tsammanin haka daga gurin ki ba daughter,zan yi magana da mahaifin ki domin gaskiya an sauke wannan aure baze yu a cutar da bangare daya ba”
Sulalewa tayi daga kan kujerar da ta ke zaune ta nufi gaban Ɗan gaske, fuska duk ya ɓaci da ruwan hawaye
“Uncle dan Allah kar ku min haka ina matukar son Haydar. sharrin shaidan ne da zuga na kawaye amma bazan sake aikata komai ba please ka janye maganar dakatar da aure na dashi “
Dafa kafadar ta ya yi “am sorry daughter bani da right din faɗin haka a yanzu, tsakanin ki da Haydar ne in har ya yafe miki se a ci gaba da gabatar da shirin aure”
Rarrafawa ta kuma yi ta isa gaban Haydar ta riƙo hannun sa na dama tana kuka
Kowa zuba musu ido yayi yana kallo,Alisha da ta mayar da su Tv in banda dariyar mugunta babu abinda take yi a ranta wannan dramar da ake yi ya ƙayatar da ita matuka gaya.
“Haydar yau auren mu saura kwana biyu kacal, kar ka juya min baya because of this useless video. Ana son a raba mu ne yasa aka yi wannan video amma babu abinda na aikata,ka yafe min Haydar you know I loved you like crazy “
Riƙe hannunta da take riƙe mai hannun sa yayi ya cire yana duban idanun ta hankali kwance tunda ya samu abinda yake so
“Am sorry Meenal amma bazan iya auren ki ba”
Sake cafke hannun sa tayi tana girgiza mai kai “ you can’t do this Haydar duniya za ta yi mana dariya. İn baka aure ni ba wacece za ka aura, wacece type din ka? Ni ce kaɗai macen da za ta so ka kuma ta kula dakai”
Murmushi ya ɗan saki jin abinda ta faɗa yanzu muryarsa a tausashe ya amsa mata da
“Alisha zan aura saboda she’s the type of woman I wanted to marry “
Cak kukan da take yi ya tsaya kamar an ɗauke ruwan sama ta juyo tana kallan Alisha da ta ke kallon Haydar cike da tsananin mamakin kalamansa she never expects ze yi wannan maganar a gaban kowa.
Dawo da kallon ta kan sa ta yi tana girgiza kai “ah ah wasa ka ke min ko? Wannan ƙaramar yarinyar za ka aura? Bazeyu ka fasa aurena akan wannan ƙaramar karuwan yarinyar nan ba she’s not worth it. Wato dama duk ganin ku da na ke yi tare abinda ku ke shiryawa kenan kuna so ne ku wulakanta ni.’ ke kuma” ta juyo kan ta
“Dama na san you’re trying to snatch my man from me,munafukar banza da wofi,Wallahi sai na ci uwar ki, sai na kashe ki kowa ya huta, dan Aliyu Haydar nawa ne ni daya “ tana maganar ta miƙe da gudun gaske ta isa gurin da Alisha take zaune ta danne ta tare da mata mummunar shaka a wuya wanda nan take Alisha ta fara tarın wahala. Da gudu kowa ya isa inda suke Haydar ya soma kokarin ɓanɓare Meenal a jikin Alisha amma ta danne ta ne bana wasa ba.
“Wallahi tallahi se na kashe ki, kuma in na kashe ki na kashe banza na kashe wofi Shegiya wulakantacciya Tsinanniya na tsane ki” haka ta dinga faɗa kamar wata psycho sai zare ido take tana faɗe_faɗe.
(tashin hankali baa sa masa rana🤧🥵🥵 wallahi kar ku bari a yi wannan tafiyar babu ku, ku hanzarta ku biya tun kafin ya koma 500)
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
35 & 36_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
35 & 36
Cikin tashin hankali ganin tana kokarin yin kisan kai Adda ta ce “Meenal ba ki da hankali ne kashe ta ki ke son yi ?”
Ta na nanike danne a jikin Alisha tace “wallahi Adda ba zan bar ta ba yau se na rabata da wannan duniyar. Tunda tayi nasaran raba ni da Haydar to ita ma se ta bar wannan duniyar”
Hankalin kowa ya tashi dan sun san yanda ta shaketan nan in ba a ɗau kwakwaran mataki ba tabbas za ta kashe ta din, domin zuwa yanzu Alisha ta gama galabaita hawaye ne kawai ke zuba daga fararen idanunta da suka rikiɗe suka koma ja dan azaba
“Haydar do Allah ɗaga ta a kan yarinyar nan kar ta illata ta “ cewar Ɗan gaske da ke tsaye kan su.
Da karfin tsiya Haydar ya finciko Meenal daga jikin Alisha ya wurgata tsakiyar falon sannan ya tsuguna gaban Alisha yana ɗagota zaune tare da dafo bayanta
Yana tambayar ta “are you okay” fashe musu tayi da kuka tana shafa wuyanta da yasha shaka
“Wayyo wuyana,mama na” ta faɗa tana kuka haɗe da shesheƙa
“Gaskiya Meenal ba ki da hankali tun da har za ki iya yunkurin kisan kai” Cewar Yusrah tana watsa mata harara
“Ai ma ban mata komai ba,se na kashe ƴar banzar yarinyar nan zan samu sukuni “ ta faɗa tana sake dunfaro gun Alisha a dari,a fusace Haydar ya miƙe ya dedeci fuskar ta sannan ya ɗauke ta da kyawawan tagwayen maruka guda biyu a Kumatu.
Wasu taurari ta gani masu yawan gaske suna mata yawo a idanu na wasu lokuta,ga wani ƙara da take ji a kunnuwanta rauuuuuuuuu,hannu na dafe da kuncinta ta tsaya kamar gunki tana kallon sa kamar yanda shima ita din ya ke kallo,amma kallan da ya ke bin ta dashi da bambanci da wanda ita take ma sa,shi ya na mata muguwar kallo ne da kuma kallon ba ki da hankali. a yayinda ita kuma ta ke masa kallo cike da so da kauna da kuma rashin yarda ita ya ɗaga hannu ya mara.
Su Ameera da ba su aka mara ba amma tabbas sai da su ka ji tamkar wannan mari a kuncinsu ya sauka tsabar yanda marin yai ƙara.
“Haydar,ni ka mara akan wannan mara gatan?”
“Na mare ki ko za ki rama ne? ”
Ta na girgiza kai ta furta “ah ah bazan rama ba amman se ka yi danasanin ɗaura hannunka a fuskata,wallahi se mahaifina ya ɗau kwakkwaran mataki akan tozarcin da ku ka min yau”
Tana faɗar haka ta bar falon. tsaki ya ja ya koma inda ta ke zaune.
Alisha da har yanzu ta ke kuka ƙasa-ƙasa ne ta ke dariya a ranta domin kuwa yanzu ta sake yanke sabuwar shawara wanda ta ke ganin ze taimaka mata wajen tarwatsa ahalin Ɗan gaske.
Adda ce ta ɗaga ta su ka zauna saman kujera tana lallashinta.
Se da ta yi shuru kowa ya nutsu sannan Ɗan gaske ya dubi Alisha zaune kan ta a ƙasa
“Alisha “
Ya kira sunan ta da yanayi na neman hankali domin magana me muhimmanci da ya ke son yi da ita.
Batare da ta ɗago ta dube sa ba ta amsa kiran.
“Haydar ya faɗa min cewa yana son ki,kuma so ne na tsakani da Allah dan babu wasa a lamarin sa auren ki ya ke son yi shin za ki aure sa?”
Shuru ta yi ba ta ce komai ba kan ta a ƙasa tana wasa da dogayen yatsunta,kowa ya zuba mata ido dan jin me za ta ce,Haydar ya fi kowa matsuwa da ya ji amsar da za ta bayar duk da be da tabbaci za ta amince amma ya matsu ya ji menene ze ta faɗi.
Ganin ta gagara magana ne yasa Ɗan gaske cikin kulawa faɗin “Kar ki ji kunyar kowa,babu wanda ze miki dole kin ji ko Alisha,kema ƴace a gurina kai tsaye ba tare da jin kunya ko nauyin mu ba ki faɗa min amsar ki”
Motsa bakinta ta yi “na amince” hakikanin gaskiya lokacin da Haydar ya tunkareta da maganar yana sonta ta ƙi amincewa ne saboda ba ta son cutar da kyakyawar zuciyarsa,amma yanzu ta gama tunani da yanke shawaran kutso kai cikin ahalin da matsayi me girma da za ta yi yanda ta ke so babu me zarginta,sai de ta san da abu daya matukar Haydar ya gano ta aure sa domin ɗaukan fansa akan mahaifin sa da ɗan uwan sa baƙaramin tsanar ta ze yi ba.
Sosai su ka ji dadin amsar da ta bayar domin sun san baƙaramin dace suka yi ba na samun ta a matsayin surka
Wani irin kallo ya ke yi mata me cike da so da kauna tsabar farin ciki ji yayi tamkar ya rungumeta tsam a gaban kowa,be taɓa kawuwa za ta amince ma sa nan kusa ba.
“Masha Allah tunda kin amince ba na son auren nan ya ɗau lokaci, ba na so ya wuce wata guda,Hajiya Zuwaira se ki yi wa yan uwan ki magana zaa zo tambayar auren ƴar su” yai maganar yana duban Adda.
Kai ta gyada “in sha Allah yau din nan zan sanar da su”
Kallon Alisha yai da har yanzu wasa ta ke da yatsun hannunta kana ba ta ɗago ba, ya ce “ƴata yanzu kin riga da kin zama cikakkiyar yar wannan ahalin,surkan gidan Ɗan gaske,ki sa ki jikin ki kema yanzu wannan gidan ki ne, kına da right din yin komai da shiga duk inda ki ke so kan ki tsaye bakya bukatar iznin kowa,Allah ya miki albarka”
Murmushi ta yi a zahiri a rai kuwa ta furta “ Dama da albarka na ka ganni ai, marigayi Ɗan gaske”
“Nagode kawu” ta faɗa a hankali,duk murmushi suka yi.
Hira a ka ɗan yi a falon Ɗan gaske wanda rabon da su zauna su yi hira irin wannan dashi har sun manta, amma yau saboda Alisha an taɓa hira. Har wajen 12:00 suna falon sa,bacci Adda ta fara ji tace
“Kai gaskiya nikam bacci zan yi se da safen ku” ta miƙe za ta tafi
“Adda ki jira ni” itama ta miƙe ta na musu sai da safe suka fita da Adda.
Falo suka shiga har za ta wuce dakin ta Adda ta kira sunan ta
“Alisha! “ dakatawa ta yi ta na jiran ta ji me za ta ce
“Zo ki zauna anan”
Zama