Showing 69001 words to 72000 words out of 96407 words

Chapter 24 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3614

tayi a kujera me zaman mutum uku kafin Adda ta zauna gefenta.

“ kin ji abinda Yallabai ya faɗa, shin ya ki ke ganin zaa ɓullowa lamarin auren nan na ku? Shi duk tunanin sa ke din dangina ce, da ya san ba ni da haɗi da ke wallahi ba ze taɓa amincewa auren nan ba. dan shi ko da yaushe maganar sa baya wuce kwarya taɓi kwarya. Shin za ki haa ni da kawun na ki ne mu yi magana ?”

Da sauri ta girgiza mata kai tana riƙo hannun Adda idon ta na ciko ruwa “ah ah Adda baza su sani ba,domin inde suka san zan yi aure wallahi se sun tarwatsa komai,ni de ina tsoro saboda kawuna ya ce inde ba ɗansa zan aura ba to wallahi bazan taɓa aure a duniya ba. Kuma yace ko mutuwa zan yi sa ina auri ɗansa, matukar yasan da wannan auren ba ze amince ba.”

Jikinta ne yai sanyi shafa kanta tayi cike da kulawa ta ce “ shikenan ki dena kukan kin ji,in sha Allah ko yana so, ko baya so se kin yi aure. Zan yi wa kannena magana su ne za su zama waliyan ki,in yaso bayan bikin se mu je gidan kawun na ki mu sanar masa da kin yi aure ko?”

Cike da samun kwanciyar hankali ta gyada kai tana share hawayen ta.

“Yawwa ƴar albarka,sai kuma abunda nake son faɗa miki,kin ga yanzu ke surkar gidan nan ce yakamata ki dinga ado saboda saurayin ki ya dinga ganin ki cikin ado da kwalliya, haka ake son mace ta kasance cikin kwalliya,duk da sanya hijab din ba laifi bane amma ki rage musamman in kina cikin gida,in za ku fita ne in kına so se ki sanya hijab din kin ji ko ƴata? Dan Allah ki dinga kwalliya ba ki ga su Ameera ba ƴan uwan ki. kema ki dinga chaba adoh saboda ki sake jawo hankalin Haydar gare ki,Hausawa sun ce ko kana da kyau tofa ka ƙara da wanka”

“In sha Allah Adda nagode sosai”

“Yawwa to se ki je ki kwanta ki yi bacci kin ga mun makara ba mu kwanta da wuri ba” sallama ta yi wa Adda ta shige bedroom,sauke ajiyar zuciya tai ta na murmushi

“Allah nagode ma ka da ka ba ni yarinya me hankali,tarbiyya uwa uba girmama manya a matsayin surka. Allah ka sa ita ce za ta kawo sauyi a wannan gida”

Ko da ta shiga daki ranta fess ta shiga toilet tayi wanka ta zo tayi shirin bacci,ta na tuna maganganun Ɗan gaske da ya ce itama yanzu ta na da right din yin komai da shiga ko ina a cikin wannan gida tunda ta zama surkar ahalin,tabbas za ta yi amfani da wannan dama tayi yanda ta ke so. Tana wannan tunanin wayarta dake ƙasan pillow ya soma ƙara,ko da ta duba ta ga Uncle Haydar ke kiranta ɗagawa ta yi bakin ta da sallama

“Alisha” ya kira sunan ta da sanyayar murya

“Naam”

“Ba ki yi bacci ba?”

Se da ta gyara kwanciyarta sannan ta amsa shi “eh amma yanzu zan yi.”

“Shikenan ki kwanta dare ya yi kar ki makara tashin sallah asuba,sai da safe “ ya faɗa yana kokarin katse kiran.

“Uncle” ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunan sa a hankali

“Naam Alisha “

“Menene ya burge ka a tattare da ni da har ka ji ka na sona kuma kana son ka aure ni?”

Sautin murmushin sa ne ya sauka mata a kunne kafin ta ji, ya ce “saboda ke ta dabance Alisha,macen da ko wani namiji ze yi fatan samu a matsayin mata da kuma uwa ga ƴaƴansa. Ke zaɓice da Allah ya zaɓa min,ashe ke zuciyata yake ta jira shisa ban taɓa jin son kowa ba se akan ki,na san ni da ke mutuwa ne kaɗai ze raba wannan alaka ta mu”

Jikinta ne ya yi sanyi sosai tana tuhuman zuciyarta da laifin amsa bukatar Haydar,domin ta san zuciyarsa ba ta cancanci mutum irin ta ba,duk da laifi aka mata take ramawa amma ai ba shi ne ya aikata mata ba hasalima bayi da masaniya akan abinda ya faru.

“ ba ka tsoron wata rana in cutar da zuciyarka? shin za ka guje ni duk sanda ka gane ina da wani mummunar hali ? uncle shin za ka goya min baya a duk sanda ka gane wani abu a dangane dani? Bazaka juya min baya ba?”

A bangaren sa yana kwance shima ya rungume pillow ya kasa kunne yana sauraranta idanun sa a lumshe murmushi yayi lokacin da ta gama masa tambayoyi

Da iya gaskiyar sa ya ce “bari in amsa miki tambayoyin ki daya bayan daya.

Na farko, ina da yakinin baza ki taɓa cutar da zuciyata ba, na biyu Alisha wallahi bazan taɓa gudun ki akan wani hali na ki ba,hakki ne akaina in ɗaura ki akan hanya madaidaiciya a duk sanda ki ka kauce. İn har bazan iya miki uzuri kuma in fahimce ki sannan in ɗaura ki akan hanyar da ya dace ba tabbas ban cancanci zama miji ba. Sai tambayar ki na uku, a ko wani hali zan kasance me goya miki baya har ƙarshen numfashi na,ba zan taɓa juya mi ki a lokacin da ki ke bukatar wani a kusa dake ba. Ina fatan Allah ya bani ikon zame miki dukka wani gata a wannan duniya, ina fatan zame mi ki uwa,uba da ahali. Na miki alkawarin za ki samu hakan a tattare dani”

Zuwa yanzu duk wani laka na jikinta ji ta yi tamkar an zare mata su, zuciyarta da jikinta yayi matukar sanyi,kalaman sa sun matukar taɓa ta da sai da tayi namijin kokari wajen shanye hawayen da suke kokarin zubo mata.

“Uncle ina tsoro “

“Shiisssh.. kar ki ji tsoron komai Alisha ina tare dake. Ni de ki min alkawarin komai rintsi baza ki taɓa rabuwa dani ba,za ki kasance da ni a ko da yaushe “

Idanun ta suna a rufe tana jin yanda kalamansa suke dukan kirjinta, ba ta san lokacin da bakin ta ya furta

“Na maka”

Murmushi ya sake, ya ce “shikenan ki kwanta ki yi bacci me dadi My Black Queen “

Murmushi ta sake itama jin sunan da ya kira ta da shi

“Allah ya tashe mu” ta faɗa ta na katse kiran nasu.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta danna kiran wani number da babu suna. ana ɗagawa ta ce

“Video yayi kyau,ina son kafin nan da zuwa safiya ka yaɗa sa a social media platform with a good caption da ze ƙayatar.“ kitt ta katse bayan ta faɗi abinda take son faɗa.

Washe gari aka sanar da baƙin da su ka zo biki an fasa aure sai nan da wata daya zaa yi da wata. haka kowa ya soma tattarawa yana koma wa inda ya fito har aka watse aka bar su a gidan,ko da Adda ta kira Hajja Hauwa ta sanar mata da duk abinda ya faru sosai ta yi murnan jin wai Haydar shine ze auri Alisha.

A gidan Hon. Habibu katanga kuwa Meenal tun a daren jiya ta dawo gidan su kusan sha daya na dare ta shigo babu ma wanda ya san da dawuwar ta sai da safen nan ta fito ta samu iyayen na ta a kan teburin cin abinci za su karya nan ta ke faɗa musu abinda ya faru. Sosai ran Hon Habibu ya ɓaci jin yanda abokin sa yake son zubar mai da mutunci.

Safa da marwa kawai yake a tsakiyar falon hannunsa goye a baya, idanun sa sun yi ja tsabar ɓacin rai,Meenal da maman ta sun yi shuru suna jiran su ji me ze ce

“Shi Modibbon ne ya ce ya sauke auren ki da na ɗansa?”

Murya a daƙile saboda da kukan da ta sha jiya ta ce “eh shi ya faɗa min daddy,kuma ya haɗa sa aure da wata shegiyar yarinya kucaka “

Jinjina kai ya yi bayan ya ji abinda ƴar ta sa ta fada

“Lallai Modibbo ya cika butulu,wato amfanina yaƙare a gare sa shine bari ya watsa min ƙasa a ido,se da na gama sanarwa duniya auren ƴata tilo ranan jummaa ne, shine ze kunyata ni to wallahi karyarsa yasha karya. Daga shi har ɗan nasa ba su isa su mayar dani ƙaramin mutum ba. Matukar ya ce an ɗage wannan aure to wallahi sai na nuna masa ni din nan ni ne Habibu katanga.”

Cikin sanyin murya Matar sa ta ce “ka yi hakuri Alhaji a bi al’amarin nan a sannu kar a yi abinda daga baya zaa zo ana danasani “

Ɗaga mata hannu yayi cike da masifa “dallah hajiya Balaraba ki rufe min baki,ba na son jin komai daga gare ki,ya zaa yi ƙimana da darajana yana girgiza za ki ce in zuba ido in yi kallo saboda ke shashasha ce ba Kya goyon bayan mijin ki da ƴar ki.”

Taɓe baki ta yi kana tayi shuru ba ta kuma cewa komai ba, kallon Meenal yayi

“Tashi mu je gidan na sa in ya isa ya sake faɗa a gaba na”

Da rana suna zaune a falo suna hira iya Adda ne se Maryam da yaron ta,Ameera Yusrah da Zainab kuma Sameer ya ajiye su a gidan Hajja Hauwa tun da safe da ze fita,Alisha kuma tana dakin ta ba ta sauko ba.

Haydar ne ya fito cikin shirin sa na zuwa Office ya yi kyau cikin shigar uniform saboda yau akwai meeting da za su yi da manyan ƴan sanda shisa ya saka uniform

“Yallabai zaa fita kenan” cewar Adda tana dariya

“ Eh wallahi. yau za mu yi meeting da minister tsaro ”

“Ayyah to Allah ya taimaka ya ba da saa”

Shigowan Hon. Habibu katanga falon ne yasa be fadɗ ameen din dake makale a bakin sa ba, shigowa yai hannun sa riƙe da na Meenal

“Barka da shigowa Alhaji” cewar Adda tana rufe jikin ta da mayafin kayanta.

Ɗaga mata hannu ya yi cike da izza “ki riƙe gaisuwar ki Hajiya Zuwaira ba shi na zo ji ba, na zo gurin danki da mijin ki ne”

Jan bakin ta yi ta yi shuru dan ta san hakan se ya faru.

“Kai kuma Aliyu Haydar akan wani ƙalilan video da be taka kara ya karya ba, wanda ma ba ka tabbatar da ita ce ko saɓanin haka ba shine za ka fasa auren saboda kawai kai ba ka gaji arziki ba? ”

“Ai ba Aliyu Haydar bane ya dakatar da auren ni ne na dakatar ni yakamata ka samu ba shi ba Katanga” cewar Ɗan gaske yana tsaye akan matattakalar bene fuska a haɗe kafin ya fara saukowa.

Dedeta tsayuwar sa yayi yana jiran saukowan sa..

“Fisabilillah ku zauna mana” ya faɗa bayan ya iso cikin falon

“Modibbo ka sani sarai ba wai zama ne ya kawo ni gidan nan ba,na zo ne in je dalilin da yasa ka zaɓi watsar min da mutunci na a tsakiyar titi.

“Wato katanga na ga alama ƴarka da ta sanar dakai abinda ya faru ba ta nu na maka video ta da wani da ya janyo na ɗage auren ba ko?”

Rai a ɓace ya ce “kwarai kuwa ta nu na min. sannan ni ban ga wani abun ɗaga hankali akan wannan video ba da har ze sa ka ce an fasa auren da mu ka yi alkawarin haɗawa tun shekaru uku da suka wuce”

“To ni na ga dalilin ɗagawa,in har kai ba ka ɗauki laifin ƴarka a matsayin laifi ba ni na ɗauka,ɗana ba ze taɓa auren irin wannan yarinyar ba”

Alisha da take falon Adda ne ta ji kamar hayaniya a falon hakan yasa ta sanya ƙatuwar hijab ta sauka,ganin hayaniyar da ake yi ne yasa ta je kusa da su Adda ta tsaya.

“Modibbo ba ka da zaɓi da ya wuce da ka mayar da wannan aure,in ko ba haka ba za ka tursasani in yi abinda ban yi niya ba. Duk duniya Meenal kaɗai Allah ya mallakamin, farin cikin ta shine nawa a domin nata farin cikin zan iya sadaukar da nawa. Ta ga ɗanka tana so ba shi ze ba ku damar yi mana wukakanci ba”

Izuwa yanzu Ɗan gaske ya gama hassala Katanga

“ Ka fara kai ni makura, ka gaggauta fice min a gida na,in kuma ba haka ba zan sa securities su fitar min da kai ta karfi ta tsiya-tsiya”

Nuna kan sa da yatsa yayı “Modibbo ni ka ke cewa za ka sa a fitar ta tsiya a cikin gidan ka? Tabbas kai butulu ne me manta alkairi. Ni ba ka isa ka butulce min ba duk irin taimakon ka da nayi ka dinga aikata mugayen ayyuka shine yau ni za ka wulakanta? To kar ka manta munanan sirrukan ka suna tare da ni zan tona su ga duniya kowa yasan kai ne nan ka Kawar da ahalin……!”

“Ina me gargadin ka Katanga,matukar magana kwara daya ya fito wallahi tallahil azim sai na binneka da ranka”

Ta na tsaye a inda ta ke ta zuba musu ido tana bin su da kallon tsana a ƙasan makoshin ta furta “shashashu za su tonawa kan su asiri, kar ku damu duk zanyi maganin ku ba sai kun tsaya kuna sa’insa da junan ku kamar wasu karnuka ba”

Yanda suke faɗe-faɗe sun ɗagawa kowa hankali Adda se lallaban Ɗan gaske ta ke ta na ba sa hakuri amma ko sauraranta be yi ba,Haydar kuwa daga inda yake tsaye ya harɗe hannun sa a kirji ya zuba musu ido kamar wanda ya samu Tv ko kusa be yi kokarin dakatar da su ba. Shi babban damuwar sa ma shine maganar da Katanga ya soma be ƙarasa ba Ɗan gaske ya dakatar dashi ,tabbas ya fahimci akwai sırrın da suke ɓoyewa.

“In ka cika ɗan halak Modibbo a yau yau din nan ka sa a binne ni,ni kuma kafin nan se na tabbatar da na baza duk wasu mugayen sirrukanka a faranti yanda duniya se ta yi Allah wadai, kuma ka zuba ido ka gani”

Ya gama faɗin haka yana jan hannun Meenal suka fita su ka bar gidan.

Girgiza kai Ɗan gaske yayi yana bin bayan su da kallo tare da sakin wani munafukin murmushi

“Ka yi gangaci Katanga ka san ni waye sarai amma ka ke ja dani,ka sani duk wanda ya ja dani baya ƙarewa ta dadi” shima ya haura upstairs ya koma part din sa.

Shuru ne ya gauraye falon kowa ya yi tsitt kamar ruwan ya cinye su,ba su yi tunanin fasa auren Haydar da Meenal ze janyo wannan hatsaniya har haka ba a tsakanin abokai ba.

Haydar ne ya sauke numfashi yana “to Allah ya kyauta, ni de na tafi Adda”

Itama se da ta sauke ajiyar zuciya kana ta ce “Allah ya tsare “

Kallon ta yayi ya ɗaga mata hannu yana murmushi, murmushi ta sakar mai ,sannan ya fice.

Adda bin bayan Ɗan gaske bangaren sa tayi Alisha ta kuma ta koma part din adda ta shige daki,haka Kaf aka watse a falon.su Yusrah sai dare suka dawo.

Washe gari bayan ta idar da sallah asuba wanka tayi. ta shafa lotion ta sa kwalli a idonta bayan ta shafa powder se lipgloss da ta gogawa ɗan karamin bakinta. Riga da skirt ta saka na atamfa dinkin pencil skirt ne da half bubu ta ɗaura dankwalinta ɗaurin duka baya sosai tayi kyau ta feshe jikin ta da turare sannan ta saka plat shoe ta fita a part din,ko da ta sauko downstairs kitchen ta shiga nan ta samu masu aikin gidan suna shirin ɗaura abincin karyawa,ce musu tai su yi aiyukan gida ita za ta yi girkin da za su yin. Haka kuwa aka yi ta ɗaura abincin karyawa,time din duk yan gidan babu wanda ya sauko saboda takwas ne saura kowa na sashinsa yana shan bacci.

Masa tayi da miyan stew sai chips da kwai sannan tayi tea da kunu. Jera komai ta yi a dinning area masu aikin da mamaki suke kallan ta ganin komai ta jera a dinning bayan ba haka tsarin cin abincin gidan yake ba

Lamı ce ta kasa hakuri ta ce “ Ƙaramar surka,yallabai da Adda fa bangaren su ake Kai musu nasu,haka ƙaramin alhaji Haydar shima a nasa bangaren ya ke ci”

Ƙayitacciyar murmushi ta sake “ Baba Lami tsarin ya canza,daga yau a tare zaa dinga cin abinci a teburin nan kowa da kowa ze hallara,abincin rana ne kaɗai bazaa ci a teburi ba, nan ma saboda uncle da Sameer ba sa gıda ne.”

Murmushi Lami tayi “Hmmm ƙaramar surka tun zuwa na gidan nan na ke ganin ake kokarin kawo wannan sauyin aman baa yi nasara ba bari mu ga ko Allah ze ba ki iko”

Fuskarta har lokacin da Lami ke magana na ɗauke da murmushi “nagode Baba Lami,yanzu ku je bangaren kowa ku ce dashi su yi gaggawan gangarowa ƙasa wani babban al’amari na faruwa ”

Dariya duk masu aikin su ka yi, sannan su ka tafi yin abinda ta ce. Kallon part din Ɗan gaske tayi sannan ta saki munafukin murmushi tana nufan part din.

Jim tayi a bakin kofar shiga falon na sa kafin ta ɗaura hannun ta akan handle din za ta tura kofar kenan ta ji maganar sa alamun waya yake yi yana faɗin

“Magot na yi magana da Damisa yau zaa zo a kwashe makaman da su ke gida na, kuma na gaya masa suna falo na a cikin secret room in sun zo ta kofar baya kawai za su shigo ba se kowa ya san da zuwan su ba. Ina son in sake faɗaɗa kasuwancina na safaran makamai din nan kafin in koma kansa”

Jinjina kai ta yi “ohh wato banda mugayen abubuwan da ka ke yi har da safaran makamai, to ai kuwa bazasu bar gidan nan ba se na san yanda zan yi dasu.” Tsayawa tayi a bakin kofar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login