Showing 51001 words to 54000 words out of 96407 words

Chapter 18 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3626

kana ta ɗaga ta sa a kunne batare da ta yi magana ba.

haka bangaren wanda ya kira shima yayi shuru,kusan minti biyu babu wanda ya ce wani abu se shi da ya ga da gaske bazata yi magana ba hakan yasa shi soma magana da sansayyan muryarsa

“Kına tsoron ki yi magana a sace ki ta waya ne?”

Muryar sa ya daki dodon kunnenta lumshe idanu tayi lokacin da ta gane muryarsa wani murmushin da bata shiryawa yin sa bane ya suɓuce mata.

Kamar wacce take gaban sa ta sa hannu ta rufe fuskarta saboda se da ta ji kunya ya rufe ta na maganar da ya faɗa

“Uncle…” ta kira sunan sa da siririyar murya.

“Naam “ ya amsa yana murmushi

“Tsoro na ji shisa ban yi magana ba,ban yi tunanin kai bane”

“Na fahimci hakan ai matsoraciya,ko kina tunanin dodo ne ya kira ki a waya yana son cinyeki?” Ya faɗa cikin zolaya.

A wannan karon ba murmushi tayi ba dariya ne ya zo mata jin abinda ya ce.

“Ina kwana?” Ta gaishe sa bayan ta dakatar da dariyar.

“Lafiya lau nake. Ya na ji muryar ki a haka? Ko de bakya jin dadi ne?”

Ɗan jimantawa tayi tana tambayar kan ta ya aka yi yasan bata jin dadi.

Tura baki tayi cikin ɗan shagwaba da masifan da ta tashi dashi ta ce “Cikina ne ke min ciwo fa“

“Sorry,su Ameera sun shigo miki ne?”

A hankali ta amsa da “ah ah ba su shigo ba”

“Shikenan bari in turo miki Yusrah ta kawo miki magani da breakfast, na san yanzu an kusa kammalawa “



Kamar za ta ce masa kar ya turo mata Yusrah amma in ya tambayeta dalili ba ta da amsar da za ta bashi hakan yasa ta ce dashi “to” kawai ya katse kiran.

Tana nan kwance tana danna wayar bayan ya katse ta shiga tiktok tana kalle-kalle c ta ji an buɗe kofan an shigo ko motsawa daga inda take bata yi ba saboda ta san wacce ta shigo baze wuce Yusrah din ba.

Cike da kulawa ta ajiye tray da ta shigo dashi ta zauna kan gadon tana “Ayyah sannu Alisha yanzu Uncle Haydar yake faɗa min baki da lafiya “

“Uhmm da sauki” ta faɗa still ba ta miƙe ba

Ganin ba ta mood din magana ne yasa ta cewa “to ga abincin ki da magani dan Allah ki tashi kisha “

Miƙewa zaune ta yi ta ɗan saci kallan fuskar Yusrah din ta ga tana ɓare mata magani da ta shigo dasu. Tana mamakin ga de mace har mace kyaun fuska da na jiki tana dashi dede gwargwado amma ta rasa me zata nema a rayuwar ta se mace ƴar uwarta abun na bata takaici.

“Yanzu ki fara yin breakfast tukuna se ki sha maganin ki” tayi maganar tana ajiye mata plate din danwaken da ta haɗa mata yaji vegetables da kwai gwanin sha'awa. Kai ta gyada mata ta ɗauki abincin ta fara ci a hankali ita kuma Yusrah se kallan ta take yi da se da ya ja Alisha ta kware . da hanzari ta ɗauki glass cup ta nufi bakinta da shi da niyar bata,karɓa tayi a hannun ta tana

“I will do it myself “

Sha tayi ta ji tarın ya tafi sannan ta ci gaba da cin abincin ta “Yusrah “

“Naam Alisha “

Tana cin abincinta batare da ta ɗago ba ta ce “kina ganin hanyar da ki ka zaɓa ze ɓulle miki kuwa? Kina ganin mahalaccin ki ze yi farin ciki dake ? Kina aikata abun da Allah da manzonsa suka yi hani dashi suka yi tsinuwa akai. Duk da gwara kunyar duniya dana lahira, amma ya ki ke tunanin Hajja Hauwa da Adda za su ji in suka san abinda ki ke aikatawa? Ki na tunanin za su ji dadi ko za su yi alfahari dake a matsayin ƴar da ta taso a gaban su suka bawa tarbiyya? Yusrah…” ta kira sunan Yusrah da jikin ta ya gama mutuwa yayi sanyi kalau ga kunya da ya rufe ta tama kasa ɗaga kai su haɗa ido, da Alisha ta ga haka se ta matso kusa da ita tana me riƙe hannunta domin ta fahimci maganganunta sun yi nasaran samun guri a zuciyar ta.

Murya a sanyaye ta ce “na san kin girme ni da kusan shekara uku zuwa huɗu, but that doesn’t mean bazan faɗa miki gaskiya ba. Ko da za ki ji haushi na hakan baze dame ni tunda na sauke nauyin dake kaina. Dan Allah ina rokon ki da ki tuba ki dena wannan abu da ki ke aikatawa. Ki yi tunanin yanzu a ce kinyi aure ki haifo yaran mata, kwatsam wata rana ki gane ƴar ki na aikata alfasha da ƴar uwar ta mace,za ki yi farin ciki da haka?”

Cike da kunya da danasani ta girgiza kai alamar ah ah.

“Good bazaki ji dadi ba,ko kin manta zina bashi ne?har yanzu kina da sauran lokaci ki koma ga ubangijinki ki roƙe sa yafiya. Ahalinki in suka gane ke ƴar maɗigo ce za su ji kamar sun gaza ba ki kulawa a matsayin su na iyayen ki”

Tunda take se yau ta ji muguwar danasani yakamata da tsantsan kunya wai yau ace yarinyar da ta bawa shekara uku ita ce take faɗa mata gaskiyan da ta kasa faɗawa kanta, duk se ta ji ta a takure.

Zuwa yanzu hawaye ya taru a idanunta suna kokarin zubowa dakyar ta iya buɗe bakinta

“I have never regretted my actions kamar yau,tun tasowata ban taɓa jin son namiji ba,yan uwana mata kawai nake so su kaɗai ne suke burgeni suke bani sha’awa. Tun da na tafi Abuja na dawo ban aikata komai da ko wacce mace ba saboda ba ko wasu kalan matan nake haɗa jiki da su ba,sannan yarinyar da muke soyayya mun yi faɗa da ita. Kawai se na dawo na tarar da ke a gidan mu wallahi Alisha ina matukar kaunar ki,tun ranar da na ɗaura idona akan ki Allah ya jarrabeni da masifar son ki”

Interrupting din ta tayi ta hanyar faɗin “ki tsarkake zuciyar ki Yusrah se ki ga Allah ya yaye miki cikin gaggawa. İn de kina sona tsakanin ki da Allah to ki mayar da shi friendship.,let’s be friends tun da dama ni bani da ƙawa ko daya. Sannan na miki alkawari your secret is safe with me “

“Nagode sosai Alisha ban taɓa jin abinda nake aikatawa ba daidai bane se yau na yi danasani sosai,ina fatan Allah ya yafe min zunubaina. Kuma na miki alkawari bazan sake kallon ko wacce mace da ido na sha'awa ba ki ta min addua Allah ya shirye ni dan Allah “

Tana murmushin samun nasara ta ce “in sha Allah zan sa ki a cikin addua na ko da yaushe. Allah yasa mu fi karfin zuciyar mu”

Bayan ta amsa da Ameen ne ta ce

“Amma menene yasa ba ki da ƙawa ko daya?”

Se da ta sakar mata ɗan murmushi ta bata amsa

“Saboda sam bana son tara tarkacen ƙawaye, ko a school bani da ƙawa gaskiya,cousins dina twins sune kawai friends din da nake dasu”

Jinjina kai ta yi cikin gamsuwa da bayanın ta “kin tabbata da you want us to be friends right?” Ta faɗa a shagwabe yanayin yanda ta yi maganar seda ya bawa Alisha dariya amma ta danne ta ce “yeah I mean it”

“Shikenan then abotan mu ya fara daga yau”

“İn sha Allah,yanzu de please can I get a pad ?”

Zuruf ta miƙe tana “yanzu zan kawo miki shi kede ki ci abincin ki, ki sha magani ina dawuwa”

Tayi maganar tana barin dakin,da murmushi Alisha ta bi bayanta se da ta fita a dakin ta sauke ajiyar zuciya tana furta “Alhamdulillah Allah ka ci gaba da tsarkake mana zukatan mu”

Bayan ta fita batare da ɗaukan lokaci ba ta dawo mata da Pad din kamar yanda ta bukata ta ta tafi. Wanka tayi bayan ta ci abinci ta sha magani ta sanya Abaya baka me fararen stones ta saka bakar hula wayarta ta ɗauka ta shiga tiktok page din Zaid ta shiga taga videos din sa da yayi kafin mummunar ƙaddarasu ya riske su, comment section din wani video da yayi ta shiga nan ta ga yanda mutane suka rubuta Rip Zaid jikinta sanyi yayi ganin yanda kowa ke tofa albarkacin bakinsa a comment section din. Ji tayi bazata iya ci gaba da kallon videos din shi ba hakan yasa ta fita a page nashi ta ajiye wayar ma kawai ta kwanta. Tana son yin waya da Mujahid amma tafi son se randa Allah yasa ta je gidan inna se ta kirashi taji ya suka sauka.

Jin shuru yau bata fito bane yasa Adda shigowa dubata nan take sanar da ita bata ji dadi bane yasa bata fito ba,Sannu ta mata sannan ta fita haka su Ameera ma sun shigo sun mata ya jiki,Haydar kuma ya tafi aiki ko da ya dawo ya samu ta ji sauki ta fito suna tare da su Yusrah a falo nan suka gaishe sa ya tafi part din sa,Meenal kuwa bata nan ta je gidan su amma tace zata dawo da dare.

Bayan kwana biyar ana shida aka fara decoration a gidan saboda waliman baikon da zaa yi wanda ake ta shirya masa kamar wanda zaa yi taron auren wasu marasa karfin. A wannan kwanaki shida Haydar da Alisha sun samu shakuwa me karfi saboda kusan kullum ita ce Adda take bawa abincin sa takai mai. in taje kuwa baze bar ta ta dawo ba se ya gama ci anan yake samun damar jan ta da hira,haka in baya nan in yana bukatar wani abu kafin ya dawo ita ce yake kira ya sanar mata. Haka a tsakanin ta da Yusrah sun ɗan shaku,sannan tun ranar da ta mata nasiha ba ta sake yi mata kallo da wani suffa na sha'awa ba kuma ta dage tana neman yafiya a gurin ubangiji.

Sameer kuwa tun lokacin da Alisha ta watsa mai hot tea a jiki be sake kulata ba amma shi kaɗai yasan abinda yake shirya mata targeting din ta yake yi yanda ze ɗau fansan abinda ta masa.

Meenal har yanzu tana nan a gidan bata koma gidan su ba duk da nan da jibi za'a sanya mata rana da Haydar,babban abin takaicinta shine ko kadan ba ta gaban sa ko kallo bata ishe sa ba,amma duk sanda yake tare da Alisha zaka tadda shi ne cikin walwala da faraa hakan yasa ta sake tsanarta kuma ta ɗau aniyar wulakantata a bainar nasi.

Zaune suke a Falo suna ta duba kayan sa ranan da aka kawo himili guda suna ta aikin shiryasu yanda ya dace,Adda ce ta duba time ta ga karfe sha daya na safe saura, girgiza kai tayi ganin har yanzu be sauko ba hakan yasa ta kirasa a waya

“Amma nikam Haydar ka manta da sako na ne ko kuwa?”ajiye wayar ta yi bayan ya bata amsa da yana fitowa. Be jima ba kuwa se ga shi ya sauko cikin shiga na ƙananan kaya sun masa kyau makura. Kamshin turarensa ne ya ankarar da ita zuwan shi hakan yasa ta ɗago idanunta hakan yayi dede da shima ya ɗago nasa suka sauke su akan na juna a tare suka sakarwa juna murmushi batare da kowa ya ga hakan ba.

“Ina sakon yake?” ya yi tambayar a gajarce wani baƙar Leda me layi-layi ta nuna masa da hannun da yake riƙe da car key din sa ya ɗauki ledar a madadin ya tafi se ya tsaya musu a kai. Kallon sa tai ganin be tafi ba

“Lafiya de kam ka min tsaye akai ?”

Ɗan murmushi yayi ya ce “yar rakiya nake nema ni yanzu tafiya anguwa ni kaɗai ba dadin sa nake ji ba”

Duk kallon sa suka yi kafin kuma suka fashe da dariya ganin yanda ya sha magani yana magana

“Yanzu Uncle nan da gidan Hajja Hauwa shine se ka nemi ƴar rakıya ahhh lallai “ Maryam ta faɗa tana dariya.

Fuskar kalan tausayi yayi “ku ne de bakwa ganin nisan anguwan. Alisha tashi ki rakani dama jiya ki ka gama ce min kina kewan Hajja Hauwa kina son ganin ta “

Waro manyan idanunta tayi jin karyan da ya shararo domin ita sam bata yi wannan maganar dashi ba,ganin yanda take kallon sa ne yasa shi kashe mata ido daya,da sauri ta janye nata idon batare da ta kuma kallan inda yake ba tacı gaba da saka gift din da zaa raba a kwalin su.

Duk babu wanda ya kawo komai a ran sa Adda na dariyar sa ta ce “ to na ba ka aron ta ku je ku dawo da wuri. Alisha tashi ku tafi”

Ba yanda za ta yi haka ta ajiye abinda ta ke yi ta ɗauki wayarta, dama akwai hijabi me madaidaicin girma da ya kawo mata har guiwa a jikinta.

Cikin sanyin jiki da sanyin murya ta ce “Adda mun tafi se mun dawo”

“Yawwa ku dawo lafiya ki gaishe min da Hajja Hauwa sosai”

Kai ta gyada kawai suka fita motar suka shiga ya tayar aka buɗe masa gate ya fita. Tunda suka fara tafiya babu wanda yace komai se da ya ga shurun ya yi yawa ne ya ce

“Ko ban burge ki ba?”

Kallon irin ban fahimce ka ba ta masa,hakan ya sanya shi sake cewa

“Na abinda na faɗa mana ko bakya son ganin Hajja Hauwa ne?”

“Ina son ganin ta, amma na san za ta zo saka ranar ka,ba se ka faɗi abinda ka faɗa musu ba”

Hankalin sa akan titi amma yana jinta ɗan kallan ta na wasu seconds ya yi “ Na faɗa ne saboda ina son ki rakani. Ko na yi laifi ?”

Yayi maganar batare da ya kalle ta ba

“Ah ah. amma kasan da Meenal na gurin dole zata ji haushin hakan ganin wanda za ta aura ze fi ta anguwa da wata macen”

“Ke ba wata bace ke daya daga cikin ahalin nan ne. Sannan kuma se me dan ta ga mun fita. By the way kema nan ba da jimawa ba za ki zama kamar ita “

Cikin rashin fahimtar inda maganar na sa ya dosa ta ce “Ban fahimta ba”

Slide smile kawai yay be ce da ita komai ba yaci gaba da driving din sa,shurun da ta ga yayi ne yasa itama ta yi shuru har suka isa gidan Hajja Hauwa. Sosai ta yi murnan ganin Alisha dan tayi kewarta,gaisawa suka yi, se tsokanar sa take Ango shi kuma yana basarwa. Sakon da Adda ta basa ne ya miƙa mata suka ci gaba da hira.

Se mun hadu ranan Monday in sha Allah,kamar yanda ku ka sanı bana posting a weekend 🥰🥰

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

Today is Friday don’t forget to recite Suratul kahf, sannan a yi wa annabi salati. Allah ya sadamu da alkairin dake cikin wannan rana.

29 & 30_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

29 & 30

Yau kowa ka gani a cikin gidan yana busy saboda yau ne ranan baikon Meenal and Haydar,kowa cikin hidima yake, face uban gayyan wato Haydar yana bangaren sa tunda garı ya waye ko fitowa be yi ba baltake ga abinda ke gudana, har se lokacin da Abokan sa suka fara zuwa nan ne suka sanyasa a gaba se da ya shirya cikin shiga ta manyan kaya light brown shadda ga tsadaddiyar hula da ya sanya.ga agogo Rolex new design a hannunsa,takalmin kafarsa half cover ce ta maza black color bakaramin kyau DCS Haydar yayi ba se de fuska ce babu fara'a,su Auwal da sauran abokan sa suna sanye da baƙaƙen shadda.

Meenal da friends dinta suna bangaren su Ameera suna shiryawa ita kuma ana mata make up gaba daya sun haushina part din nan da surutu da kiɗa se tashi yake.

Ameerah,Zainab da Yusrah bangaren Adda suka koma saboda hayaniyar kawayen Meenal ya ishe su.su ma su na can suna shiryawa a dakin Alisha. Duk sun ɗan yi light make up a fuskarsu amma banda Alisha da ta ce sam ita babu kwalliyar da za ta yi, tana sanye da katuwar hijab din ta. Jiran su ta ke su gama kwalliyar su fito da kayan da Adda ta yi musu musamman dan walimar baikon. Yusrah ce ta buɗe akwatin Kayan ta fito da zafafan laces guda hudu duk design din daya ne amma colors kowa da nashi kuma duka kayan dinkin doguwar rigace fitted gown me hannun pencil. Kallon Alisha Yusrah ta yi tace

“Mun ɗan fi ki jiki wannan ne ina ga ze mi ki riƙe sa mu ga” karɓa lace din tayi da ya kasance orange color se touches din baki da aka yi kwalliya da shi. Toilet ta shiga ta saka rigar ta fito ta samu suma duk sun sa nasu. Dukkansu ido suka zuba mata ganin yanda rigan ya yi bala'in yi mata kyau, ya kwanta luf a jikinta ga shape din ta me kyau da ya tafi da dede da jikinta ya fito yayi kyau se ta fito tamkar ita ce amaryan irin kyawawan siraran amare din nan da komai suka saka yake fitting nasu. Ganin yanda suka tsare ta da ido suna kallo yasa cikin shagwaba ta ce

“Be min kyau ba ko?”

Zainab ce ta soma magana “Wallahi da kin ga yanda ki ka yi musulmin kyau baza ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login