Showing 90001 words to 93000 words out of 96407 words
Chapter 31 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
ta” sadeeq ya faɗa.
Taimaka mata Adda tayi ta zauna har time din idanun ta rufe amma duk abinda suke yi sarai tana jin su.
Fito da abin gwada Bp yayi ya zauna kusa da ita yana fara kokarin dubata ya ce
“Sannu amarya,me da me ki ke ji a jikin ki, me yake miki ciwo?”
Motsa lips din ta tayi “Zazzaɓi , ciwon kai”
Kallonta yayi ya ga yanda take sauke ajiyar zuciya a hankali
“Se kuma me? “
“Ciwon kirji”
Dama yayı tunanin haka saboda yanda ya ga tana sauke ajiyar zuciya dama ya yi tunanin akwai ulcer.
Bayan ya gama dubata ne ya fito da su drip ze sa mata ya gama seta komai sai kuma yayi tunani.
Ya furta “Akwai wani special treatment din da ake miki na ciwon kirjin ne ko kuma de maganin da ake rubuta miki?”
A hankali ta ce “eh”
“Okay wani magani ne?”
Shuru tayi ta ƙi magana duk su ka zuba mata ido suna jiran amsarta ,amma ba ta ce komai ba sai da Adda cikin kulawa ta ce
“Ƴata wani magani ne ki ke sha”
A sannan ne ta iya buɗe baki, ta ce “Beta blockers ,Atenolol din “
Cike da tsananin mamaki Sadeeq ya ke kallan ta jin sunan maganin da ta kira ya sa shi mamaki ba ɗan kaɗan ba wanda har ya jefa mishi shakku.
“Alisha,atenolol fa ki ka ce? Maganin masu ciwon zuciya ne? kına da ciwon zuciya ne”
A hankali ta gyada mai kai, duk da ba ta so su sanı ba amma in ta yi shuru to tabbas ita ce za ta cutu saboda rashin wannan maganin za ta iya rasa rayuwarta.
Da tsananin mamaki duk dakin suke kallanta ganin amsar da ta ba sa ta hanyar gyada mai kai,tabbas sun yi mamaki,mamaki kuma ba ɗan kaɗan ba,yarinya ƙarama da ita tana fama da heart attack,duk zaman da suka yi da ita nan ko da wasa ba su taɓa sanın haka ba,sosai ta ba su tausayi,shi kansa Haydar da yake tsaye sai da ya kusan zama saboda yanda maganar ya dake sa,he couldn’t believe what his ears are hearing, Alisha da heart attack amma meyasa ba ta taɓa gaya mai ba? Ɗan duban ta yayi cike da tausayinta yana jin ƙarin soyayyarta a zuciyarsa. yana me yiwa kansa alkawari baze taɓa rabu wa da ita ba domin ya ɗau wa kansa alwashin ɗauwamar da farin ciki da murmushi na har abada akan kyakyawar fuskar ta.
Cike da damuwa Adda ke duban ta tana jin mugun tausayin ta ta ce “ Allah sarki menene ya jawo miki Heart attack ƴata?”
Buɗe idanunta ta yi slowly tana duƙar da kan ta ƙasa “mutuwar iyaye na”
Jiki a sanyaye duk suka yi musu addua tare da nema musu rahaman ubangiji.
Canza treatment din da ze mata Sadeeq yayi ya sa mata ruwa tare da rubutawa Haydar maganin na ta, ya tafi domin siyowa.
Bacci ne ya ɗauke ta bayan Sadeeq ya gama mata treating, a cikin alluran da yayi a ruwan har da na da bacci, dan ta na bukatar hutu me yawa. Ganin bacci ya ɗauke ta ne yasa suka fito a dakin, Adda na rufeta da duvet suka fita,ko da Haydar ya dawo da magungunan,,Adda da ya samu a falo its ya bawa ya wuce na sa part.
saura 1 page free pages su ƙare☺️☺️☺️wanda ya biya madallah, wanda be biya ba kuma ya samu ya biya dan kar a yi babu shi.
Don’t forget to comment,like and share ☺️🫂❤️
45 & 46_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
Last free page
45 & 46
Wayarta dake kasan pillow ne ya soma vibrating,gunjinsa sam ya hana ta ci gaba da baccin da ta ke,a wahale ta buɗe idanunta da suka yi mata nauyi kamar ba na ta ba ta ƙarewa dakin kallo ,a hankali ta sauke ajiyar zuciya bayan ta ga ruwan da aka ɗaura mata ya kusa ƙarewa,kuma Alhmdullh ta ji sauki sosai daga zazzaɓin,ciwon kai da zafin zuciyar duk yanzu ta ji su da sauki sosai da sosai sai de jikinta ne ba karfi. Lallabawa tayi ta samu ta zauna tana dakatar da ruwan sannan ta cire sa a hannunta,wayar ta lalubo ta duba dan ta ga me kiran na ta, ko da ta duba sunan Mujahid ta gani,duba time tayi ta ga karfe daya saura, me yasa ze kira ta by this time har four missed calls ya mata. Bin kiran ta yi tana kara wayar a kunne.
“Hi Mujahid”
Mujahid dake kwance kusa da Zaid ne ya danna handsfree kana ya ce
“Barka dai baby sis ykk “
Sai da ta ɗan ɗauki seconds kafin ta amsa “ Uhmm ina lafiya”
“Okay. Magana ce akan memory card din da ki ka bani jiya,na duba na gani baɗalanci ne kawai da Sameer ya aikata a ciki,mata da shaye-shaye,amma abun tambayar anan waye ne ya masa wayannan video? Ko de shi yawa kan sa?”
Shafa wuyanta tayi kafin ta furta “I don’t know,na de samu wannan video a dakin matar sa,in har de ba daga gun sa aka yi wayannan videos ba to akwai ayar tambaya akanta. Yanzu de duk ba wannan ba,me ka ke tunani in wannan video ya fito gaf da zaɓen sa?”
Dariya ya tuntsire dashi jinjina mugunta irin na Alisha “His image and reputation will be ruined forever,babu wanda ze ba sa zaɓe”
Murmushin mugunta ta sake, sannan a hankali ta ce “ then post it,ka yaɗa sa a duniya. ina san in ga ya ze yi in ya rasa wannan zaɓe,ze mutu ne ko ze haukace”
Wani dariya Mujahid ya kuma sawa da karfi kamar ba dare ba, dan wallahi Alisha tana tashin kansa moves din ta suna burgesa matuka.
“An gama your majesty,amma ya na ji ki so low hope you’re fine?”
Zaid dake danna dayar wayan Mujahid da yayi pretending kamar be san da Alisha suke waya ba ya kasa kunne dan jin me za ta faɗa dangane da tambayar da Mujahid ya mata na ƙarshe.
“Uhmm kai kam tun dawuwa ta banida lafiya, sai da aka ɗaura min ruwa yanzu ne ma na tashi na cire guntu”
“Subhanallahi, sorry sis Allah ya ba ki lafiya,sannu kin ji”
Ya faɗa cikin damuwa “ameen ameen nagode,shin ya Zaid yayi bacci ne?”
Ta faɗa ƙasa-ƙasa,duban Zaid da shima idon sa akan sa yayı
“Eh ya kwanta” ya ba ta amsa.
“Okay,ka kula min dashi good night “ ta katse kiran bayan ta kare faɗan hakan.
Ruwa me zafi ta haɗama kan ta kamar wata me jego tayi wanka dashi sannan ta ɗauro alwala ta gabatar da duka sallolin da ake binta yau mangriba da isha din da ba ta yi ba. Yunwa take ji but babu abinci a dakin na ta,kai babu dankwali sai jallabiyar mata dake jikinta milk color tana tafiya a ciki zalalo-zalalo saboda yanda ba ta da kwari ,har faɗawa tayi wannan ciwon da tayi fuskar nan yayi fau,falon Adda ta nufa ta ga wuta a kunne,bakin dakin ta tsaya tana kwantar da kanta a kofar
“Adda,yunwaaaa” Adda da ta idar da nafila tana zaune kan sallaya ta ji kamar muryar Alisha,kasa kunne ta yi dan san gasgatawa
“Adda yunwa” ta faɗa murya a marairaice.
Ai ko yanzu ta tabbatar da ita ce da sauri ta nufi kofar dakin ta buɗe,Alisha dake kwance a kofar ta sulalo ta faɗa jikin Adda.
“Ya salam yanzu na ke cewa bari na idar da sallah in duba ko ruwan na ki ya ƙare”
“Uhmmm ya ƙare “
Dakin Adda ta riƙe ta suka shiga ta taimaka mata ta kwanta akan gado,.
“Adda yunwa na ke ji” ta faɗa a karo na uku tana ɗaura hannu akan shamulallen cikinta.
“Bari in kawo miki abinda za ki ci sa iki sha magani ki kwanta anan”
Ta faɗa tana fita, kitchen ta shiga da kanta ta san yanzu kowa yayi bacci bazata so ɗaga su ba,Indomie da Kwai ta yi mata me ƙarancin barkono.
Shigowa falon Adda yayi yana kokarin sa na shiga dakin Alisha ya duba ta ya jiyo motsi a kitchen, hakan yasa ya fasa shiga kawai ya ƙarasa kitchen. Adda ya gani ta ba sa baya ta na juye indomie da ta gama dafawa a plate.
“Adda ke da kan ki ne a kitchen ?“
Murmushi ta saki tana ɗaukan plate din ta juyo garesa
“Eh mana ƴata na jin yunwa shine na ke dafa mata abinda ya sauwaka “
Jim yayi kafin, ya ce “wai Alisha har ta farka?,ko de ruwan ne ya kare ?”
Gaba tayi tana “ni kaina ganin ta kawai na yi a bakin kofa na, ina buɗewa kuwa ta faɗo jikina,alamun ta cire ruwan ne yunwa ya azalzale ta”
Bin bayan ta yayi har cikin dakin ya tadda Alisha kwance kan gadon alamun bacci ya sace ta bata re da ta shirya masa ba.
“Allah sarki har ta gaji da jira ta kwanta,bari in kwaso mata magungunan nata”
Ta fita.
Zama yai a bakin gadon yana tsura wa kyakyawar fuksarta ido,ba ya jin ze iya barin ta ta kwanta haka empty stomach,ya san rabonta da abinci kila tun rana.
“My Black Queen”
Ya kira ta a hankali ga mamakin sa sai ya ga ta buɗe idanun na ta akan sa amma ba ta motsa ba tana de daga kwance tana kallan sa kawai.
“Ya jikin na ki? Hope yanzu kin samu sauki ko?”
Ɗan murmushi tayi “jiki da sauki uncle na dena jin ciwo a ko ina, karfin jiki ne kawai bana dashi sai yunwa da nake ji”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ɗauko plate da suka shigo dashi, ya ce “Adda ta dafa miki indomie da kan ta,sa mu ki ci sai ki sha magani ki kwanta “
Tallafota yay ya taimaka mata ta zauna sannan ya sa spoon ya fara feeding dinta indomie ,ba ta wani ci sosai ba duk da yanda take maganar yunwa-yunwa, amma kaɗan ta ci wanda be fi five spoons ba ta girgiza mai kai alamar ta koshi,ruwa ya zuba a glass cup ya nufo bakinta dashi aka turo kofar da sauri ya tashi daga kan gadon ya koma gefe ya tsaya hannu riƙoe da cup na ruwa, duk da bacci ne a idonta sosai amma sai da ya ba ta darıya ganin yanda ya bar kan gadon a dari ganin shigowan Adda,ita ko Adda yi tai kamar ba ta ma san me suke yi ba ta shigo da maganin.
“Madallah kin samu kin ci abinci saura magani” ta faɗa tana me zama a inda Haydar ya tashi sannan ta ɓare mata maganin ta dube sa
“To yallabai za ka ban kofin ruwan ne ko kuma de kai za ka ba ta ?“ babu shiri ya miƙa mata yana sun-sunar da kai ƙasa,dariya ne sosai a cikin ta amma bazata iya yi ba sai kawai ta dukar da kanta ƙasa ta na sakin murmushi.
Bayan ta sha maganin ne Adda tace mata ta kwanta,itama ta hau gadon ta kwanta a gefen ta, su ka bar sa nan tsaye kamar wani wanda aka shuka a gun.
“Auu har yanzu ka na nan? To je ka sai da safe “
Fita yayi yana shafa sajen fuskarsa yana murmushi ya nufi na sa part din.
Washe gari Alhamdulillah ta farka da ishashen karfin jiki se abinda baa rasa ba, Sallah ta yi a dakin Adda sannan ta kuma komawa baccin ta. Adda ba ta dakin amma tafi kyautata zato ko tana falo ko kuma de downstairs.
Ruwa ta sha ta kwanta ba wai dan tana son komawa bacci ba,har yanzu abinda ya faru jiya tsakaninta da Zaid be bar kan ta ba, in ta tuna sai ta ji nauyi a zuciyarta.
“Ka yi hakuri Ya Zaid dina” ta faɗa murya a sanyaye.
Ameera,Zainab,Yusrah ne su ka shigo dakin Adda dan su gaishe ta da jiki,saboda sun haɗu da Adda a downstairs ta sanar musu Alisha na dakin ta, zama suka yi suna gaishe ta da jiki.
“Jiki ya yi sauki sosai se abinda baa rasa ba” ta ce da su.
“Wayyo meyasa zazzaɓi ze mana haka be san ke amarya bace nan da wasu kwanaki kalilan? “
Tana murmushi ta ce “ hmm Ameera Kenan shi ciwo ai ba ruwan sa,Allah de yasa mu dace”
“Ameen ya Allah, na so a ce a bikin Uncle mu yi event ko sisters day ne amma uncle ya wani ce No,haka zaa yi aure salam fisabilillah “ Zainab ta faɗa a shagwabe
Yusrah da itama abinda ke ran ta Kenan itama ta furta “ki bari kawai! Zee na ɗauka zaa yi a grant wedding da Kaf Gombe sai ya ɗauka,amma wai babu abinda zaa yi gaskiya a duba wannan lamari aure salam dan Allah kai kai kai”
Ita de tana daga kishingide ta zuba mu su ido tana kallo batace komai ba sai ma bin bakunansu da kallo da ta ke
“Anty Alisha do something please ki yi wa Uncle magana “
Waro ido kaɗan tayi “ Na banu waye antyn ki rufa min asiri”
Dariya ta ba su sannan Yusrah, ta ce “ Kwarai kuwa ke yanzu Auntyn mu ce tunda yayanmu mafi soyuwa a gare mu za ki aura,kin ga kuwa dole mu miƙa wuya”
Ta faɗa tana mata siginal cike da tsokana..
Karamar pillow dake kusa da ita ta jawo tana wurgawa Yusrah da suke mata dariya.
“Darlings adduo’in ku yafi events da zaa yi,in aka yi fatan alkairi sai ki ga aure yafi yin albarka”
Ta faɗa musu hakane dan ta gaji da samun ta da suke yi da maganar events kusan ko da yaushe se sun yi maganar,ita da ba ta so Allah ya haɗa ta da wayanda suka san ta, ta ya za ta amince a yi wani event a wannan aure kalan asirinta ya tonu batare da ta kai ga gashiya ba.
“ eh hakane amma daren da aka ɗaura auren ku sai mun yi ko house party ne, ko Zee?” cewar Ameera tana duban Zee
“Kwarai kuwa, zan yi inviting friends dina “
“Nima haka” Ameera ta kuma faɗa.
Hira su ka tayata kafin Haydar ya shigo cikin shirin sa na zuwa aiki, yayi kyau sosai cikin shiga na baƙaƙen suit rigar ciki fari yana sanye da farar glass fuskar nan ɗauke da yalwataccen murmushi da ya sake fito da kyawunsa.
“Good morning young ladies “ ya faɗa yana ɗaga musu hannu a tare su ukun banda Alisha su, ka ce
“Morning lovely Uncle “
Sai da ya zauna a kujera dake kusa da ita yana fuskantar ta, ya furta
“Ban yi tunanin kun farka da wuri haka ba,ku da sai 10:00 or 9:30 ku ke tashi ku ne a nan 7:40 ? Am surprised gaskiya”
Yusrah ce ta yi farfar da ido tana cewa “ Uncle mun tashi tunda mu ka yi sallah asuba, ba wacce ta koma bacci mun zo duba amarya ne mu ga ya ta tashi da jiki”
Ta ƙasan ido ya dubeta, ta sunkuyar da kai tana shafa lallen hannunta ta kura wa hannu ido kamar me neman wani ɓataccen zane da baa yi a cikin lallen ba.
Dawo da duban sa kan Yusrah da tayi magana yai softly, ya ce “Amarya ta yi sauki Alhamdulillah you can see that yourself,ko My Black Queen???”
“Awwwwwwwwwn Wayyo love” Su Ameera suka faɗa su na blushing cause yanda ya yake magana yana jifanta da kallon soyayyah really killed them.
Harara ya wurga musu “ Yaran nan kun gama raina ni gaskiya “ nan ma dariyar suka kuma sawa, Yusrah dake musu video secretly ne ta ce
“ Allah Uncle kai da Alisha will definitely makes a perfect couple”
Ita de har yanzu she didn’t alter a word,kanta ƙasa just blushing and squeezing her hands.
“Barka da safiya Uncle” ta faɗa murya a sanyaye
“Kin tashi lafiya ya jikin na ki? Hope da sauki sosai ?”
Kai ta gyada kawai ta ƙi ɗagowa sam ta kalle sa kuma abinda yake so kenan. he wants to look at her sexy and beautiful eyes before he leaves amma Alisha ƴar gari didn’t gives him a chance.
Ameera da take ankare da su ne cikin zolaya ta ce “Awwwn, Our wife ɗan ɗago manaaaa ki kalli angon kiiiii”. Tayi maganar tana jaaan sa
Hararan wasa ta mata tana murguɗa ɗan bakinta cike da shagwaba ta dube sa tana rau rau da ido
“Uncle Haydar ka gan ta ko??”
Dariya suka yi dukkan su har dashi amma murmusawa kawai yayi yana kallanta yanda ta tura baki really drives him away,komai na ta, komai tayi yana burgesa, komai in tayi gani yake duk duniya ta fi da cewa da yin wannan abun.
Seta tunanin sa yayi yana “ Kyale ta zan yi maganin ta”
Ya miƙe yana zaro chocolate diary milk a aljihun wandon suit din sa ya isa gurinta ya ɗaura mata akan hannu saying
“Ni zan tafi gun aiki,, I have an important investigation to report, take good care of yourself okay?”
Kai ta gyada “thank you Uncle Allah ya tsare”
“Ameen Queen” ya fita.
“Omoh see love, ga inda love yake kuka yana neman agaji “cewar Yusrah tana faɗawa kan gado tana rufe ido, dan ita yasin yau Haydar da Alisha sun matukar tashin kanta, yau ne ta ƙara ganin yanda suka yi mugun da cewa da junan su, they are really perfect match for each other ta gama hango hakan.
Smiling Ameera, ta ce “ ki bari kawai my sister I just they wonder ko rako mata nayi, ganin Uncle da Alisha yau se da naji tamkar in koma soyayyah “