Showing 60001 words to 63000 words out of 96407 words

Chapter 21 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3610

din lauyan Dr Sagir suna jiran shigowansa,tun zuwan su babu wanda ya ce wa ɗan uwansa sannu bayan gaisawan da suka yi, domin Alhaji Musthapa a cike yake da ƙanın nasa gani yake shi ya hana a bayar da duk wasu ƙadarori na Dr. saɓanin Alhaji jabir bawan Allah be san komai ba,da tuhuman da Alhaji Mustapha yake masa ya ishe sa ne yasa yace su taho kotun gun lawyer din kawai.

Shigowa Lawyer yayi ya zauna yana miƙa mu su hannu suka gaisa cikin girmamawa.

Alhaji Mustapha fa ne ya fara magana dan lamarin ɓakaramin ci masa zuciya yake yi ba

“Barrister Abakar ka faɗi tsakanin ka da Allah ina ne inda asalin dukiyar Sagiru take? domin ka san komai na sa a matsayinka na lawyer sa dole ka san yanda yayı dasu,domin baza mu zuba ido mu bar dukiyar ɗan uwan mu ya salwanta a banza ba.”

Girgiza kai barrister yayi tare da sakin murmushin takaici sannan ya jawo lokan da yake ajiyar muhimman takaddu ya buɗe,wata jan file ya ɗauko dake ɗauke da farar paper ya ɗaura kan table sannan ya tura musu gabansa batare da ya musu cikekken ƙarin bayani ba.

Alhaji Jabir ne ya jawo paper gaban sa ya gyara zaman sa ya soma karanta copy rubutun dake rubuce me ɗauke da sa hannun ɗan uwan su marigayi Dr Sagir lelewal

“Ni Sagir Mohammed Lelewal a rana irin ta yau na mallakawa Ƴata mace Alisha Sagir lelewal dukkan wasu ƙaddarorin da na mallaka a duniya, hatta suturan sawa na ita ce mamallakiyar su daga yau. In na ce komai ina nufin komai Kama daga gidan mai dina dake by pass,da kuma gıdan siyar da abinci na sannan da kuma manyan hotels dina guda uku,manyan campany dina na sarrafawa Shinkafa suma duk na mallaka mata su,hatta filaye da gidajen da na mallaka duk yanzu sun zama mallakinta. Da kuma duk abinda matata hajiya fatima ta mallaka duk ya zama mallakin ƴar mu mace Alisha “

A ƙasan rubutun ga sa hannun sa,baƙaramin girgiza Alhaji Mustapha yayi ba jin wasikar da alhaji Jabir ya gama karantoaw,tambayar da ya kewa kan sa shine to amma meyasa Dr ze aikata haka,.

Bayan Alhaji Jabir ya gama karantowa ne Barrister ya ƙara da

“Ana gobe duka ahalin za su rasu Dr ya ziyarce ni ya sanar da ni niyansa akan dukiyar sa da kuma ƴar sa. Ni kaina nasha mamaki sosai ganin Alisha ai macece kuma ba ita bace babban ƴarsa ba Zaid ne, to meyasa yake son ta gaji komai na sa ita kaɗai?. Amma ko da na tambayesa se ya ce min be san meyasa ba zuciyarsa ne da gangan jikin sa suka yanke masa hakan. Yana son ya tura Alisha ƙasar waje dan karatu a washe garin. Yi masa abinda ya bukata na yi a cikin ƙanƙanin lokaci duk abinda lelewal ya mallaka a duniyar har da Kayan jikinsa ya koma mallakin Alisha Sagir lelewal. Sannan na hada masa duk takaddun tabbatar da hakan ya tafi dasu. Wannan shine asalin abinda ya faru”

Sosai jikin alhaji Jabir yayi sanyi, tabbas akwai abinda yasa Dr ya aikata wannan, haka kawai baze mayar da ƙaddarorinsa da sunan ƴar sa mace ba,in ma yana son a gaje sa ai Zaid ne na miji,tabbas jikin sa ya ba sa akwai abinda ba dede ba, amma ta ya ze san wannan gaskiyar?menene Dr ya ɓoye musu wanda ba su sani ba kafin mutuwar sa, sosai ya faɗa duniyar tunani,muryar Alhaji Mustapha ne ya dawo dashi daga duniyar da ya antaya na tunani

“To yanzu menene mafita Barrister? Ka san de daga shi Sagirun har ahalinsa mutum daya be tsira ba daga wannan gobara komai ya ƙone kurmuss a wannan gida, ko tsinke ba'a iya cirowa ba”

Cikin son fahimtar da su Barrister ya furta

“Hakane kam babu abinda aka iya cirowa a wannan gida. Amma ko da zaa yi shekaru darı bazaku taɓa iya mallakar koda naira daya a cikin dukiyar Dr ba, saboda shi da kan sa ya rubuta yabarwa ƴarsa komai, kuma takaddun duk suna wajen su ni wannan ce shaida ta da na yi copy. doka baze taɓa mallakar muku da dukiyar matacciya ba ta hanyar ƙa'ida ba. Amma ni ban san meyasa jikina ya ke bani cewa wayannan takaddu suna nan cikin koshin lafiya ba. In de suna nan komin daren daɗewa zaa samo su kar ku damu”

Alhaji Jabir ya ji dadin wannan bayanın na Barrister saboda ko bakomai shima yanzu ze huta da masifar yayan sa akan dukiyar da ba na su ba. Miƙewa yayi ya bawa Barrister hannu suka kuma gaisawa

“To Barrister mun gode sosai da sosai se wani lokacin”

“Nagode nima Alhaji Jabir a koma gıda lafiya”

Fita yayı yabar alhaji Mustapha zaune ya kasa koda miƙewa tsabar ya girgiza da jin yanda dukiyar Dr suka yi. Takaici da azabar haushi ne suka sa shi ya kasa miƙewan saboda ya matukar sa dukiyar Dr a ransa ya yi Imani inde ya ninka dukiyar akan nasa to tabbas ze zama babban attajiri, saboda Dr yana da dukiya me tarın yawa wanda ba ki bazasu iya lissafawa ba sede a rubuta a takadda da biro.

(Hmmm alhaji Mustapha ka nuna wa duniya kudi ya fi maka radadin mutuwar dan uwan ka da iyalansa🥺😔😒)

4:00 dede ta farka daga dogon baccin da ta yi. sosai ta ji dadin baccin dan ta jima ba ta samu natsatsen baccin rana haka ba,fuskanta da idon ta sun ɗan kumburo kaɗan saboda baccin da tasha. alwala ta je ta yi ta shimfida sallaya ta gabatar da sallah la’asar addua ta yi wa iyayen ta na samun rahamar ubangiji, ta kusan minti talatin zaune kan sallaya kafin ta idar ta miƙe ta nufi kitchen dan da mugun yunwa ta farka a kitchen din ta zauna ta ci abincinta sannan ta shiga dakin Inna ta hau gadon ta ta kwanta suka fara hira.

Wannan karon inna ce ta musu abincin dare tuwo da miyan ganye, ba wani sosai ta ci tuwon ba,bayan ta yi sallah mangriba ne ta yi wanka ta fito ɗaure da towel. Text ta gani da number Haydar

“Kin gama?”

Kallon sakon ta tsaya yi dan in bata manta ba kamar yace se ya yi sallah isha ze zo ɗaukan ta.

Mayar mai da amsa ta yi “ah ah amma bayan isha na san zan gama komai”

Da tura masa da sake turo mata wani sakon ko minti daya be kai ba kamar wanda ya riƙe wayar yana jiran sakon ta.

“Okay” kawai ya tura mata.

Har za ta ajiye wayar se ta tuna da Mujahid ya tura mata da number wanda zasu yi magana, kiran sa ta yi suka yi magana tace mai ya tura mata account details dinsa.

Ba ta shirya ba sai da ta tura masa da kudaden aikin sa ta account Inna, sannan ta shafa lotion ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshin gaske. ta saka wandon falazo da riga me guntun hannu sannan ta yi fakin gashin ta gu daya se kyalli yake, ta saka doguwar hijabin da ta zo dashi.

“Inna ni zan wuce,se mun yi waya “

“Allah ya tsare ƴar nan, Allah yakare ki, ya ba ki saa akan ƙudurin ki”

“Ameen my inna “ ta faɗa tana rungumeta.

A bakin babban layin anguwar ta samu napep nan ta cedashi da ya kai ta Asibitin Burkachuwa. A nan ya ajiye ta ya ja mashin din sa yayi gaba bayan ta biya sa kudin sa.

Sai da ta wuce asibitin sannan ta tsaya a bakin wani shago tana jiransa.

Tunda ya iso layin da suka haɗu kwanaki ya rage speed din gudun da yake yi yana dubawa ko ze ganta tunda ta tura mai da text tana jiran sa a kan hanya,hango ta yayi ita kaɗai tsaye ta harɗe hannu a kirji tana kallon ƙasa with her beautiful innocent face. babban hijab din da ta sanya iska na kaɗa kasan hakan ya bawa hijab din daman mannewa a jikinta,tunda ya sanya ta a ido ya ji wani sanyi ya ratsa zuciyarsa haka ya dinga driving har ya isa inda take tsaye. Horn ya matsa da ya ankarar da ita zuwanshi kafin ya sa hannu ta mazauninta ya buɗe mata kofa. Cikin nutsuwa ta shigo tana tattare hijab din ta ta gyara zaman ta keeping her phone on her lap.

“Ina wuni Uncle “ta gaishe sa da zazzakar muryarta.

Se da ya lumshe idonsa yana jin wutar son ta na sake ruruwa a zuciyarsa,be amsa mata ba se da ya kashe motar ya juyo gare ta

“Lafiya Lau nake “

Jin yanda idon sa ke yawo a jikinta ne yasa ta gagara ɗago nata idon ta dube sa se da kyar ta iya cewa

“Masha Allah “

Ya so ko sau daya ta ɗago ido ta kalle sa ko ze ji abinda yake ji akan ta ya sassauta, amma ba ta yi hakan ba saboda nauyin da idon sa yake dashi a gare ta,idanun sa na da kaifin da sau tari bata iya sanya na ta cikin su.

Murmushi kawai ya yi ya tada motar ya soma driving yana sarrafa steering motar a hankali kamar wanda ba ya so,shurun da ya ratsa ne ya bawa ko wannen su daman faɗawa duniyar tunani ko wanne da abinda yake tunani akai, ga kamshin su da ya gauraye cikin motar ya ba da wani scent na musamman da ya sake dulmiyar da su a duniyar da suka kai kan su.

Hankalin sa akan hanya ya ɗan saci kallon ta fishaa ya ga yanda ta kwantar da kanta a seat din idanun ta lumshe da duka alamu tana cikin yanayı na tunani,cikin son Kawar da yanayin shurun da su ke ciki kamar wasu kurame ya ce

“Meyasa bakya son bin su Yusrah duk lokacin da suka shirya fita yawon shan ice cream suna yawan faɗa min ke bakya bin su”

Sarai ta ji abinda ya faɗa hakan yasa ta ware idanunta akan sa yana driving a hankali

“Uncle ka yi magana ne?”

Kallon ta yayi ya ga itama shi take kalla, ya san sarai ta ji sa so kawai take ta mai alaye.

“Kin ji ni ai”

“Haka kawai lokacin da suke zuwa min ni kuma a lokacin ina cikin yanayı na son kaɗaituwa ne bana son hayaniya, amma ina son yawo sosai da sosai”

Murmushi ne ya suɓuce mai jin yanda ta yi maganar karshen cikin karsashi.

Buɗe ba ki yayi ze yi magana wayar sa ya soma ƙara ,ɗauka yayi be ce komai ba har wayar ya katse, ajiye wayar yayi batare da hasken screen din ya mutu ba,idonta ne ya sauka akan haɗaɗɗen hotonsa cikin kakin uniform ya matukar yin kyau ga bakin glass din da ya sanya sosai hoton ya tafi da imanin ta,a hankali ta furta

“Masha Allah hoton nan ya yi kyau sosai”

Murmushi yayi jin abinda ta faɗa wanda ita kam sam ba ta san ya fito fili ba. Se ji tayi ya ce

“Faɗi gaskiya Hoton ne yayi kyau ko ni?”

Runtse ido ta yi ba ta yi tsammanin maganar da ta yi a hankali ya fito fili da har ya ji ba,dariya sosai ta ba sa ganin yanda ta yi da fuska kamar me shirin sa kuka dan kunyar da ta ji. amma se be yi dariyar ba sema ɗaura mata wayar ta sa da ya yi akan cinyar yana cewa

“Ki yi ta kallan hoton har mu isa gida”

“Ni fa ba haka na faɗa ba” tayi maganar a shagwabe

“To me ki ka faɗa “

“Cewa na yi inda ka yi hoton ya yi kyau kamar ba Nigeria ba”

Wannan karon se da ya yi dariya da be shirya masa ba jin ta sauya abinda ta faɗa bayan kuma ya jin ta

“Yeah baa Nigeria bane mun je wani seminar ne a Isreal shekara daya da ya wuce”

Shekara daya da ya wucen da ya faɗa ne ya tabbatar mata da ba ya ƙasar lokacin da Mahaifin sa da ɗan uwan sa suka yi musu barna dan son tabbatar da hakan ya sa ta furta

“Nagane! can i see more of the pictures please ?”

He suspects nothing ya ce “let me pack se in nuna mi ki su” yayi maganar a dede lokacin da ya tsaya a bakin gate yana matsawa me gadi horn. Wangale masa gate aka yi bayan me gadin ya leko ya ga shine. Dede packing space ya kashe motar kana ya dau wayar a cinyar ta ya shiga gallery din sa.

Nuna mata hotuna ya shiga yi ya na faɗa mata time da date da kuma a ƙasan da ya ɗauka. sosai su ka shagala da kallon pics da har ta matso kusa dashi jikinsu yana gogan na juna duk ba su ankara ba hankalin su yayi gaba,sosai ta saki jiki tana kallon pics din na sa duk wanda ya mata kyau se ta yaba.

Muryarta can ƙasa ta ce “Yawancin pics din baa Nigeria ka yi su ba uncle, duk sun yi kyau musamman wannan” ta faɗa ta na dawo da hoton sa da suka wuce yana sanye da babban farın jacket kansa da p cap, hannunsa da safan hannu an yi hoton a cikin dusar kankara,baƙaramin kyau yayi a hoton ba kamar irin handsome black American actors.

Shima muryar ta sa can ƙasa ya ce “wannan hoton ya ɗan jima kusan three years yanzu “

Yanda suke magana ƙasa-ƙasa ko da ace akwai mutum a cikin motar in ba ya kasa kunne sosai ba tofa baze taɓa jin su ba.

Sosai su ka ɓata lokacin su wajen kallan hoto da ya hana su fitowa cikin motar.



Fitowa Meenal ta yi cikin matsananciyar ado se baza kamshi ta ke, ta tsuke cikin matsatsiyar doguwar rigar lace ko ina tabb ko numfashi bazaka yi tunanin za ta iya yi ba. kan nan yasha gashin doki, tayi ɗaurin ture ka ga tsiya babu gyale akan ta se jaka da wayar ta da kuma car key da ta riƙo. Gun daga bakin falo ta hango motar Haydar a packing space. sosai ta ji dadin dawuwar sa a wannan time din saboda tana so kafin ta fita ta nuna mai wannan ado da ta chaba hakan yasa cikin tafiya na yanga ta nufi motar sa,kasancewar motar da ya fita dashi yau ba tinted bane kuma glass a sauke, yasa tana zuwa daf da motar ta hango sa zaune ga Alisha manne kusa dashi jikin su a haɗe suna kallon abu a waya se murmushi suke kamar wasu newly couples.

Wani irin tafarfasa zuciyar ta ya fara tsaban kishi da zallan tsanan Alisha ne kawai yake tokare mata kirji a tsawa ce ta kira sunan sa

“Haydar” Ɗagowa shi da Alisha su kai su na kai duban su gare ta,ganin irin muguwar kallon da ta ke bin su dashi ne yasa Alisha ta nuna alamun tsoro,riƙe hannun Haydar ta yi gam ta ƙi sakewa. domin daga shi har ita sun fahimci abinda ya sanyata fusata haka ganin su da ta yi a manne ne wanda sam basu aikata hakan da niya ba.

Haydar kuwa ɗaure fuska ya yi kamar ba shi ne ya gama murmushi yanzu ba ya kalli yanda Alisha ta rƙke hannun sa daya ga fuskar ta ya nuna alamun tana jin tsoron Meenal. Fitowa ya yi daga motar ya zagayo ta gaban Meenal din ya buɗe mata amma se ta ƙi fitowa ganin haka yasa ya riƙo hannun ta ya fito da ita daga cikin motar



In ban da harara babu abinda ta ke aika musu “amma wallahi Haydar ka ji kunya,yau auren mu kwana bakwai ne zuwa takwas, amma shine tsaban rashin tsoron Allah za ka ɗauki wannan karuwan yarinyar kana yawo da ita”

Cikin son tunzurata ta ce “kai, kai, kai, wallahi ni de ba karuwa bace. kuma Allah ya isa na kirana karuwa da ki ka yi” a fusace ta kai hannu za ta damkota aiko Alisha ta yi sauri ta koma bayan Haydar ta tsaya tana soma kukan shagwaba. Hankali a tashe ya juya gareta dan kwata-kwata ya ƙi jinin abinda ze taɓa ta

“Am sorry Alisha ki yi hakuri ki dena kukan, ki shiga ciki ina zuwa zan yi magana da ita”

Make kafaɗa tayi kamar ƙaramar yarinya “ni de ah ah ,na san bi na za ta yi ta dake ni”

“Noo I promise you ba za ta mi ki komai ba”

Ita de izuwa yanzu in bakin ciki da takaici na kısa tofa da Meenal ta jima da mutuwa har wani dishi-dishi take gani burinta daya yanzu be wuce ta figo Alisha ta mata dan burauban duka ba ko za ta huce abinda ta ke ji.

“Allah wadaranka wallahi. wannan ƴar ƙaramar yarinyar ce za ta tsaya ta na juyaka kamar wainar masa,ko da yake baa banza ba tunda kana danne ta a sirrance dole ka zama rakumi da akala “

“Meeenal” ya kira sunan ta a cikin tsawan da dukkan su biyu se da hantar cikin su ya kaɗa, baya dashi kaɗan Alisha ta ja ta manne a jikin motar ta fashe da kukan kissa hawaye wannan na bin wannan non stop.

Ita kuma Meenal one time ta dawo hayyacinta ta fara danasanin abinda ɓacin rai da kishi ya sanya ta furta masa, a yanda ransa ya ɓaci din nan yanzu ya za ta yi in ya ce ya fasa auren ta.

Cikin tsananin bacin rai da ya Kwan biyu be shiga ba amma ta dalilin kalamanta ya shigesa ya nu na ta da yatsa

“How dare you? I said How dare you Meenal?” Ya ƙarasa maganar da wani tsawan da ya fi na ɗazun.

Zuwa yanzu jikin Meenal rawa kawai yake yi tana ja da baya sanadiyyar kusantota da take, tsoronta daya kar ta sha kyakyawar mari a kumatunta da basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login