Showing 45001 words to 48000 words out of 96407 words

Chapter 16 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3609

suka dinga hiran.

Tana cikin tafiya ta jiyo muryar Meenal tana waya tana tahowa da alamun ƙasa za ta sauka. Batare da ta nu na ta san da ita ba ta bata hanya, ita ko Meenal tana ganin Alisha ta katse kiran da take yi tana iso wa inda take ta yi murmushi tana binta da kallo cike da tsana gami da kaskanci

“Har an dawo daga yawon tazubar din kenan ?na ɗauka ai kin tafi kenan ashe za ki dawo “

Yi ta yi kamar bata ji ta ba ta sa kai za ta wuce amma sai Meenal ta tsare mata hanya

Cikin sanyin murya ta ce “Meenal kin tare min hanya”

“And so?? Ko za ki ture ni ki wuce ne?”

“Hmm….. ni de ban iya rigima ba, dan haka dan Allah ki matsa min”

Taɓe baki tayi tana me ci gaba da watsa mata banzan kallo “baƙar munafuka me fuska biyu ai na gama gano ki, kına abu simimi-simimi baa san guba bace. Su ne suke miki kallon innocent amma ni da ki ka gan nin nan tarr nake ganin ki. Na san dalilin zuwan ki gidan nan….”

Da wani expression ta ɗago ta watsa mata narkakkun idanunta da suke lumshewa da kan su tsabar yanda ran ta yake ɓaci, saboda tsare ta da Meenal tayi tana faɗa mata baƙaƙen maganganu,ƙara kankance su tayi tana gyara tsayuwar ta. Duban ta ke ido cikin ido with her real color ta ce

“Kin san dalilin zuwa na gidan nan ki ka ce …..?”

“Kwarai kuwa na san abinda ya kawo ki wannan gida da har ki ka zo ki ka mannu da su kamar cingam “

“To tun da kin sani se ko fada min,menene dalilin zuwa na gidan nan din ?”

Watsa mata wani harara tayi ta ja tsaki tare da nuna ta da ɗan yatsanta da ya sha dogon farce na bogi an fente su da cottes

“Kin zo gidan nan ne ba dan kowa ba se dan Haydar Ɗan gaske, na gama gane take-taken ki yanda ki ke kokarin jawo hankalin sa izuwa kan ki. To bari ki ji Haydar ba kalan ki bane,ni ce nan matar da ze aura nan ba da jimawa ba. Dan haka ze yi kyau ki yi gaggawan barın gidan nan tun kafin in sa a yi miki koran kare”

Wani irin dariya me karfi ne ya kubucewa Alisha ta hau yi babu kakkautawa har ya kai ga tana riƙe cikin ta tsaban dariyar da take yi tana yi tana kallon meenal tana nuna ta daga sama zuwa ƙasa, kai kace ta ga wani abu a jikin ta. hakan se da ya sanya Meenal tsagurwa ta fara tunanin to meye ya sa Alisha take mata wannan dariya tana mata wani kallo

Cikin dariyar da yaƙi dakata mata ta nuna ta tana “Shame on you yan mata… shame on you “ta faɗa tana kuma fashe wa da sabuwar dariya.

“Me ki ke nufi da kika tsaya kina min dariya?”

Kugu ta riƙe tana kuma ƙare mata kallo fuskarta ɗauke da murmushi da ya ƙara mata kyau “to ai dole in yi dariya saboda wayannan maganganun na ki,yanzu ke na miki Kama da macen da za ta biyo namiji har gidan su? Ke ce de mara class ki ka biyo na mijin da ko kallon ki baya son yi gıda,abin kunya de ke kam ya haɗu miki banza ballagaza “ tana gama gaya mata haka ta wuce ta tana ci gaba da dariyar ta. in da ta bar Meenal in shock maganganun Alisha sun matukar hassala ta da ya sa ta nufi downstairs a fusace.

Tunda suka ga irin saukowan da take yi suka san ba lafiya ba amma babu wanda ya nuna ya san da tahowanta,tana sau kowa ta nufi gun Adda ta ja ta tsaya.

Cike da rashin manners ta fara magana kamar wacce take magana da sa'arta

“Adda wallahi ba ze yu ba,ba ze yu wannan kucakar yarinyar ta zo tana faɗa min maganganu in Kyale ta ba,dole ne ta bar gidan nan yau din nan tunda ba gidan uban ta bane yawwa “ dukkanin su da mamaki suke kallon ta domin ba su san da waye take yi ba.

Cikin kulawa Adda ta ce “Meenal ke kuma ke da waye haka?”

Cikin tsiwa ta ce “waye in ban da wancan yar iskan yarinyar da ku ka ajiye a gidan ku Alisha”

Maryam de taɓe baki tayi,a yayinda Zainab da Ameera su ka ja tsaki. Yusrah kuwa ko ɗago kan ta bata yi ba.

Da ɗan mamaki Adda ta furta “ikon Allah Alisha kuma..? Me ya haɗa ku haka da ita yarinyar da babu ruwan ta “

“Adda har ni yarinyar nan za ta kira mara class, wai na biyo saurayi har gidan su saboda rashin class,Wallahi se na koya mata hankali.”

Dariya duk suka fashe dashi amma banda Adda da ita take iya kokarin ta wajen danne nata dariyar.

“To ai ba karya ta faɗa ba. Gaskiyane wanda ni dake da duk wanda yake wannan gida ya san da haka. Rashin class da rashin sanın mutuncin kan ki a matsayin ki na ƴa mace ne ya sa ki biyo namiji har gidan su”

Cewar yusrah tana girgiza kafa tana danna wayar ta kamar ba ita ce ta yi maganar ba.

Adda ganin yusrah na son tayar da husuma ne yasa ta saurin faɗin “yi hakuri Meenal in sha Allah zan mara magana “ ko amsa bata bata ba ta fita a falon cikin sauri.

25 & 26_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

25 & 26

Fitowarta farfajiyar gidan yayi dede da fitowan Sameer daga motarsa, ganin tana kokarin wuce sa ne yasa yayi saurin damko hannun ta “hi baby girl wannan saurin fa? Seems like wani ya ɗata miki rai “

“Waye kuma da ya wuce wancan banzan yarinyar “ ta faɗa tana huci.

Calmly ya ce “ wata yarinya kenan ?” yai tambayar yana massaging hannun ta da ya riƙe.

“Sameer can you imagine wannan yarinyar ni za ta tsaya tana faɗawa baƙaƙen maganghhat, har ni za ta kalla daga sama har ƙasa tace wai bani da class? In ban kashe ta ba hankali na baze taɓa kwanciya ba” nan ta kwashe komai ta faɗa masa. Be yi mamaki ba saboda shima Alisha ta watsa masa hot coffee dan kawai ya je da niyan toasting din ta, kuma dama yayi alkawarin se ya ɗau fansan abinda ta mai a ran sa.

Langwabar da kai yayi cikin salon ƴan duniya yana bin ta da wani kallo yace “Yanzu akan wannan ƙaramar yarinyar za ki tsaya kina ɓatawa kan ki lokaci ? Common Meenal ajin ki ya wuce haka. Ni da kaina zan rama miki abinda ta yi miki I promise you. Kawai ki bar komai a hannuna let’s go and have some fun “ ya yi maganar yana kashe mata ido. Motar sa suka shiga shi da ita suka fita batare da ya shiga ciki ba.

Har ta shige bedroom dinta bata dena dariyar Kalmar da Meenal ta faɗa mata na cewa wai ta zo gidan Ɗan gaske ne saboda Haydar, bata san saboda shi Ɗan gasken da kansa ta zo ba. Zama tayi bayan ta cire hijab din jikinta kan ta babu dankwali sai gashin dake tufke. tunanin ta gaba daya ya koma kan Mujahid da Zaid fatan ta de Allah yasa a yi aiki lafiya.

Ba zato babu tsammani kawai ta ga shigowan Ameera da Yusrah tana kokarin jawo dankwali ta ɗaure gashinta ta ji suna faɗin

“ Kai turbarakallah “

Yusrah ta ce” dama haka ki ke da gashi ba mu taɓa sanı ba? Gaskiya kina da halittan suma me kyau” tayi magana tana zama hankalinta gaba daya a kan gashin Alisha.

“Wallahi kuwa anty yusrah nima ban taɓa sanın Alisha na da gashi har haka ba saboda kullum tana sanye da dogon hijabi da dankwali”

Murmushi kawai tayi bawai dan ta so su ka shigo suka gan ta a haka ba amma ya za ta yi tunda har sun gani.

Bayan sun gama yabon dogon gashin ne yusrah ta tambayeta me ya haɗa ta da Meenal. bata ɓoye musu komai ba ta faɗa musu cikin farin cikin abinda tayi matan Yusrah ta ce “in de ta sake tunkarar ki da zantukan banza ki faɗa mata abinda ya fi wannan “ nan ma murmushi kawai ta yi ba ta ce komai.

Hira suka ɗan yi duk da ita se jifa-jifa take magana har kusan karfe 6 suna gurin ta kafin suka ce bari su je su yi alwala tunda lokacin sallah ya kusa.

Itama wanka ta shiga ta dauro alwala.



“La ilah ya Najib Allah in ka fita da Ilhaam ita kadai wallahi sai na faɗawa mama” cewar Imaan da ta tsaya masa a kai,kallon ta kawai Najib yayi “Imaan kefa jiya ki ka ce bazaki je dadin kowa ba, baki biyu Ya Khalil na tambayan ki kina cewa baza ki ba, yanzu kuma nice za ki je ?to babu inda za ki bi ni “

Bubbuga kafa ta fara yi tana kokarin sa kuka,Kallon yayan na su Ilhaam ta yi “ ya Najib dan Allah mu tafi da ita bazata ji dadi ba in muka bar ta a gıda bazata ji dadi ba”

“Shikenan to je ki shirya in ki ka ba ta min lokaci kuma tafiya zamu yi “

Tsalle suka yi su biyu din tsaban farın ciki dan sun san yau kam babu kwana a gida se kwana a dadin kowa wajen kakarsu wacce ta haifi mahaifiyar su,zasu je biki.

Dariya mama ta yi “yaran nan akwai shiririta,Nikam Khalil har yanzu be gama shiryawa bane ko menene?”

“Mama kin san shi in za'a tafi guri dashi har se ka ji ran ka ya ɓaci saboda African time.”

Girgiza kai ta yi tana ɗaga wayanta za ta kira sa kenan ya fito yana baza kamshi cikin shiga na bakar yadi half jumfa ya masa kyau sosai kuma dama ga shi kyakyawa Masha Allah

Murmushi yayi ya ce “na ji yo ku fa kuna gulmata “

Cikin raha Najib ya furta “eh mana Allah kai duk sanda zaa fita da kai se ka jawo an yi letting “

“Yanzu gani nan na fito ai. Ina Twins suke ?”

A wannan karon mama ce ta ce “ suna can suna shiryawa”

Bayan su Twins sun fito ne suka shiga motar sannan suka dauki hanyar zuwa dadin kowa biki.

Bayan ta idar da sallah ne ta shafa lotion sama-sama sannan ta saka doguwar riga dinkin material daga sama ya kamata ta ƙasa kuma ya bazu batare da ta saka hula ko ta ɗaura dankwali ba ta yafa babban gyale sannan ta feshe jikin ta da turare,ta fita a dakin dan zuwa taya Adda hira.

Ko da ta shiga falon Adda babu kowa cikin sa se de tana jiyo motsi a kitchen din tabbacin akwai mutum cikin sa kan ta tsaye ta nufi kitchen din nan ta iske Adda na jera abinci akan fansy plastic tray.

“Sannu da aiki Adda”

Dan juyowa tayi ta kalle ta fuska da faraa kafin ta ci gaba da abinda take yi tana faɗin “yawwa ƴar albarka dama yanzu na ke tunanin kiran daya daga cikin ku,maza kai wa Uncle din ku abincinsa ya dawo ɗazun nan “

Tayi maganar tana miƙa mata tray din,karɓa tayi tana “to Adda”

Knocking tayi a bakin kofar falon sa daddaɗar muryarsa ta ji ya amsa da “come in”.

Se da tayi jim kaɗan kafin ta shiga bakin ta ɗauke da sallama,da sauri ya ɗago daga kwancen da yake domin ko kusa be yi tunanin jin muryarta ba. Ya kasa janye idanunsa akan ta ya har ta iso ta ajiye tray aka table.

“Barka da warhaka Uncle Haydar”

A madadin ya amsa gaisuwan sai cewa yai “Alisha…? Yaushe ne ki ka dawo?”

Kan ta na kallan ƙasa tana wasa da yatsunta ta ce “Tunda safe around 11 “

Idon sa akan ta ya gyada kai yana me gyara zaman sa.

“Me yasa ki ka tafi batare da kin min magana ba? “

“Ka yi hakuri uncle nima ba da san raina hakan ya kasance ba,ban so na daga muku hankali ba” bayan ta faɗi haka ta gaya masa abinda ta sanar da su Adda.

Jinjina kai yai “Shikenan amma next time in za ki je gidan ki sanar min in kai ki saboda in san gidan okay?”kai ta gyada masa.

A karo na biyu ya ce “kuma sannan me yasa ba ki taɓa ce min ba ki da waya ba?”

Tana wasa da ƴan yatsun ta, murya a hankali ta amsa masa “Bakomai…bana san ɗaura muku nauyi ne”

Slowly ya matso kusa da ita hannayenta da take wasa da su ya riƙo duka biyu yana matsasu cikin nasa da sauri ta dube sa, shima itan yake kallo domin tun shigowanta be janye sexy eyes din sa akan ta ba har zuwa yanzu da ya riƙo tausasan hannayenta

Cikin kulawa da kwantar da murya ya ce”ke ba nauyi bace akan mu Alisha,you’re part of us now,kema yanzu daya daga cikin ahalin gidan nan ne. Dan haka bana son in sake jin kin faɗi wannan Kalmar.”

“In sha Allah bazan sa ke faɗa ba Uncle” slide smile ya yi

“Haydar faɗa mu ji…”

Da hanzari ta zare hannun ta a nasa, tana waro idon ta waje jin abinda ya faɗa nan ta hau girgiza mai kai tamkar ƙaramar yarinya

“Ahh ahh ni gaskiya bazan iya Kıran ka da asalin sunan ka ba”

“Why?!” ya jefa mata tamabya

“Saboda sunan yana min nauyi in faɗe sa gatsau,kuma ma de ai ka girme mu sosai, su Ameera da kowa Uncle fa suke ce maka se ni ce mara kunya in kira sunan ka?”

Sosai ta bashi dariya da se da ya ɗan dara

“Hmmm…… Allah ya ba ki miji me sunan Haydar se in ga ya za ki yi” ya faɗa hakan cikin son jin menene abinda za ta faɗi.

Lokaci daya ta ji nauyinsa dan ba ta yi tsammanin jin haka daga gare sa ba,haka kawai se ta ji kamar da biyu ya faɗa maganar, domin tana jin yanda idanunsa suke yawo a jikin ta hakan yasa nervously ta ce

“Uhmm”

A karo na sau babu a dadi ya kuma sakin siririn murmushi ganin yanda ta daburce “why are you nervous Alisha? Did I said something wrong?”

Da sauri ta girgiza kai alamar ah ah

Ganin haka yasa shi kuma faɗin

“Then why all the sudden change? Ko bakya son auren namiji me suna Haydar ne?”

Tambayar da ya mata na yanzu yafi wanda ya mata da farko nauyi, ta rasa takamammen amsar da za ta ba sa se kawai ta miƙe tana kokarin tafiya

“Dawo ki zauna” shagwabe fuska tayi ta soma yarfa hannu “Ayyah Uncle Haydar ka ci abincinka kar ya yi sanyi”

“To zauna ki yi serving dina in na gama ci se ki tafi da shi” ba ta da wani zaɓi haka ta zauna ta fara serving din sa, da ta gama ta ajiye masa a gabansa ta zauna a hannun kujera,cikin nutsuwa yake cin abincin be ci yakai rabi ba ya matsar gefe saboda koshin da yayi be ce da ita komai ba ya shiga bedroom din sa ya fito riƙe da kwalin waya,zama yai a inda ya tashi yana

“Ga wayan ki nan akwai sim a ciki duk inda za ki je ya kasance dake saboda tsaro”

Karɓa tayi cikin murna da farin ciki, cikin nutsuwa ta ce “nagode sosai Uncle Allah ya saka da alheri Allah ya biya maka dukkan bukatunka na alkairi”

Sosai ya ji dadin addua da tayi ma can ƙasan maƙoshi ya furta “ameen Alisha “

Buɗe kwalin wayar ta fara kamar yanda ya umarceta tana buɗewa daya daga cikin takaddun kwalin ya faɗi ƙasa. ajiye wayar ta yi bisa kan kujera ta sauko ta ɗauki takaddan ta koma mazauninta ta zauna tana ci gaba da buɗe wayar har yanzu da wannan murmushin kan fuskar na ta be gushe ba.

Kira ne ya shigo wayar sa ko da ya duba ya ga Auwal da Sadeeq ne suke kiran sa group video call kamar ba ze ɗaga ba se kuma ya ɗaga suka fara waya,suna ta hiran su amma shi hankalin sa duk yana kan ta saboda ya ga yanda take struggling wajen ciro ɗan alluran da ake cire sim a ledar sa be san meyasa ba ya ji sam hankalin sa ya gaza kwanciya gani yake kamar abun ze yi hurting dinta.

“Kai wai me ka ke kallo ne haka ? Ka bar mu se zuba mu ke kana ganin wani abu daban” cewar Sadeeq yana watsa mai kallon up and down. Dawo da hankalin sa kan su yai saying “sorry guys ya ake ciki to ?”

Yana rufe bakin sa ya ji ta sa ɗan siririn ƙara tana yarfa hannu cikin shagwaba tare da faɗin “Wayyo Uncle hannu na,ya ɓula min hannu na” batare da ya kashe kiran ba ya ajiye sa yana isa gabanta da sauri ya riƙo hannun da ya ga ta riƙen, babban yatsanta ya gani jini ɗan kaɗan ya tsarto,kun san yanda yake in ka ɗan caki hannun ka da allura to haka yayi shine take wannan kukan.

Yatsan nata ya sa a baki yana tsotsa a hankali yana kuma hura mata iska yanda za ta ji raɗaɗin ya ragu mata. runtse ido tayi jin yanda yake hura iska da tsotsan ɗan yatsan, zafin da take ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login