Showing 18001 words to 21000 words out of 96407 words
Chapter 7 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
wani mutum amma na kasa tuna wanene” a hankali ta dakatar da wanke Kwanon
“Ze yu kawai kama ne”
“Yeah nima na yi tunanin haka” ya faɗa yana fice wa a kitchen din.
Se karfe biyu da rabi ta gama wanke tulin kwanukan.
“Hi Alisha “
“Hi” ta faɗa tana kallon Ameera da ta shigo kitchen din
Murmushi Ameera tayi ta ce “sunana Ameera Ɗan gaske ƙanwar uncle Haydar”
“Sannun ki Ameera “ ta mayar mata da martanin murmushi
Ameera tace “tunda ki ka dawo ki ke ta shan aiki naga ko abinci baki ci ba balle ki yi sallah. Yakamata ki ci abinci kiyi sallah in ya so anjuma kici gaba”
“Kar ki damu Ameera am fine in na kammala ayyukana zan yi”
“Ai gaskiya Ameera ta faɗa miki ni na lura kamar bakya son cin abinci”
Cewar Hajja Hauwa da ta shigo da flask din ruwan zafi a hannunta.
“Maza maza ki bar wannan aikin mu je ki ci abinci Kisha maganinki “. Ba ta iya mata musu ba ta ajiye towel din hannunta ta bi bayanta.
A daren yau Ɗan gaske ya zo ganin jikansa tare da Sameer daga nan aka mayar da auren Sameer da Maryam, saboda Ɗan gaske yace wannan abun kunya ne a gare sa ace baa yi sunan jikansa a gidan sa ba. Maryam ba ta so Hajja Hauwa ba ta so amma ba yanda suka iya haka aka mayar da auren a daren aka mayar da maryam can family house din Ɗan gaske.
Gidan yayi saura iya Hajja Hauwa ne da Alisha. Ko da ta ga Hon Ɗan gaske se da ta ji Ina ma ta ɗauki wuka tayi ta soka masa har se ya mutu.
Tunda Maryam ta koma can gida Haydar be sake zuwa gidan Hajja Hauwa ba dan itama tana zuwa can din ne dubo maryam sede ta bar Alisha a gida.
Safiyar suna Hajja Hauwa ta sameta tare da ce mata ta shirya zata su je gidan Ɗan gaske saboda yau sunan maryam.
Wanka tayi ta shirya cikin kayan yusra sannan ta sanya babban hijabi kalar Kayan
“Hajja hauwa na gama”
“Kin yi kyau sosai amma meyasa baki sa gyale ba kin yi adonki kuma ki sa katon hijab “
Kallon jikinta tayi “Hajja Hauwa ban saba sanya gyale bane shi sa “
“To shikenan mu je ko driver na jiran mu” fita suka yi driver ya ja su izuwa katafaren gidan Ɗan gaske. Tunda suka shigo take kallon ko ina
“Na zo kenan babu fita har se na kammala aiki na” ta yi wannan maganar a ranta ne a yayinda suke fitowa a motar suka shiga main falo inda suka seme sa a cike da mutane,gaisawa da mutanen wajen Hajja Hauwa tayi itama Alisha ta gaishe su sannan suka haura can upstairs bangaren Sameer da babban hoton sa dake kafe a falon sa suka fara cin karo. Iya maryam da yan uwan ta suka samu a nan. zama suka ɗan yi kafin su Adda suka shigo suka gaisa.
“An yi suna lafiya ?me aka sa wa yaron” Hajja Hauwa ta tambayi Adda
“Umar aka sanya masa inkiya Aryan”
Ta bata amsa
Idanunta ne suka ciko da hawaye lokacin da ta ji nickname din jaririn a hankali ta furta “Aryaaaaan” Duk kallon ta suka yi
Hannu ta miƙawa Maryam “Anty Maryam dan Allah in ga Aryan” cike da mamaki suke kallon ta ganin idon ta tab da hawaye miƙa mata maryam ta yi
Kallon jaririn take kamar ta cinye sa se sakin murmushi kawai take tana tuna ɗan ƙaramin ƙanın ta Aryan,ji tayi farat daya so da kaunar wannan jaririn ya shiga ranta ji take yi tamkar ta gudu dashi.
“Allah ya rayaka Aryan,Allah ya sa ka yi rayuwa me tsayi. Allah ya maka albarka”
Da ameen suka amsa suna kallonta.
Se yanzu ta ankara da kallon da suke mata hakan yasa ta gane ta kusan kwafsawa miƙa jaririn tayi tana cewa “Adda ba aikin da zan yi muku?”
“Alisha sarkin son aiki, ke da ki ka zo mana suna ai kya huta de ko?”
Adda ta faɗa tana dariya,murmushi tayi “kar ki damu Adda in de akwai abani in yi”
“Wanke-wanke ne ina ga baa yi ba. bari in haɗa ki da wata se ku yi tare “
“To”
Da Adda ta fita ne itama ta bi bayan ta bangaren masu aiki suka nufa nan ta kira wata tace su je su yi wanke-wanke tare da Alisha a can backyard. Hanyar backyard din suka nufa.
Yana waya ya hangota kamar daga sama,yana mamakin yaushe suka zo domin be san da zuwansu ba,yanda take tafiya kawai yake kallo,kanta a ƙasa hannunta a cikin hijabi tana tafiya kamar Sarauniya. Katse kiran yayi saboda suna daf dashi
“Hi Alisha “ kallon sa tayi domin sam bata san yana gaban su ba saboda kan ta dake kallon ƙasa
“Ina wuni uncle Haydar”
“Lafiya lau yaushe ku ka zo haka?”
Tana murmushi ta ce “eh bamu jima da zuwa ba an yi suna lafiya?”
“Alhamdulillah,se ina kuma”
Kallon wacce suke tare da tayi,ta dan matsa gefe da su
”zamu je mu yi wanke-wanke ne”
Lokaci daya yanayin fuskansa ya sauya abin ya basa mamaki ita kenan ko yaushe kullum cikin aiki kamar engine,sam bata yi kama da wacce zata juri yin aiyuka ba.
“Wai ke ko yaushe cikin aiki ki ke bakya gajiya? Yakamata a ce yau tunda suna ku ka zo be kamata a ce an sanya ki aiki ba”
Sosai ta hango rashin jin dadin hakan a cikin idanunsa wanda yasa ta yi murmushi “ Uncle Haydar kar ka manta ni fa ƴar aiki ce ban ga wani abu a ciki ba dan an sani aiki anan ba,a ganina da gidan Hajja Hauwa da nan ai duk daya ne”
Girgiza kai ya yi “ ƙananun shekaru gare ki kar ki bar wahala ya bi jinin ki Alisha”
“Wahala ya bi jinina daga lokacin da na rasa iyayena uncle “ tana faɗin haka ta wuce sa wacce zasu yi aikin tare ta bi bayanta. Da kallo kawai ya bi su har suka bace wa ganin sa,furzar da iska yayi. Yana jin ba dadi a ransa saboda haka kawai Alisha take matukar basa tausayi musamman da yaji ita din marainiya ce. Ga shi a duk sanda ze kalli fuskanta se ya hango tsantsan damuwa a cikin idanunta. Haka kawai ya ji yana son taimaka mata baya son ganin ta tana wayannan aiyukan wahalan.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
11 & 12_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
11 & 12
Wanke-wanke suke yi amma kamar kara yawan kwanukan ake yi kwanuka ne himili ga manyan kuloli da manyan tukwaye,gaba daya ta ji ta galabaita ba ƙaramin gajiya tayi ba ga yunwan da take ji. Suna cikin aiki wasu yara suka zo hannun su ɗauke da plate din glass da gudu. daya daga cikin sune ya faɗi plate din hannun sa ya fashe ya yi raga-raga a gurin da sauri ta miƙe dan ɗaga yaron, amma cikin rashin sanı tana zuwa batare da ta san akwai fasassun plate din agurin ba ta taka ya yanka mata tafin kafa, wani azaban raɗaɗin da ta ji ne ya sanyata sanya siririyar ƙara tana faɗuwa ƙasa. hawaye nan take ya fara zarya a idanunta saboda yankewan da tayi ba ƙaramin yankewa bane. Da sauri ƴar aikin da suke aiki tare tazo ta riƙe kafan tana mata sannu, sosai ta ji tsoro ganin irin yankan da tayi yasa da sauri ta bar backyard din tana cikin tafiya tama rasa wa zata kira kawai ta hango Adda da Haydar suna tsaye a compound alamun magana me muhimmanci suke yi ta nufesu da sauri
“Adda yarinyar ta ji ciwo sosai “
“Wata yarinya kenan Rashida ?” Adda ta tambayeta tana kallon ta
Cikin son tuna sunan Alisha ta ce “wannan da ki ka ce muyi wanke-wanke tare da ita Ameesha ne ko Aneesha ita ce kwalba ya yanketa sosai ne kuma”
Daga Adda har Haydar lokaci daya damuwa ƙarara ya nuna akan fuskokinsu hakan yasa basu tsaya bin ta kan Rashida ba suka nufi backyard din cikin gagagwa suna shiga suka sameta a zaune a ƙasa tana kuka ga kafarta dake ta zubar da jini
“Innalillahi Alisha garin ya haka ya faru ?“ Adda ta tambayeta hankali a tashe.
Gaban ta ya isa ya tsuguna yana riƙe kafar nata ko da idon sa ya sauka akan yankan se da ya runtse idanu saboda yanda ya ji tamkar yankan a jikinsa ne, be san dalili ba yaji ransa ya yi mugun ɓaci kallon fuskarta yai yaga kuka kawai take yi tana sauke ajiyar zuciya.
Duban Adda dake tsaye akan su fuska cike da damuwa yai ya ce “ fisabilillah Adda ya zaa yi yarinyar nan daga zuwa suna a sanyata wanke-wanke dan Allah dan annabi”
“Wallahi Haydar ni kaina ban so ba ita ce tace zata yi shisa na barta,dan Allah ɗauke ta mu je bangare na ta kofan baya bana son idon mutane ya dawo kan ta”
Tunani ya fara ta ya ze ɗauketa,tunda yake be taɓa sa hannu ya taɓa macen da ba muharramarsa ba, wannan dalili yasa ya gagara ɗaukanta se kallon yanda hawaye ke gangaro daga idanunta yake yi.
“Haydar me ka ke jira ne kam?” Ya ji muryar Adda tana masa magana saboda ta ga ya tsaya be ɗauke tan ba.
Bashi da wani zaɓi da ya wuce ya sa hannunsa duka biyu ya ɗauke ta cak kamar jaririya,Alisha da ta ji kamar zata zame ne yasa tayi saurin zagoya da hannunta a wuyansa batare da ta buɗe idanunta ba saboda bazata iya haɗa idanu dashi ba.
Bangaren Adda ya nufa da ita yakai ta wani extra room da ya kasance na saukan baki ne. kawai kwantar da ita yayi akan gado amma bata cire hannayenta da ta zagaye su a wuyansa ba, hakan yasa ya dubeta ya ga har time din idanunta a rufe suke ga hawaye da suka bushe a saman kumatunta ga wasu da suke kan saukowa.
“Alishaa bari in ɗauko First aid kit “ a hankali ta buɗe idanunta da har sun fara kumbara saboda kukan da tayi ta sauke su akan sa da sauri ta janye su sanda suka haɗa ido ta koma kallon ƙasa murya na rawa ta ce “ka yi hakuri uncle “ tana cire hannayenta a wuyansa.
“Never mind “ yace sannan ya fita a dakin, be jima da fita ba ya shigo da first aid kit ya zauna a kusa da kafarta. riƙe kafar yayi yana kallo yana jin kamar ya cire mata ciwon domin daga iya kallon kwayar idanunta ya fahimci irin azabar da take ji.
Cikin yanayı na rashin jin dadi ya ce”Amma dan Allah meyasa bazaki dena wayannan aiyuka masu wahalan ba? So ki ke ki lalace da kananun shekarunki? Manyan mata ma in suna aikin wahala basa Kyan gani balle ke yarinya dake”
Yana magana ne a yayinda yake goge jinin da ya ɓata mata kafar da cotton da spirit,yatsina fuska tayi tana bubbuga hannunta akan gadon tare da jujjuya kai cikin jin zafi saboda motsa kafar ma idan yana yi har cikin ranta take jin zafi.
“Sorry Alisha” ya faɗa a tausashe a haka tana kuka din ya mata dressing din kafan nata se de kam tasha kuka sosai da se da ta ji kanta ya fara mata ciwo,fahimtar hakan da ya yi ne yasa ya bata magani ta sha,zama yayi akan kujera yana dubanta da kyau gaba daya tayi lakwas se ajiyar zuciya da take saukewa lokaci-lokaci.
“Alishaaaa” ya kira sunan ta a sanyaye
Da shanyayyun idanunta ta kalle sa jin yanda ya kira sunan nata.
“Shin bakya da yan uwane ? I mean dangin mahaifiyar ki ko na mahaifin ki,meyasa bazaki koma wajen su ba ki ka zaɓi ki zo kiyi ta wahala?”
Shuru tayi tana lalubo karyar da yakamata ta yi masa wanda ze amince da ita dari bisa dari batare da ya yi tunanin komai ba.
Marairaicewa ta yi ta share hawayen da ya gangaro daga idon ta
“uncle Haydar lokacin da iyayena su ka mutu nima na ɗauka yan uwansu zasu share min hawayena,zasu ɗauke ni tamkar yar su ashe nayi gurguwar tunani domin ba haka yake a gurin su ba. Nasha wahala sosai a hannun su duka da zagi se da yasa na ji nima da mutuwa nayi na bi iyayena,tsangoma kuwa baa cewa komai wannan dalilin yasa na tsame kaina a cikin su na gwammaci in nemawa kai na mafita wannan dalilin yasa na nemi aiki.”
Haydar zuba mata ido yayi har ta karishe magana be iya ɗauke idanunsa a kanta ba,ya jima be ji labari da ya sosa masa zuciya irin labarin da ta basa ba,hakan yasa ya ƙuduri a niyar taimaka mata ta hanya mafi sauki.
“Shin zaki zauna tare da mu anan?”
Duk da wannan shine burinta samun gurin zama a gidan Ɗan gaske amma se ta ji tambayar ta sa ya zo mata a bankwarakwai da yasa bata san lokacin da ta furta
“Ban fahimce ka ba”
Se da ya lumshe idanunsa na yan sekonni ya buɗe sannan yace “ina nufin zaki zauna anan gidan mu?”
“Uncle to mezancewa Hajja Hauwa? Ita nake yi wa aiki,haka kwatsam in ce mata ni na dawo nan na san zata ji ba dadi sosai “ girgiza mata kai yayi yana kokarin magana Adda ta shigo ta zauna kusa da Alisha tana me ɗan rungumeta
“ Na ji komai duk maganar da ku ke yi da Haydar na saurara batare da kusan ina bayan ku ba,Alisha tabbas kin ga rayuwa bana fatan kuma a ce Allah ya bamu yanda zamu taimake ki amma mu kasa. Za ki iya zama a wannan gida namu har iya lokacin da ki ke so sannan batun Hajja Hauwa kuma na san abinda zan faɗa mata “
Sosai ya ji dadin maganar mahaifiyarta sa saboda yayi niyar yaje ya same ta ne da zancen se ga shi cikin ruwan sanyi Allah yasa ta ji su. dama ya san ba ze samu matsala ta bangarenta ba saboda Adda macece me son mutane da tausayi. “Nagode Adda Allah ya biyaki “ ta fada hawaye na sintiri a fuskanta wanda a cikin zuciyarta kuma farin ciki ne ya dabaibayeta yanzu ta samu abinda take so ta samu dalilin zama a cikin gidan Ɗan gaske.
“Haydar zancewa mahaifinka Alisha dangina ce iyayen ta sun rasu shisa ta zo ta zauna damu”
Kai ya gyada mata kafin ya fita a dakin, zama Adda tayi da Alisha tana mata hira sama-sama har bacci ya ɗauke ta. ganin tayi bacci ne yasa Adda ta gyara mata kwanciya sannan ta fita tana ja mata kofa. Tunda ta fara bacci ba ita ta farka ba se goshin mangriba ta sha mamakin irin baccin da tayi domin kuwa ta jima bata yi irin wannan bacci ba. So take yi ta fita a dakin amma ba hali bazata iya takawa ba, ta rasa yanda zatayi tai ga shi sallah take son yi amma ba damar tashi. Buɗe kofar aka yi Zainab da Ameera suka shigo a tare
“Sannu da jiki Alisha “
Suka faɗa a tare tana buɗe idonta dan dama sun kasance a lumshe ta ce “nagode dan Allah ina Hajja Hauwa?”
Ameera ce ta riƙe haɓa tana zama kusa da ita “Tabb tsohon zance ai Hajja Hauwa takai awa daya da tafiya,ta shigo miki ya jiki ta tarar kina bacci shine ta tafi”
A marairaice ta furta “na so in ganta kafin ta tafi” tayi maganar kamar zatayi kuka
“Kar ki damu inde Hajja Hauwa ce very soon za ki ganta ai, tana zuwa gidan nan da anty maryam ta koma gunta ne ma yasa ta rage zuwa” cewar Zainab. Kai ta gyada musu sannan ta roƙesu da su taimaka mata tayi alwala.
Bayan ta yi alwala, sallah daga zaune tayi sa Adda da kanta takawo mata abinci se da ta tabbatar da taci ta kuma sha magani sannan ta fita ta barta da su Ameera suna tayata hira.
Haydar tunda ya fita ya wuce office aikin binciken da ya ke yi yana zaune yana kallon CCTV footage na gidan Hashim zakewa na wannan ranan da aka yi kisan amma ya kalla yafi sau biyar be ga komai na zargi ba, hakan yasa ya fahimci cewa tabbas wannan makashin yana da wayo domin se da ya lalata cctv kafin ya shiga gidan,ɗan dukan table yayi da pen din hannun sa yana furta “shitt “ hade da shafa sajen sa. gaba daya abin ya ɗaure masa kai yau kwana bakwai da fara wannan binciken amma har yanzu ko shaida kwakwara guda daya be samu ba. abin na matukar damunsa domin tunda yake be taɓa cin karo da binciken da ya wahalar dashi irin wannan ba. saboda duk binciken da ya sa a gaba baya ɗaukan lokaci yake gama wa amma wannan babu shaida ko daya.
“Yallabai DCS zamu iya shigowa ne ko kuma mu tsaya daga waje?” Suka yi maganar suna tsaye daga bakin kofa wurga musu harara yayi ya ce “ ku tabbata a gurin “ dariya suka yi suka tafa sannan suka shigo. Auwal ne da Sadeeq sun kasance aminan Haydar ne su tun na yarinta dukkan su biyu likitoci ne.
Zama suka yi suna ƙare masa kallo kamar wayanda suka ga wani abu a jikin sa kafin suka kalli juna suka