Showing 63001 words to 66000 words out of 96407 words
Chapter 22 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
taɓa experience wani abu wai shi mari ba.
(😂😂😂😂 haaa this page hot 🥵😂)
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
33 & 34_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
33 & 34
“How dare you? I said How dare you Meenal?” Ya ƙarasa maganar da wani tsawan da ya fi na dazun.
Zuwa yanzu jikin Meenal rawa kawai yake yi tana ja da baya sanadiyyar kusantota da yake tsoronta daya kar ta sha kyakyawar mari a kumatunta da ba su taɓan experience wani abu wai shi mari ba.
Murya na rawa ta soma cewa “I’m sorry Haydar raina ne ya ɓaci”
Wani mugun kallo ya watsa mata da yasa ta jan bakinta tai shuru dan in ta ci gaba da magana akwai alamun ranta ze yi mummunar ɓaci
“Ke har ki na da bakin aibata ko zagin wani? Ke bakya kallon kan ki ne? Wai ƴar musulma wacce akwai kudin auren wani akan ta ne take wannan ɗan iskan shigar hankali kwance kuma ta fita. Ba domin Baba ba ke din sam ba kalar matar aure na ba ce. I will never married someone who is classless like you,kina ganin waye wa ne abinda ki ke yi ? Ki saka matsatsun kaya su fitar miki da sura ki fita kina nunawa kattin maza ko? Ki ci gaba kar ki fasa, amma bari ki ji wallahi se na karya ki ki ka kuskura ki ka min wannan shigar a a cikin gidana. Wannan kuma yarinyar, eh Alisha da ki ke zagi ki ke wa ƙazafi tafi ki komai,Tarbiyya, kamun kai da kunya ta san mutuncinta, kuma ta na tsare sa a matsayinta na ƴa mace. Dan haka tafi ki ko a gaban Allah mahaukaciyar banza. Ɓace min da gani kafin in canza miki kamanni a rasa gane amarya ce ko kuma patient “
Da gudu ta nufi main falo tana fashe wa da kuka, tsaki ya ja sannan ya koma jikin motar sa da Alisha ke tsaye tana kuka ƙasa-ƙasa.
Hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon yanda idonta dake rufe yake tsiyayar da ruwan hawaye, hannun sa daya yasa ya share mata shi,softly ya furta
“Yanzu ko aure mu ka yi haka za ki bar kishiyar ki ta ringa sa ki kuka baza ki kwatarwa kan ki ƴanci ba?”
(Ni de Isham this is what I have been waiting for 🥰🥰🤭ga shi an zo gun )
A sukwane ta buɗe dara-daran idanunta ta sauke su akan sa domin maganar da ya faɗa ba iya a zuciyar ta ya tsayawa ba, sai da ya haura cikin kwakwalwarta sannan ya sauko zuuu har tafin kafarta.
Ganin yanda take binsa da kallo ne yasa ya gyada mata kai cikin tabbatar mata da abinda ya faɗa
Girgiza kai tayi tana cire hannun sa daga riƙon da yai ma haɓarta
“Menene ka ke nufi Uncle ?”
Ruƙo hannayenta dukka biyu yai yana kallon ta cikin kwayar idon ta, ba ya ji ze ci gaba da ɓoye wa, ba ze iya ɓoye abinda ke ransa ba yakamata ya furzar mata ta san inda ya dosa, kar ya kasance shi kaɗai yake kidin sa kuma yake rawan sa wanda daga karshe ya tashi a tutan babu.
Se da ya sauke ajiyar zuciya ya tattaro duka courage din sa sannan ya matse hannun ta dake cikin nasa
“Yes Alisha,na gaji da ɓoye mi ki sirrin da ke raina. I love you Alisha! Kece mace ta farko da ta yi nasaran sace zuciyar da bata yarda da wata aba wai soyayya ba. You’re my first love Alisha. Kece ta farko a cikin zuciyar Aliyu Haydar,please ki ba ni dama in nu na miki yanda nake tsananin kaunar ki,don’t say no. Will you marry me Alisha ?”
Cak ta ji kwakwalwar ta ya dena aiki na wucin gadi, kallan sa kawai ta ke yi tamkar yau ne ta soma sanya sa a idanun ta,she never expect anything like this from him,wani irin luguden duka kirjinta yake yi ta na ji kamar ze faɗo ƙasa,wai ita ce yau Haydar Modibbo Ɗan gaske yace yana so. Wanda ya kasance ɗa a gurin babban makiyinta. Shin ta ya ma za ta iya yin soyayya da jinin Ɗan gaske.
Da sauri ta fisge hannun ta a cikin nasa tana girgiza mai kai idon ta kyarr cikin nasa tana hango tarın kaunar ta cikin su amma bazata amince da wannan kauna ba duk da cewa Haydar is nothing like his father and brother,he’s different komai din sa ya fita daban da nasu amma sam bazata amince da wannan bukatar na sa ba.
“Uncle Haydar dan Allah ka bar wannan maganar, i do respect you alot bana son abinda ze rusa hakan ya shiga tsakanin mu. Besides kai fa nan da kwana takwas za ku yi aure kai da Meenal Kenan ni menene matsayata ko da na amince maka?”
A karo na biyu ya kuma riƙo hannayen nata cikin tsananin son faɗa mata yanda yake son ta zama mallakin sa, ta zama uwar ƴaƴansa domin yasan she will be a perfect mother and a perfect wife,yana son farantawa ƴaƴan da ze haifa ta hanyar samo musu uwa ta gari wacce za ta tarbiyantar da su ko bayan ran sa.
“Alisha kin san de ni na miji ne an yarje min auren mace daga daya har zuwa hudu matukar zan iya riƙe su. Na rigada na yi magana da Baba ya san da nufi na. Duk gidan nan kowa ya san bana son Meenal zan aure ta ne dan biyayya. Kece wacce nake so. Bayan aurena da Meenal zan aure ki kuma har Baba na faɗawa hakan kuma ya amince”
Ja baya tai ta na kuma girgiza mai kai looking into his innocent eyes bata son ta aikata kuskuren da har ƙarshen rayuwarta ya kasance tana danasani, ba ta son hurting feelings din sa saboda shi mutum ne me kyakyawar zuciya,da ya san ita wacece da ko kusa ba ze taɓa kusantar inda ta ke ba,da ya san duk duniya ba su da enemy kamar ta ba ze yi mata maganar aure ba,da yasan ita ce makashiyar da yake nema ruwa a jallo wanted da ya jima da tsananta
Murya a raunane ta furta “noo Uncle you didn’t deserve someone like me,you deserved better in your life.” Tana faɗin hakan ta bar sa wajen tsaye kamar wanda aka shuka. dakyar ya iya mayar da kansa ya shiga motar sa kawai ya zauna yayi shuru, dama abinda ya ke tsoro kenan shisa tun farko ya gagara sanar da ita abinda ke ransa,ba ko wace mace ba ce za ta amince da hakan ba,amma be sare ba sam saboda yana ji a jikinsa bayi da matar da ta wuce Alisha.
Da gudu-gudu ta shiga falon cikin saa ba ta samu kowa a ciki ba haka yasa ta nufi bedroom din ta,tana shiga ta cire hijab ta yasar kan gado ta zauna tayi shuru kalamansa yana dawo mata sabo fil.
Saukowa tayi akan gadon ta zauna a ƙasa ta haɗe kanta da guiwa ta fashe da kuka me taɓa zuciya wanda ta rasa dalilinsa amma sure yana da nasaba da kalaman Haydar.
A fili ta ke faɗin “noo Haydar kai din mutumin kwarai ne I will never ever hurt you,idan da a ce ka san ni wacece ko kallon inda nake bazaka taɓa yi ba. You’re a good person Haydar ba ka cancanci rayuwa da mutum iri na ba,duk da cewa mahaifinka da ɗan uwanka sun min laifi amma kai ba ka san komai ba,ba ze yu in baƙanta ma ka akan laifin da ba kai ka yi sa ba. Maganar soyayyah ko aure a tsakanin mu babu shi ,na zo gidan nan ne saboda Ɗan gaske da Sameer ina gama aiki na kuma zan bar ku cikin firgici da tashin hankali.
Baka aikata min komai ba in har na cutar da kai Allah se ya kamani da laifin hakan” tai maganar cikin kuka mara sauti.
Se da ta kwashi kusan mintuna ashirin zaune sannan ta shiga toilet ta sakarwa kan ta ruwa se a nan ta fara jin ta fara dawuwa hayyacinta amma duk wanda ya ganta yasan tana cikin damuwa kuma ta yi kuka.
Sallah isha da ba ta yi ba a gidan inna ta samu ta gabatar,gun Adda ta je ta dan ta san ba su san da dawuwar ta ba, saboda lokacin da ta shigo bangaren Addan babu kowa hakan ya na nuni da tana dakin ta kenan.
Tana zaune akan tsakiyar gadon ta, hannun ta riƙe da Aryan yaron Maryam ta na yi masa wasa murmushi ta yi tana zama akan kujera tare da gaishe ta
“Kin dawo kenan?ai ɗazun su Yusrah su ka shigo gurin ki da yake ba su san kin fita ba “
“Ayyah,na dawo Adda”
Se yanzu ta ɗago ta kalli fuskar ta jin yanda muryarta ke fita a disashe,kallo daya ta mata ta fahimci akwai abinda ke damun ta hakan yasa ta faɗin
“Alisha shin akwai abinda yake damun ki ne? Kamar ma kin yi kuka ko?”
“Ah ah Adda ban yi kuka ba. kai na ne kawai yake ɗan min ciwo?”
Kallon ta kawai ta yi badan ta yarda ba,bata son takura mata ta faɗa mata amma ta san karya ta mata babu wani ciwon kai da ke damunta
“Kin sha masa magani de ko?”
“Eh nasha” ta yi saurin faɗan hakan ta na ɗan ragwafowa ta karɓi Aryan a hannun Adda.
“Adda ki samu ki huta zan tafi dashi part din su Ameera”
“To shikenan dama kamar kin sani tun ɗazun na ke son rintsawa “
Murmushi kawai ta yi ta fice,da kallo Adda ta bi ta har ta fita ɗauke da Aryan
Girgiza kai tayi cike da tsananin tausayin ta “Allah ya yaye miki damun ki Alisha am,yarinya ƴar ƙarama amma damuwa da tunani sun mata yawa “
“Ashe kin dawo yau kafata biyu a bangaren Adda ai ba ki nan”cewar Zainab
Zama tayi tana kwantar da Aryan akan cinyar ta tana fara yi mai wasa “Wallahi kuwa na yi tunanin kuna bacci ne shisa ma banzo na sanar muku ba”
Yusrah dake latsa wayarta ne ta ce “Ayyah mu ma bayan fitan ki mun raka ya Sameer Government house kin san yana neman mukamin shugaban matasan Gombe,nan da yan satuttuka zaa fara gabatar da zaɓe “
A zahiri murmushi ta yi “woww gaskiya na taya sa murna wish him all the best “
Amma fa a cikin ranta dariyar ƙeta kawai ta sake dan tayi murna da jin wannan labari, domin ta ƙuduri aniyar tarwatsa Sameer ko ta wacce hanya.
“Kana ji kana gani zaa ɗauki mukamin shugaban matasan Gombe a bawa abokin takaranka “
Ta faɗa cikin ranta,muryar Zainab ta ji tana
“Yusrah ina falo kawai naga shigowar mutumiyar ki tana kuka ta shiga dakinta da gudu ko ita da waye se Allah,amma ni fa na fi tunanin Uncle Haydar ne ya kaɗota ciki”
“Hmmm Allah shi ƙara ai, ba ta ga komai ba ma tukun. Ai wallahi ina mugun tausayin Uncle da aka haɗa sa da wannan ballagazar wacce ko ruwan zafi bata iya tafasawa ba a haka ne zata kula dashi? A haka ne zata sauke hakkinsa da yake kanta. Wallahi Uncle be yi deserving mace irin Meenal ba sam. Yanda ya ke me tausayi da kulawa kamata ya yi ya samu mace da ta dace dashi wacce za ta so shi tsakani da Allah “
Cewar Yusrah
Ameera se yanzu ta ce “hmm Allah de ya kyauta amma Uncle in ta ishe sa da mugayen halayyanta za ta yabawa aya zakin sa ne”
Ita de tana jin su amma ko kusa ba ta sako mu su baki a maganar su ba domin ba abinda ya shafeta bane hiran su ne na ahali dan haka tayi shuru kawai tana ɗan bubbuga bayan Aryan da yake son fara kuka.
Yusrah da iya gaskiyar ta ta furta “ na rantse da Allah da ina da ƙawar da Uncle ze kwarewa wallahi da se na tarwatsa auren nan,kawai de kun san Uncle inde akan mata ne tofa shi makaho ne sam ba sa gabansa. Tun da ku ke kun taɓa jin yau ga buduwarsa?”
Duk su biyun girgiza kai suka yi, Yusrah taci gaba da faɗin
“ you see! Uncle Haydar din mu har yanzu be samu the type of woman he wants ba,an zo an wani haɗa sa da wannan bunzumar. Wai ma da taci shegen adoh da daren nan ina za ta je haka ?”
Ameera na yatsina fuska ta ce “hmmm me zaa fasa Allah de yasa bayan auren su ta dena yawon bin maza”
Izuwa yanzu Alisha bin bakunan su kawai take da kallo ganin yanda suka zauna suna zagin Meenal da kuma faɗar wasu halayen nata wanda ita bata ma san da su ba,miƙewa ta yi ta musu sallama ta je ta kai Aryan gun maman sa Sameer na zaune a falon ta same su, miƙa wa Maryam shi ta yi sannan ta fita.
Haka kwanaki suka ci gaba da tafiya har yau yayi saura kwana biyu ɗaurin auren Meenal da Haydar,a bangaren Alisha kuwa tundaga wannan ranan da Haydar yai confessing son da yake mata ta fara wasan ɓuya dashi, yanzu rabon da ya sa ta a ido tun wannan rana,duk wata hanya da ze haɗa ta da shi ta datse in de yana gida tofa ko kusa ba ta yarda ta fito a dakinta,a waya kuwa ko ya kira ta ba ta ɗagawa har ya dena kiran ya zubawa sarautar Allah ido.
Baƙi har an fara taruwa gıda ya soma tara al’umma,Meenal kuwa gobe ne za ta koma gidan su tunda auren saura kwana biyu ne kacal.
Misalin tara na dare tana zaune ita daya cikin dakinta a tsakiyar gado hannunta riƙe da Qur’ani tana rera karatu cikin zazzakar muryarta me dadin sauraro muryar na fita a sanyaye ƙasa-ƙasa,duk da karatu ta ke yi amma tana jiyo muryoyinsu a falon Adda se hira suke yi kamar yanzu ne gari ya waye musu ko kuma yau ne ranan bikin,muryar su Yusrah duk ya fi na kowa yawa zama ka yi tunanin su kaɗai ne a cikin Falon bayan kuma Adda,da Maryam duk suna ciki amma su da yake maganar su a tsanake suke yin sa shisa baa jiyo nasu muryar.
Maida qur’ni mazauninsa tai bayan ta kammala karatun, ta ɗauki babban mayafi ta yafa akan doguwar rigar da ta saka baka. ta sa silipas ta fita a dakin.
Cikin tafiyanta me ɗaukan hankali ta isa cikin falon duk suka ɗago suna kallan ta har da Haydar da ko kusa ba ta yi tsammanin ganin sa a wannan lokacin ba,sosai suke kallon juna rabon sa da ita tun kwana biyar se yau Allah ya yi ze sa ta a ido saboda wasan ɓuyan da take yi dashi.kawar da na ta idon ta fara yi ta nufi gun Adda ta zauna kusa da kafanta tana gaishe ta.
“An fi to Kenan Alisha ai na ɗauka ma ko bacci ne ya ɗauke ki “
“Ah ah ido na biyu Adda”
Satan kallon sa tayi ta ga yanzu ba ita yake kallo ba danna wayarsa yake yi
“Barka da dare Uncle”
Be yi tsammanin za ta yi mai magana ba hakan yasa ya ɗago kyawawan idon sa ya kalle ta dasu kafin ya amsa
“Lafiya “
Hiran su suka ci gaba da yi amma banda Alisha da Haydar da duk suka yi shuru kamar basa cikin falon,ita Alisha na wasa da yan yatsunta while Haydar yana danna wayarsa amma time to time yana ɗagowa ya kalle ta.
Wani sako ne ya shigo wayarsa da bakuwar number,shiga yayi ya ga an tura masa da video har na tsawon minti biyu ba tare da yayi tunanin komai ba ya yi playing din video din,fuskar Meenal ya ci karo dashi zaune akan cinyar wani katon na miji jikin sa babu kaya se iya boxer ita kuma tana sanye da bakar Egyptian Abaya amma rigar ya sauko kasa dede cinyarta fararen nonuwanta dake cikin bra duk a waje, hatta pant dinta ana gani, hannun ta yasha lallen bikin da aka mata jiya se shafe juna suke yi. Runtse ido yayi yana jin babu dadi bawai dan yana son ta ba se dan bakin cikin wai shi ne ze auri wannan abar,idanunsa kafe akan wayar ya ce
“Wallahi ko Baba ze tsine min bazan taɓa auren wannan yarinyar ba”
Da mamaki kowa yake kallon sa jin kalaman da ya furta dan babu wanda ya tsammace haka musamman da ya kasance yau aure saura kwana biyu.
“Lafiyan ka kuwa Haydar? ya za ka ce ba za ka aure ta ba jibi ne fa auren nan”
Adda ta faɗa tana duban sa da kyau. Shima itan ya kalla be ce komai ba ya wurgawa Yusrah wayar ta sa ai kuwa ta yi caraf ta cabe,bayan ta kalli video ne ta hau faɗin
“Innalillahi wainnailaihi rajuun! amma wallahi Meenal ta ɓata wayon ta,yanzu ana auren ta saura kwana biyu ma se da ta fita ta haɗu da wani a waje. Allah Uncle da gaskiyar ka. Allah ne kaɗai ya san me kuma za ta ci gaba da aikatawa in ka aure ta”
A wannan sa’in hakurin Adda ya ƙare burin ta be wuce ta ga wani video ne wannan da har ya sa su wannan zantukan.
“Ke miƙo min wayar nan “
Miƙa mata wayar Yusrah tai bayan sun gama kallo da su Ameera.
Sosai ta