Showing 96001 words to 96407 words out of 96407 words
Chapter 33 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
da ita suka tsaya suna zare face mask din su ƙasa fuskar su ya bayyana
Kallon fuskar ɗan uwan na ta ta yi kana ta dubi Sameer
“Wannan sunan sa Zayyad Sagir Lelewal, ni kuma sunana Alisha Sagir Lelewal “
Wani jiri ne ya ji na neman kayar dashi cikin tashin hankali yake kallan su su biyun. tabbas ya san fuskar Zaid, kuma daga fuskar Zaid ya ke hango fuskar Alisha saboda yanda suke tsananin kamanni da juna,hankali a tashe jikin sa ya soma tsatstsafo da zufa ya nu na su da yatsa
“It can’t happen. wannan ba gaskiya bane,dama ba ku mutu ba? Amma ai da hannu na na kashe ku, Noo it’s a lie” ya faɗa yana ja baya.
Slide smile ta sake “ ka yı mamaki ko? To ba mu mutu ba, Allah ya ƙara mana tsawon kwana ne dan mu ɗauki fansar abinda ku ka aikata mana, kuma Alhamdulillah ana samun nasara tunda na samu nasaran Kawar da Zakewa sannan na Kawar da Peter, cikin rashin saa kai da ya kamata ka zama a karshe yanzu kai ne na uku a madadin katanga, kisan ka sai yafi na sauran muni da iznin ubangiji, kai ne mutumin da ya rabani da mutuncina. ka keta min haddina a gaban iyayen da su ka tsuguna suka haifi ni, na fi tsanar ka Sameer shisa mutuwarka ze fi na sauran taɓa zuciya da muni“
Mukut ya haɗiye wani yawu me ɗaci da zafi har yanzu jikin sa rawa yake dakyar ya iya, furta
“Dama ke ce ki ka kashe Zakewa da peter? To wallahi ƙarshen ki da makircin ki ya zo karshe, zan fita yanzu in sanar da Haydar makashin da ya jima yana farauta ba namiji bane macece, kuma se ya kama ki an yanke miki hukuncin kisa, ki sanı matukar ina raye bazan taɓa barın ki auri ɗan uwana, ba domin ba da zuciya daya za ki aure sa ba “
Ya faɗa yana isa bakin kofa ya soma kokarin buɗewa
“Kana tunanin yanda ka san komai dangane da ni za ka ci gaba da rayuwa ne? Ba zan taɓa barinka ka tona min asiri ba Sameer,Ya Zaid ku yi abinda ya dace”
Ta fada tana kallon su biyu din.
Alhamdulillah anan na kawo karshen book one, book two din na kudi ne duk me bukata ya min magana ta whataspp 08166018849 Mrs Isham or 09024503194 Mrs Isham.