Showing 6001 words to 9000 words out of 96407 words
Chapter 3 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
sunanta a matsayin itace ma mallakinsu
“Papa what are you doing?”
“Ina mayar da komai a sunan ki ne darling “
“Amma meyasa haka,there’s no need for all this papa”
Be ce mata komai ba har ya gama ya haɗa komai a guri daya takaddu masu muhimancin kuma ya sanya su a cikin wata ƴar ƙaramar jaka tare da duk wasu ATM nasa dana Mommah ya damka mata su a hannu.
“Ko me ze faru ki tabbatar baki yasar da wannan jaka ba kin ji darling?”
“Papa menene yasa ka ke yin duka wayannan abubuwan? kuma sannan menene yasa ka ke son in bar Ƙasan nan? Shin menene abinda ya haɗa ka da wayannan mutane kuma su waye su?”
Sauke numfashi ya yi “ duka zan baki amsarki yanzu kuma zan faɗa miki sunan su,sannan a cikin jakan nan akwai duka bayanan su. Hon. Modibbo Ɗan gaske,Hon Hashim zakewa, Chairman Habibu Katanga,chukuemeka Peter,Dr Jamal,Dr Idris Ali,Dr Ahmad wayannan mutane sune suke son ganin bayana. Se kuma babban ɗan Hon Ɗan gaske wato Sameer Ɗan gaske.” Nan ya kwashe komai ya faɗa mata be boye mata ba. Sannan yakara da cewa
“Alisha darling tabbas Ina ji a jikina akwai abinda ze faru zuciya na se bugawa yake yi da karfi ko bayan rai na…”
“Shissh papa please ka dena irin wannan maganar zaka sani kuka. Babu abinda ze faru da izinin Allah babu abinda zasu iya mana Allah ya fi su. İn sha Allah se asirin su ya tono. Gaba dayan mu muna cikin damuwa saboda halin da ka ke ciki,papa ko abinci mun gagara ci pls ka saki ranka ka zo mu ci abinci Aryan tun dazun yake mana kuka”
“Am sorry bana son ku shiga damuwa saboda ni,maza mu je yanzu is time to chill “ya faɗa yana miƙewa ya ɗauke ta sama yana hajijiya da ita dariya kawai take yi haka suka fito falon. suna ganin su a haka Zaid da Aryan suka miƙe suna ihun murna tare da nufan mahaifin su suka rungumesa murmushi kawai Mommah ta yi.
Zama suka yi suka ci abinci tare,.. sannan suka buɗe sabon babi na hira,kallon ƴaƴan nasa kawai yake yi jikin sa na faɗa masa yau shine rana na karshe da zaka sake ganin su.
Har karfe sha biyu suna falo suna hira Mommah ne tace kowa ya tafi yaje ya kwanta shi de Aryan maƙe kafaɗa yayi yace yau tare da su Papa ze kwanta haka kuwa aka yi duk suka shiga suka kwanta.
Ko da ta shiga dakinta jakan da Dr ya bata ne ta sanya shi a ƙasan filo sannan ta yi wanka ta sa kayan bacci. Ta kwanta.
BAƘIN DARE
karfe biyun dare wata baƙar jeep ya yi packing a kofar gidan Dr Sagir aka kwankwasa me gadi yana buɗe wa aka soka masa wuka a wuya nan take ya faɗi ba rai. Wasu mutane ne jifga-jifga sanye da bakaken kaya suka shigo cikin gidan su uku. Se kuma Wasu guda hudu suna sanye da kananan kaya amma sun rufe fuskokinsu. Ta kofar baya da ya kasance a buɗe suka shiga cikin falon,wutar gidan gaba daya suka kashe,sannan suka kunna hasken wayoyinsu wanda be bayar da wani gamsashiyar haske ba. nan suka nufi bedroom din Dr Sagir suna shiga suka same sa yana kwance sun sa Aryan a tsakiya suna bacci. daya daga cikin su ne yasa gindin bindiga ya daki kan sa sallati ya sanya ya miƙe zaune yana jin kan sa na sara masa. A firgice Mommah da Aryan suka miƙe zaune ganin wasu mutane a tsaye akan su yasa tsoro ya kamasu rungume Mommah Aryan yayi.
Se ta su suka yi da bindiga “maza ku tashi mu tafi falo “ ƙin tashi suka yi hakan yasa suka cukumi wuyan Dr suka fita dashi waje,,haka sauran ma suka damki gashin Mommah suka fitar da ita Aryan kuma dama yana rungume da ita. A tsakiyar falo suka wurga su.
Kallon Ɗangaske da ɗansa da kuma sauran yan siyasan suka yi zaune hakimce akan kujera suna sakar masa murmushi yai.
“Likita bokan turai. Dama na faɗa maka ai zaka jawa kan ka da iyalinka.”
Cikin mawuyancin hali domin ba ƙaramin buguwa kansa yayi ba yace “Ɗan gaske na roƙe ka da ka cire iyalina a cikin maganar mu,faɗan ku da ni kaɗai ku ke yi. ku yi min komai amma dan Allah ku cire su”
“Kai ka bukaci haka ai har office din ka muka zo da Babana saboda a yi sulhu amma ka yi mana koran karnuka “ cewar Sameer Ɗan gaske.
“Son, dena ɓata yawun bakin ka. Wai Ina sauran yaran nasa maza ku fito min dasu gaba daya” yana faɗin haka wayannan masu kiran samudawan suka shiga dakin Alisha tana bacci ta ji an jawo ta akan gado an wurgata tsakiyar falo da gudu ta nufi Dr hankali tashe ganin iyayen ta gurfane a ƙasa ga wasu mutane zaune a falon su . Duk cikin su mutum biyu ta gane wato Hon Ɗangakse da ɗan sa suma saboda goggling da tayi ne yasa ta gane su.ga shi gidan dulum babu enough light se ka kurawa mutum ido sannan zaka gansa.
“Papa what’s going on “
Ta faɗa murya na rawa.
“Kiyi shuru darling “
Suna haka a ka fito da Zaid duk da ganin abinda ke faruwa amma da yake sarkin zuciya ne yasa ya hau zagin su daya daga cikin su ne ya buga masa gindin bindiga akai shima nan take ya zube kan guiwowinsa jini ya soma zuba akan sa.
Ihu Mommah,Alisha da Aryan suka saka suna rarrafawa izuwa wajensa suna kuka musamman ma Aryan kuka yake yi sosai jikinsa har rawa yake yi. Dr kam kukan zuci yake yi ji yake yi tamkar ya hadiye zuciyarsa ya mutu tsabar dacin da yake ji a ransa.
“Wai ku wasu kalan marasa imani ne? menene abinda yayana ya muku?Wallahi Allah se ya saka mana da wannan zaluncin “
Ta faɗa tana kuka kamar ranta ze fita. miƙewa Sameer ya yi yana murmushi tare da binta da mayen kallo saboda rigar baccin jikinta yana da tsantsi ya kwanta a jikinta luf.
Yana isa gabanta yasa hannu ya damki gashinta ya dauke ta da maruka lafiyayyu guda biyu da seda hancinta da bakinta ya fashe idonta kuma ya tara jini.
“Wato akan ki ne mahaifin ki ya ci mana mutunci ni da mahaifina ko?”
“Kai ɗan la’ananne ka sakar min kanwata Dabba mara imani tsinanne jahili wanda be san darajar mace ba” cewar Zaid yana huci,kallon wayannan kattin yayi yace “ku dake sa har se ya mutu” yana basu umarni kuwa suka soma dukan Zaid da bindiga tamkar Allah ne ya aiko su. duk da irin dukan da suke mishi ko tari be yi ba balle ihu se zagin Sameer da yake yi. Duka suka masa ko ina na jikinsa jini kawai yake zubarwa numfashinsa dakyar yake iya fitowa.
Sameer kuwa har lokacin yana damke da gashin Alisha da take ta kukan wahala. Mommah kam zuwa yanzu zuciyarta yana barazanar bugawa saboda bakin cikin. Dr kuwa kuka yake yi yana rokan Allah da ya ɗauki rayuwarsa domin ba ze juri ganin yanda ake azabtar masa da ƴaƴansa ba. Falon kuwa kukan Aryan ne ya cika musu kunne se tsawa suke masa amma yaki yin shuru hakan yasa
Hon Hashim zakewa ya fito da ƴar ƙaramar bindiga mara ƙara a aljihunsa be yi wata wata ba ya harbi Aryan a goshi nan ya faɗi a mace jini na zuba a kan sa. Wani irin ihu Mommah ta sanya tana ɗaukan Aryan da ya riga da ya mutu ta ɗaurasa a cinyarta tana kuka tare da kiran sunan sa.Alisha kuwa zuwa yanzu kwakwalwarta yana son dena aiki kallon Aryan dake kwance a mace take yi tana kiran sunan sa a hankali ga Sameer da ke riƙe da gashin ta cizo tayi masa a damtsen hannunsa da ya sashi sakinta ba shiri da gudu ta isa inda Mommah take da Aryan ta riƙe sa tana kuka. Zaid kam duk abinda ake yi dishi-dishi yake kallon su. Muryoyinsu ma kamar a mafarki haka yake jin sa a kunnuwansa hawayen azaba ne suke masa sintiri.
“Wayyo papa sun kashe Aryan sun kashe mana Aryan din mu” cewar Mommah tana riƙe da setin zuciyarta.
“Ku dena ɓata lokaci ku gama dasu “ cewar Ɗan gaske. Finciko Alisha Sameer yayi ya wurgata a tsakiyar falo ya zare belt din wandon sa yana kallon cikin kwayar idanun Dr cikin muryar buguwa na mashayan giya yace
“Ai dama na gaya maka a gaban idanunka zan yi yanda nake so da ƴarka”
“Dan Allah Sameer kar ka yi haka wallahi yarinya ce ƙarama. kar ka aikata haka Sameer dan girman Allah ka bari “
Dr ya faɗa yana haɗe hannayensa alamar roƙo amma ko sauraransa be yi ba ya dunfaro Alisha dake ja da baya tana girgiza masa kai. Mommah kam zuciyar ta zuwa yanzu ya dena aiki kawai tana zaune ne amma bata iya gane komai
Suna ji suna gani a gaban idanun su Sameer ya yiwa Alisha fyade ihunta gaba daya ya cika gidan sunan Papa,Mommah da Zaid kawai take kira amma babu taimako. Wasu hawayen bakin ciki ne suke zubo wa Mommah wanda a take ta hadiyi zuciya ta mutu a zaune ga Aryan a cinyar ta.
Da idanunta da suka kumbura take kallon fuskan iyayen na ta numfashinta na fita dakyar
“Pa..pa “ ta Kira sunan Dr dakyar amma be amsa mata ba se kukan da yake yi jini na zuba a hancinsa
“Ya Zaid “ shima shuru idanunsa a rufe amma yana jin sautin kukanta a cikin kunnensa.
“Mommah” tana zaune idanunta sun kafe suna kallon guri daya ta riga da ta mutu.
Gyara jikinsa Sameer yay yana karban bindiga a hannun Hon Hashim zakewa ya yiwa Dr harbi biyu a ciki daya a kai,Mommah da ta riga da ta mutu ma se da ya harbe ta a goshi sannan ya je kan Zaid ya harbesa a ciki duk suka mutu yayi saura ita kaɗai. Dakyar ta rarrafa ta isa inda Dr ke kwance matacce tana jijjigasa tana kiran sunan sa amma shuru haka jikinta na zubar da jini ta nufi gun Mommah nan ma shuru haka ta dinga bin su daya bayan daya amma duk sun mutu.
Ihu ta sanya tare da sakin marayan kuka tana kiran sunan su “kar ku min haka, kar ku tafi ku bar ni a wannan duniyar dan Allah ku tashi ku tashi papa Mommah Aryan Zaid ku tashi “
Haka ta dinga kuka tana kiran sunayensu kamar zararriya. dariya suka sanya chukuemeka Peter ya ce “waya gaya miki kema zaki rayu? Ai inde muka bar ki asirin mu ya tonu”
Yana gama magana itama suka mata harbi biyu a ciki ta fadi itama a cikin gawawwakin iyayenta.
“Ku hanzarta ku sakawa gidan wuta ku kona ko Ina yanda ba zaayi zargin wani abu ba”
“To yallabai “ fetur suka watsa a ko Ina a cikin gidan sannan suka fita waje suka kyasta ashana suka jefa a ciki nan take ko Ina ya kama da wuta balbalbal. Dariya suka yi suka tafa sannan suka shiga motar suka tafi.
Kar ku manta wannan tuna baya ne wato waiwaye.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
5 & 6_*🦋FANSAR MACE🦋*-
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi, to Kar ku yi ƙasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin nawa 08166018849 Mrs isham domin a tallata muku hajar ku.❤️😊
5 & 6
A hankali ta buɗe idanunta ta ga yanda falon yake ci da wuta Dr Sagir da su Mommah har wuta ya soma kona su dakyar ta iya tashi tsaye tana kallon fuskokinsu tana kuka,tana rike da cikin ta inda aka harbeta se zubar da jini yake ta nufi inda gawan Zaid amma se kayansa kawai ta gani alamun wuta ya cinye gawarsa.
“Allah ya jikan ku iyayena da yan uwana wallahi se na ɗau fansar kisan gillan da aka muku”
Ta faɗi hakan tana nufan dakinta dakyar take iya taka kafarta. tana shiga ta ga nan ma wuta ya na ci a dakin kayayyakinta da su laptops din ta duk sun kone. pillow ta ɗaga ta ɗauki jakan da Dr ya bata ta fita ta kofan baya,titi ta nufa tana tafiya jiri na ɗibanta. Wata tsuhuwa ce da ta fito domin yin bara saboda lokacin har karfe uku ya wuce ta hango Alisha da sauri ta nufe ta
“ ke kuwa yarinya me ya same ki su waye suka miki haka?”
“Dan Allah ki taimaka min ki ɗauke ni daga man. zan baki ko nawa ki ke so matukar zaki ɓoye ni,zan baki daga daga abinda yayi million daya har zuwa dari “ ta na faɗin haka ta suma zata faɗi tsohuwar ta yi saurin riƙota. Tana ƙarewa anguwar kallo. Mutane sun fara fitowa suna kiran taimako saboda yanda wuta ke cinye gidan se ihun mutane ke tashi babu wanda ya ankara dasu. Da sauri matar ta bar gurin da Alisha.
Gari da ya waye labari ya karaɗe ko Ina kancewa gobara ya tashi a gidan Dr Sagir Lelewal ya kashe sa da matar sa da yaransa. Sosai aka cika da alhinin mutuwar Dr da iyalansa,mutuwarsa tabbas ya taɓa zukatan al’umma saboda mutum ne me taimako. Talakawa sun yi kuka sosai da wannan rashi haka aka zo aka kwashi tokansu aka yayyafa ruwa aka musu sallah aka binne su. Yan uwan sa da suke kumo sun zo zaman makokin dan uwan su. sosai suka yi kuka saboda wannan babban rashi ne da aka yi. Haka social media ya yaɗu da labarin mutuwarsu ana saka hoton Dr da kuma Zaid saboda ba kowa ne yasan Alisha ba. Haka aka yi ta zaman makokinsu batare da zargin komai ba saboda babu wanda yasan gaskiyan abinda ya faru se Allah.
CI GABAN LABARI
“Wayyo dan Allah kar ka kasheni,ni fa me gadi ne kawai a wannan gıda. Ka taimaka ka yi min rai ina da iyali kuma da ni kaɗai suka dogara. Ka rufan asiri kamar yanda Allah ya rufa maka.” Mai gadi ya gama wannan zance cikin tsananin tashin hankali domin kuwa bindiga ce a kansa kunama ce kawai baa harba ba,wanda ke riƙe da bidigar kuwa yana sanye ne da bakaken kaya, daga sama har ƙasa se wani iriyar fuska da ya sanya. A gefe da su kuwa gawan me gidan ne da wannan makashin ya kashe se matar me gidan da ya liƙewa baki da gam se kuka take yi tamkar ranta ze fice yabar jikinta saboda ganin mijinta kwance ƙasa matacce,a dayan gefen kuwa ɗan jaririnsu da be wuce wata bakwai bane ke ta tsalla ihu amma babu halin uwar ta ɗauke sa.
Kallon me gadin makashin ya yi kafin ya sake gyara bindiga akan sa yana kokarin harbawa kenan aka fara kiraye-kirayen sallah asuba tare da soma jin sahun takun mutane wannan dalilin ne yasa ya daki me gadin da gindin bindigar akai nan take ya faɗi ya suma shi kuma makashin ya sanya bindigar a aljihunsa na baya sannan ya fice a farfajiyar gidan yana me bin kofar baya da gudu cikin saa kuwa ya bar area batare da kowa ya gansa ba.
“Dan Allah driver ka hanzarta wannan irin tafiyar da ka ke yarinyar nan zata iya haihuwa a motar nan matukar baka yi sauri ba.”
“In sha Allah Hajiya zamu isa asibitin nan da wuri”
Cewar driver yana ƙara gudu kamar yanda ta basa umarni.
“Washhhhhhh,Innalillahi zan mutu. Dan Allah Hajja hauwa ku cire min abinda ke cikina in ba haka ba zan mutu dan azaba. Wayoooo ni Maryam yau karshe na yazo.”
“Haba ke kuwa se ka ce akan ki aka fara ciki da haihuwa maryam, a ce kina naƙuda amma ba za ki dinga wa kan ki fatan alkairi ba,to babu kyau ki dinga addua kawai.”
Cikin azaban naƙuda maryam bata ko kula ta ba se ma yarfa hannu da take yi kawai tare da dafe maranta da ta ji yana mata barazanar rabewa biyu.
Duk irin gudun da driver yake shararawa fa hakan be sa hajja hauwa ta yi shuru ba gani take tamkar a hankali yake tafiya saboda yanda maryam ta kiɗima mata hankali da sambatun wahala.
Waro ido Driver ya yi lokacin da idon sa ya sauka akan inuwar mutum a tsakiyar titi ya tsaya kamar gunki ya ki matsawa. sa'ke sitiyarin motar ya yi cikin mamakin abinda ya gani ya juya ga hajja hauwa yana faɗin
“Hajiya kin ga mutum a tsakiyar titi”
Watsa mai harara ta yi cikin masifa ta ce “ehhh Kwarai yau na yarda baka da hankali labaran,waye ze tsaya akan wannan titin a irin wannan lokacin dal….”maganar makale mata a baki ya yi lokacin da ta ankara da driver labaran fa ya sa'ke sitiyarin motar ne a yayinda ya juyo gareta yana mata magana. cikin tsananin tashin hankali ta soma rafka salati domin shine kawai mafita saboda ta riga da ta hango mutuwa ƙarara da idon ta.
“Innalillahi wainna’ilaihi rajuun labaran yanzu saboda kana son ka kashe mu shine ka sake sitiyarin motar ?”
Ta faɗa tana dukan kirjinta hatta maryam da ke naƙuda se da gabanta ya faɗi lokacin da ta ji abinda hajja hauwa ta furta.nan ta ji ɗan cikin ta ya yi wani irin juyawan da se da ta koma ta kwanta bata sanı ba.
Cikin gaggawa labaran ya dawo hayyacinsa ya