Showing 15001 words to 18000 words out of 96407 words

Chapter 6 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3606

gari tunda ta idar da sallah, ta soma aiki ga baƙi se shigowa suke yi se ta yi mopping yara su zo su yi ta ɓatawa, baƙin ciki kamar ta mutu amma haka zata shanye ta sa'ke gogewa. so take yi ta gama kafin karfe sha daya yayi dan tana da bukatar ta fita,ga shi abincin da aka dafa sam ba cimarta bane,tuwo ce da kuma cus-cus kuma ita bata cin tuwo balle cus-cus, hakan yasa har yanzu bata karya ba. Sallama Adda da su Zainab suka yi suka shigo, har ƙasa ta tsuguna

“Adda ina kwana ?”

Fuska cike da fara'a Adda ta amsa gaisuwan nata,a gefe daya kuwa tayi mamakin ganin ta a gidan har yau,sannan gashi har aiki ma take yi ta ce “lafiya lau Alisha ya karfin jiki?”

“Alhamdulillah “

“Masha Allah sannu ko “ ta faɗa tana shiga ciki miƙewa tayi ta ci gaba da aikin ta. kallon agogo tayi ta ga karfe goma da mintuna arba’in. sosai ta ƙara sauri gurin ganin ta kammala aiyukanta a gaggauce.

“Sannu da aiki ƴar albarka”

Cikin sanyin murya ta ce “Sannu Hajja Hauwa”

“Alamun ki sun nuna har yanzu ba ki karya ba ga shi ina son in aike ki. Kin san tsohuwar kasuwa ai?”

“Bakomai Hajja Hauwa har yanzu ban fara jin yunwa ba, ki ka wo aikan in na dawo zan ci abincin “

A tsanake ta kalle ta cikin damuwa da nuna kulawa “kin tabbata ?”

“Eh ki kawo kawai”

Murmushi tayi saboda hankali da nutsuwar yarinyar yana burgeta, uwa uba girmama manya ga sanyi.

Faɗa mata abubuwan da zata siyo tayi sannan ta bata ATM tare da dubu daya kudin napep.

“A dawo lafiya kar ki jima kin ji?”

“To Hajja Hauwa”

Dama riga da skirt ne a jikin ta se babban gyale da ta yafa da ya rufe mata jikin. Daki ta koma ta ɗauki doguwar hijabi har ƙasa golden yellow, ta sanya sannan ta ɗauki niqab da ta gani a cikin wardrobe din ta ɗaura kyakyawar kwayar idonta ne kawai a waje.

Fita tayi a falo tana tafiya cikin nutsuwa ta hango sa yana tahowa hannun sa na riƙe da hannun yara maza guda biyu

“Ina kwana uncle Haydar?”

Hakikanin gaskiya da farko be gane ta ba se da ya kai duba ga fuskarta,kyawawan fararen idanunta ya ci karo dasu sakamakon sune kaɗai suke a bayyane. kwayar idanunta da yana ganinsu ya ji gabansa ya faɗi. tabbas ya san wani me irin idanun nan amma waye?sam ya kasa tunawa da wanene wannan.

“Lafiya lau Alisha “ ya amsa mata yana wucewa itama ta wuce. Me gadi ya buɗe mata kofa bayan ta gaya masa Hajja Hauwa ce ta aike ta.

Ko da ta fito bakin titi napep ta tara “malam anguwa uku” kawai ta faɗa ta shige batare da ta tambayesa kudin sa ba.

Tafiyar mintuna talatin suka yi suka iso anguwa uku nan ta dinga masa kwatance suka dinga shiga can ciki har kusa da kwari,nan suka iso wani gida me madaidaicin kyau flat a kusa da kwarin. 1k din da Hajja Hauwa ta bata ta miƙa masa sannan ta sauka. Se da ta ga babu kowa a area sannan ta shiga gidan.

Bata tsaya ko ina ba se a falon da ya kasance matsagaici yana da kyau dede gwargwado da ɗan furnitures masu kyau babu kowa a falon. hakan yasa ta fahimci ta na daki bata shiga dakin ba, ta shiga dakin da ya kasance nata,tana shiga ta sunce niqab din da hijab ta ajiye su kan gado. Daki ne me girma dake ɗauke da gado da katifa se babban mirror ga wani babban table da aka jera takaddu da computers akai. a bangon kuwa hotunan mutane ne da yawa a jiki wanda ko wanne hoto a ƙasan sa akwai rubutu ƙanana.Hulan dake kanta ne ta cire tana warware gashinta ya sauka a gadon bayanta gwauron numfashi ta sauke kafin ta saki murmushi. Table din ta nufa ta ɗauki maker ta nufi wajen da wayannan hotunan suke manne,wayannan hotunan bana kowa bane face na wayannan mutane takwas Hon zakewa shine hoton sa yake a farko,Chaiman Habibu katanga,chukuemeka Peter,Dr Jamal,Dr Idris,Dr lawan musa,Sameer Ɗan gaske,Hon Modibbo . Wayannan sune hotunan da ta manna a bangon dakinta ko wanne da date din sa a ƙasan hotonsa. Hoton Hon zakewa ta zana cross akai saboda shi labarin sa ya ƙare. Sannan ta nufi hoton chukuemeka a gefe ta rubuta next target.

“Alisha ta, yaushe ki ka shigo?”

Ta ji muryar ta a bayanta hakan yasa ta juyo tana jujjuya maker hannunta.

“Innata ban jima ba. na ɗauka bacci ki ke yi shisa ban shigo dakin ki ba”

Kallon hoton da ta zanawa cross akai da kuma Wanda ta zana circle ta yi “ Bana fatan wayannan azzaluman mutanen su ci gaba da rayuwa me dadi”

“Inna a yayinda suka tarwatsa min farin cikina da ahalina ta ya zan bari su su yi rayuwar farin ciki ? “ tayi maganar tana zuwa gaban mirror ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo. Zip din rigan ta ja ƙasa tana cire sa. yai saura daga ita se skirt da bra shamulallen cikinta ta tsirawa idanu tana kallon tabon bullet din dake cikinta har guri biyu.

“Yau shekara guda kenan da samuwar wannan tabon,shekara guda kenan da mutuwar ahali na,shekara guda da aka kassaramin rayuwata na koma marainiya mara gata da galihu. Shekara guda da na rasa dukkan farin cikina. Wayannan mutanen sun rusa min rayuwata a dare daya, a abinda be wuce awa daya da rabi ba suka kwace komai daga gare ni. Taya zan manta wannan? taya zan manta yanda suka kashe ɗan ƙaramin ƙanina cikin rashin Imani? sannan suka kashe ɗan uwana da duka ahalina,sannan suka min fyade a gaban idanun iyaye na suna ji suna gani,taya zan manta lokacin da Mommah na ta haɗiye zuciya ta mutu saboda bakin ciki? Sun kashe min kowa na wa. Hakan be ishe su ba suka sawa gidan mu wuta komai ya kone tokan ahali na kawai aka iya samu ta ya zan manta haka?. Inna Kece ki ka bani sabuwar rayuwa ta hanyar taimaka mini,kin yi min magani kin boye ni kin mayar dani tamkar ƴar da ki ka haifa.”

“In sha Allah se kin ɗau fansar ki yarinya ta,se sun san da cewa Fansar Mace me rauni ya fi ko wani irin fansa zafi. Ban taɓa ganin inda aka gudanar da rashin Imani irin wannan ba. Wayannan mutanen sun zalunce ki,sun ruguza miki rayuwa. Ina bayan ki duk abinda za ki aikata ina goyan bayan ki dari bisa dari.ke ce gatana Alisha ban taɓa sanın dadin rayuwa ba se da ki ka shigo duniyata. ban san ya dadin kasancewa uwa yake ba se da na same ki. Kin yi min komai a rayuwata ci da sha sutura duk da arzikin ki ke min komai… da farko da na same ki na kai ki gıdana na yi tunanin mutuwa zaki yi na yi kuka sosai lokacin da na ga irin illar da suka miki ban taɓa tunanin za ki tashi ba, se de ke din jaruma ce,wacce zuciyarta yake cike da son ɗaukar fansa,duk da kin samu matsalar kwakwalwa wanda yai sanadiyyar haukacewa saboda bala’in da ki ka gani amma kullum zancen ki baya wuce se kin ɗau fansa. A haka ki ka kwashe tsawon wata shida baki san a duniyar da ki ke ba se daga baya Allah ya baki lafiya . Allah zai saka miki. Rama cuta ga macuci ba laifi bane, dan haka ki ɗau fansar ki cikin salon rashin Imani fiyeda yanda suka miki,kar ki Kyale ko daya daga cikin su”.

Abinda ya faru shine,bayan Inna ta kawo Alisha da ta suma bata san duniyar da take ba gidanta na laka, wanda ya kasance daki daya ne rak nan ta soma bata taimakon gaggawa kasancewarta tsohuwar me bada magungunan gargajiya,Allah ya mata baiwa sosai ta hanyar yin magani,kawai rayuwa ce da ta juya yasa komai yafi karfinta har yakai da ta fara bara a bakin hanya har Allah ya haɗa ta da Alisha.

A wannan daren ta mata duk abinda ya dace ta cire mata bullet da kuma sa mata magani a ciwukanta,gari ya waye shuru bata farka ba,aka sake kwana nan ma shuru se da aka kwashe kwanaki goma sannan Alisha ta farka. ko da ta farfaɗo cikin rashin saa ta tashi da ciwon hauka sosai,saboda kwakwalwarta ya samu shock,brain din ta bayi da karfin ɗaukan abubuwan da suka faru shine dalilin da yasa ta samu matsala. Sosai inna ta yi kuka na tausayin halin da ƴar ƙaramar yarinya ta shiga. cikin so da kauna ta ci gaba da kulawa da ita tana kuma yi mata magani. Se da suka kwashe watanni shida da sati biyu sannan Alisha ta dawo hankalinta, tun da ta dawo hankalinta ta koma so silent ko magana bata son yi kullum tana zaune cikin daki ta kafe guri daya da ido tana tuna ahalinta da aka wa kisan gilla ta gagara manta hakan ko da na minti daya. Tunani da yawan damuwan da take sanya kanta ne har yasa ta kamu da ciwon zuciya . Duk da yanda Inna take matukar bata kulawa amma fa ita ko magana bata mata sede ta yi ta binta da ido kawai tana kallon yanda take hidima da ita.

Rashin maganar ta sosai ya ɗagawa Inna hankali ta yi tunanin ta kurmance ne bata san zallan miskilanci da trauma bane,dakyar da suɗin goshi Inna ta samu Alisha ta soma magana, duk da ba ko yaushe ba. har ta saki jiki da ita ta ɗauke ta tamkar uwa. Se da ta gama dawuwa nutsuwarta tukuna Inna ta bata tarihinta. Ta ji tausayin matar sosai jin tunda take bata taɓa aure ba har ta fara tsufa babu miji babu yaran da zasu kula da ita,hakan ne yasa ta ɗauki a niyyar bata farin ciki iya iyawarta kamar yanda ta kula da ita tamkar ƴar cikinta. Jakan da Dr. Sagir ya bata ta dauka ta duba duk abubuwan da suke ciki,ATM din Mommah ta bawa inna tare da ce mata a nemo masu gini a gyara gidan sannan a sa duk wani abun ya dace,hakan kuwa aka yi kasancewar akwai kudi a satı biyu rak gidan Inna ya koma hadadden gıda komai an zuba a ciki ba laifi kuma dakuna har uku aka fitar masu girma ko wanne da toilet ga falo da kitchen gida yayi kyau an zuba komai cikin sa.

Kasancewar suna can ciki kusa da kwari bazeyu su ja wuta ba se kawai aka sa solar,tsabar farin ciki inna se da tayi kukan dadi tana gode wa Alisha domin bata taba tunanin har iya rayuwar ta zata zauna a cikin gida irin haka ba kuma wai nata ga kayan abinci da komai na morewa.

Dakin da ya kasance nata kuwa bangon dakin ta bi ta manne hotunan enemies din Tana me rubuta next target akan hoton Hashim zakewa.

Wannan shine abinda ya faru.

Ci gaba

Ɗaura hannunta tayi tana shafa cikinta “shin ko kin san abin mamaki inna,ƙaddara ya jefani cikin ahalin Ɗan gaske. Kuma na samu gurbin zama a cikin wannan gida, na rantse da Allah da ya busa min numfashi se na ɗeɗeta rayuwar su,se na shiga jikinsu yanda bazasu taɓa iya ɓanɓare ni daga jikinsu ba. se na zama bangare na rayuwarsu da se sun yi kuka fiye da wanda na yi. zan tarwatsa Ɗan gaske. Zan zame musu mage me kwanciyar ɗaukan rai. Zamana a gidan uwar gidan sa be wadatar ba, dole in koma asalin gidan Ɗan gaske saboda yin aikina yanda ya dance. dole zan kawo ƙarshen zamana a gidan Hajja Hauwa. Inna wanda ya kasance next target dina Shine Peter, satin da zamu shiga shine satin mutuwar sa a yayinda ake binciken mutuwar Hashim zakewa,a wannan lokacin labarin mutuwar Peter ze karaɗe ko ina.”

“Yarinyata amma zuwan ki gidan Ɗan gaske baze tona miki asiri ba kuwa? Me ze faru idan Ɗan gaske ko kuma ɗan sa Sameer ya gane ki?”

Rolling dara-daran idanunta tayi “bazasu taɓa gane ni ba! saboda babu wanda yasan fuskana a cikin su. A wannan baƙar daren se da suka kashe wutan gidan mu sannan suka farmake mu. Duk wannan abinda ya faru flashlight din wayar daya daga cikin su a ka kunna,dan haka bazasu taɓa gane ni ba”

“Allah ya taimaka,ya baki saa ya kare ki daga sharrin wayannan azzaluman,saboda zama cikin ahalin su ma duk ze yu gurbatattu ne”

“Ameen ameen. se de abin mamaki shine gidan Ɗan gaske kowa da irin halinsa yanda na lura da kuma yanda naji ɗan sa na biyu suna magana da matar Sameer alamu ya nuna su biyu ne shedanun. Halayen su ya bambamta matuka da wannan zan yi amfani in samu babban guri a zuciyarsu “

“Hakane Alisha dama ana haka, ba duka a ka haɗu aka zama daya ba. Amma ki bi su a hankali. Alamun ki sun nu na ko karyawa ba ki yi ba bari in zubo miki abinci” ta faɗa tana fita a dakin.

Babban hoton enlargement din family photos din su ita da iyayen ta dukkan su biyar ne a hoton fuskokin su ɗauke da murmushi ta kalla.

Gaban hoton ta nufa ta tsaya tana shafa fuskar Dr Sagir

“papa na,Mommah na, kun tafi kun barni a wannan duniyar da banida kowa se ku. Bana jin dadin komai a rayuwata ina fatan daga na gama ɗaukan fansa ta nima in biyoku duniyar da ku ke. Aryan ɗina ɗan karamin kanina nayi kewarka,ya Zaidu na nayi matukar kewan ku gaba daya zuciyata ya bushe hawaye na ya ƙame,na kawar da duk wani tausayi ko shauki a rayuwata babu wani dalilin da zesa in Kyale makasan ku”

Shigowa inna ta yi hannunta riƙe da plate a hannunta da kuma kofin tea cikin plate din kuma Kwai ne soyayye da slices bread da kech-up.

“Zo ki karya rana na yi” zama tayi ta soma karyawa inna kuma taje kan table ta ɗauko magungunanta na ciwon zuciya da take fama dashi,domin tun mutuwan iyayenta ta kamu da ciwon zuciya.

Gama karyawa tayi ta sha maganin ta sannan ta yi wanka ta mayar da kayan da ta zo dasu. duba lokaci tayi ta ga karfe daya ake nema hakan yasa ta yi wa inna sallama ta fita tare da mata alkawarin nan da kwana biyu zata zo gida.

Kasuwa ta shiga ta yi siyayyan da Hajja Hauwa ta aiketa sannan ta koma gidan,duk a falo ta same su suna zaune suna ta hira ana dariya.

“Hmmm uban su ya tarwatsawa wasu farin ciki amma su ga su nan suna dariya,very soon wannan dariya ze koma kuka” ta faɗa a zuciyarta

“Har kin dawo?” Cewar Adda domin ita haka kawai yarinyar ta burgeta sannan wani ɓari na zuciyar ta taji dadi da Hajja Hauwa ta ce mata ta ɗauke ta aiki.

“Ehh na dawo” ta faɗa tana nufan Hajja Hauwa ta miƙa mata aikan,dubawa tayi ta ga duk abinda ta aike ta ta siyo dede

“Ahh bakya mantuwa ashe, ai se da ki ka tafi na yi tunanin za ki manta wani abun”

Murmushi kawai tayi tana satan kallon Haydar dake danna wayarsa.

“To kai min su dakina ATM din kuma ki ajiye a gefen gadona “ hakan tayi ta ɗauki kayan ta kai su dakin sannan ta wuce dakinta ta cire hijab da niqab din ta zauna tana hutawa

“Alishaaaaaaa” ta ji an kwala mata kira seda ta ja tsaki sannan ta miƙe ta yafa babban gyalen dazun ta fito kanta a ƙasa.

“Naam”

“Zo ki gyara gurin nan”

Cewar Hajja Hauwa

Kallon gurin tayi yara ne suka ci abinci suka bar kwanukan watse a gun ga abincin da suka zubar a gurin. To tace sannan ta kwashe kwanukan takai kitchen sosai tayi mamakin ganin irin kwanukan wanke-wanke da aka tara kamar ba dazun da zata fita tayi wanke su ba. amma yanzu an tara kwanuka kamar wanda aka yi kwana biyu ko uku baa yi wanke-wanke ba. Wani baƙin ciki ne ya tokare mata wuya da seda ta ji kamar ta kurma ihu,abinda bata yi yanzu tazo gidan wasu tana yi musu,gidan ma gidan makiyanta,amma da ta tuna da dalilin zamanta se ta ji sauki a ranta. Broom da faka ta ɗauka ta gyara inda suka ɓata sannan ta shigo kitchen din ta fara wanke-wanke tana yi rai a haɗe.

“Zan sha fura” ta ji muryansa a bayanta ɗauraye hannunta tayi ta ɗau kofi ta zuba nonon sannan ta dama masa kamar yanda taga Hajja Hauwa tayi jiya. duk abinda take yi yana kallon ta komai dinta cikin nutsuwa take yin sa ba rawan kai.

Data gama ta miƙa mai “nagode meyasa daga dawuwanki ko hutawa ba ki yi ba za ki fara aiki?”

Ɗan murmushin da ya tsaya a fatar baki tayi “Uncle Haydar aiki na ne fa,kowa yana da kwarewa akan aikinsa. kuma ba wanda yake son aiki ya dinga taruwa masa. Ka ga kuwa kayi aikinka a lokacin da ka ke da dama, yanzu in na gama se in je in huta gaba daya se kuma dare”

Murmushi ya yi bayan ya gama sauraronta “magana cikin hikima,duk da haka yakamata ace yanda ki ka kwaso rana da kin huta ga duka alamu aiyukan da ki ke yi ba ki saba ba”

“Uhmm…… tabbas ni ƴar gata ce a gurin iyayena. lokacin da suke a raye ko tsinke bana ɗagawa in ka ga na shiga kitchen to abinci na je dubawa.amma yanzu da ya kasance banida da yanda zan yi dole in koya aikin da zan rufawa kai na asiri.”

“Allah ya ji kan su da rahama rashin iyaye babban rashi ne. Allah ya baki hakurin rashin su”

“Ameen uncle nagode” ta faɗa tana ci gaba da wanke wanken.

“Dazun da ki ka sanya niqab se na ga kwayar idanun ki sun yi min kama da na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login