Showing 72001 words to 75000 words out of 96407 words
Chapter 25 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
ta ƙi shiga se da ta tabbatar da ya gama wayar da kusan minti biyar sannan ta tura kofar ta shiga fuskar ta da murmushin da yafi komai hatsari.
“Ah ah Alisha Kece? ƙaraso mana” cewar Ɗan gaske yana ajiye wayarsa,shigowa tayi ta zauna a ƙasa tana
“Barka da safiya Kawu, Katashi lafiya?”
“Lafiya lau Alisha “
Shuru ta ɗan yi tana motsa bakin ta alamar tana son ce wani abu, da ya fahimta ne yasa shi cewa
“ƴata ya aka yi ne akwai abinda ki ke so a yi miki ne?”
Gyada kai tayi sannan calmly ta soma magana
“Kawu kai ne ka ba ni damar yin komai a gidan a matsayina ta sabuwar surkar ka,kai ne ka ce min duk abinda nake so in taho kaina tsaye in same ka batare da shakkan komai ba in sanar maka “
Gyada kai yayi “kwarai kuwa ni ne na faɗa miki haka,shin menene ki ke so?” Ya tambayeta cike da kulawa
“ ina neman alfarma ne kawu,ina son haɗe kan wannan ahali dan jikoki suma su taso su yi koyi da hakan. Ina son mu dinga haɗuwa kullum a teburin cin abinci a matsayin ahali. Wannan shine kaɗai alfarman da nake nema daga gareka Kawu”
Murmushi ya yi yana sake jinjina hankalinta da zurfin tunani da sam be san cikin makircin ta bane, ya ce
“Na miki wannan alkawarin in sha Allah daga yau kowa a teburin cin abinci zaa dinga haɗuwa,yanzu bari in shirya se in fito kin ji ko?”
Cike da murna ta ce “nagode Kawu” ta miƙe ta bar part din.
A tsakiyar falo duk ta same su, sun yi cirko-cirko irin wannan kira da aka yi musu sun yi tsammanin wani gagarumin abu ne yake faruwa a downstairs din amma se su ka ga babu komai,da suka tambayi masu aiki me yake faruwa.
Basu ce da su komai ba ganin Alisha na saukowa falon
Ganin yanda ta yi ado tayi kyau kamar sabuwar amarya ne yasa duk suka tsaya kallon ta abinda ba su taɓa ganin tayi ba sai sau daya rak, nan ma a walimar sa ranan Haydar da Meenal ne.
Ganin duk kallon ta suka tsaya yi ne yasa ta isa gaban Adda ta riƙo hannayenta
“Adda na haɗa mana breakfast, daga yau dukkan mu a tare zamu dinga cin abinci”
Duk da mamaki suke kallanta jin abinda ta faɗa,kallan fuskar Haydar Adda ta yi ta ga ya tsura musu ido sannan ta dawo da duban ta kan Alisha
“My dear ni kaina wannan shine fata na,ina son ganin ahalina a haɗe guri guda kamar ko wani ahali amma Yallabai baya bukatar wannan kusancin “
“Kwarai Alisha nima lokacin da na shigo gidan nan nayi tunanin zan gyara komai a matsayina ta sabuwar surka sede sam hakan ya gagara yuwa “
cewar Maryam.
“Nayi niyar haɗe kan wannan ahalin Adda. kuma in sha Allah I’ll succeed dan Allah ku zo mu ci abinci akan teburin ahali”
Duk suna son hakan amma suna tsoron Ɗan gaske saboda shi ya hana hakan,jikin Adda a sanyaye ta dafa kafaɗarta
“Nasani in sha Allah you will bring a change to this family “
“Mtsssssww aikin banza aikin wofi,daga yau kar a kuskura a sake gangancin shiga bangarena akan maganar wani banzan cin abinci a tare. Ke wato ga ki ƴar iyayi, kar ki kama kan ki. Munafuka kawai” Sameer ya gama faɗa yana watsa mata muguwar kallo.
“Sameer ya isa haka,kar ka sake kiranta da munafuka” cewar Haydar calmly.
Tsaki ya kuma ja “aikin banza ni na wuce part din a, ke Maryam zo ki wuce mu tafi,kuma abiyo mu da abincin mu sama.”
Ya fara tafiya maryam ta bi bayan sa ba dan ta so ba
Muryarsa suka ji yana “babu wanda ze je ko ina daga yau kowa da kowa a dinning area zaa dinga cin abincin”
Kowa zare idanu yayi cike da zallan mamaki suka juyo suna kallon Ɗan gaske da yake tsaye a bayan su.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
37 & 38_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
37 & 38
Ganin yanda duk suka zuba mai ido suna masa kallon mamaki ne yasa shi gyada musu kai
“Kwarai kuwa daughter in-law ta kawo sabon tsari kuma na ga ya dace,dan haka duk a zauna a ci abinci a tare”
Murmushi su ka saki na farin ciki dan ba su yi tsammanin faruwar haka,ban da Sameer da ya wuce dinning kamar iska be kulasu ba ya zauna shima Ɗan gaske ya je ya zauna.
Fuskar Adda ɗauke da murmushi ta ce “nagode Alisha wannan shine buri na ko da yaushe,ke ta dabance ƴata”
“Babu komai Adda,na ga dacewar a matsayina ta sabuwar surka yakamata in gwada saa na,kuma Allah ya ba ni saa”
“Hakane kam mu je ko ƴata, mu je mu ci abinci” tayi maganar tana wucewa dinning din,Gaba daya dinning din su ka je suka zauna yayi saura ita da Haydar ne tsaye a falo,a hankali ya tako in da take tsaye cikin tafiyarsa na jarumai,hannunsa na cikin aljihu ya zuba mata narkakkun idanun sa.
“Black Queen in faɗi wani abu ?”
Motsa lips din ta da suka sha lipgloss tayi “eh sai de na manta ba mu gaisa ba,barka da safiya”
“Ohh hakane kwalliyar ki ne ya zautar dani har na manta ba mu gaisa ba ai,fatan kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah mu ƙarasa dinning”
Kai ya gyada sannan ta yi gaba ya bi ta a baya
Serving din kowa abincin tayi according to abinda ka ce kana so,sai da ta sawa kowa sannan ta zauna suka fara karya wa.
Bayan sun gama ne aka koma falo ana hira. Sameer da haushin su kamar yayi yaya ne ya miƙe ya haura sama,bangaren sa Ɗan gaske ya koma ya ce musu to shi ze je ya rintsa,ko da ya shiga falon sa waya ya ɗaga yana danna kiran Sameer ya umarcesa da ya zo bangaren sa. Be ɗau lokaci ba sai ga shi ya iso fuska a haɗe alamun yana cikin fushi.
Duban sa yayi yaga yanda yake shashshan kamshi “ zauna mana Sameer,wannan ɓata ran na menene?”
Zama yayi yana kuma haɗe fuska “ Baba gaskiya ni ba ka min adalci ba,ya zaa yi ka sakewa wannan yarinyar fuska har ka dinga yarda da abinda ta faɗa maka,kuma sannan har ka haɗata aure da Haydar bayan ni Ina son in shoshale da ita.”
Dariya Ɗan gaske ya fashe dashi irin na bosawa dama ya san damuwar Sameer din duk baze wuce akan hakan bane
“Gaskiya Sameer ba ka dama. To wannan yarinyar de ina son ka ɗauke idon ka cak akan ta saboda matar ƙanin kace. Abinda yasa kuma na sakar mata fuska yarinyar tana da hankali ta cececi rayuwata ranan da na samu asthmatic attack. Kar ka wani ɗaga hankalin ka inde ƴan mata ne akwai su bunchers suna jiran ka,amma fa se bayan zaɓenka. ka ga yanzu siyasa ce a gaban ka, kar ka yi abinda ze sa abokan hamaiyarka su samu dama akan ka. Ka ji ko? Ka rage shan giyan nan da ka ke yi sannan kuma ka rage zuwa hotels saboda idon mutane yanzu gaba daya kan ka ze koma”
“Shikenan Baba amma de ta shiga rai na”
Yana dariya yace “kuma haka za ta fita ba”
Dariya shi din ma yayi “ Yawwa ɗazun Damisa ya kira ni yace yau za su zo gida kwasan wayannan kaya “
“Ehh zaa tura su Lagos,Sameer ka tabbatar da Kayan nan sun isa Lagos lafiya “
“Kar ka damu”
Sulalewa tayi ta bar su a falo suna hiran da yaƙi ci yaƙi cinyewa in ji ta da faɗa,tana shiga dakinta ta murza key sannan ta ɗau wayarta, wasu numbobi ta sa sannan ta kira,ringing biyu yayi aka ɗaga
Da sauri ta sa hannu a bakin ta sannan ta soma magana
“Dan Allah ina magana da Gombe division ne?”
Muryar wani namiji ta ji ya amsa mata da “eh wacece kuma daga ina ki ke kira?”
Sake rufe bakin ta tayi, tana “sanın wacece ni ko kuma daga ina nake a yanzu bashi da amfani. na kira ne saboda sanar da ku wani information da na samu kuma ba karya bane ko jita-jita, Hon Modibbo Ɗan gaske ya na safaran mugayen makamai kuma in ba ku zo nan da awa daya ba tofa zaa fitar dasu a gidan,makaman suna falon sa a wani dakin sirri”
“Ke din ya aka yi ki ka sanı?” ba ta ba sa amsa ba ta kashe kiran tana kuma danna wasu numbobi.
“Hello progress Tv akwai labari me zafi,ƴan sanda suna hanyar su na zuwa gidan Modibbo Ɗan gaske domin bincikar sa,an samu mugayen makamai a gidan sa,ku ka yi sanya bazaku samu rahoton yaɗawa a kafafen sada zumunta ba.”
Nan ma tana faɗan abinda take son faɗa ta katse kiran ta na cilla wayar kan gado tana sakin killer smile
“Ku kuka fara wasan ni kuma zan ƙarasa mu ku shi”
Falo ta koma ta zauna cikin su kamar saliha aka ci gaba da hira da ita, kallon time yai ya ga lokaci ya ja “Bari in yi wanka in shirya in tafi office Adda”
“Yakamata kam gaskiya kar ka makara”
Haurawa bangarensa yay ya shiga wanka bayan ya fito yana shafa mai a gaban mirror ya ji jiniyar motar ƴan sanda suna approching din su. dakatawa da shafa mai din da ya ke yai, yana ɗaure da towel a kugunsa ya isa bakin window yana ɗage labule dan tabbatar da hasashensa, wangale gate ya ga me gadi yayi motar ƴan sanda guda uku suka shigo se a bayan su da akwai motar yan jarida guda daya. Da sauri ya je ya ɗauki jallabiya kawai ya zura yana tambayar kansa menene abinda ya kawo police gidansu har da yan jarida.
Suna zaune a falo ana hira su ka ji jiniyar motar ƴan sanda a cikin gidan kafin su ankare ƴan sanda mutum goma sun shigo cikin uniform din aikin su.
Da mamaki suke kallon su ganin yanda suka shigo mu su falo kai tsaye
“Barka Mrs Ɗan gaske mun zo ne domin yin bincike akan mijin ki”
Babban ɗan sanda ya faɗa yana ƙarewa ko ina kallo a falon
“Amma ai ku na da bukatar izini kafin ku shigo mana gida kai tsaye “
ACP ne ya sakar mata murmushi “Apologies ran ki shi daɗe,amma ba mu da wannan lokacin saboda bincike ne na gaggawa mun samu information akan mijin ki Hon Modibbo yana safaran makamai da powder iblis.”
“What???????” Su ka faɗa gaba ɗayan su cike da tashin hankali maganar da ACP ya faɗa ya matukar girgiza su jin wai Ɗan gaske yana safaran makamai da Powder iblis taya hakan ze faru suna zaune gıda daya dashi a ce wai ba su sani tabbas wannan zance na su akwai sharri da ayar tambaya akai.
Saukowa Haydar yai ya na riƙe da jallabiyar da ya sanya,yana shigowa ya miƙawa ACP hannu suka gaisa sauran ƴan sandan suka sara masa hannu kawai ya ɗaga musu yana maida duban sa kan ACP
“ACP Lukman menene abinda yake faruwa kun zo babu izini”
Ze ba sa amsa kenan Sameer da Ɗan gaske a tare su ka sauko ƙasan suka same su a tsaye,fuska a murturke ya furta
“Menene ya kawo ku gida na batare da neman izini ba?”
“Yallabai mun samu information kan cewa kana shigo da haramtattun makamai har ma kana safaransu tare da powder iblis.”
Haydar da se yanzu yake jin dalilin na su na zuwa ya dubi mahaifin na sa ya ga yana bin ACP da kallon mamaki
“Officer am very sure information din da ku ka samu is invalid. Babu makami a gidan nan da ya wuce gun dina sai kuma gun din yallabai wanda yake da license. Ze yu wrong information aka sanar da ku”
Cikin mutuntawa da girmamawa ACP Lukman ya dubi Haydar “Yallabai DCS Haydar na san ka san doka ka san ya tsarin yake wannan umarni mu ka samu daga sam, dan Allah ku ba mu haɗin kai mu yi aikin mu,ka ga in accusation ne se mu yi tafiyar mu”
Ya san abinda ACP ya faɗa gaskiya ne,ba shi da right din hanasu duk kuwa matsayin sa ya fi nasu amma doka tafi karfin wasa.
Yana wani bin su da kallan wulakanci ya ce “dallah malamai ku ɓacewa mutane da gani,sharrin na ku na ƴan sanda har ya zo kan gidan mu kenan. To babu wanda ya isa ya mana wani banzan bincike a gidan nan “
“Yi shuru Sameer,bari in kira commissioner din “ cewar Ɗan gaske yana zaro wayansa a aljihu.
Su de su Adda duk suna tsaye sun yi jugum suna ganin ikon Allah.
ACP ne ya miƙawa Haydar wani farin envelope tare da cewa “Wannan umarni ne direct daga high court dan Allah ku barmu mu yi aikin mu yanda ya kamata “
Buɗewa ya yi ya karanta sannan ya komar mai dashi ya dubi Ɗan gaske
“Baba ku bar su su yi aikin su please umarni aka basu daga sama, ko commissioner ba shi da halin dakatar da su balle ni “
“Aliyu Haydar yanzu har na yi lalacewan da ƴan sanda za su shigo min gida da zargin ina safaran makamai?”
Cikin kwantar da murya ya ce “ Baba babu abin ɗaga hankali in har kasan kana da gaskiyarka ka bar su suyi abinda ya kawo su a dena ɓata wannan lokaci “
Murmushi ACP Lukman ya yi yana “thank you DCS Haydar “ yana faɗan haka su ka wuce sashin Ɗan gaske. Bin su da kallo kawai suka yi sannan suka zauna.
Ranta fess ta san yau dole sunan Ɗan gaske ya ɓaci tunda har ta haɗo mai da ƴan jaridu.a fili kuwa fuskanta ya nuna damuwa.
A gefe guda Ɗan gaske ji ya ke kamar yayi bombing dan takaici ransa na kuna da tafarfasa yasan bakowa bane ze masa wannan shunen ba da ya wuce Habibu katanga saboda sun samu matsala.
Su na tsaye a falon kuwa se ga ƴan sanda sun fara fito da mugayen makaman daga part din Ɗan gaske cike da zallan madaran mamaki suke kallon Ɗan gaske da ya haɗe fuska.
Haydar kallon sa kawai yake yi cike da takaici da mamaki domin be taɓa tunanin mahaifin su ze aikata abu makamancin haka ba duk da ya jima yana zarginsa akan aikata wasu ƙananun laifuka amma be kawo har wannan mummunar abun yake aikata wa ba.
“You’re under arrest for this crime Hon Modibbo Ɗan gaske “ Cewar ACP
Wani daga cikin yan sandan ne ya ce da ACP “sir ƴan jaridun nan fa mu su ke jira, in ce su shigo su ɗauki rohoto ne?”
“Don’t try this rubbish,na barku kun yi binciken ku cikin ruwan sanyi amma bazan yarda da wannan tozarcin ba,maza ku tabbatar kafin nan da mintuna biyu kun Kora duk wani ɗan jarida a layin anguwan nan”Haydar ya faɗa rai a ɓace dan yasan aka ɗauki rohoto tofa mutuncin gidan su ya gama ɓaci.
Sara masa ɗan sandan yayi yana “yes sir “ sannan su uku suka fita suka Kori duk wasu yan jarida kamar yanda ya umarce su. A ciki kuwa Alisha sam ba ta ji dadin Koransu da Haydar ya sa aka yi ba amma hakan ma she’s happy tunda iyalansa sun fara sanın kaɗan daga mugayen abubuwan da yake yi.
Adda kam mamaki sam ya hana ta cewa komai se ma tagumin da ta buga ta na kallon bakin su in wannan ya faɗa se wannan ma ya faɗa.
“Yallabai DCS ka yi wa mahaifin ka bayani dole ne mu tafi dashi tunda har mu ka tabbatar da zargin mu akan sa dole ya bi mu caji office “
Kai ya gyadawa ACP da ya gama magana sannan ya ɗan kalli Ɗan gaske fisha, saboda takaicin sa da yake ji dakyar ya iya buɗe bakin sa ya ce mai
“Baba dole ka bi su,dan Allah ka dena wahalar da shari'a ku je office din ni ma ina zuwa a bayan ku”
Haka ba dan ya so ba ya bi su a motar yan sanda suka wuce dashi caji office Sameer a take ya bi bayan su da motar sa.
Yana tsaye a tsakiyar falon har yanzu ya kasa yarda wai an fito da wayannan makaman a gidan su,a ce yana jami’i amma be san abubuwan da ake yi a gidan su ba, ji ya yi tamkar ya gaza a aikin sa tunda har za su iya kwana da wannan makaman amma be san dasu ba.
Murya a karye Adda ta dube sa “shin kana ganin mahaifin ku ze aikata haka?”
“Tabbas wayannan makamai sai na sake bincikar su na bibiyi daga ina suka fito. Kar ki sa damuwa aranki Adda yanzu zan bi su in ji ya ake ciki ” ya nufi part din sa bayan ya gama magana.
Duk shuru su ka yi babu Wanda ya kuma cewa komai bayan tafiyan Haydar.kowa da abinda ke ransa, ga bakin su na cike da tambayoyi da yawa amma sun zaɓi su yi shuru dan ko sun tambayi Adda ba amsa za su samu ba tunda ita kan ta bata da amsar da za ta tawa kan ta dangane da Ɗan gaske….
Yusra latsa wayar ta ta fara ta shiga Facebook kawai ta fara scrolling wani post ta gani da ya ba ta mamaki