Showing 57001 words to 60000 words out of 96407 words
Chapter 20 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
ya ɓata mun rai,amma ya zan yi tunda an rigada an sa musu ranan aure se ki ga inda rabo bayan auren su ta canza “ Ɗan gaske ya faɗa yana karkaɗa kafa dan ran sa ya ɓaci kawai be nuna bane saboda yar abokin sa ne.
Adda da tun da suke maganar su ba ta ce komai ba se yanzu ta ce
“Ai kowa ya siya rariya ya san za ta zubda ruwa,tun farko se da mu ka faɗa maka yarinyar nan bata da isasshiyar tarbiyya amman da yake ƴar abokin ka ce kayi burus. Allah de yasa wata rana rashin kunyar nata ya biyo ta kanka” tayi maganar tana barın falon ta nufi part din ta da kallo suka bi ta,Hajja Hauwa ma bin bayan nata tayi tana
“To Allah ya kyauta”
A falon Adda suka same su nan suma suka bata hakuri akan abinda ya faru cikin jin kunyar su tace babu komai.
Ko da dare yayi ya tura aka kira masa Meenal part din sa ,faɗa ya mata tass kamar ze cinye ta sannan ya kira Alisha tana zuwa ta tadda su cikin falon sa,umartan Meenal yayi da ta ba ta hakuri aikuwa badan ran ta ya so ba ta bata hakuri cikin kıssa irin nata ta ce “babu komai ai ya wuce”
Bayan ya sallame su ta koma dakin ta ne ta rufe ta kwanta tana murmushi dan zuwa yanzu har ta fara tausayawa Meenal dan abinda za ta yi mata ko bayyana fuskar nata a duniya se ya gagare ta.
“Ban yi niyar aikata miki komai a matsayin ki ta ƴa a gurin katanga, ba amma ke ki ka jawa kan ki,sai da ki ka tursasani na saka ki cikin target dina. Zan fara dake tukuna ina son sunan ki da sunan uban ki ya lalace kafin nan in koma kan sa”
Tayi maganar ran ta fess.mirginawa tayi akan gadon ta kifu ta rungume pillow tana ta murmushi ita kaɗai, tana wasa da kafafunta.
“Yakamata in yi upgrading taku na ,daga gobe Ɗan gaske za ka shigo hannu na”
Washe gari da sassafe ta sulale tabar part din Adda kafin ta fita sai da ta ɗauki ƙaramin dustbin na karfe da leta da kuma jaridu,seda ta fahimci babu wanda yake kallon ta sannan ta shiga sashen Ɗan gaske,cusa jaridun tayi cikin dustbin din ta sa musu wuta ta rufe. Ta ajiye mai a tsakiya falo nan take hayaki ya soma tashi yana turnuke ko ina har ya soma shiga dakin baccin sa.
Se da ta ga ko ina ya bule da hayaki sannan ta kashe wutan ta fita a part din tana rufe komai kirif ta je ta boye dustbin din a wani lungu.
Yana cikin baccin sa numfashin sa ya soma carkewa hakan yasa shi tashi yana tari babu kakkautawa, ganin hayaki nashigowa bedroom din sa ne yasa ya miƙe dan zuwa yaga meye ne yake faruwa a falon,ko da ya fito falo nan fa ya tarar da hayakin da yafi na dakin nan fa tarın da yake yi yafi na ɗazun. cikin ƙankanin lokaci numfashinsa ya fara yankewa idanun sa suka kada sukayi jaa tsabar azaba ko magana ya kasa se ma faɗuwa ƙasa da yayi yana riƙe da kirjinsa yana kokawa da numfashi. gaba daya ya gama wahala da galabaita. Nishi kawai yake yi na azaba shi kaɗai yasan abinda yake ji.
Tura kofar tayi ta shiga tana “Innalillahi wainnailaihi rajuun kawu me ya same ka ?” Ta yi maganar tana tsugunawa a gabansa cikin alamu na tashin hankali. Sama-sama yake jinta sannan dishi-dishi yake kallon ta.
Dakyar ya iya cewa “Ciwo na ne ya tashi”
Se da ta fakaici idon sa ta yi murmushi dan ta san sarai akan ciwon da yake magana dan kwana ki abakin su Ameera ta ji suna cewa ai Baban su na da Asthma.
“Ta ya zan taimaka maka? "”
Murya na fita dakyar yace “inhaler na a bedside drawer na”
Da sauri ta shiga dakin nasa tana buɗe drawer kuwa ta ga inhaler a ciki dauka tayi ta kawo masa ta taimaka mai ya shake sa se da ya samu mintuna kusan goma kefin ya fara dawuwa dede. Barın sa tayi ta je ta buɗe labulayen windows din falon saboda har yanzu akwai sauran hayakin. Komawa tayi inda ta bar shi ta samu ya tashi zaune ya jingina jikinsa da kujera yana kallan ta.
“Sannu kawu shin akwai abinda ka ke bukata ne?”
Kai ya girgiza mata, sannan ya mata alama ta zo da hannu zuwa ta yi ta sunkuya a gaban sa.
“Yarinya ba ni da bakin da zan iya gode mi ki. saboda kin ceci rayuwata yau ba domin Allah ya turo ki ba da ban san me ze faru dani ba. Allah ya miki albarka,Alisha ko?”
Kai ta gyada masa cikin nutsuwa yana murmushi ya ce “Nagode sosai you really saved a life. Duk abinda ki ke so a gidan nan kar ki ji shakka ki zo direct ki faɗa min kin ji ko?”
“ to kawu ,dama na zo neman Adda ne se na yi tunanin tana bangaren ka da na shigo shine na ji kana numfashi wani iri”
“Ai zuwan ki yayi amfani”
Miƙewa ta yi “ shikenan kawu Allah ya ƙara sauki bari in je kar Adda ta neme ni” haka ta fita tana dariyar mugunta tasan yanzu ta gama siye zuciyar Ɗan gaske tunda har ta ceto rayuwarsa.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
31 & 32_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
31 & 32
*Kamar yanda ku ka sani wannan littafin paid book ne,yanzu saura pages kaɗan free book ya ƙare,ya kamata tun yanzu ku fara biya kafin lokacin ya yi, dan banason ɓata lokaci ina gama book one za'a ɗaura da book two in sha Allah*
*Ga duk me son biyan littafin FANSAR MACE naira ₦300 ne only ga mutane 20 da zasu fara biya yanzu,in mutane 20 din sun cika an biya ze koma 500 . Za'a biya via opay account 8166018849 Aisha Abbas bidami opay account,idan mutum ya tura da kudin se ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta whatsspp number ta 08166018849 Mrs Isham.*
Ga wa'yanda basa iya tura kudi ta opay account,zasu iya sawa ta wannan account din 2309617787 Fatima Abbas UBA BANK.duk wanda ya tura ya yi screenshot na evidence of payment ya tura min.
After three weeks
Tun bayan tafiyar su Mujahid har yau bata samu damar yin magana dashi ba saboda bata je gidan Inna ba balle ta yi magana dashi,sannan babu lambar sa akanta,duk yanda ta so ta fita a gidan abu ya gagara saboda Haydar yanzu ko nan da nan za ta je se yace shi ze kai ta, hakan yasa ta hakura da maganar fita. Shima kuma a bangaren sa sosai yake aikin sa na bincike da yasa a gaba amma se de har yanzu shuru hujja kwara daya be samu ba amma be yi kasa a guiwa ba ya sake zurfafa binciken sa,yau ya yi saura kwana takwas bikin sosai ake shirye-shirye a both gidan iyayen Ango da na amaryan.
Ɗan gaske tun lokacin da Alisha ta ceci rayuwarsa ya ɗauke ta da muhimmanci har ya bawa Haydar da su Adda labarin abinda ya faru babu wanda ya yi zargin wani abu se ma dadin da suka ji ganin yanda Ɗan gaske ya ke ta yabon ta,musamman Haydar ya fi kowa farin cikin kasantuwar hakan saboda yasan yanda Ɗan gaske yanzu yake ganin Alisha a matsayin yarinya me nutsuwa da hankali yasan ko ya je masa da batun aurenta ba ze samu matsala ba.
Izuwa yanzu Meenal ta fara shirye-shiryen event din da za ta yi da friends din ta saboda Haydar yace babu event ko daya da ze halatta. farko ma cewa yayi babu event da zaa yi amma se Adda ta ce mai tunda tana son yi ya barta tayi ko da shi baze samu halatta ba.
Shiryawa ta yi tsaf bayan ta tabbatar da Haydar baya gıda ta shirya cikin Hijab kamar yanda ta saba ko da yaushe sannan ta ɗauki wayanta ta nufi gun Adda tana zaune akan sallaya ta same ta.
“Barka da hutawa Adda “ ta yi maganar tana zama a kusa da ita.
“Barka dai,naga kin shirya alamu ya nuna fita zaki yi?”
Sunkuyar da kanta tayi ƙasa “dama zan je gidan kawu na ne akwai abinda nake son ɗauka”
Jinjina kai tayi ta buɗe pause da ta ajiye kan sallaya ta fito da sabbin 2k ta bata tare da cewa “ga kudin abun hawa, a dawo lafiya”
Karɓa tayi tana mata godiya sannan ta fita,abun hawa be mata wahala ba har anguwa uku a kofan gidan aka sauke ta. Tana shiga ta samu Inna na ninke kaya da alamun wanki tayi. Sanın bata ga shigowanta bane yasa ta je ta rungume ta ta baya tana
“Na yi kewar ki Inna ta “
“Wai! ƴar nan ai se ki sa na tsorata dan ban san da shigowanki ba,sam ban yi tsammanin dawuwar ki yau ba,ba ki taɓa jimawa ba ki dawo gida ba kamar wannan karon “
Sake ta tayi ta zauna beside her se da ta cire hijab din tukun ta samu damar magana
“Rayuwa a gidan Ɗan gaske dole se ana takatsantsan Inna. Bana manta da cewa suna da gwararen ɗan bincike wanda komai yana fakaice dashi a gidan su”
“Hakane ki ci gaba da takun ki a hankali yanzu ya ake ciki ?”
Ba ta labarin duk abinda yake faruwa a gidan ta yi ta kara da “bari in shiga ciki ina da muhimmiyar maganar da zan yi da Mujahid “ ta yi maganar tana shigewa bedroom.
Wayar ta da take bari a gida ta ɗauka ta kunna,zama tayi kan kujera tana lalubo number Mujahid har za ta kira ta tuna na Nigeria ne so ko ta kira baze shiga ba, hakan yasa ta ɗauki number ta sa a wayar da Haydar ya siya mata. Duba sa tayi a WhatsApp aikuwa cikin saa ta gansa a online kiran sa tayi a voice call
“Hi Mujahid”
Yana jin muryar ya gane wacece hakan yasa shi faɗin “thank Goodness ina ta expecting kiran ki amma na ji shuru na kira Layin ki a kashe hope kina lfy?”
“Ina lafiya Mujahid,ku fa? Ya jikin Zaid yana samun sauki ? An yi aikin? Me doctors din suka ce ?”
Ta jero masa tambayoyi duk a jere. Dariya me sauti yai
“Calm down Alisha darling. Albishirinki? An yi Surgery successfull in ki ka ga Zaid yanzu bazama ki gane sa ba”
Cike da tsananin farin cikin da ta shiga wanda sai da ta ji ruwan hawaye ya taru a idon ta tsabar jindadin wannan labarin
“Dagaske Mujahid? "Oh Allah, Alhamdulillah I'm truly grateful for Your endless kindness. Yanzu to yaushe za ku dawo ?”
“Za mu iya kai wa wata daya i guess, kamar yanda doctor yace saboda har yanzu be farfaɗo ba,sannan akwai sauran treatment din da baa ƙarasa masa ba”
“Shikenan Allah ya nuna mana Allah ya ba sa lafiya. Mujahid” ta kira sunan sa daga ƙarshe
“Naam Alisha “
Sai da ta goge hawayen da suka zubo mata kafin ta ce “Ka yi ɗawainiya damu sosai banida bakin da zan gode maka Allah ya biya ka da gıdan aljanna “
A bangaren sa ya furta “kar ki damu Alisha yi wa kai ne. Zaid tamkar ɗan uwa yake a gare ni ,nasan da shine a madadina ze yi min fiye da haka”
Jinjina kai tayi saboda tabbas ta san gaskiya ya faɗa Zaid mutum ne me zuciyan yi, ga tausayi da taimako kamar mahaifin su, sai de akwai taurin kai da zafin zuciya da rashin yafiya. Kawar da tunanin da ta ke yi ta yi tare da cewa
“Ina bukatar taimakon ka Mujahid”
“Faɗi ina jin ki”
Ɗaura kafanta daya akan daya ta yi tana rufe idanunta take wulakancin da Meenal ta mata ya dawo mata, idanun ta was still closed ta ce
“Ina son ka tura min number wani da ka aminta da shi sosai ina son ya min aiki akan wata ne, zan biya sa,so nake ya yi duk hanyar da ze yi ya shawo kan ta ta amsa goron gayyatar sa duk inda yake”
Murmushin mugunta yayi domin daga jin yanda take masa magana ya gane akwai abinda aka mata take son ramawa.
“Wata mara sa'ar ce ta yi gigin shiga gonar ki haka?”
Itama a nata bangaren murmushin ne ya suɓuce mata “Ƴar Habibu katanga,ina son in fara da ƴar kafin uban “
“Shikenan akwai number wanda zan tura miki mayen kudi ne,inde akan kudi ne ze iya aikata komai”
“Shikenan nagode se mun yi magana”
Ajiye wayar ta yi ta fito ta samu Inna ta gama ninke kayan, ɗago kai tayi ta dubi Alisha dake zama kusa da ita
“Amma yau kam wuni za mu yi ko?”
“Yeah se dare zan koma,ba ki yi komai bane inna ? dan yunwa nake ji “
Kwashe Kayan tayi ta nufi dakin ta dasu se da ta kusan shiga ta ce “kunu da kosai na yi da safe. Nasan kosan yayi sanyi baze mi ki dadin ci ba, kunun kuma ya ƙare dama iya bakina nayi sede in za ki mana girki”
“Tom bari in dafa mana ko jollof din shinkafa ne”
Tayi maganar tana miƙewa ta shiga kitchen, buɗe freezer tayi nan ta ga Kayan miya da ganyen alehu da ganyen ugu,yanke shawara tayi zata musu jollof din da ganyen ugu.
Boiling din foreign rice din tayi ta barsa cikin basket a gefe sannan ta haɗa ruwan haɗin jallof din ta sa kifin da ta gani a cikin kwali. da yake gas ne shaf shaf ta gama komai ruwan har ya fara tausa hakan yasa ta zuba shinkafar tana maida tukunyar ta rufe. Towel ta ɗauka tana goge hannunta a wannan sa’in ta ji wayar ta na ƙara,yatsina fuska ta yi dan gandan zuwa dakin nata ta ke ji, ga shi a nan ta baro sa. ba ta ko motsa ba duk da bata san wanene ke kiran na ta ba.
Se inna ce ta shigo ta bata wayar ta san Alisha sarai bawai bata ji ƙaran bane, kawai komawa dakin ne take jin ƙiwiya.
Karɓa ta yi, inna ta fita,duba wa tayi nan ta ga two missed call din Haydar tana tunanin ajiye wayar kira ya sake shigowa,kafe wayar ta yi da ido tana kallo kamar me son hango wani abu, sai da ya kusan katsewa kana ta ɗaga bakin ɗauke da sallama
“Ina yini Uncle” ta gaishe sa a sanyaye,be ko amsa gaisuwar da take mai ba ya wurga mata tambaya
“Ina ki ka je ?”
Dama ta san zaa rina yanzu haka be wuce ya dawo gidan ya samu ba ta nan bane yasa shi yi mata wannan kira kamar wani wanda take zaman sa,tura baki tayi dan sam a rayuwar ta babu abinda ta tsana sama da takura
“Na je gidan kawu na ne,kuma da zan fita na sanar da Adda”
Daga cikin wayar ta jiyo saukan numfashin sa “shikenan karfe nawa ne za ki dawo ? Zan zo in ɗauke ki. ki tura min address “
Zare ido ta yi jin yana neman ta tura masa address din gidan da take ɓoyewa duniya,gidan da ya kasance mafakanta inda take samun kwanciyar hankali a cikinsa,ko da wasa bazata yi wannan gangancin ba.
Shurun da ya ji ta yi ne yasa murya a tausashe ya ce “kin ji?”
Dawuwa taitayinta tayi jin muryarsa, sosa wuyan ta tayi ta dede ta nutsuwar ta kana ta ce.
“In ka tuna inda mu ka haɗu gaba kaɗan da Asibitin Burkachuwa kafin traffic gidan na ta gurin,kuma se dare zan dawo”
Da daddaɗar muryarsa ya furta “shikenan zan zo in ɗauke ki in na yi sallah isha “
“Okay.”
A haka kiran ya katse,ta fi minti biyu tsaye ba ta motsa ba tana tuna abinda ya faɗa mata na ta tura mai Address din inda take. Ita de ta san ko ana ha maza ha mata bazata taɓa barın kowa yasan da tana rayuwa a wannan gida ba shine kaɗai safe place din da take dashi.
Duba abincin da ta ɗaura tayi ta ga har ruwan ya tsotse hakan yasa ta sauke sannan ta zuba musu a tray kasancewar dama tare suke ci da Inna dan haka innan ta sabar mata.
A falo ta ajiye sannan ta ɗauko musu ruwan sanyi,ta zaune kan carpet tayi zaman cin abinci ta kwala kiran Inna
“Inna na gama fa”
“To ga ni nan ƴar albarka” ta fito tana zama. Bayan sun kammala cin abincin ne ta shiga tayi wanka da alwala saboda lokacin sallah azahar yayi ga shi bacci take son yi amma sai da ta yi sallah kafin ta sa ƙananan kaya wando iya guiwa da yar singilet ko hula bata tsaya sawa ba tabi lafiyan gado ta kwanta.
Wayar ce tayi ɗan ƙara alamar sako ya shigo, dubawa tayi ta ga Mujahid ne ya turo mata da number kamar yanda ya ce ze turon ga sunan mutumin a gaba da number Al’ameen. mayar da wayar tayi ta kifa kan ta dan ta fi so se ta farka daga wannan baccin da yake azalzalanta sannan sai ta kira sa.
GOMBE HIGH COURT
Alhaji Mustapha Lelewal tare da Alhaji Jabir Lelewal zaune su ke a office