Showing 30001 words to 33000 words out of 96407 words

Chapter 11 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3605

ba ta juyo gaba daya rai a ɓace saboda yanda ta shigo mata daki without her concerned ya bata mata rai. taya za ka shigo bedroom din mutum ba knocking ba komai what if ka same sa a wani yanayı yanzu bata san for how long take cikin dakin batare da sanın ta ba wannan dalilin yasa ta dube ta

“Amma kin san hakan ba dede bane ko? Ta ya za ki shigo min daki kai tsaye haka? What if ina sauya kaya ko wani abu?”

Langwabe kai tayi tana ɗage kafaɗa alamar I don’t care “to menene dan na shigo kina sauya kaya? Kina mace ina mace I see nothing wrong with that Alisha just relax Hajiya “ Wani bakin ciki ne ya tokare mata wuya ta ji kamar ta wanke ta da mari amma she tries to cool her temper saboda ta san in ranta ya baci tsaf zata iya illatata.

“Yusra ki ke ko? İn haka ki ka saba yi a gidan nan to don’t dare try this nonsense with me again, saboda ni ba yar iska bace kar ki kuskura ki ƙara min wannan abin bana so I so much love my privacy you gerrit?”

Kamar wacce ta ɗauki abinda ta ce din ta hau nodding head cikin kissa ta ce “calm down angry bird,na zo ne in ta ya ki hira sannan kuma in ba ki tsaraban da na kawo” ta yi maganar tana zaro chocolate daga aljihun wandon jeans ta sake cewa “na bawa su Ameera na su shisa naga kyautuwan in biyo ki in kawo miki naki” ta faɗa ta miƙe ta isa inda take zaune ta ajiye mata shi a gabanta, sannan ta ɗaura hannunta kan kafaɗarta tana wani shafawa kamar wata mai shafa mai “Ban yi tsammanin haka ki ke da zafi ba, I love that “ ture hannun nata tay a jikinta tana wurga mata harara.

“Take care “ ta faɗa tana fita a dakin bayan ta sakar mata murmushi me kashe zuciya. cike da takaici take shiryawa saboda Yusra ta gama ɓata mata mood din ta,duk abinda take yi ta gama gano take-taken ta tana jiran ta sake gwada mata wannan haukan ne ta mata abinda ba ta yi tunani ba, dan se ta nu na mata true color nata.tana shiryawa tana jan tsaki minti-bayan minti.

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

17 & 18_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

17 & 18

“Mtssssw wannan gida na Ɗan gaske be haɗu ba, kowa da kalan iskancin sa aikin banza” yau ne karo na farko da ta yafa babban mayafi akan doguwar riga fitted gown da ta sanya, be wani kamata ba tayi ɗaurinta simple ta feshe jikinta da turare ko kallon kanta bata yi a mirror ba ta fita a dakin domin ita ba Ma’abociyar kwalliya bace ko kwalli bata sawa balle wani kwalliya. Dakin Adda ta je suna hira kamar wayanda suka jima da sanın juna.

Suna cikin hira bacci ya saci Adda wani tunani ne ya zo mata da sauri ta fita tunda ta sauko har ta fice a main falo bata haɗu da kowa ba, gun me gadi ta nufa.

“Adda ta aike ni karɓo mata saƙo a junction “ jin ta ambaci Adda ne yasa ya buɗe mata kofa yana kallon lokaci ya ga yanzu Karfe 8:20 yana mamakin to me zata karɓo a wannan lokacin. se da tayi ɗan nesa da gidan sannan ta samu abin hawa.

Inna na zaune ta ga shigowar ta kana ganin fuskarta ka san tana cikin damuwa amma lokacin da Alisha ta shigo se ta sauke numfashi tana faɗin “Alisha lafiya kuwa na jiyo ki shuru ?”

Zama tayi a kusan ta tana duban yanayinta “Inna meke damunki?”

“ Ƴar nan babu komai, kawai na shiga damuwa ne saboda shurun da na ji ki ina ta addua Allah yasa komai lafiya “

Yanda take son ta da kaunar ta ne yake bata tausayi bayan ita tasan bazata yi wani tsawon rai ba saboda ciwon zuciyar da take ɗauke dashi,bayan ahalinta inna ita ce macen da take matukar so domin ita ce ta zamo mata uwa bayan Mommah,hakan yasa take yi mata komai domin ta faranta mata,matar da ta riƙe ta, ta so ta lokacin da ta samu taɓin kwakwalwa ai dole ta so ta, domin ta zauna da ita tsakani da Allah ne bawai dan kudin da take dashi ba,slowly ta kwantar da kanta akan cinyar Inna ta yi shuru a yayinda Inna hannunta yake kan ta tana shafawa.

“Bazeyu in tafi da wayata can gidan ba da za mu dinga waya ai,amma bazeyu ba dole za ki yi hakuri na wasu kwanaki saboda yanzu ma dakyar na iya fitowa ina son in yi in koma gida ne kafin mazan gidan su dawo”

“Shikenan ki kiyaye don Allah dan wayannan mutanen ba abun yarda bane “

Kai ta gyada kana ta shiga dakin ta tana me jan kujerar table din ta zauna ta kunna system din ta da komai ta fara kallon gidan Peter da ta sanyawa karamar camera batare da sun sani ba saboda ta je gidan ne a matsayin an aikota man ta sa camera a bakin gate ta ciki. Duba abubuwan da take bukatar gani tai maganar da ta ji masu gadi suna yi ne yasa ta fahimci baya ƙasar kashe komai tayi ta tashi ta ɗau maker sannan ta canza masa date.

Haydar da ya fito daga gidan Sadeeq ya ɗau hanyar gida ne ya hango ta a junction din jeka da fari, tana tsaye ya gane motarta ne yasa mu matsala be yi niyar tsayawa ba ya murtuke fuska kamar be santa ba ita kuwa tana ganin motar sa ta tsaya a gaban sa tana roƙonsa da ya tsaya

se da ya ja tsaki kafin ya tsaya ya fito yana haɗe fuska.

“Haydar please can you help me fix my car?”

Wani uwar harara ya wurga mata “na miki Kama da machanic ne?”

Girgiza kai tayi alamar ah ah tana matso kusa dashi cikin tafiyar yanga ta ce “Tom ka taimaka ka kaini asibitin Zainab burkachuwa dan Allah "

Shi se yanzun da ta matso ya lura da irin kayan da yake jikinta riga da wando ne sun kamata se gyale da ta ɗaura akanta girgiza kai yayi takaici kamar ya yi yaya wai wannan ita ce ake so ya aura. Ko kaɗan be yi niyar tsayawa ba balle ya mata magana, kuma ba domin ta haɗa sa da Allah ba babu abinda ze sa ya taimaka mata.

Motarsa ya koma ya shiga yana matsa horn ba ɓata lokaci ta zo ta shiga gaban ta zauna tana masa murmushi “thanks my husband to be “ be kulata ba suka ɗauki hanyar asibitin Zainab burkachuwa suna isa ta kira waya “na iso kuna ciki ne?”

Be ji abinda aka sanar mata a wayar ba ya sake jin ta ce”okay kun koma gida Kenan to shikenan se gobe kawai zan zo gidan “ta katse kiran

“Honey wai sun koma gida. mu je gida kawai” se da ya watsa mata banzan kallo sannan ya soma driving.

Wani keke napep ne yazo kusa da motarsa kamar an ce ya ɗaga kai aikuwa idanunsa suka sauka kanta duk da ta sanya face mask amma seda ya gane ta. A can ƙasan maƙoshi ya kira sunan ta “Alisha “ya faɗa yana kallon time yanzu karfe tara ne da minti arba’in tunani ya fara me ta fito yi a wanann lokacin, se kallon ta kawai ya ke cike da mamaki amma ita bata gan sa ba saboda kanta ba ya setin inda motar nasa yatake

Yin gaba napep din yayi ba shiri ya bi bayan su yana me shan gaban napep din ganin abinda ya yi ne yasa ta kallan sa “honey lafiya “ko uffan be ce mata ba ya sauka a motar.

Sosai ta ji gaban ta ya faɗi lokacin da tayi arba da kyakyawar fuska Haydar da yake dunfaro su,ji tayi kamar ta zama tsuntsuwa ta fire, yanzu in ya tambaye ta wani irin karya za ta masa she’s so nervous but tried to calm her self down.

Leko kansa cikin napep din yayi a setin da take zaune har kamar fuskarta ze taɓo nasa kamshin turarensa yana me dukan hancinta bata san lokacin da ta shaka ba tana sauke ajiyar zuciya a ɓoye nan ta ji ta sake samun nutsuwa. Hannu yasa ya janye face mask din ƙasa yana duban yanda ta tsuke fuska cikin tsare gida dan kar ma ya zo mata da wasu tambayi da bazata iya amsa shi ba.

“Daga ina ki ka fito a irin wannan lokacin Alisha ?”

“Na je kwaso sauran abubuwa na ne a gidan kawu na amma sun hanani shiga gidan “ ta faɗa tana yin rau-rau da ido ga idon da yake sheki kamar ruwa ya taru a cikin su.

“ But why will you even go to them? mutanen da su ka nu na clearly ba sa san ki, fito mu tafi” ya faɗa yana riƙo hannun ta tafito,duk abinda suke yi tana zaune a motar tana ganin su ta cika tam kamar zata fashe ganin yanda Haydar yake wani nan nan da Alisha. Fito da 2k yayi ya miƙawa me napep din motar sa suka isa ya buɗe mata gidan baya ta shiga. kamshin turaren mace ne ya doki hancinta da sauri ta kai duban ta gaban motar sa ta ga macece a zaune bata yi tunanin komai ba ta gyara zamar ta.

Ta mirror ya kalle ta ya ga yanda ta ke ta lumshe ido cike da kulawa ya ce “Alisha are you okay?”

Da sauri ta dube sa kawai se ta gyada masa kai,a karo na biyu ya kuma cewa “are you sure “

Murya a marairaice ta ce “uncle Haydar ba komai fa “ kai ya gyada sannan ya soma driving da ga nan kuma ba wanda ya sake cewa komai a cikin motar, ita Alisha tana tunanin wannan din da take zaune gim gaban motar wacece,haka ita ma Meenal abinda ke ranta kenan sannan wani wutar kishi ne yake ta hayayyako mata a kirji ganin yanda Haydar yake yi mata.



“Ke ai na zan ajiye ki ni gida zamu wuce” ya yi magana idon sa na kan hanya.

Cike da kissa ta ce “Honey nima kawai mu wuce gidan, dama gobe zan zo ni amma yanzu tunda ga ni ga kai se mu tafi gidan “

Saboda baya son yawan magana se kawai ya ce “okay “ Alisha da ta ji ta kira Haydar da honey ne yasa ta fara tunanin ko de budurwarsa ce,hakan yasa ta ɗan leka fuskarta kafin ta taɓe baki ta kwantar da bayan ta tana jan tsaki ƙasa-ƙasa yanda babu wanda ze ji,duk abinda take yi idanun sa na kanta yana kallanta a mirror, dariya ta ba sa time din da ya ga tana lekan Meenal da kuma yanda ta taɓe baki ta ja tsaki murmusawa kawai yai.

“Honey yanzu yaushe Uncle ya ce zaa fara shirye-shiryen auren mu”

Ɗan satan kallan ta yai again ta mirror ya ga yanda ta saki ɗan ƙaramin bakinta tana sauraran Meenal,da be yi niyar amsa mata ba amma dan ya ga reaction na ta yasa shi cewa

“Meenal ban sani ba ki bari in mun je gidan se ki tambayesa kawai”

“Ohhh nagane ita ce Meenal din kenan yar Habibu katanga dakyau “ ta faɗa a ranta tana ɗan gyada kai.

Dariya tayi jin irin amsar da ya ba ta “shikenan ai ni zan tambayi uncle din gobe da safe,Honey wacece wannan ko yar uwar ku ce”

“Eh “ kawai ya faɗa yana tuki,side din Alisha ta juyo tana kallanta, se da gabanta ya faɗi ganin yanda take da tsananin kyau,, ta fita kyau nesa ba kusa ba, duk da ita farar fata ce Alisha kuma baƙa, amma ta mata fintinkau a kyau hakan yasa ta shan jinin jikinta “hi sunana Meenal fiancé uncle din ku“

“Ohhh sannun ki” ta faɗa a takaice dan wani haushin ta ne yakama ta ganin yanda take abu irin na cikakkun ƴan bariki ga wasu yan iskan eye lashes da ta saka sun tsaya tsage-tsage.

Yana jin su kuma yana kallon su ta mirror, yanda take tsumewa ne ya sa dariya kusan kufce masa amma ya yi kokarin dannewa.

“Kina bukatar wani abun ne ?” Da sauri ta ce “Noo honey babu abinda nake so” ɗan hararan ta yayi “ba dake nake yi ba,Alisha kina bukatar wani abu kafin mu isa gida?”

“Nothing uncle” a haka suka isa gida Meenal se jan Haydar da hira take yi shi kuma yana bata amsa sama-sama kamar wanda aka wa dole. Ita kuwa tana baya tana jin su idanun ta lumshe kamar wacce ta fara bacci. Yana yin fakin ta bude motar ta fita ta ba su guri,bin bayanta yayi ya bar Meenal ita kaɗai a motar.

Cin mata yai yana “Saurin kuma duk na meye ne?”

Cire facemask din da taji ya matse mata kunne ta yi “am just tired ina son in je in huta ne “

Gyara tsayuwar sa yayi yana kallan yanda fuskar ta har yanzu babu walwala “kina jin babu dadi ne?“

Bakatatan tambayar ya zo mata domin ba ta yi tsammanin sa ba “akan me fa?” Ita ma ta jefa mai tambaya a madadin bashi amsar tambayarsa.

Ɗaga kai yayi ya kalli sama yaga yanda sararin samaniyan yayi kyau ga taurari ko ta ina, batare da ya saukar da kan ba yace “kina son amsa tambaya da tambaya”

Za ta yi magana kenan Meenal ta iso inda suke zura hannunta tayi cikin tafin hannunsa ta riƙe gam tana murmushi,kallon ta yai ze yi magana ta yi saurin ɗaura hannun ta akan lips dinsa tana kashe mai ido daya “kar ka ce komai Honey”

Taɓe baki tai ta wuce ciki abun ta

Buge hannunta yai “ba ki da hankali ne? Kar ki sake taɓa ni kina ji ko?” Ya wucewa ciki bin sa tayi tana dariya tare da kiran “Honey” amma ko juyo wa be ba.

Su Yusra da suke zaune a main falo suna kallo ne suka ga shigowarta “Alisha ina ne ki ka je ki haka tun dazun mu ke ta dubak?” Ameera tayi maganar tana zuwa gurin ta tana riƙo ta suka zauna.

Yusra da tunda ta shigo take bin ta da ido ta kasa janye idanun ta akan ta tayi shuru tana jiran ta ji amsar da zat a bayar.

“Na je gidan kawu na ne kwaso wasu abubuwana amma suka hanani shiga gidan shine a hanyar dawuwa na haɗu da Uncle Haydar mu ka dawo tare”

Jikin su yayi sanyi matuka yanda take magana ya sa su jin ba dadi, domin yanda muryarta ke fita kamar zata yi kuka rungumeta Ameera tayi tana ba ta hakuri,cikin kula wa duk suka ta ce mata tayi hakuri wata rana su da kan su za su nemeta. A haka su Haydar suka shigo suka same su

Ba ƙaramin mamaki suka yi ba ganin sa da Meenal dan basu yi tsammanin hakan ba zama tayi a cikin su suka gaisa sama-sama dan duk ba wani yin ta suke yi ba musamman Yusra sam ta tsani Meenal hakan yasa ta jan tsaki ta bar falon.

Shima Haydar part din sa ya wuce Zainab ce tana yatsina fuska ta ce “amma me ya kawo ki gidan mutane da dare haka?”

A gadarance ta amsa “sooner or later In brother din ku ya aure ni gidan nan zan dawo dan haka i have the right to come anytime na ji ina son hakan” tayi maganar tana ɗaukan hand bag din ta ta nufi part din su Ameera din da banzan kallo suka bi ta “kai Subhanallahi yanzu me Baba ya gani a jikin wannan yar iskar da har yake son aurawa ɗean sa ita dan Allah “Zainab ta faɗa cike da takaici

Tsaki Ameera tayi “hmm kema de kya faɗa. wlh uncle Haydar sam be dace da irin wannan ba,mutum me hankali da kamala amma zaa haɗa sa da wannan abar”

Alisha da ta sako baki cikin hiran su din ne ta ce “ku dena aibatata se ku ga uncle Haydar ya zama silar shiryuwanta” duk zaro ido suka yi suna haɗa baki wajen faɗin “wannan din? lallai “

“Ke Alisha anya a cikin Gombe ki ke ma kuwa? Ke kin san hau din Meenal ? To babu wanda za ki faɗa masa sunan ta yace be san taba. Ke bara ki ji Meenal yar iska ce ta gaske shine kawai “ murmushi tayi ta girgiza kai domin yanda Ameera ke magana ne ya bata dariya

“Ameera Allah ya shirye ki” ta faɗa tana murmushi .

“Eh mana ai gaskiya ta faɗa Alisha,kin ga Yusra da Meenal ba sa jituwa. saboda wata ƙawar Meenal wai ta taɓa ce wa Yusra yar lesbian nan suka yi ta case dakyar maganar ya mutu, daga nan ne fa Yusra ta tsane ta” Zainab ta ba ta labari jinjina kai tayi a ranta ta ce “ai ba sharri ta mata ba yar less din ce “ a fili se cewa tayi “lallai kam ba su kyauta ba”

Tashi tsaye Zainab tai ta kashe TV ta dube su “ ku zo mu je mu kwanta “

“Alisha meyasa ba zamu dinga kwana a part din mu tare ba?”

Yaƙe ta yi itama ta miƙe ta riƙo hannun Ameera din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login