Showing 9001 words to 12000 words out of 96407 words
Chapter 4 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
yi hanzari wajen ganin ya riƙe sitiyarin amma fa lokaci ya kure masa saboda wani haske da ya dauke masa ido nan suka bugi abinda bazasu iya cewa ga sunan sa ba. nan motar na su ya dinga juyawa akan titi dan ma Allah ya taimake su ba su bugu da gungumen icen dake gefen titin ba.
Gaba dayan su suman yan mintuna suka yi sanadiyyar fargaba da suka shiga se bayan wasu mintuna tukun suka dawo hayyacin su, inda kowa ya hau duba jikin sa amma babu ciwo, hakan yasa suka hau godewa Allah.
Buɗe murfin motar ya yi ze fita hajja hauwa ta hau cewa
“Labaran ina kuma zaka mu da zamu godewa Allah sannan mu ƙarasa asibiti”
“Hajiya na ji mun buge abu shine nake son ganin menene wannan kar ya tare mana hanya”
Kai ta gyada masa shi kuma ya fita a motar,kamar wani mara gaskiya Labaran ya fara tafiya yana dube-dube saboda shi de ba baya ba inde wajen tsoro ne to ze iya lashe lamban yabo.
A gaban motar na su yaga mutum kwance alamar de su ne suka yi sanadiyyar hakan. cikin tsoro-tsoro ya tsuguna ya sa hannu a fuskar da yake rufe da abu, ya yaye sa nan yaga matashiyar budurwa kwance gefen kanta na zubar da jini,hannu ya sa a hancinta ya ji tana numfashi sama-sama da gudu ya isa motar yana kwankwasa glass din gefen hajja hauwa zugewa ta yi tana mai kallon lafiya,saboda ganin sa da ta yi a wani irin yanayi.
“Ya aka yi kuma?”
Murya na rawa ya ce “Hajiya wallahi mun yi kisan kai wayyo mun shiga uku”ya ƙarasa maganar yana ɗaura hannun sa akai
Kallon shi duk suka yi a firgice da sauri ta ce “Labaran kamar ya kisan kai?me kake nufi da kisan kai wa mu ka kashe?”
“Hatsarin da mu ka samu yanzu ashe ita muka buge tana nan kwance cikin jini “da sauri ta buɗe ta fito tana me faɗawa maryam da kar ta je ko ina.
Ko da suka isa inda matashiyar take babu ɓata lokaci suka kamata suka sanyata a motar suka shiga suka nufi asibiti.
Karfe hudu da rabi dede suka shiga asibitin ZAINAB BURKACUWA suna shiga kuwa nurses din da suke night duty suka tare su tare da wucewa da Maryam labor room ita kuma matashiyar suka nufi Emergency room da ita. Zama Hajja Hauwa ta yi tana girgiza kai ta rasa ta ina zata fara addua kawai take yi a ranta Allah ya fito da dukan su biyu lafiya.haka yake a bangaren labaran driver shima zama ya yi ya buga uban tagumi kamar wanda aka wa mutuwa.
Se karfe biyar aka fito da jariri aka kawo mata tare da mata albishir maryam ta haihu lafiya ta haifo ɗa namiji.
Murmushi ne ya subuce mata lokacin da ta yi arba da jikanta me tsananin Kama da Uncle din sa wato ƙanin mahaifin sa saboda babu abinda ya bari na sa.
Kallon doctor ta yi ta ce “to ita kuma wancan baiwar Allah fa??”
“Gaskiya ba domin ku din kun zo a mawuyacin hali ba da gaskiya ba za mu taɓa wancan yarinyar ba. saboda case ne da se police sun sa hannu wannan ya kasance doka,amma yanzu ana bata taimakon gaggawa kuma Alhamdulillah komai na tafiya dede saboda bata wani raunata sosai ba”
“Allah ya maka albarka yaro. ni na sanı kuma kun yi kokari yanda ku ka cece rayuwar yarinyar nan Allah ya saka muku.”
“Ameen hajiya “
Dakin da aka mayar da Maryam ta nufa ta zauna a gefenta tana kwantar da yaron a jikinta tare da kura musu ido.
Bayan ta idar da sallah asuba ne tana kan sallaya bata motsa ba ta aika labaran driver ya je ya ɗauko mata wayar ta. Nan ta fara kiran yan uwa da abokan arziki tana sanar da cewa maryam ta haihu.
Kafin 7:00am an fara zuwa asibiti inda kowa ya zo yake taya maryam murnan sauka lafiya,tare da yaba kyau da yaron ya yi nan aka soma shirye-shiryen komawa gida da mai jego.
Shigowa wata nurse ta yi ta dubi hajja Hauwa ta ce “Hajiya yarinyar ta farka”
“Masha Allah bari ina zuwa”
Kallon ta duk suka yi banda maryam Wata babban mata ta ce
“Hajja hauwa wata yarinya kuma ake magana akai ?”
“Wallahi Adda jiya a hanyar mu na zuwa nan mun haɗu da hatsari inda muka buge wata yarinya,shine yanzu suke sanar da ni ta farfaɗo mu je mu dubata “
Babu musu duk suka rufa mata baya ko da shigan su dakin da take, samun ta suka yi ta haɗe kai da guiwa ta dukunkune jikinta da bakar doguwar hijabi tana kuka ƙasa-ƙasa.kan ta da ta bugu an naɗe mata shi da bandege ga dogon gashinta dake zube a gadon bayanta.
Sallama suka yi suka shigo duk suka tsatstsaya,hajja hauwa ta zauna a kusa da ita tace
“Yarinya sannu ko!.. mune muka buge ki jiya bisa tsautsayi fatan zaki yafe mana kuma ki bamu damar mayar dake ga iyayen ki?”
Sautin kukan ta ne ya ƙaru ba tare da ta ɗago kai ko ta kula su ba ta ci gaba da rera kukanta. Kallon juna suka yi ganin bata ce komai ba hakan yasa Adda ta zauna a gefenta ta ɗaura hannunta a bayan ta
ta furta
“Yi hakuri yan mata kin ga baki da lafiya ki yi hakuri da wannan kukan ki ɗago mu yi magana dan Allah kin ji ko?”
Jin tana haɗa ta da Allah ne yasa ta ɗago black beauty face din ta a hankali da kumburarrun idanunta ta dubesu tana kuma dukunkunewa gu daya tana musu kallon tsoro saboda ba ta san su ba,murmushi duk suka yi ganin yanda take musu kallon tsoro.
“Kar ki ji tsoron mu,mu ma mutane ne kamar ke,ya'ya sunan ki?”
Sukunyar da kanta ta yi ta soma wasa da yatsunta a yayinda hawayen ke ci gaba da zuba a idon ta. Da siririyar muryarta ta ce
“ALISHA”
Ta faɗi sunan a taƙaice.
“Suna me dadi. ke din daga ina ki ke ?ko de anan cikin Gombe kema ki ke tare da iyayen ki?” Hajja hauwa ta mata tambaya,a madadin ta bata amsa se ta fashe da kuka tana rungume guiwowinta da hannayenta.
Fahimtar da suka yi yawan tambayoyin da suke mata ne yasa take kukan yasa suka sauya maganar ta hanyar faɗin
“Shikenan dena kukan tashi mu tafi gidana, in yaso in kin samu sauki se mu yi magana kin ji ko?”cewar Hajja Hauwa
Gyada mata kai ta yi kawai without saying a word,. riƙeta Adda ta yi ta taimaka mata ta miƙe suka fice a dakin suka nufi filin fakin din motar. inda motar biyu yake jiran su shiga suka yi suka bar asibitin.
Kai tsaye anguwar ARAWA suka nufa,horn driver yayi a bakin gate din matsagaiciyar gıda me kyau. buɗe gate din me gadi ya yi duka motoci biyun suka shiga. gida ne flat me kyau de de zaman mutum daya zuwa biyu ne ba wai wani babba bane yana da tsari sosai. Fitowa suka yi suka nufi kofar falon inda Hajja Hauwa ta buɗe suka shige. Adda da maryam da wasu mata biyu suka shiga daya daga cikin dakuna uku da suke ciki. Inda Hajja Hauwa kuma ta nufi wani bedroom room da Alisha . Dakin babu wani tarkace katifa ce six by six akan gado,se wani wardrobe,gefe kuma wasu akwatuna ne guda biyar a jere. ga kofar da ze sadaka da toilet Dakin ya haɗu sosai.
Tunda suka shigo dakin kan ta a ƙasa, sannan kuma yatsun damanta tana amfani dasu wajen wasa da zoben azurfa dake hannunta na hagu.
Murmushi Hajja Hauwa tayi bayan ta karanci Alisha na wasu mintuna ta fahimci yarinyar tana da matukar kunya,miskilanci,da kuma tsoro haɗe da rashin son hayaniya sosai.
Fuskarta a sake ta ce “Alisha...wannan dakin ƴata ce Yusra ita ce yar auta ta,yanzu tana abuja taj e hutu gurin dangin mahaifinta,za ki kasance a nan dakin na ta kuma sanan kasancewar ba ki da kaya zaki iya amfani da kayanta.”
Kai kawai Alisha ta gyada mata tana tsaye ƙiƙam ta ki motsawa,saboda yanda take jin ta a takure.
“Ki yi wanka yanzu zan zo miki da abinci da kuma maganin ki.“ tayi maganar tana ficewa a dakin.
Bayan fitanta ne Alisha ta ɗago kyakyawar fuskarta ta ƙarewa dakin kallo, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe manyan idanunta da suka kumbura. A hankali ta taka har izuwa bakin kofar sannan ta danna key ta zare dogon hijabin jikinta ta ajiyesa a kan gadon a tsanake. Masha Allah Alisha kyakyawa ce sosai kasancewar ta doguwar mace me karancin shekaru,kuma baƙar mace son kowa ƙin wanda ya rasa tana da doguwar fuska me ɗauke da manyan fararen idanu me zagaye da zara-zaran gashin ido,se dogon hanci da ɗan ƙaramin bakinta da ya kasance pitch color,idan muka kai duba izuwa goshinta ɗauke yake da kwantaccen saje da ya sake bayar da damar ɗawata kyakyawar fuskar na ta,se gashinta da ya kasance dogo me tsantsi wanda ya ke zube a bayanta,Alisha kyakyawa ce ajin farko se de daga yanayinta zaka fahimci akwai miskilanci ,domin daga yanayin ta zaka fahimci tana da matukar sanyi kuma sannan mara son hayaniya ce ga kalar fuskar tausayi. Jikinta na sanye da English wears riga da skirt hannu ta kai tana me taɓa bandeging kan ta nan ta ji zafi ya ratsata domin ta ɗan bugu akan dogon tsaki ta ja.
“Aikin banza kawai “ tayi maganar tana zama akan gadon wayanta dake vibrating ne ta zaro a cikin breziyarta keypad ce tana fito dashi ta ga me kiran nata ‘Inna ta’
“Hello inna kin tashi lfy?” Ta yi maganar kamar bata so
A bangaren inna kuwa cike da damuwa ta ce “Ayyah Alisha na Ina ne inda ki ka tsaya har yanzu ba ki dawo ba? Hankalina sam ya gaza kwanciya, shin kin yi abinda ya kai ki kuwa?”
Murmushi tayi yanda ta ga Inna hankalinta ya tashi
“Nayi. Wasu ne suka buge ni a hanyata na dawuwa gida bayan na binne kayan aikina, amma zan dawo soon” batare da ta jira amsar inna ba ta kashe wayarta.
A can dakin me jego kuwa hira suke yi “Adda har yanzu Sameer be dawo bane da baze zo ya mayar da matarsa dakinta ba ko be san dacewa ta yi yaji bane?”
Ajiyar zuciya Adda ta sauki ta dubi gwaggo Indo da tayi magana “ Wallahi yanasani sarai ni ban san menene matsalar Sameer ba”
Hajja hauwa da yanzu shigowanta ta samu guri ta zauna “Ai Sameer ba ze taɓa canzawa ba wani lokacin ji nake kamar bani ce na haifesa ba. Halin uban sa ya ɗauko. Ni wannan jaririn yafi min shi kuma Maryam bazata koma gidan sa ba”
“Ah ah Hajja Hauwa bazaa yi haka ba dan Allah. Wallahi nasan yanzu in ya san ta haihu ze nutsu inde ya san ya zama uba ze dawo hayyacinsa “cewar Adda.
“Hmmm Sameer fa baze canza ba,ya ɗauko dabi’un ubansa wanda a gaba za su yi danasanin wannan mummunar halin nasu. Kullum ina gode wa Allah da ya rabani da Modibbo Ɗan gaske. gashi tunda na rabu dashi nake rayuwata cikin kwanciyar hankali. Yanzu Haydar ba ɗanki bane Adda? Ko kuma ba ƙanın Sameer bane? Meyasa shi be zama shashasha irin Sameer ba. Wallahi kullum ji nake dama a ce Haydar ne ɗa na ba Sameer ba”
Hajja Hauwa ta gama magana cike da masifa.
Gwaggo indo ne tace “kiyi hakuri be kamata kina fushi da yaron ki ko da yaushe ba,ke de kawai ki dinga masa addua “
Maryam dake riƙe da jaririnta kanta a kasa duk abinda suke cewa bata ɗago kan ta ba.
Adda ne ta dubeta “Maryam ki yi hakuri da halin Sameer in sha Allah ze shiryu da izinin ubangiji”
“To Adda. Ina uncle Haydar?”
“Yana can gida bari in kira sa” ta ɗau waya zata kirasa Kenan ta ga ‘Mrs Hashim zakewa’ na kiranta ɗagawa ta yi bakinta ɗauke da sallama yanayin fuskanta ne ya sauya
“Innalillahi wainnailaihi rajuun,kulli nafsin za'ikatul mauut”
Duk kallon ta suka tsaya yi dan jin waya rasu bayan ta gama wayar ne Hajja Hauwa ta tambaye ta “Adda waya rasu?”
“Matar Hon. Hashim zakewa ce ta kirani take sanar dani daren jiya wani ya shigo har gida ya yi wa mijinta Hashim zakewa kisan gilla yanzu haka ana zaman makoki”
Gaba daya dakin ne ya kaure da salati sosai mutuwar Hon Hashim zakewa ya taɓasu, domin Hon Hashim Zakewa aminin mijin Adda ne wato Hon Modibbo Ɗan gaske.
“Allah yaji kansa. Bari in je in kaiwa yarinyar nan abinci kar in bar ta da yunwa “ Hajja Hauwa tayi maganar tana sawa Alisha abinci sannan ta fice
Kwankwasawa tayi Alisha dake tsaye ne ta koma ta zauna tana “a shigo”
“Sannu yarinya ga abincinki da magani, kin ji ni shuru wallahi rasuwa aka mana “ tayi maganar tana zama kusa da ita.
Cikin sanyin murya ta ce “Allah sarki waya rasu haka?”
“Hon Hashim zakewa ne,wai wani makashi ya shiga gidan sa ya masa kisan gilla”
Ta ƙasan ido ta kalli Hajja hauwa da kyau “Allah sarki amma ku meye haɗin ku dashi ?ko ɗan uwan ku ne?”
Girgiza kai Hajja Hauwa ta yi “ah ah ba ɗan uwan mu bane. Hashim zakewa aminin tsohon mijina ne wato Hon Modibbo Ɗan gaske nice uwar gidansa,se kuma wannna matar da mu ka zo gurinki tare ita ce matar sa ta biyu. Amma ni yanzu mun rabu dashi “
Tunda take magana Alisha ta tsareta da ido tana kallon ta kwakwalwarta se juya maganganunta take, wato de yanzu ta shigo cikin ahalin Ɗangaske batare da sun san ta ko ta san su ba lamarin ya matukar bata mamaki kuma ya mata.
Cikin son shan cikinta domin ta lura da Hajja Hauwa akwai surutu irin mutanen nan ne da ake Kira faɗi baa tambayeka ba
“Kenan wacce ta haihu ƴar ki ce?”
Dariya tayi “ ah ah ba ƴata bace surkata ce. Mata ce a gurin babban ɗana Sameer Modibbo Ɗan gaske”
What a coincidence 🔥🔥🔥🔥🔥🔥
(Da ni da ku duk mun girgiza 🤭😳 Allah baya bacci cikin ruwan sanyi Allah ya wurgata cikin su)
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
7 & 8*_🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi, to Kar ku yi ƙasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin nawa 08166018849 Mrs isham domin a tallata muku hajar ku.❤️😊
7 & 8
Dariya tayi “ ah ah ba ƴata bace surkata ce. Mata ce a gurin babban ɗana Sameer Modibbo Ɗan gaske”
“Ban taɓa tunanin ƙaddara za ta shigo da ni cikin ahalin Ɗan gaske ba,tabbas wannan dama ce babba a gare ni”
Tayi maganar a ranta
Ɗan taɓata tayi “Alisha tunanin me ki ke yi haka?”
“No babu komai”
“Shikenan to ga abincinki ki ci, se ki sha magani” tayi maganar tana barin dakin.bin bayanta tayi ta sa key ta dawo tana riƙe kugu tare da kallon sama
“Allah baya bacci”
A can kuwa office din commissioner of police manyan polices ne zaune suna meeting akan yanda zaa fara binciken kisan Babban ɗan siyasa da aka yi wato Hashim zakewa.
“Wannan babban case ne dole muna bukatar kwararren jami’in da zamu ɗaura akan wannan binciken. Shisa na kira kwararren jami’in da ya kware wajen binciken masu laifi da bayyana gaskiya”
DPO ne ya dubi commissioner da ya yi magana yanzu “wa kenan yallabai?”
“ Detective chief superintendent HAYDAR MODIBBO ƊAN GASKE (DCS Haydar) shine wanda ze yi wannan binciken. ina da yakinin ze nemo wannan makashin ,yanzu haka na kira sa nasan ya iso ko ya kusa isowa"
knocking aka yi "come in "
wani kyakyawan saurayi ne ya shigo kalan fatar sa ruwan tarwada yanada tsayi. jikinsa a murɗe yake,yana da matsagaitan manyan idanu da dogon hanci, bakinsa ɗan karami pink,fuskansa na kewaye da saje ga kuma gemu ɗan dede. gashin kansa bashida yawa saboda aski low-cut da yayi fararen idanunsa na manne da farin glass. Jikinsa na sanye da farar shirt da wando brown yayi stuck in. Hannunsa ɗaure da Rolex takalmin kafansa cover shoe baƙi. Detective chief superintendent Haydar kyakyawa ne na karshe handsome caramel guy,domin masu kalar fatar sa su ne ake kira da masu caramel skin,shi ba baki ba kuma ba fair skin ba,jikinsa glowing kawai yake. Ya haɗu iya haɗuwa. Very gentle guy kana ganin sa ka ga natsatse kuma kamilallen saurayi ɗan shekara ashirin da bakwai zuwa da takwas.
Da zazzakan muryarsa ya furta “can I come in?”
Murmushi duk suka yi “Bismillah DCS Haydar”
Shigowa yayi ya sara ma commissioner sannan ya zauna
“Sir kiran gaggawa da ka yi min shin akwai aikin da zan maka ne?”
“Kwarai kuwa Haydar. nasan cewa ka ji labarin mutuwar aminin mahaifinka da aka shiga gida aka kashe sa. Na kira ka ne domin in sanar dakai binciko wannan makashin ya rataya a wuyanka “
Shuru Haydar ya yi yana shafa sajen sa “okay sir “
Miƙa masa file din Hon Hashim zakewa da aka buɗe yayi tare da faɗin “ko ƙarkashin ƙasa wannan makashin ya shiga ka nemo sa. Sanin kan ka ne Hashim zakewa abokin mahaifin ka ne”
Ɗaura