Showing 87001 words to 90000 words out of 96407 words

Chapter 30 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3628

ba ya gida saboda a kwanakin nan in ya fita tun safe sai dare yake dawuwa,ta san Adda kuma ba ta da matsala da ita, a falo ta samu Adda zaune da wata baƙuwa su na hira har ƙasa ta tsuguna ta gaishe su kafin ta isa kujerar da Adda ta ke zaune ta matso kusa da kunnenta yanda ita kaɗai za ta ji abinda ta faɗa sannan, ta ce

“Adda zan je bakin junction akwai abinda zan karɓo ba zan jima ba”

Ciki da faraa Adda ta ce “to shikenan a dawo lafiya”

“Nagode “ ta furta tana fita.

Ko da ta isa gidan kamar kullum tura kofar ta yi ta shiga ba wanda ta samu a cikin gida,wucewa dakin Inna ta yi, ta me ta kwance amma ba bacci take ba hannunta da carbi,motsin da ta ji ne yasa ta ɗago haɗa ido suka yi ta miƙe zaune

“Alisha ke ce tafe?”

“Eh inna” ta faɗa tana zama a bakin gado.

Lallen hannunta inna take bi da kallo kafin ta maida duban ta izuwa fuskarta ta ga yanda take wani ɗaukan ido ga wani tsadadden kamshi da take bazawa,kamo hannun nata tayi ta na kurawa henna din ido dan yawansa da design din ya wuce normal henna se de na amare

“Alisha wannan lallen menene?”

Sai da ta dubi bakin kofa ta ga ba kowa sannan ta ce “Inna ina Zaid da Mujahid”

Tana bin ta da kallon tuhuma ta ba ta amsa da “su na dakin ki”

Ɗaura dayan hannunta akan na inna ta yi cike da gwarin guiwa ta soma faɗin

“Innata na san ke za ki fahimce ni,ranan jumma’a aure na ni da Haydar Modibbo Ɗan gaske,tun ranan da na zo na yi niyar in faɗa mu ku amma sai Allah be yi ba,na rigada na gama yanke hukunci zan aure sa saboda samun damar yin duk abinda na gadama,matukar ina so in ɗau fansata dole ne in shiga jikinsu “

Sosai Inna ta kura mata ido tana kallo kafin ta iya cewa “amma Alisha kina ganin wannan mafita ce me kyau kuwa? Auren jinin Ɗan gaske daya yake da jefa kan ki a matsala”

Girgiza kai ta yi tana sake runtse hannun ta gam “ah ah inna babu wata matsala da hakan ze haifar in sha Allah “

“Wani banzan shirme ne kunnuwana suke jiyo min daga bakin ki Alisha kin haukace ne?”

Su ka tsinkayo muryar Zaid a bayan su,kallan sa inna da Alisha suka yi yana tsaye a bakin kofa fuskar nan a haɗe kamar hadari.

Miƙewa duk su ka yi Alisha ta iso shi tana kokarin masa bayani amma ya ɗaga mata hannu

“Bana son jin wani ƙarin bayani daga bakin ki Malama,ashe dama abinda ki ke yi Kenan a gidan Ɗan gasken? soyayyah da ɗan sa har da maganar aure ? Wai ko nikam Alisha ko kin manta abinda mutanen man suka yi mana ne? A dare daya suka tarwatsa mu,su ka mayar da mu marayu,shine a maimakon ki ɗau fansar ki, ki ka ɓage da soyayyah da jinin wayannan la’anannun mutanen”

Kamo hannun sa da yake ta masifa dashi ta yi ta riƙe tana me girgiza mai kai

“Ya Zaid na san dole za ka ji wani iri a yayinda ka ji maganar aure na da ɗan Modibbo, amma there’s nothing like what you think,wallahi ban taɓa son Haydar ba,ban taɓa jin sa a zuciyata dede da na minti daya ba,sam baya gaba na fansata shine abinda yake raina. Na amince da wannan auren ne dan in kaskantar da ahalin Ɗan gaske. in sa su yin kuka kamar yanda suka sa mu,ban da wannan babu wani abu,sannan kana magana akan wai soyayyah ? Wannan zuciyar babu gurbin zaman soyayyah a cikin ta,abinda take so da kauna da buri guda daya ne wato ɗaukan fansar ta”

Fincike hannun sa yayi yana mata wani irin kallo me wuyan fassara kafin, yace

“Ki ka ce babu soyayyah Haydar a ran ki ko? Fansa ce kawai a gaban mu kawai Alisha,Ina son bayan mun gama da su muyi kyakyawa kuma sabuwar rayuwa me cike da inganci. In aura miki miji wanda na aminta da shi,wanda ze kula min dake tamkar kwai. Dan haka ki fasa wannan aure Alisha matukar dagaske fansa ce a ran ki”

“Noooo Ya Zaid, in na fasa auren nan shirina ze tarwatse,wai ba ka ji menene na faɗa maka bane? Bana son sa,bana son sa. Kawai na amince da auren ne saboda fansata. sau nawa ka ke son in faɗa maka haka,bana son Ɗan gaske da ahalin sa”

Murmushi ya sake wanda ya sake fito da asalin kamansa shi da ita,ya matso gap da ita jikin su na gogan na juna yana kallon ta ido cikin ido, ya furta

“To inde haka ne ki kashe Ɗan gaske da duk wani wanda ke cikin ahalin, daga babba har ɗan tatsitsin yaro. in kuma ba haka ba,zan kashe Haydar sannan ni da kai na in kashe kowa a cikin family wannan shine zaɓin da ki ke dashi. Dole ne kowa ya mutu a wannan ahalin”

Karo na farko da ta ji tsoro ya kamata,asalin tsoro ba wai tsoro irin wanda take pretending ba,ta san wanene Said,ta san muguwar baƙar zuciyarsa.

“Meyasa za mu aikata haka? They are innocent meyasa za mu kashe wayanda ba su da masaniya akan zunubin da Ɗan gaske da Sameer suka aikata? nooo Zaid I can’t do this ,we can’t hurt innocent souls”

Ƙanƙance idanunsa yayi akan ta “ina hango hakan a cikin idanun ki Alisha. ina hango so da tausayin mutanen nan a zuciyar ki,kına ta faɗin wai they are innocent, mu din ba innocent bane iyayen su suka mana haka?ko lokacin da su ke cutar da mu sun manta cewa ba mu da laifi bamu yi mu yi musu komai ba. Especially you Darling! they raped you out of mercy. they tore your soul apart, darling, and left you bleeding in silence. ke wannan be isa ya zama hujjan da za ki kyamaci jinin su ba? Abinda su ka mana kina tunanin abu ne da toɓansa ze goge a cikin zuciyar mu? Kina tunanin makiyinka ze dawo abokine bayan ya cutar da kai? ko kaɗan ba haka lissafin yake ba. Bari ki ji abinda ba ki sanı ba, Daga Ɗan gaske har ƴan ahalinsa sai na ɗau mummunar fansa akan su. musamman Haydar da ya ja raayinki har ki ka fara son shi,laifin sa Kenan da ya aikata kuma dole ya karɓi hukunci”

“Have you lost it or what? Kar ɗaukan fansa ya rufe maka ido ka aikata abinda za ka yi danasani Zaid,ɗaukan fansar mu a iya wayanda su ka mana ba dede bane,why putting innocent people a abinda ba su da masaniya an yi sa,Noo Zaid bazaka yi haka ba,and for Haydar? Zan daki kirji sau dari in faɗa maka bana son sa ko da ɗigo daya, but that doesn’t mean zan bar ka ka yi hurting dinsa. Mutum ne shi me kirki da sanın darajan ɗan adam babu ruwanka dashi Zaidddddd” ta ƙarashe maganar a kausashe da cizewa tana nuna sa da yatsa alamun gargadi.

Kallon yatsan yayi yana jinjina kai wani sabon tsanan Haydar na cika masa zuciya sakamakon ta dalilinsa ne har ƴar uwarsa da yake matukar so da kauna take jayaya dashi har da nuna masa yatsa.

Murmushin takaici ya saki, yana girgiza kai haɗe da taune lips din sa na ƙasa. yana cikin bacin rai amma yana dannewa saboda yasan matukar Alisha ta fusata shi ta tabbas ze iya zuwa ya cinnawa gidan Ɗan gaske wuta cikin dare uban kowa ma ya mutu.

“Kin ja na sake tsanan sa,na yarda duk duniya in tabka kuskure amma ban da kuskuren haɗa jini da makiyana,wallahi matukar ki ka matsa se kin auri Haydar to zan tabbatar miki da abinda nake faɗa bawai wasa bane,zan kashe sa. Dan haka ina gargadan ki da ki fasa wannan auren ko kuma?”

“Ko kuma me? Wait kai ka san me ka ke faɗa kuwa? Kasan irin risk din da na ɗauka kafin na samu damar shiga wannan gida sannan rana tsaka ka zo kana ce min in fita a gidan without achieving what I wanted? you must be sick or something.” Ta faɗa tana jifansa da death stare.

Inna da gaba daya sun gama ɗaga mata hankali ne ta soma kokarin dakatar da cacar bakin da suke yi amma ta gaza,gaba daya sun ƙi sauraranta,hankalin ta ya tashi sosai ganin yanda suke cacar baki ba ta taɓa tsammanin hakan ba saboda yanda suke matukar so da kaunar junan su.

“Kin bani kunya, I’m very disappointed in you,wai Kece ki ke wayannan maganganun. To bari ki ji Alisha ko da mutuwa za ki yi sai na kashe Haydar in kuma ba haka ba ni in mutu. Bazan taɓa barın ki auri jinin makiyinmu ba kin ji ni ko?” Ya faɗa da tsawa da sai da gidan ya ɗauka,iron sa sun yi jaa tsabar ɓacin rai.

Harɗe hannunta ta yi a kirji ta na watsa masa kallo da zararrun idanunta da in suka rikiɗe suke komawa na asalin serial killer she used to be,her death stare is something to be afraid of too. Daga kallon idanunta da yanda take suka koma za ka gane she’s dangerous when she changes her face.

“I dare you Zaid, kace za ka kashe sa ko? Then go ahead. amma ka sanı bazan taɓa ba ka damar hakan ba,I’ll protect Haydar from you till my last breath,bazan taɓa barın ka yi masa komai ba,hakikanin gaskiya wutar ɗaukan fansa ko da yaushe sake ruruwa yake a zuciyata amma bazan taɓa tafka kuskuren taba wayanda basu da laifi ba. Sannan ka ce me? Bazan auri Haydar ba? Just wait and see in the next 6 days zan aure sa sannan in cika muradina sannan in bar gidan.”

Tayi maganar ne a yayinda take sakar masa shaidanin murmushinta.

Mujahid dake bacci ne ya ji yo hayaniyarsu da ya gaza gane shin hayaniya ce ko kuma de hira, ya fito a dakin ya shiga na inna nan ya tarar da abinda ke faru he was shocked to witness what is happening.

“ in haka ne kuwa zamu mutu,ki ka yi kuskuren auren Haydar sai na kashe sa dashi da iyayensa, sannan in kashe ki?in kuma kashe kaina game over “

Ya faɗa mata hakan da iya gaskiyarsa domin kuwa Zaid yana da baƙar zuciya in yace ze yi abu tofa se yayi. In kuma yace ya tsani abu to ya tsana Kenan har abada,kamar de yanzu ji yake duk duniya ma babu wanda ya fi tsana sama da Haydar saboda yanda Alisha ta nu na ta damu dashi abun ya sosa masa rai matuka da ya ja duk bugun zuciyarsa yana bugawane da muguwar tsanarsa kuma ya ɗau alwashi me girma akan sa.

“Wai me ku ke yi haka ne? Ku da yakamata ku haɗa kai dan ganin ƙarshen makiyanku ya za ku tsaya kuna fada Akan mutum daya why please, this is not the right time for all this”

Cewar Mujahid cike da damuwa dan ya ga abun na su in aka kai wani mataki to labari ze iya canza wa saboda Alisha da take tsaye tana sakar musu murmushinta me ban tsoro,dan tunda ta dawo hayyacinta ta zama psycho Alisha bawai normal bane irin kowa saboda tabin hankalin da ta samu changed her completely,matukar ran ta ya ɓaci to fa za ta iya aikata komai.

“Mujahid babu ruwan ka da abinda yake faruwa,stay out of this.” Ta faɗa tana komawa kan gadon inna ta ɗauko wayarta ta dawo inda take ta buɗe bayan wayan sanan ta fito da memory dake cikin gidansa ta dubi Mujahid

“Wannan memory na same sa ne a bangaren Sameer,ina son ka duba min menene a ciki za mu yi waya”

Ta miƙa mai ta nufi hanyar fita,daga inda ya ke tsaye ya sa hannu ya ɗamko damtsenta ya fisgota da karfi kamar ze karyata ya dawo da ita tsakiyar dakin.

“Alisha ba za ki koma gidan Ɗan gaske ba,kin gama rayuwa a cikin wannan gida, ba kuma za ki ƙara taka kafan ki a can ba”

Ba ta kulasa ba ta sake nufan hanyar fita a dakin,a karo na biyu ya kuma riƙo damtsenta da karfin tsiya ya jawota yana me wurgi da ita akan gadon inna.

“Dole na ƙarasa abinda na fara? hanani hakan ze janyo mana matsala me girma a tsakanin mu”

Ta faɗa tana gyara wuyan hijbinta da sulale.

“Zaid please let her go,akwai muhimmin abinda zan maka bayani please amini na” Mujahid ya faɗa ƙasa-ƙasa Zaid kaɗai ya ji sa.

A karo na uku ta miƙe ko sallama ba ta yi wa kowa ba ta fice a gidan sam wannan karon be yi yunkurin hanata ba se ma komawa dakin ta da yayi ya kwanta yana tuna abinda ya faru.

Ko da ta koma gidan Ɗan gaske ba ta samu kowa ba har ta isa izuwa dakin ta alamu suna ciki suna sallah La’asar wayar ta ajiye akan gado ta shiga toilet da katuwar hijab din ba ta cire sa ba,sauka idonta yai akan jacuzzi dake cike tab da ruwa, ba ta yi wani dogon nazari ba ta shiga ciki batare da ta cire hijab din ba ta nitse a ciki fuskanta ne kaɗai a wane tana jin yanda sanyin ruwan yake ratsata idanunta rufe kirif,abubuwan da suka faru tsakanin ta da Zaid kawai take tunawa. she can’t believe wai ta yi faɗa da ɗan uwanta because of a stranger who means nothing to her,se yanzu ta ke danasanin yanda ta tsaya sa’insa da shi duk da ta san ranta ne ya mugun ɓaci kuma in ya ɓaci ba ko da yaushe ta ke iya control kanta ba. Ta rigada ta san dama Zaid ba fahimtanta ze yi ba,kuma ita bazata iya fasa wannan aure ba saboda yana da muhimmanci a cikin plans din ta, ba wai dan tana san Haydar ta yi haka ba se dan tana son cika muradinta. Za ta yi hakuri da Zaid har zuwa lokacin da za ta cimma abinda take so,tasan ze yi fushi da ita me tsanani muddin ya ji an ɗaura auren.

Haka ta kwashe kusan awa daya cikin ruwan idanu rufe tana tunani iri-iri har se da ta ji ta dawo normal sannan ta fito,ta kwabe kayan jikin ta gaba daya ta yi wanka da al’awala ta fita ɗaure da towel. Sallah ta yi ta kwanta ba dan tana jin bacci ba se dan ta samu nutsuwa.

Su kuwa babu wanda ya san da dawuwar ta, Maryam ce ma ta leko dakin ta dubata nan ne ta hango ta kwance kan gado ganin kamar tana bacci ne yasa ta rufo mata kofar batare da ta san idanunta biyu ba kawai ta ƙi motsawa ne saboda ba ta san magana da kowa.

Kafin zuwa mangriba zazzaɓi ya sauko mata da ciwon kai, zuciyarta ya fara mata ciwo,ko da aka yi sallah ta ji amma ta gagara ta miƙe saboda yanda ta ke jin zazzaɓin na nukurkusan naman jikinta,tana kwance a nan din aka yi isha nan ma ba ta miƙe ba kuma bawai bacci ta ke ji ba,shuru shuru da Adda ta ji ta ne yasa ta dubi Ameera dake danna waya ta ce

“Wai ko lafiya Alisha ba ta sauko ba? Maryam tun yamma ta ce min ta ganta tana bacci. Je ki dubo min ita don Allah “

“To Adda” ta faɗa tana haurawa sama,yanda Maryam ta tadda ita itama haka ta same ta,dakin ta shiga ta tsaya akanta ta kira sunanta har sau uku amma ba amsa.

“Alisha bacci ki ke yi ne na ji shuru”

Dakyar ta iya cewa “uhm uhm”

Zama tayi gefen ta tana jin yanda numfashinta ke fita,ɗaura tafin hannunta tayi akan goshin ta nan ta ji shi rau kamar ta aza hannu man gaushi

“Subhanallahi me yake damun ki haka?"

Ba ta ce da ita komai ba,ganin haka yasa ta fita da sauri ta gangaro ƙasa ta samu su Adda

“Adda wallahi ba ta da lafiya sosai zazzaɓi ta ke yi mai zafin gaske, kuma numfashinta wani iri yake fita.”

“Ya salam haba ni na san yarinyata haka kurum bazata ƙ saukowa ba,Allah sarki baiwar Allah ashe ba ta jindadi ne” ta ƙare maganar ta na miƙewa ta nufi part dinta,bin bayanta dukkan su suka yi.

Ko da su ka shiga dakin samunta suka yi hannunta riƙe da setin zuciyarta hawaye me zafi yana gangarowa daga idanunta. Cike da damuwa sosai Adda ta zauna kusanta tana

“Alisha “

Dakyar ta iya buɗe baki, ta ce “uhmmm”

“Sannu mama na,Sannu ko “ ta faɗa tana ɗaura hannunta a jikin Alisha, jin yanda jikin yayi zafi sosai ne ya ba ta tsoro, ba ta taɓa jin zafin jiki irin haka ba. gyara zamanta tayi a kan gadon tana ɗaura kan Alisha a cinyarta tana me yi mata sannu.

“Zainab ban wayata in kira yayan ku”

Ba ta wayar Zainab tai, Adda ta danna wa Haydar dake office kira,bayan ya ɗaga ta ke sanar mai da rashin lafiyan Alisha.

Haka suka zauna dukkan su a dakin suna me mata sannu ko iya amsa su ba ta yi. ita zuciyanta ne ma yafi damunta ba zazzaɓin ba. ga shi ba ta taɓa tunanin ɗauko maganin ta ba,amma de yau kam ta yi danasani yafi cikin kwando tana daga kwance ,da ace ta ɗauko da yana fara mata ciwo za ta sha.

Baa fi mintuna arba’in ba Haydar da Sadeeq suka shigo part din Adda Ameera ce ta leka tace da su su shigo.

Tunda ya shigo yake kallan ta cike da tausayawa. gaisawa Sadeeq dake riƙe da jaka a hannun sa suka yi shi da Adda yana mata ya mai jiki.

Tsayawa Haydar yayi a gefen gadon ya zuba mata ido ganin ko motsi me kwari ba ta yi.

“Adda a samu ta ɗan zauna in duba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login