Showing 3001 words to 6000 words out of 96407 words

Chapter 2 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3620

kasa yi.

“Dr Sagir Lelewal ka yi shuru ba ka ce komai ba,da fatan zaka bamu haɗin kai ta ruwan sanyi?” Hon Hashim zakewa ya tambayesa ganin ya yi shuru.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya soma bin su da kallo daya bayan daya kana ya ce “ lallai kun ban mamaki musamman Doctors da ku ke taimakon al’umma shine da ku zaa haɗa baki wajen kisan kai? Saboda abin duniya shine zaku haɗa hannu a cuci talakawa? Haba dan Allah. Wallahi kun ban mamaki. Sannan kai kuma Hon Ɗan gaske na juyo gareka. Shi Dr William din babu mutane a ƙasar su ne da baza su yi gwajin magungunan akan su ba se sun zo Africa ? Wato Africa ne marenin wayon su? Ku yi tunanin suna so ne su durmusar da Nigeria hakan yasa suka ɓullo ta wannan hanyar. turawan nan sun tsani baƙin fata. Kar ku manta a shekara ta dubu daya da casa’in da biyu an yi irin wannan case din inda turawa suka zo Africa da rigakafi da sunan taimako suka dinga kashe mutane da wannan rigakafin. Shine yanzu zaku yarda a sake wannan abu!? To wallahi ku tuna da duk abinda ku ke yi Allah yana kallon ku dede da rai daya ku ka salwantar se Allah ya tsayar da ku a gobe kiyama. Kar ku bari son abin duniya ya kai ku ya baro ku.”

Jin maganganun sa ne yasa duk yanayin fuskansu ya sauya rai a bace suke kallon sa suna masa kallon wanda be san abinda yake yi ba.

“Dr billion Dari dari fa,kana tunanin muna ji muna gani zamu bar 100 billions su wuce mu? One hundred billion fa?”

cewar chukuemeka peter

“And so what ? Na san da cewa kana da abinda yafi two hundred millions a cikin asusunka se me dan baka karbi kudin haram ba? Kar ka manta Allah shine me bayarwa. Duk da addinin mu ba daya ba amma nasan kasan illar cin haram”

Miƙewa tsaye Hon Ɗan gaske yayi yana goya hannunsa a baya ya soma safa da marwa a cikin dakin taron

“Na ji bayaninka Dr. kuma na fahimce ka,duk duniya sun san ka kai mutum ne me gaskiya da riƙon amana da taimakon talakawa, shisa ka ke ganin bazaka iya wannan harkallar ba. Amma bari ka ji babu abinda ze sa mu yi cancelling wannan dama da ya zo mana saboda kai. Kuma ko kana so ko baka so to tabbas se ka sa mana hannu.”

Miƙewa tsaye shima yay a wannan lokaci ransa ya gama ɓaci hakurin sa ya ƙare, ya dubi tsakiyan idanun Hon Ɗan gaske yace

“Tabbas na jima ina jin ana cewa yan siyasa azzalumai ne amma ban taɓa yarda ba se yau da naji kuma na gani da idanuna. Ni Sagir Lelewal bazaa taɓa haɗa hannu dani a cutar da talaka ko daya ba. Haka kuma bazan taɓa barın burin ku ya cika ba se na rubuta ƙara a kan ku se na tona muku asiri duniya ta san da wannan muguwar shirin ku azzaluman banza da wofi “

(dan Allah in kun karanta ku yi sharing )

Cikin tsoro Dr Jamal yace “Dr dan Allah ka yi hakuri wallahi nima yanzu da na ji manufarsu har ga Allah na hakura. Ina bayanka mu da mu ke taimakon al’umma be kamata a ce mun juya mun zama dodanni a idanun su ba.”

Ɗage kafaɗa yayi yace “wannan kuma matsalar ku ce. ni de na gama magana bazan taɓa haɗa hannu a yi zalunci dani ba kuma bazan bari a yi ba se inda karfina ya ƙare Wallahi “.

Yayi maganar yana ɗaukan wayarsa da makullin motarsa ya nufi hanyar fita

“In kuwa haka ne wallahi zaka yi matukar dana sani a rayuwarka,dakai da kuma iyalanka da ka ke ji dasu tabbas zaku shiga hatsari. Zaka dawo da kan ka kana rokon da a sasanta wannan alkawari na ne”

Batare da ya juyo ba yace “ Allah ya fi ku duk wani mugun nufin ku kan ku ze koma. Wai kai a haka ne ka ke shugabantar al’umma? tabbas nasan ɗan ka na biyu HAYDAR da ya kasance jami’in CID ya san abinda ka ke aikatawa da yayi Allah wadai da kasancewarka uba a garesa”



Yana faɗin haka ya fice a dakin taron da sauri Dr Jamal yabi bayan sa. A ciki kuwa Hon Ɗan gaske ya matukar fusata da abinda Dr Sagir Lelewal ya faffaɗa masa sun yi masa zafi matuka

“Tabbas ka debu ruwan dafa kan ka. se ka san da ce wa ni Modibbo Ɗan gaske ba tsaran yin ka bane. Se na tarwatsa wannan ɗan ƙaramin ahalin nasa da yake tunkaho dashi in ban yi haka ba sunana ba Ɗan gaske ba.”.

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

3 & 4 _*🦋FANSAR MACE*_🦋

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

3 & 4

“Innalillahi wainnailaihi rajuun papa haka ku ka yi da su? Lallai mutanen nan shedanu ne, in sha Allah aniyar su ze koma kan su kar ka sanya wannan damuwar a ranka ya dame ka pls. Kasan yaran nan baza su ji dadin ganin ka a haka ba

pls papa ka rabu dasu tunda de kai ka cire hannunka ko a gaban ubangiji ba ka da laifi”

Mommah ta yi maganar hannunta riƙe da nasa fuskarta ɗauke da ƴar damuwa saboda tunda ya shigo ya ba ta labarin abinda ya faru hankalinta ya tashi amma se ba ta nuna masa ba saboda kar ta ƙara sanya masa masa wani damuwar.

“Ni kuwa nake da laifi sweetheart,taya zan bar wannan maganar a matsayin sirri? Kina tunanin za su fasa abinda suka yi niya ne?wallahi ban taɓa zaton son zuciya ze sa ɗan adam sanya hannu a cutar da rayuka da dama ba”

“Na sani papa na san hankalin ka baze taɓa kwanciya ba, amma please for the sake of yaran mu ya kamata ka cire wannan damuwan a ranka pls. Basu isa su mana abinda Allah be mana ba”

Magana ze yi idansa ya sauka akan inuwa a bakin kofa alamar an laɓe ana sauraran tattaunawarsu. Hakan yasa shi sauke ajiyar zuciya kana ya Kira sunan ta

“Alisha darling come here “ simi-simi ta shigo dakin tana sanye da doguwar rigan bacci da ya tsaya mata a guiwa gashin kan ta kuma ta raba su biyu ta kitse bindin suna lilo a baya.

Zama tayi kusa dashi fuskan ta ɗauke da ɗimbin damuwa

“Mama na baki san babu kyau yin laɓel ba? Musamman wa iyayen ki”

Idanunta ne suka yi rau rau da hawaye tace “am sorry papa,am sorry Mommah amma ba laɓel na muku ba,I came to say good night shine na ji kuna wannan maganar,papa wayannan mutanen su waye su? “

Ɗan dariya yayi saying “ke yarinyace my child bazaki gane komai ba. Bana son ki dinga jin maganganun da suka fi karfin shekarun ki.”

“Please papa I want to know what’s going on tsakanin ka dasu,na ji kana kiran sunan Hon Ɗan gaske shi din waye?”

Har ya buɗe baki ze ba ta amsa Mommah tayi saurin rigasa cewa

“Alisha darling ya isa haka ba kyau titsiye kin ji ko? oyah go and sleep Mommah and papa loves you so much “ tayi maganar tana manna mata kiss a goshi,shima Dr haka yayi suka mata seda safe badan ta so ba haka ta fita a dakin jikinta a sanyaye.

Ko da ta shiga nata dakin gagara bacci tayi, hakan yasa ta zaro wayanta ta shiga goggle tayi searching sunan Ɗan gaske aikuwa se ga hotonsa ya bayyana nan ta gane ɗan siyasa ne. Haka ta dinga bincike akan sa har bacci ya ɗauke ta batare da sanın ta ba. Shigowa dakin na ta Dr yayi karfe sha biyu domin tabbatar da ta yi bacci ya ganta kwance rungume da laptop da waya. zare waya din yai a hankali ya ga sunan Ɗan gaske ne a search bar din ta sosai ya yi mamaki, ya ɗauka ta manta da maganar da suka yi ashe ita abin na ranta har da su shiga goggle. Murmushi yayi a ransa ya furta

“So proud of you Alisha Allah ya raya min ke”

Ya faɗa yana rufeta da blanket ya kashe mata wuta ya bar dakin.

Washe gari bayan sun yi sallah ne Mommah ta je ta tashi Aryan domin ya yi wanka ya shirya ya fito driver na jiransa. Daga dakin sa kuma dakin Zaid ta shiga yana kwance yana sharan baccinsa

“Zaidu!zaidu nikam yau baka da class ne kake kwance har yanzu? Karfe bakwai fa yanzu”

Cikin muryar bacci ya ce “Mommah please ki bar ni in yi bacci jiya ban samu bacci ba “

“Na sani ai ka tsaya yin live a TikTok Ina zaka samu yin bacci dama “

Tayi maganar tana fita a dakin direct dakin ta ta wuce. ta san ko ta je tashin Alisha darling ma yanzu ba tashi zatayi ta dadi ba tunda babu abinda zata yi.

Har Dr Sagir ya yi breakfast ya tafi aiki Alisha bata farka ba kuma ya hana a tashe ta.

Dr. Sagir yana office signing some files wata nurse ta shiga “ Dr kana da baƙi a waje sun ce gurinka suka zo”

Ajiye pen yayi “su waye ne?”

“ Ɗan gaske ne da babban ɗansa Sameer Ɗan gaske”

“Kar ki bar kowa ya shigo min office nurse Nabilat “

“Okay “ ta fita

Tunani ya fara shin menene kuma abinda ya kawo Ɗan gaske da ɗan sa Office din sa.

Yana wannan tunanin ya ji an shigo masa offices. Ɗan gaske ne da ɗan sa batare da ya musu tayin gurin zama ba suka zauna

“Barka da wannan lokaci likita,mun zo kawo maka ziyara ni da ɗana amma aka hanamu shigowa whyy doctor?”

Murmushi ya yi yana harɗe hannunsa a kirji looking straight into their eyes

“Duk wayannan ba abinda ya shafe ni bane. Menene abinda ya kawo ku office dina?”

Sameer Ɗan gaske ne ya ce “actually Baba na ya sanar min da kana da wata kyakyawar yarinya a gidan ka,kuma zamu dace sosai. shine na ga yakamata in zo in tambayi auren ta ta zama na biyu a gida na. Daga nan alakar ku zata sake karfi sosai “

“You’re very stupid. Ƴata bazata taɓa shiga cikin ahali irin na ku ba. Musamman kai da ka ɗauko mummunar dabi’ar mahaifinka,ƴata ta fi karfinka. Kuma bari in sanar maka! da in aura maka ita gwara in aurawa talakan da bashi da komai wallahi. Ku yi maza ku bar office dina kafin in sa a fitar da ku”

A fusace Sameer ya miƙe Ɗan gaske ya riƙe hannunsa yana masa alama da ido da yayi shuru

“Tunda haka ka ce a gaban idannunka ɗana ze keɓance da ƴarka “

Sosai idanunsa suka yi jajir ya dau tsawon lokaci rabon da ya shiga bacin rai amma yau sun tunzurasa matuka

“Ku fice min a office marasa tunani. Kuma zan sake nanata muku ƴata tafi karfin kai da mahaukacin yaron ka”

“Zamu fita amma ka sani rayuwar ku kai da ƴar ka yana cikin hatsari” cewar Ɗan gaske sannan suka fita

Zama yayi yana runtse idanunsa kafin a hankali hawaye me zafi suka fara sintiri a idanunsa.

“Menene abinda Alisha ta yi musu da za su shigo da ita rikicin mu? My little princess da bata san komai ba? Nooo way dole in yi gaggawan fitar da ita daga ƙasan nan saboda wayannan mutanen are capable of doing anything. Amma kafin nan se na kai ƙaran wayannan azzaluman tukuna“

Ya faɗa a fili yana miƙewa cikin sauri ya fita. direct office din commissioner of police ya nufa sosai suka tattauna ya sanar masa da komai be boye masa ba bayan ya gama sauraran Dr Sagir ya jinjina al’amarin matuka “nagode sosai da wannan information din Dr. kuma na maka alkawari daga yau zaa fara bincike akan su in sha Allah “ miƙa masa hannu ya yi suka yi musabaha “nagode commissioner “

“Mommah ke da su waye ki ke waya haka?”

Kallon ta tayi tana girgiza kai a ranta tace “yau wata rana Alisha ansa manyan kaya” domin kuwa doguwar rigar lace ne a jikinta da aka yi masa dinkin bubu ya mata kyau sosai se de kanta ba dan kwali.

A fili kuwa ce wa tayi “Alisha se yanzu ki ka farka Kenan ? Ni da Umman ku Fatima nake waya wai zaa yi family meeting a kumo next week “

“Ohh nagane” ta faɗa tana samun guri ta zauna tana kallon bangaren Dr “Mommah,papa kamar ya fita ko?”

“Yes darling kina bacci ai sanda ya fita. Yanzu ki tashi ki je kiyi breakfast din ki. Shima Zaid jira nake 10Am yayi in be farka ba inje in kuma tashin sa”

“To “

Tea kawai tasha da slice bread da be fi uku ba ta dawo falo tana kwanciya a jikin Mommah.

“Oyoyo Papa” ta faɗa tana miƙewa zaune,murmushin yaƙe yayi ya zo ya zauna kusa dasu.

Kallo daya Mommah tayi masa ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa amma se kokarin boye wa yake ta hanyar kwakulo murmushi.

“Papa is everything alright?”

“Yes sweetheart,Alisha “ ya Kira sunan ta in a serious tone.

“Yes papa!”

Fito da passport da visa da ticket ya yi daga aljihun sa yana ɗaura mata su akan cinyar ta.. daga ita har Mommah zuba masa ido kawai suka yi without saying a word

“Alisha nasan kina da burin yin tafiya me nisan zango domin yin karatu. Ga passport din ki da komai gobe zaki bar ƙasar nan. na samo miki admission a Harvard university of California. Kin ji ko?”

Duk yanda take son barın gombe amma jikinta se da yayi sanyi haka kawai take jin there’s something da mahaifin nata yake ɓoye mata,... musamman yanda yake magana kaɗai za ka gane shi kan sa ba son hakan yake yi ba.

“Papa please ka faɗa min menene yake faruwa. Na ji muryarka yanda yake fita akwai tsoro da fargaba a cikin sa. Bazan iya tafiya in bar ka cikin damuwa ba”

Ta faɗa idanun ta na ciko da hawaye,shafa kan ta yayı “Noo my daughter babu komai believe me. Kawai Ina son cika miki burin ki ne”

“Papa ko de mutanen da naji kana magana kai da Mommah akan su ne jiya?” Da sauri ya kalle ta yana girgiza mata kai

“Na faɗa miki babu komai,ki dena min tambayoyi am doing this for your own sake darling dole ki yi nesa da mu”

“And what’s going on here?” Gaba daya suka mayar da kallon su bayan su da suka ji muryar Zaid isowa yayi falon yana ɗaukan passport din dake kan cinyarta

“Papa me yasa ka ke son tura Alisha darling nesa damu? ko de akwai abinda ka ke boye mana ne?”

Mommah ne tace “Zaid babu kyau titsiye iyaye. Duk decision da mahaifin ku ya yanke yana yi ne domin ku maza ka ba sa hakuri”

“Am sorry Papa. But please menene ya sa ka ke son tura Alisha wata Ƙasa?”

Miƙewa tsaye yayi yana duban su gaba daya “na riga da na gama magana. Darling ki fara shiri “ yana faɗar haka ya nufi bangarensa ya barsu zaune cike da tarın damuwa domin tunda suke ba su taɓa ganin sa a irin yanayı na yau ba.

“Wai me yake faruwa da papa ne,duk kan ku kun yi shuru kun ƙi bani amsa”

“Zaid papan ku sun ɗan samu hatsaniya ne shida wasu ƴan siyasa yasa suke threatened dinsa”.

“Mtsssw wallahi se na rubuta ƙara akan su “

“Zaid ka ganka ? To babu ruwanka kuma muddin mahaifin ka ya ji ka shiga maganar nan ranka in ya yi dubu se ya ɓaci”

Cewar mama. Ita de Alisha shuru kawai ta musu bata iya cewa komai gaba daya ta shiga damuwa saboda ganin Dr a wannan hali ya matukar ɗaga mata hankali.

Shigarsa daki ke da wuya aka kirasa da bakuwar number ɗaga wa yayi

“Wato kai me taurin kai ko ? har kana da kwarin guiwar kai sirrikan mu gun yan sanda ko? To ka jira ka gani. Duk abinda ya faru dakai ka yi kuka da kan ka.”ana gama faɗin haka aka kashe wayar zama yayi ya rasa gaba daya inda ze sa kan sa. Dama yasan mutanen nan suna da haɗin baki da ƴan sanda,tunda ga shi maganar da ya tattauna da commissioner har sun ji.

Shi ba ma barazanar da suke masa bane ya damesa damuwar sa daya shine Alisha baya son abinda ze taɓata. tunda suka sako ta a wannan hatsaniyar ta su kuma yasan bazasu Kyale ta ba.

Haka Dr Sagir ya wuni a dakin sa sannan ya hana kowa shigowa wajen sa,ya faɗa musu yana son kasancewa shi kaɗai hakan yasa duk suka zauna a falo cikin damuwa gaba daya gidan yau ya koma mara dadi. rashin walwalar mahaifinsu shine ya hana su walwala su ma. Zaid kam yau ko makaranta be tafi ba Aryan ma da ya dawo daga school ƙin zuwa islamiyya yai.

Bayan isha shine lokacin da suke cin abincin dare amma Dr ya ce su ci kawai shi baya jin yunwa.

Kasa hakuri Alisha tayi ta nufi bedroom dinsa ko knocking bata yi ba ta shiga ta samesa ya baza takardu yana ta signing zama tai tana leƙawa ta ga takaddun ƙadarorinsa ne da duk abinda ya mallaka yake rubuta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login