Showing 78001 words to 81000 words out of 96407 words
Chapter 27 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
/>
“Tabb waya gaya mi ki ? Wallahi sai da ya bayar da 10 million a matsayin bailing yanda maganar za ta mutu kafin nan aka rufe case din. Kin san a ƙasar nan in da akwai kudi a lalitarka tofa babu abinda ze gagara”
“Idan ya yi amfani da kudi ya kuɓucewa doka,baze yi amfani da kudi wajen kuɓucewa ukubata ba. Zan nu na masa ba komai ne kudi ke magani ba”
Ta yi maganar a ranta tana zama kusa da Ameeran.
“Hakane kam iya kudin ka iya shagalin ka” tayi murmushi a yayinda ta yi maganar.
“Kin ga ni ko sallah la’asar din ma ban yi ba tsabar farin ciki,bari in je bedroom din Adda in yi” ta fice a dakin
Kwafa Alisha ta yi ta furta “Modibbo Ɗan gaske ka gode wa Allah ka tsallake wannan tarkon,amma bawai hakan na nufin ka tsallakewa azaba da uƙubata bane, da kai da mara mutuncin ɗanka . Wanda ya raba mace da mutuncinta, ya zuga zuciyarta.
Da zafi na ke rayuwa, amma da hakuri nake ɗaukar fansa ta. Wato kun shagala kun manta da abinda ku ka aikata min, sai de wanda ya manta da zunubi, kada ya manta da sakamako,sai na yagalgala ku fiye da yanda ku ka yi wa ahalina,sai na mu ku azaba kafin mutuwa kamar yanda ku ka azabtar da ni da iyayena. Sai na hanaku kwanciyar hankali yanda ko runtse idanun ku se ya gagare ku,kafin daga ƙarshe in tura ku inda baa dawuwa,in ban ɗauki fansa ta ba to tabbas ban cika sunana Alisha Sagir Lelewal ba.”
Karfe 8:30 duk sun hallara a dinning table za su ci abinci, ƙarewa kowa kallo Ɗan gaske yayi ya ga ba ta gurin. kallan Ameera ya yi, ya ce
“Ameeratu ina Alisha ta ke? naga ita kaɗaice ba ta sauko ba”
“Bari in je in kira ta Baba” ta miƙe za ta bar dinning kenan sai ga Alisha ta ƙaraso ta na sanye da katuwar hijabi,komawa Ameera ta yi ta zauna.
Zama ta yi itama kan ta a ƙasa cikin girmamawa ta furta
“Barka da dare Kawu. Ya mu ka ji da abinda ya faru? To Allah ya tsare,Allah ya kareka daga sharrin abokan hamayya “
Har cikin ran Ɗan gaske ya ji dadin wannan Addua na ta? hakan yasa fuska da faraa ya amsa da
“Ameen ameen daughter. Ai sharrin su ze koma kan su, Allah ya fi su. Na san ba kowa bane ze min wannan shunen da ya wuce Katanga saboda na dakatar da auren Aliyu Haydar da ƴar wajen sa.”
A hankali ta furta “Allah ya tsare na gaba” da ameen suka amsa gaba dayan ban da Haydar da tunda ta sauko yake kallanta a wayance, gudun kar Adda ko Ɗan gaske su kamasa yana kallanta.
Ba tare da ta ɗago ta kalle sa ba ta murguda ɗan ƙaramin bakinta dan ta san sarai yana kallonta shisa take jin ta uncomfortable a wajen, sanyayyar murmushi ne ya suɓuce masa lokacin da ya ga abinda ta masa? hakan ya tabbatar mai da ta san da yana kallan ta.
“Hajiya Zuwaira shin kin sanar da kawunan ta gobe zaa zo tambaya da saka rana?”
Ya tambayi Adda yana sipping din black tea
“Zan faɗa musu a daren nan in sha Allah “cewar Adda
“To Madallah”
Tun daga nan babu wanda ya sake cewa komai gurin yayi shuru kamar babu mutane,sai ƙaran chokali da ke haƙuwa da plate ke tashi a hankali. Jifa-jifa Haydar da Alisha suke haɗa ido a duk sa’ilin da dayan su ya ɗago,tofa se sun haɗa ido.
Yusrah ce kaɗai ta lura da su, ɗan taɓa Ameera ta yi ta nuna mata su. bayan ta ga yanda suke kallan juna ne su ka yi dariya ƙasa-ƙasa yanda babu wanda ze ji su.
Washe gari Alhamis kamar yanda Ɗan gaske ya faɗa hakan aka yi. uncles din su Haydar mutum uku tare da abokansa Sadeeq da Auwal ne aka je gidan brother Adda da ta sanar masa komai ,da wasu ƙannen sa mutum biyu dashi na uku aka yi gaisuwa, sannan aka sa rana nan da kwana ashirin da takwas zaa ɗaura musu aure.
Bayan an kammala komai ne, su Sadeeq suka kira sa suka sanar mai sosai ya yi farin ciki jin wannan daddɗar labarin,ji yayi yana bukatar ganin ta domin sanar da ita wannan abun farin cikin,part din Adda ya nufa ko da ya shigo babu kowa a falo hakan ya tabbatar mai da Adda na bedroom din ta. hango kofar dakin Alisha yayi a buɗe kaɗan nan ya nufi dakin na ta.
A bangaren Alisha kuwa fitowanta kenan daga toilet ta yi wanka ta wanke doguwar sumanta,tana ɗaure da ɗan towel wanda da kaɗan ya rufe mata tudun hips dinta.hannunta kuma na riƙe da ƙaramin towel madaidaici tana goge gashin nata, tana a tsaye a bakin mirror sai ji ta yi an buɗe kofar dakin nata, da wani irin hanzari ta juya dan ganin wanene. Ya Subhanallah su na haɗa ido da Haydar da sam be yi tunanin ze shigo ya same ta a haka ba? tai saurin zubewa ƙasa tana kare kirjinta da hannu, ta dukunkune ta kwantar da fuskanta akan guiwowinta hakan ya bawa lallausan dogon gashin ta damar zubowa ya rube mata gadon bayanta da kuma jikinta tamkar wacce ta yafa baƙar gyale,shi kuwa Haydar wani irin haushin kan sa ne ya kama sa, be san lokacin da yasa tafukan hannayensa biyu ya rufe fuskar sa ba
With a nervous voice ya furta
“Am so sorry My Queen, ban san zan tarar da ke haka ba na zo ne in sanar dake daddaɗar labari”
Ƙin ɗagowa ta yi, tana nan a dukunkune a ƙasa, ta ce
“Ni kam Uncle ka fita,Wayyo na banu na”
Ta faɗa muryarta na cracking alamun kuka take son yi.
Cike da danasanin shigowa a irin wannan lokaci ya ce
“Ban ga komai ba, yanzu zan fita,kin ga my eyes are even closed “
“Ni de ka fita kawai ,I don’t want to see you “
Tayi maganar cike da tsiwa dan ta ga ba fitar kamar yake son yi ba, batare da ta san shi idanun sa ma a rufe suke ba.
Dama ba wai ya gama shigowa dakin bane yana daga bakin kofa ne a kasamu wannan mishkilan,idanunsa are still closed din ya fita a dakin ya ja kofar kirifff ya rufe mata.
“Ohhh ni Haydar me ya kawo ni a irin wannan lokacin?” Ya tambayi kansa murya can ciki,duban kofan dakin Adda yay, yana rufe hakan yasa ya bar part din kawai.
Ita kuwa sai da ta ji ƙaran rufuwan kofan sannan ta ɗan ɗago kan ta kaɗan ta ga ba ya cikin dakin,miƙewa tayi tana gyara daurin towel din nata da yake kokarin suncewa. Sai kumbara fuska take yi ta na kunkuni ita kaɗai,da ta san ze shigo bakatatan haka, da ba ta fito daga toilet din da wuri ba,yanzu shikenan ya kalle mata jiki.
Tana shiryawa amma ta yi tsaki yafi a kirga. tana gama sa skirt na atamfa ta saka riga body hook fari da ya kwanta a jikin ta. Ringing ta ji hakan yasa ta nufi inda ta ajiye wayar tana dubawa kuwa ta ga Mujahid da sauri tayi picking sakamakon kiran na kokarin tsinkewa.
“Hey Mujahid ku na lafiya”
A bangaren Mujahid, ya ce “ahh lafiya lau mu ke, fatan ke ma haka ? Dama na kira ki ne in tambaye ki address inda zamu haɗu ko da mun dawo”
Zama ta yi daga tsayen da ta ke “ har an gama masa treatment din? Yaushe ne za ku dawo din ?”
“No dear na tambaye ki ne incase in mun tashi dawuwa mu wuce can din direct okay,amma da ɗan saura tukun”
“Ohh! yanzu zan tura ma ka da address din ta whataspp “
“Okay thanks” ya kashe wayar
Kunna data ta yi ta hau WhatsApp ta ga yana online nan take ta hankaɗa masa da address din gidan Inna.
Tana kokarin ajiye wayar kenan ta ga sakon Haydar ya shigo “sorry my black Queen “ da emojis irin na tausayi din nan.
Murmushi ta ɗan saki kana ita ma ta tura masa da “you’re forgiven “
TWO WEEKS LATER
Abubuwa da dama sun ɗan faru a cikin sati biyun nan,sosai aka fara shirye-shiryen biki babu kama hannun yaro, Hajja Hauwa ita da kanta ta haɗawa Alisha Lefe na gani na faɗa wanda duk wanda ya gani sai ya yaba da abubuwan da aka zuba a cikin seti uku na akwatunan,kuma ko wanne seti na ɗauke da akwatuna 6, An kashe wa lefen kudi na ban mamaki. Ga gyara da ake yi na kece raini a part din Haydar an yi sabon painting da duk wani gyaran da ya dace an zuba sabbin furnitures da Kayan electricity,kitchen dake part din ma yasha gyara an zuba duk wani abinda mace take da bukata a cikin sa. sosai dukiya yayi kuka wajen ƙawata part din. Duk wanda ya shiga yasan tabbas amarya ce za ta shigo wannan ƙawatacciyar part din.
Tunda aka saka ranan auren nan Alisha ba ta je gidan Inna ba har yau, sai de suna waya sosai tana jin lafiyarta,amma fa har izuwa yanzu ba ta sanar da ita maganar auren ta da Haydar da ake shirin yi ba. ta fi so sai ta je tukuna ta faɗa mata baki da baki. Maryam da wata matar uncle din su Haydar su ne suke mata gyaran jiki a gida ta yi kyau sosai, fatar nan in banda ɗaukan ido da sheƙi da tsantsi ba abinda yake yi gyaran jikin sosai ya karɓeta. Yau ne ya kasance za su je Asibiti yin genotype ita dashi,leƙo dakin na ta Yusra ta yi ta ga tana sallah, zama tai tana jiran ta idar.
Bayan ta idar ne ta ninke sallayan ta ajiye, Yusrah ta ce
“Uncle Haydar ne dama ya ce in gaya miki yana jiran ki a motar, ki zo ku tafi asibitin”
“Ki ce masa gani nan zuwa na tsaya yin sallah ne”
“To” ta faɗa tana barin dakin.
Dama already ta yi wanka kafin nan ta yo alwala,sama-sama ta shafa lotion sannan ta yi fakin gashinta da ƙaton ribbon black. Buɗe wardrobe ta yi ta fito da Egyptian gown me mayafi ta saka, rigar ya kasance bubu, ta yafa babban mayafinsa ya rufe mata jiki sannan ta feshe jikinta da turarrukan da Maryam ta kawo mata masu bala’in kamshi da kwantar da hankali. Wayarta kawai ta ɗauka ta sa takalmi ta fita a dakin,dakin Adda ta shiga ta same ta suna hira ita da matar uncle Shu’ibu (matar uncle din su Haydar)
“Adda mun tafi”
Duban ta suka yi fuska ɗauke da faraa suka musu addua dawuwa lafiya, sannan ta fita.
Motar da ta ga yayi packing a harabar gidan ne ta nufa tana kwankwasawa,buɗe mata yayi ta shigo tana maida murfin ta rufe.
“Barka da wannan lokaci Uncle”
Ajiye wayan hannunsa yay ya maida hankalin sa kanta yana shakar kamshin mayun turaren da ta fesa,lumshe sexy eyes din sa yay kafin a hankali kuma ya ware su akanta yana duban yanda ta sukuyar da kai tana kallon cinyarta.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya riƙo hannun ta daya,ta ƙasan ido ta dube sa ta ga yanda ya zuba mata ido yana kallo kamar ze cinyeta
Softly ya furta “ Kin yi kyau sosai “
“Thanks” shine kawai abinda ta faɗa a hankali batare da ta ɗago ba.
Be sakar mata hannu ba kuma sannan be ɗauke idanunsa akanta ba sai ma kwantar da bayansa da yai a jikin kujerar motar yana jin yanda bugun zuciyarsa ke sauyawa a hankali, ga wani malalacin kasala ya sauko masa uwa wanda ya yi wani gagarumin aikin gajiya,mayataccen kamshinta yana ci gaba da dukan hancin sa har ma da kwanyar kansa,ya yi imani wannan turaren na ta da ta sanya ne ya sauya masa lissafi lokaci guda, dan kuwa wani yanayı ne yake taso masa har idanunsa rufe kan su suke suna buɗuwa akan ta.
Alisha kuwa da ba ta san komai ba,ba ta san a cikin turarukan da ta feshe jikinta da su akwai wanda baa sawa se in ana tare da miji ba,kuma Maryam da su ka kawo mata su basu tsaya mata bayani ba dan ba su yi tunanin za ta yi amfani da su ba.
Murya a narke ya kira sunanta “Alisha”
Ɗan kallon saa tayi ta ga yanda yanayinsa ya koma kamar be shirin yin bacci? idanunsa ne suka sanar da ita hakan duba da yanda suke lumsar da kansu.
“Naam “
“Wannan turaren na ki kamshin sa yayi yawa ze jawo hankalin mutane izuwa kan ki, wanda ni kuma ba zan so wani ya kalle min mata ba. do me a favor go and change your clothe please “
Sai yanzu ta masa kallon tsanake ta ga fuskar sa babu alamar wasa ta gyada kai ta cire hannun ta cikin nasa ta fita a motar
“Kar ki sa turare a kayan”
Ya faɗa yana kallan cute face nata
“To” kawai ta ce sannan ta tafi, shi kuma bin bayanta yayi da kallo kafin ya sauke gwauron ajiyar zuciya ya kifa kan sa a siteri, yana daidaita nutsuwarsa ta hanyar rufe idonsa tare da sauke numfashi akai-akai har ya ji ya soma jin dede.
Ta na shiga falo za ta haura kenan suka yi clear da Maryam da ita ma part din za ta shiga
“Ah ah aka ce kun tafi asibiti ko har kun dawo ne?”
Cikin nutsuwa ta girgiza mata kai kana, ta ce “ uncle ne ya ce in je in sauya kaya tukunna”
Da ɗan mamaki take dubanta, ta ga de babu abinda ya samu Kayan na ta, shigan da tayi shiga ne na mutunci ko ina a rufe tana kokarin yin magana ne kamshin turaren ya daki hancin Maryam, hakan yasa ta matso kusa da ita tana me kamo gyalen Kayan ta shunshuna,tabbas sai yanzu ta gano dalilin da yasa Haydar ya ce ta je ta canzo kaya. Riƙo hannunta tayi su ka haura izuwa part din, suka shiga dakin Alisha din a tare tana me blaming kan ta na rashin sanar da Alisha yanda za ta yi amfani da turarukan
Ɗauko su tayi ta hau nuna mata “ na manta shaf ban miki bayani ba,wayannan turarukan ba ko wanne bane za ki fesa shi in zaki fita saboda akwai masu tayar da hankali,kamshin su yana dagawa namiji hankali kin ga kuwa mijin ki kadai ne yakamata ya ji kamshin sa. İn de kına gida ne za ki yi amfani dasu amma in zaki fita ki yi amfani da normal perfume saboda kamshin turaren nan yana tayar da feelings shi sa Uncle ya ce ki zo ki sauya kaya. Yanzu kin gane ?”
Cike da kunya ta gyada mata kai tana tuno yanda ta ga Haydar ya sauya time da ta shigo motar a she wannan turaren ne sila.
“To shikenan ki sauya kayan ki samu ki je kar ki bar sa yana jiran ki “
“Nagode Anty Maryam “ murmushi tayi ta bar ta dan ta samu ta sauya din.
Koda ta cire kayanta still jikinta na kamshin turaren saboda ya Kama fatar ta mayen turare ne da baya fita gaba daya ta dadi,still kalan kayan da ta cire ta kuma sawa but different design and color,kamar yanda ya ce mata kar ta fesa wani turaren ba ta fesan ba ta bar dakin.
Hango ta yayi cikin sabuwar shiga hakan yasa shi sakin murmushin gefen baki, sai kuma ya girgiza kan sa kaɗan, buɗe mata kofar ya yi ta ciki, ta shigo ta zauna batare da ta dube sa ba.
Har yanzu yana jin kamshin turaren sai de ba kamar na ɗazun ba,a ƙasan makoshinsa ya furta
“My beautiful lady” ta ji abinda ya faɗa amma se ta fuske kamar ba ta ji ba, amma a ƙasan ranta ta ji dadin Kalmar a fuska ne kawai ba ta nu na ba sai ma tsuke fuska da tayi.
Dariya ta so bashi ganin yanda ta haɗe fuska ta ƙi ɗagowa. yana danne dariyar ya tada motar suka bar gidan,ganin sun nufi hanyar cross ne yasa ta kallan sa
“Uncle Haydar wani hospital za mu je”
Hankalin sa akan hanya ya ce “Medical center “
Gabanta ne ya faɗi daram amma ta aro jarumta ta yafa, amma deep down hankalin ta ya ɗan tashi jin asibitin da ya Kira wanda a nan ne Dr Sagir yake aiki kuma yawancin abokanan aikin sa sun san ta. ta ya za ta yarda ta kai kanta da kanta bayan duniya ta gama shaida sun mutu.
Gyara zaman ta tayi tana ɗan kallon sa ta ga gaba daya hankalin na kan hanya a hankali, ta ce
“Uncle ni de kar mu je can. mu je wani asibiti da yake kusa”
Kallan ta yayi na ƴan sakanni kafin ya kuma maida kan sa kan hanya
“Saboda me? ” ya tambaye ta yana driving
“Haka kawai ni asibitin ne bana so please “
Cike da kulawa ya ce “shikenan to mu je Specialist kawai”
Be tsaya a ko ina ba sai a harabar Specialist hospital, ya fito ya zagaya ya buɗe mata kofa ta fito,a jere su ke takawa har suka shiga cikin asibitin ya nufi wani office batare da ya nemi izinin shigowa ba ya buɗe kofar,Sadeeq da Auwal da suke cin abinci ne suka ɗago kan su a tare,ko da ganin Alisha da Haydar ne ya sa su sakin murmushi suka soma faɗin
“Kun ga ango na Alisha, angon satı biyu ba da kan ka a sare” su ka faɗa a tare,hannu ya ba su suka gaisa suna dariya banda Alisha da ta tsaya a bayan sa tana jin su.
Sadeeq ne ya jawo kujera ya ajiye mata “Amarya Bismillah ga gurin zama”