Showing 27001 words to 30000 words out of 96407 words

Chapter 10 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3622

jikinsa,gaba daya bata cikin hankalinta kallon Sameer ya tuna mata da baya ɗan ƙaramin haukar da tayi lokacin da ta rasa kowa nata ne yake kokarin dawuwa. tana riƙe da iya empty tray da cup da kuma magani ta soma tafiya bata san inda take wurga kafarta ba,tana shiga part din ta maida kofar falon ta rufe da karfi tare da yin wurgi da tray ya faɗi tsakiyar falon jinginuwa tayi a jikin kofar ta zame ƙasa a hankali ta fashe da kuka.

Tun shigowar ta yabar wayan da yake yi da Sadeeq ya dubeta ganin yanda ta shiga da yanda ta wurga tray din sannan ta zame a gun tana kuka ya tabbatar da ba klau take ba, sannan bata san inda ta shigo ba da hanzari ya nufe ta yana sunkuyawa gaban ta tare da kiran sunan ta murya a sanyaye “Alishaaa” ɗago jajayen idanunta tayi ta ɗaura su kan sa sam bata gane waye a gaban ta ita de namiji kawai ta gani hakan yasa bata yi wata-wata ba ta sa hannunta dukka biyu ta ture sa da se da ya kusan kaiwa ƙasa.

Nu na sa da yatsa tayi cikin gargadi ga hawayen da ke gangarowa a idanunta “kar ka kuskura ka zo kusa dani,ka rabu dani kar ka motso. İn har ka zo kusa dani zan kashe kai na”tayi maganar tana miƙewa tsaye, mamaki iya mamaki ya Kama Haydar ga kansa da ya kulle tabbas akwai abinda yake faruwa a rayuwar Alisha,be yi ƙasa a guiwa ba ya sake miƙewa yana kokarin matsowa kusa da ita amma ja da baya take yi tana nuna sa da yatsa tare da girgiza mai kai alamar kar ya kusanto ta

“Alisha calm down kin ji is uncle Haydar,look at me it’s me Alisha,cool your mind and tell me what happened kin ji? ”

“Kar ka zo kusa dani na ce maka kar ka zo kusa dani”ta yi maganar ta na sake ja da baya tana nufan tsakiyar falon. Saboda yanda take tafiya ta baya bata san da wani ƙaramin table a bayan na ta ba? hakan yasa ta bugesa ta yi tangal-tangal za ta faɗi yai azama wajen riƙo hannunta daya sannan ya jawo ta da karfi ta faɗo jikinsa,kokarin fincike kanta tayi tana sambatu da fisge-fisge amma sam ya ƙi bata damar hakan hakan yasa ta sake fashe masa da kuka tana dukan kirjin sa but still he refused to let go.

“Shisssh Alisha,ki nutsu no one is going to harm you as far as kina wannan gida, kuma ina tare dake babu wanda ya isa ya cutar dake saboda yanzu kina karkashin kulawar Director chief superintendent Haydar….ki yi shuru kin ji ki dena dukan Uncle okay” ya faɗa mata a cikin kunnenta cikin sigan lallashi. Lokaci guda ta nutsu tayi shuru tare da yin luf a jikinsa. hannunta ta sanya duka biyu da take dukan kirjinsa tayi hugging din sa back tana jin wani nutsuwa da karsashi na sauko mata idanunta na lumshe sauke ajiyar zuciya kawai take yi a hankali ga heartbeat din ta da yake bugawa da sauri,saboda yanda jikinsu yake a haɗe ne yasa yake jin yanda zuciyarta ke bugawa.

Ɗago ta yake kokarin yi daga jikin sa”Alisha..” noƙewa tayi tana faɗin “don’t let go of me please “ tayi maganar kamar zata yi kuka hakan yasa ya barta sannan ya soma shafa kanta dake cikin hijab. Haka suka kasance har na tsawon ten minutes kafin ta dawo hayyacinta ta tuna Duk abinda ya faru runtse idonta kawai tayi

“Innalillahi wainnailaihi rajuun Alisha what have you done?what if you said something da ze sa Sameer and Haydar su fara suspecting din ki? oh no,I have to come up with a lie da zan faɗa” ta yi maganar a zuciyarta.

Da sauri ta fisge jikinta ana Haydar tana kallon ƙasa tare da fara wasa da ƴan yatsunta tama rasa me zata ce masa, kunya kaɗai yasa ta gagara haɗa ido dashi. shi kuma ya tsaya kawai yana kallon ta ganin yanzu ta dawo dede ne yasa ya ji hankalin sa ya kwanta

Murya na rawa kamar me shirin sa mai kuka ta ce” Am sorry Uncle Haydar,ka yi hakuri “ matsota yayi ya na riƙe hannunta ya ja ta zuwa kan kujera suka zauna, amma har time din ta ƙi yarda su haɗa ido,bayan ya sakar mata hannu ne yake tsareta da ido ya san sarai dalilin da yasa ta ƙi yarda su haɗa idanu, saboda kasancewa da suka yi rungume da juna na tsawon mintuna goma wanda shima wannan shine karo na farko da hakan ya soma faruwa dashi, be taɓa ɗaukar mace a hannun sa ba se a kanta, be taɓa rungumar macen da ba muharramar sa ba se akan ta.

With his gentle voice ya furta “Alishaaaa”

Ji tayi sunan ya mata dadi a yanda ya kira din, hakan ne yasa ta ɗago manyan idanunta ta sauke su kan sa ganin yanda yake kallon ta ne yasa ta janye na ta idon

“Are you okay?”

“Eh” tayi maganar a hankali sosai domin kuwa be ji ta ba iya leben bakin ta ya kalla ya gane hakan

“Meyake faruwa dake did something happen to you in the past saboda I noticed you were traumatized. Faɗa min menene ?”

Girgiza mai kai ta yi alamar ba komai,hannun sa ya kyasta mata a kusa da fuskarta kallon sa tayi a karo na biyu

“Baa yi min karya Alisha,by looking into your eyes I have seen that,se de kawai za ki ɓoye min ne saboda ban kai jin damuwar ki ba”

Bata san time din da ta ɗaura hannunta akan hannun sa ba tana girgiza mai kai idanunta na kawo ruwa,kallon ta yayi sannan ya kalli hannun nata da ta ɗaura kan na sa,maida idon sa kan ta yayi yana ɗaga mata gira daya alamar yana jin ta.

“Please don’t say that Uncle,abun da ya faru dani is my past ko tunawa bana son yi saboda halin da nake shiga. An cusa min tsoron maza a raina,amma yau.”ta dakata tana kallon sa

Softly ya tambayeta “amma yau meye?”

“Yau se na samu nutsuwar da na gaza samu tsawon lokaci,Uncle I feel comfortable a lokacin da na ke tare da kai,kai ne mutum na farko da ya sa naji nutsuwa ya zo min”

Tun da take magana ya ke kallon ta ya san iya gaskiyarta take faɗa masa maganganunta sun sanya jikinsa mutuwa.

“I understand you Alisha and in sha Allah zan ba ki kariya da iya iyawata nothing will happen to you okay,Uncle Haydar will always be there for you”

Gyada Kai tayi “nagode Adda ta bani coffee in kawo maka da magani sun zuɓe kayi hakuri “

Murmushin gefen baki yayi “is okay” ɗan ware idanunta tayi “ba ka ji haushi ba?”

“Nope ban ji ba”. ya faɗa yana dariyar yanda ta zaro masa idon ta da suka kumbura. Dariyar da yake mata ne yasa ta murguda masa ɗan ƙaramin bakinta tana kunkuni “to meye na dariya”

Sarai ya ji ta hakan ya sanya shi girgiza kai kawai “ɗauko min maganin to “

Haka kawai ta ringa jin ta tamkar ƙaramar yarinya a gaban sa hakan yasa cikin shagwaba da ta manta ya ake yin sa ta ce “Uncle Haydar ai ban san inda ya shiga ba”

Kwaikwayon yanda tayi maganar yai “To ai se ki dubo saaa” dariya ta fashe dashi domin ba ƙaramin dariya ya bata ba wai shi a dole ita ya kwaikwaya. Yanda take dariya sosai ta tafi da imaninsa komai na ta burgesa yake yi ya rasa me yasa yake jin wani abu a dangane da ita, ba ya taɓa iya ɗauke idanunsa akan ta ya rasa wannan sabon al’amarin daga ina.

“Murmushi yana miki kyau Alisha “ yayi maganar in a serious tone, ɗan kallan sa ta yi ta ga yanda ya shagala da kallon ta nutsuwa tayi ta fara wasa da hannun hajib dinta sabanin dazun da take ta dariya

Zuruf ta miƙe tsaye tare da faɗin “Adda na nema na Uncle” ko second ba ta ƙara ba ta fice a falon cikin sauri. Da kallo kawai ya bi ta yana murmushi a fili ya furta “Alisha “ da wani sanyayyar murya. Tana fita a bangarensa ta tsaya ta dafe kirji tana sauke nauyayyan ajiyar zuciya saboda tayi escaped amma dakyar fifita ta fara yi wa kan ta da hannu tana faɗin

“Alisha!Alisha!Alisha you have to be very careful around Haydar. Kar ki bari ganin Sameer ko Ɗan gaske ya sa kiji tsoro ko rauni. ki samu ki yi abinda ya kawo ki gidan nan sannan kiyi tafiyar ki.” Jinjina kai tayi tana kyasta hannunta tare da yin kwafa da kuma ɗaukan alwashin bazata sake barin makamancin abinda ya faru ya sake faruwa ba.

“Zainab, Alisha kam shuru ko de da ta kaiwa Haydar coffee ta wuce daki ne? Ki je ki ce mata ta sauko ta karya”

Har Zainab ta miƙe za ta nufi part din Adda kenan se ga Alisha ta sauko tana tafiya Simi-simi kamar kazar da Kwai ya fashe wa a ciki.ganin ta ne yasa Zainab komawa ta zauna

“Adda na kai masa”

“Yawwa yar albarka ai yanzu nake cewa Zainab ta dubo ki ko kin koma dakin ki ne”

Murmushi me sanyi ta sakar mata tare da faɗin “Ayyah Adda gani nan dama na tsaya duba abu ne”

Serving din su breakfast me aiki ta yi sannan suka fara ci Ameera da ta kalla Alisha ce ta ce “Alisha wai ke yawo da katuwar dogon Hijab kullum baya damun ki ne?”

Duban jikinta ta yi sannan ta maido da idon ta kan Ameeran “ai da yake na saba haka tun ina gida shisa baya damuna “

Murmushi Adda tayi kawai tana jin su suna cin abinci suna haɗa wa da magana.

Tana gama cin abinci ta taimakawa me aiki suka kwashe kwanuka suka kai kitchen tayi yunkurin taya me aikin aiyuka amma sam Adda ta ce ta ta bari ba se ta yi ba hakan yasa ta koma bedroom na ta.

Yau saura kwana uku date din Peter ya yi amma har yanzu bata bar gidan ba balle ta san abinda zata gudanar. sam ta rasa excuse din da za ta bayar ta fita. ga shi yau Saturday Haydar na gida in ya ji za ta fita se ya tayi mata tambayoyi maybe daga karshe ma ya ce shi ze kai ta tsaki tayi ta zauna a bakin gado tana tunani kalla daban-daban.

Karfe 11:50am ya fito daga gidan su ya jima tsaye a bakin hanya amma be samu abin hawa ba dama haka anguwar Bomala take dakyar ake samun abun hawa musamman yanzu da ake sabon titi ya jima sosai wanda a kalla ya kai kusan mintuna goma tsaye ga rana da ake yi wani me mashin ya gani bashi da choice kawai ya tara

“Me mashin ka san gidan Hon Ɗan gaske?”

“Eh na sani “cewar me mashin,yana jin amsar sa kawai ya hau yana “to nan za ka kai ni”

Suna isa tudun wadan sarki me mashin ya faka sa a kofar gidan ya sauka ya basa kudin sa,kwankwasa gate yayi me gadi ya leko suka gaisa

“Bawan Allah, dan Allah ko za ka taimaka ka min magana da Haydar Modibbo Ɗan gaske ka ce mai yana da baƙo “

Kare masa kallo me gadi ya yi kafin ya ce “yau asabar ƙaramin Alhaji ba ya haɗuwa da kowa gaskiya,dan wannan umarni ya bani ka da in bar kowa ya shigo da neman sa se a ranakun aiki”

Marairacewa ɗan saurayin ya yi cike da damuwa yace “nasani, amma dan Allah ka jaraba nasan Sir Haydar mutum ne me fahimta,ka sanar dashi magana me muhimmanci zamu yi akan ceton rayuwa please “

Girgiza masa kai me gadi ya yi “gaskiya bazan iya taimakon ka ni kuma in rasa aiki na ba, dan haka hakuri kawai za ka yi ka dawo ranan litinin warhaka” yana faɗin haka ya rufe kofar ya bar sa tsaye kamar gunki haka ba yanda ya iya ya sake hawan mashin.

Zaune suke a falo su uku suna hira Ameera da Zainab suna ta faman ba ta labarin elder sister su wato Yusra ƙanwar Sameer da take Abuja. ita kawai jin su take amma bawai tana wani gane wa hiran bane saboda hankalinta ya yi wajen inna ta san tana cikin damuwa na rashin ji daga gare ta.

Shigowa ta yi falon tana jan trolley dayan hannun kuma ta riƙe da Hand bag. ta sa abaya maroon tayi rolling din gyale tana taku daya-daya cikin yanga ganin sam ba su lura da shigowar ta bane ya sa ta ajiye hand bag din akan trolley tana riƙe kugunta da dayan hannun sannan ta furta “hello girlssssssss” a tare duk su ukun su ka jiyo wani ihu Ameera da Zainab suka sanya suna furta “speaking of the devil “ suka je da gudu suka rungumeta suna ihu cike da farin cikin ganin ta.

“Wayyyoo Adda kina ina yaran ki za su ɓalla ni “ ta faɗa tana ɓanɓare su a jikinta tana dariya

“Wowww Beb kin ga yanda ki ka sake kyau ne, gaskiya zaman Abuja ya karɓe ki” kallon Ameera da tayi maganar tai

“Awwwn ! awwwn ki ce na yi fresh “ dariya suka fashe dashi haka suka ƙaraso falon ita de Alisha kallo kawai take bin su dashi.

Se a sannan ne ta ankara da Alisha da take zaune kan kujera ta zuba musu na mujiya.

Ƙare mata kallo ta yi domin ba ta san ta ba tana matsowa kusa da ita ta ce “gurls yaushe mu ka yi ɓakuwa a gidan haka?”

Caraf Zainab ta amsa mata “yau kusan week kenan ai “

Miƙa mata hannun ta daya ta yi tana sakar mata murmushi me tafiya da hankali ta ce “Hi sunana Yusra Modibbo Ɗan gaske “

Kallon hannun na ta tayi da yatsun ko wanne da zobe a jikin sa tai kafin ta kama hannun tana ƙaƙalo murmushi itama ta ce “hi sunana Alisha nice to meet you Yusra” da yatsunta take amfani wajen shafa tausassan tafin hannun Alisha tana wani binta da mayataccen kallo kamar zata cinyeta, ga ta ƙi sakin hannun na ta,shekeke take kallon ta ganin yanda take mata wani kallo me wuyar fassaruwa nan ta ji ta tsargu da irin abinda Yusran take mata da kuma irin kallon da take bin ta dashi,janye hannun ta tayi tana wayancewa tunda ta ga ita bata da niyar sakar mata hannu.

“Wait, what! waye na ke gani kamar Yusra “ cewar Haydar da ya ke saukowa ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya.

Farfari da ido ta yi “uncle Haydar din mu I really missed you “tayi maganar a shagwabe cikin wasa ya ja kumatunta “kamar da gaske “ tura baki tai ta fara bubbuga kafa kamar ƙaramar yarinya “Uncle Haydar wallahi I did”

“Na yarda “ ya ce yana satar kallon Alisha dake zaune kallan sa ta yi ta ga yanda yake ta satar kallon Alisha din hakan yasa ta matso dede da kunnen sa ta ce “she’s beautiful right ?”

Rankwashi yai mata yana “okay abinda ki ka koyo kenan a abujan gulma ko?”

Dariya su Ameera suka sheke dashi ganin daga dawuwar ta sun fara dramar su da Haydar, dama sun saba saboda sun fi shakuwa,kuma itama tafi shakuwa dashi din fiye da yayanta Sameer dan ba ko yaushe suke jituwa ba.

Jikinta ne ya ba ta ana kallon ta tana ɗagowa kuwa ta kamasa,janye na ta idon ta yi saboda bata ga alamar shi ze ɗauke na sa idon ba. me aiki ce ta katse sa daga kallon na ta “Ƙaramin Alhaji, Adda ta ce tana son magana dakai” kai ya gyada sannan ya nufi part din

Tana zaune bi sa kan sallaya alamun ta idar da sallah azkhar take yi. sallame wa tayi bayan ya samu guri ya zauna shafawa shima yayi yana “ameen “

“Barka da rana Adda na”

“Barka,na kira ka ne saboda maganar da baban ku ya faɗa maka da safe,dan Allah Haydar kar ka ja min magana dan gani yake yanzu kamar ni ce nake zuga ka,kayi hakuri ka karɓi zaɓin mahaifinka. Ni kaina na fi son ka auri yarinya yar gidan mutunci, me cikekken tarbiya amma tunda Meenal ita ce wace mahaifinka ya zaɓa ma se ka yi hakuri ka karɓeta se ka ga kai ne silar shiryuwanta in sha Allah. In ta zo se ku daidaita kan ku Allah ya sa haka shine mafi alkairi”

Sarai ya san abinda yasa ta nemi ganin sa kenan, da ya furta shi baya son Meenal amma ba ya son ganin damuwa a fuskan Addan sa dan yasan duk abinda ya je ya dawo tofa Ɗan gaske ita ze ɗaurawa laifi.

“Shikenan Adda zan yi yanda ki ka ce amma ku sani daga zaran na samu macen da nake so to zan ƙara aure”

“Ahaf Haydar ai namiji mijin mata hudu ne in ka samu wacce ka ke so din se ka aura amma yanzu de ka fara yin biyayya tukuna.”

A haka suka ƙarƙare magana daga nan kuma ya fita a gidan saboda ze je gidan Sadeeq da ya damesa da kira.

Alisha tana ji tana gani haka har dare yay bata samu hanyar barin gidan ba,tana nan kunshe a daki tunda suka ci abincin rana bata sake fitowa ba haka zalika babu wanda ya shigo dakin ta. Yanzu ma fitowarta kenan daga wanka tana ɗaure da towel da tsayinsa dududu be wuce cinyar ta ba,tana goge gashin kanta da karamar towel tana tsakiya da gogewa kawai ta dakata cak haka kawai ta ji jikinta ya bata ba ita kaɗai bace a dakin hakan yasa ta juyo bayanta

.

Tana zaune a bakin gadon ta kafa daya kan daya tana sakar mata murmushi tare da yi mata waving hand “ Hi Alisha “

Murtuke fuska ta yi kamar bata taɓa dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login