Showing 54001 words to 57000 words out of 96407 words

Chapter 19 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3633

faɗi haka ba,dama haka ki ke da kyan jiki kullum ki ke rufe kan ki cikin katuwar hijab?”

Murmushi tayi jin abinda Zainab din ta faɗa “Nagode zee “

“Yanda ki ka yi kyau am sure ko Meenal bazata kai ki ba. Lace din nan ya miki Kyau sosai “

Cewar Ameera

Yusrah ce ta wurga wa Ameera da ta yi magana yanzu harara “Yoo dama za ki haɗa Alisha da Meenal ne? Alisha asalin ta kyakyawa ce ta ƙarshe. Kin san Allah Alisha “ ta faɗa tana juyowa kan ta.

“Hakuri za ki yi kawai ki zauna in yi miki light,light, light make up wanda be kai na mu nauyi ba, wallahi baƙaramin kyau ze miki ba. Please don’t say no”

“Yusrah please ki bar ni haka bana son sha'ani da wannan make up din ni”

“Dan Allah fa nace kaɗan zan miki” ganin in bata amince ba Yusrah za ta ji babu dadi hakan yasa ta je ta zauna a gaban mirror Yusrah ta soma mata make up din. Mintuna goma kacal suka ɗauka tana mata kwalliyar,kamar yanda tayi alkawari light make up kuwa ta mata se de kwalliyar ya matukar dacewa da fuskarta da skin color din ta sak amarya ta fito. Se yaba irin kyawun da tayi suke, ita kanta da ta ga kanta a mirror se da murmushi ya suɓuce mata saboda ta san tayi kyau sosai. Ɗauri Yusrah ta fara mata me step-step.

Su Ameera da suke zaune suna kallon su duk ba su ɗaura ankwali ba har ita Yusrah ba ta ɗaura nata dankwalin ba.

“Yusrah mu ma fa ke muke jira in kin gama mata ki yi mana”

Zainab ta faɗa tana riƙe da nata ɗankwalin.

“To bari in gama da ita se in muku”

Bayan ta gama mata ne ta tashi akan kujeran, ta ɗauki gyale chantali kalan kayanta ta saƙalashi a kafaɗa. Sannan ta feshe jikinta da perfumes masu dadi ta tsaya a gefe tana kallan ana ɗaurawa Zainab ɗankwalin. Turo kofar aka yi Maryam ce ta shigo idonta kyam akan Alisha

“Tubarkallah Masha Allah Alisha kin gan ki kuwa? Kin ga yanda ki ka yi kyau. Wai wannan ko amarya iya ka kenan ai”

Dariya duk suka yi Alisha ta ce “Nagode “ haka Maryam ta din ga gwaɗata har da cewa ai in Adda ta ganta bazata gane ta ba.

“Yawwa wata a cikin ku ta zo ta kai wa Uncle da friends din sa abinci dan basu karya ba har yanzu “

Duk su ukun kallon Alisha suka yi saboda ita kaɗai ce ta shirya a cikin su “Ayyah dan Allah Alisha ki je ki kai musu tunda kin ga ke daya ce ki ka gama shiryawa “ Ameera ta faɗa a marairaice.

“To “ ta faɗa kana ta bi bayan Maryam suka tafi kitchen,already an gama shirya komai a babban tray. Se da su ka zo kuma Maryam ta ga kamar Alisha bazata iya ɗaukan tray din ba saboda yana da girma kuma da nauyi.

“Alisha za ki iya ɗaukan wannan tray din kuwa?”

Dan ta gan ta ba wani kumari ne da ita ba ga babu jiki .

“Zan iya anty Maryam “ tayi maganar tana ɗaukan tray din. Tabbas ya mata nauyi, amma a haka ta ɗauka ta haura upstairs din ta nufi part din sa. Tun daga bakin kofar falon sa take jiyo hayaniyar abokansa. Knocking tayi Sadeeq dake zaune yana ta ma Haydar tsiya ne ya furta “come in”

A hankali ta tura kofar ta shigo bakin ta ɗauke da sallama. Jin siririyar murya ne yasa duk suka mai da kallon su kan ta. Wani irin bugawa kirjinsa yayi lokacin da idanunsa suka sauka akan ta,be taɓa ganin ta a kaya irin haka ba,wani irin kyau ta yi masa kamar yau ya fara ganin ta haka ya tsaya yana kallan ta, sosai ta tafi da İmanın sa. Kallon yanda take marairaice fuska kaɗai da yayi ya fahimci tray din ya mata nauyi hakan yasa ya miƙe ya nufeta yana karɓan tray din a hannun ta. Idon sa akan ta yace

“Alisha waye ya baki wannan tray din haka? wannan tray din ai yafi karfin ki”

Murmushi ta sakar mai da ya sake narkar masa da zuciya.

“Uncle babu wani nauyi fa sosai”

Be kuma magana akan tray din ba se ma cewa da yayi “kin yi kyau sosai “

Cike da kunya ta sa hannu ta rufe fuskanta tana dariya. Murmushi yayi ganin ta rufe fuskarta

“Kina son ki ɓata min kwalliyar na ki ne?”

Cire hannun ta yi tana kamo ƙasan gyalenta ta fara wasa dashi,cikin kunya ta ce “ai Kaima ka yi kyau sosai kamar ma yau ne ɗaurin aurenka tsaban Kyan da ka yi. Meenal ta yi dacen miji “

Yabon da ta masa baƙaramin dadi ya masa ba,” kema ai kin yi dacen miji”

Murmushi kawai tayi saboda ba wai ta fahimci in da maganar ya nufa bane.

Su Sadeeq kallon su kawai suke yi domin zuwa yanzu sun yi imani Haydar da Alisha sun manta da su a cikin falon ganin yanda suke hiran su hankali kwance. Sadeeq da Auwal kuwa tun shigowarta da suka ji Haydar ya kirata da Alisha suka gane ita ce yarinyar da yake basu labarinta. Sosai suka ga yanda suka dace shi da ita.

Wani daga cikin abokan sa ne me suna Ramadan ya yi gyaran murya “Uhmm Uhmm” juyawa yayi side din da yake zaune ya watsa masa harara duk dariya suka saka ganin irin kallan da ya mai.

Cike da kunya ta gaishe su,amsawa suka cikin faraa.

“Romeo in kai ba ka jin yunwa mu ka ajiye mana abinci muci “ cewar Auwal,be ko kula su ba ya ce da ita

“Shikenan ki tafi thanks” dan ya ga suna kokarin fara masa tsiya ne a gabanta hakan yasa shi ce mata ta tafi.

Se da ta fita sannan ya ajiye musu abincin,Ramadan da be san komai ba ya ce “gaskiya kanwarkan nan ta burgeni a taimaka a bani ita in aura” Wani mugun kallo ya watsa masa.

Sadeeq da dariya ke son kufce masa ne ya ce “ba ka da hankali yarinyar da ze aura din ce ze ba ka aure ?”

Cike da mamaki sauran abokan na su suke kallon Sadeeq jin abinda ya faɗa.

“Bangane wacce ze aura ba, ita Meenal Katangan fa?”

Usman ya tambaya cike da mamaki.

“Ita ze fara aura. ita wannan ita ce ta biyu”

Sadeeq ya ba sa amsa. shi de abincinsa ya ke ci a nutse kamar ba ya dakin dan ko tari be yi ba. Haka suka dinga hiran har suka gama cin abincin su.

Ko da ta koma dakin ta samu su Zainab tsaf sun gama shirinsu. su ma sun yi kyau sosai suna ta ɗaukan hoto,babu yanda basu yi ta shiga hoton ba aman ta ƙi shiga. A babban falon dake downstairs an yi decoration me kyawun gaske saboda anan ne zaa yi walimar saka ranan, duk girman falon nan se da aka ƙawata ko ina da ado ga table an jera drinks da snacks kala daban-daban duk abinda ka ke so se de ka ɗauka.

Karfe sha daya aka fara gudanar da walimar inda ba wani gayyan mutane aka gayyato ba yan uwan Meenal ne da iyayen ta se kuma friends din ta. shima Haydar friends din sa ne se kawun nan su da suka zo. Hajja Hauwa ma ta zo ta. Meenal da Haydar suna zaune a kujera daya. Haka Ɗan gaske da katanga suna zaune kana kallon fuskarsu zaka gane suna cikin tsantsan farin ciki. Kowa yana zaune su Alisha da Ameera suna zaune suma a gefe suna na su hiran.

Katanga ne ya soma magana “muna farin ciki da Allah ya nuna mana wannan rana, a gurguje batare da ɓata lokaci ba zan sanar da ku lokacin da mu ka yanke domin yin wannan aure. Mun yanke nan da wata daya in sha Allahu. Da na ce wata biyu amma aminina yace be ga amfanin sa auren yayi tsayi haka ba.”

Tana zaune cikin su Ameera ta tsare sa da ido se murmushi ta ke saki a ranta tana faɗin “wannan shine jawabinka na karshe da za ka yi a duniya katanga”

Bayan an kammala jawabai ne aka soma walima aka fara ɗaukan hotuna, ga waƙa an sanya amma an rage volume se ya zamana waƙan na tashi ne a hankali.Adda ce ta sanya Su Ameera su fara raba drinks dake cikin glass cup da kuma snacks. Su uku kawai suka miƙe banda Yusrah tunda sune ƙanana.

Tana kan rabawa har ta isa kujeran da suke zaune,miƙa masa ta yi fuskarta ɗauke da farin ciki a hankali ta ce

“Congratulations Uncle”

Murmushin shima ya sakar mata ya karɓa,tana kallon su ji tayi kamar ta shaketa ta kashe dan kishi.

Ita ko Alisha ba ta yi hakan da wata manufa ba ran ta fess ta miƙawa Meenal cold drink din, ta zo karɓa kenan ɗan kaɗan ya zuba mata a hannu cikin rashin mutunci da reni ta dubi hannun nata da drink din ya zuba har kan agogonta me tsada.

“Wayyo am sorry Mee..” makalewa maganar yayi a makokoronta sakamakon wani irin sanyin da ta ji ya ziyarceta tundaga fuskarta har zuwa kirjinta yayi ƙasa. Wani shock ta ji a ilahirin jikinta da yasa ta kasa gane komai na wasu yan dakiƙu,

“Meenal ba ki da hankali ne? Wannan wani irin hauka ne za ki watsa mata drink a jikinta” se muryar Haydar da ta ji yana dakawa Meenal tsawa ne ya dawo da ita daga suman tsayen da tayi.

Nan take hankalin kowa ya dawo kan su ganin abinda Meenal ta aikatawa Alisha sosai ran da yawa ya ɓaci, domin ko wannan abinda ta aikata wulakanci ne da kaskanci.

Yatsina fuska ta yi cikin rashin danasani ta furta “kai ba ka ga abinda ta yi min bane? zuba min fa ta yi a kan diamond watch dina. In ya lalace biyana za ta yi? ko duk danginta akwai wanda yake da kudin da ze biya ni? Dama a ce ubanta na da kudi nasan za ta iya biya, amma ƴar malam shehu ce. matsiyaciya masu bakin ciki da mai kudi”

Zuciyarta tafarfasa kawai yake yi yana rawa, ranta in ya yi dubu ya ɓaci,kokarin kai mata hannu take ta shake ta har se ta bar duniyar amma zuciyanta na dannata saboda kar ta aikata abinda za ta yi danasani batare da ta biya bukatarta ba. Idanunta take suka koma ja dan bakin ciki hawaye me zafi ya fara zubowa daga idanunta. tunda take baa' taɓa ci mata mutunci da wulakantata a idon mutane ba se yau.

“Na rantse da Allah se na sanya ki baƙin ciki fiye da yanda ki ka sani Meenal Katanga. se na wulakanta ki a idanun duniya,se na tarwatsa wannan auren da ki ke tunkaho dashi, in kuma ban yi haka ba ni ba yar halak bace”ta ɗau wannan alwashin a cikin zuciyarta.

Cike da ɓacin rai su Yusrah suka iso wajen suka riƙe ta ganin yanda ta kafe Meenal da ido tana hawaye sosai ta ba su tausayi.

Habibu katanga ne ya ce “haba daughter ya za ki yi haka?”

Cikin shagwaban da ta saba masa ta furta “Daddy ta ya zan bar yar talakawa me aiki ta lalata min agogona da ka siya min? ”

Adda da su Hajja Hauwa takaici da baƙin ciki ya hanasu furta komai.

“Na san ba ki da hankali amma ban yi tunanin rashin hankalin ki ya kai haka ba” Haydar ya faɗa yana miƙewa tare da zaro hanky a aljihunsa ze miƙawa Alisha. Baya ta ja tana fisge hannun ta dasu Ameera suke riƙe dashi ta bar gurin da gudu tana goge hawayenta ta haura upstairs. Bayan ta ya bi shima yana kiran sunanta

“Alisha!Alisha!Alisha”

Amma ko waiwayowa ba ta yi ba.

Wani kututun bakin ciki ne ya tokare ta a kirji ganin yanda Haydar ya bi bayan Alisha yana kiran sunanta. Murmushi Yusrah ta yi ta sassauta muryar ta yanda iya Meenal din ce zata ji ta

“Ko banza kin ga kin sake zubarwa kan ki mutunci a gaban mutane,a gaban idanunki wanda za ki aura ya bi bayan wata domin rarrashinta. gobe ki sake banza kawai “ tana gama faɗin haka ta ja hannun su Ameera suka bi bayan Alisha su ma.

Tana shiga daki ta zube kan gado ta hau sakin ajiyar zuciya saboda yanda zuciyanta yake mata tururi. Duk yanda za ta yi tana kokarin calming kan ta dan in ta bi ta abinda ta ke ji a zuciyarta da kwakwalwarta za ta iya illata Meenal a yau din nan koma ta kashe ta kowa ma ya wuta. Wanda kuma ba ta son haka domin duk zaman ta dasu tana iya kokarinta ne tana boye musu true color ta amma yau ta kai ta bango. Tana daga kwance ji take kamar za ta yi hauka, hakan yasa ta miƙe ta fara safa da marwa a cikin dakin tana hasaso abinda zatayi mata domin rama wulakantata da tayi yau din nan.

Hannunta ta sanya a kai ta cire ɗaurin dankwalin ta yasar sannan ta cusa hannun duka a cikin gashinta tana hautsina su. “Ruwan sanyi,ina bukatar ruwan sanyi” tayi maganar kamar wata zararriya,fita ta zo yi a dakin domin zuwa fridge din Adda ta ɗau ruwa me mugun sanyi ko zata sauko kenan suka ci karo.

Baya ya ja ganin ta da yayi ba dankwali ga gashinta da ya barbaje,ta gefensa ta bi ta wuce batare da ta kalli ko inda yake ba,kamar za ta tashi sama ta isa gaban fridge din Adda ta buɗe nan idanun ta ya sauka akan ruwan gora da yayi sanyi kalau har jikin goran na naso, ɗauka tayi ta buɗe ta na zama a ƙasa ta kafe goran a bakinta tana sha.

Shi de mamaki ya hanasa isa inda take,amma in ya fahimta tana kokarin Kawar da fushinta ne ta hanyar shan ruwan sanyi domin sanyaya mata zuciya. Be isa inda take ba ya tsaya kawai yana kallan ta.

Ba ta cire goran a bakinta ba tunda ta kafe sai da ta shanye ruwan kaf sannan ta ajiye tana sauke numfashi samun relief. Lokaci daya fuskarta ya koma innocent Alisha da take.

“Alisha am sorry akan abinda ya faru ɗazun,ban taɓa zaton Meenal za ta iya aikata haka ba.”

Sanyayen murmushi ta sakar masa da ya sanya sa kusan suma a inda yake tsaye,murmushi fa ya ga tana mai wanda be yi tsammani ba,yanda ya shigo ya same ta be yi tunanin za ta sauko yanzu ba, amma cikin abinda be wuce mintuna biyar ba ta dedeta kan ta har tana iya yi mai murmushi bayan abinda aka aikata mata a falo, wanda ko shine se yafi kwana da kwanaki yana fushi da hakan,be gama girgiza da ita ba se da ya ji muryar ta tana faɗin

“Bakomai Uncle,laifina ne da na zuba mata lemo a hannu bisa rashin sani,dole ta ji babu dadi”

Izuwa yanzu Haydar was speechless kallon ta kawai yake ba kakkautawa,a hankali ya isa inda take zaune ya sunkuya a gabanta. Haɓarta ya ɗago da hannun sa lumshe idanunta tayi saboda bata son haɗa ido dashi.

“Are you okay Alisha? “

Batare da ta buɗe idon ba ta gyada mai kai alamar eh, “to ki buɗe idanun ki inde kına son in yarda da hakan” slowly ta ware idanuntan da suka yi ja akan kyakyawar fuskansa.

“Me yasa ki ke kokarin danne fushin ki bayan kuma ran ki yayi matukar ɓaci?”

Langwabe kai ta yi still hannunsa na tallafe da haɓarta ta ce “saboda na san ko ma menene nice mai laifi,kuma yin fushi a kan laifin da ka aikata rashin hujja ne”

Yanda take zaro zance kawai yake sauraro kamar wacce ta zauna da tsohuwa,duk sanda ta yi wani maganar se ya yi ta mamakin aina ta ke jin wayannan manyan zantukan.

Se da ya furzar da iska me zafi kafin ya ce “ko da ke ce da laifi be dace ta watsa miki lemo a jiki ba,hakan wulakanta ɗan adam ne. Am sorry on her behalf. Kuma zan sa ta ta ba ki hakuri okay? Oya smile for Uncle”

Murmushin ta sakar mai kamar yanda ya bukata. Se yanzu ya ji hankalin sa ya kwanta suna a haka ne su Yusrah suka shigo suka same su hannun a haɓarta suna kallan juna.

Kallan kallo suka tsaya yi da juna ganin yanda suka sa me su, gyaran murya Yusrah tayi da yasa Alisha ta ɗan ja baya yanda hannunsan ya bar haban nata.

ƙarasawa inda suke suka yi nan suka ta ba ta hakuri akan abinda Meenal din ta yi mata. a fili kuwa nuna musu tayi bakomai ya wuce amma a zuciya faɗi take

“Dama dena ɓata bakin ku kuka yi domin Alisha ba ta yafiy, duk wanda ya mata se ta masa wannan alkawari ne”

A can falo kuwa sosai mahaifiyar Meenal ta hau yi mata faɗa inda se kumbura baki take yi se kace wacce tayi abin arziki,su Adda kuwa taɓe baki suka yi dan sun san wannan faɗan babu abinda ze canza a halin Meenal a haka aka tashi a walimar kowa ya tafi gidansa amma banda Meenal din da ta haura part din su Ameera bayan tafiyan iyayenta.

Falon ya yi saura iya su Adda da kawun su Sameer se su gwaggo indo da shi Ɗan gaske din.

Gwaggo indo da ta kasa hakuri ne ta dubi Ɗan gaske ta ce “Yanzu Modibbo wannan yarinyar ce za ka aurawa ɗan ka Haydar?yarinyar da sam babu tarbiya a tare da ita.

Gaskiya baka yi tunani me kyau ba yanzu ka duba abinda ta aikata a idan jamaa, baiwar Allah nan babu abinda ta mata amma ta ci mutuncinta a gaban kowa. Kuma mahaifinta be ce mata komai ba”

“Ni kaina abin da yarinyar nan ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login