Showing 84001 words to 87000 words out of 96407 words
Chapter 29 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
Alwala, da sauri ta isa inda ta ke ta na ƙare mata kallo
“Inna ta fatan kina lafiya? Hankali na ya tashi da irin wannan kiran gaggawa da ki ka min wanda a da can sam ba ki taɓa yi min makamancin sa ba. hope komai na lafiya?”
Ajiye butar hannunta tayi tana gyara zaman dankwalin kan ta tace
“Lafiya lau Alisha babu abinda ya same ni kawai na kira ki ne saboda na yi kewar ki,ki je falo ina shigowa bari in idar da alwala”
Kallan ta tayi kawai bawai ta yarda da abinda ta ce mata bane saboda Adda ba ta taɓa mata haka ba,falon ta nufa tana me yaye labulen falon ta shige,turus ta ja burki ta tsaya tana girgiza kan ta cike da son karyata abinda idanun ta suke gane mata.
Baya ta ja tana girgiza kanta tare da amfani da tafukan hannunta ta toshe bakinta a hankali ta furta
“No is a lie”
Murmushi dukkan su biyu suka sake bayan ganin reaction din ta, miƙewa tsaye ya yi yana buɗe mata hannun sa duka biyu da zazzakar muryar sa ya furta
“I miss you so much my darling sister”
Wasu irin zafafan hawaye ne suka hau kwararowa daga idanunta kafin a karo na biyu ta kuma buɗe bakin ta ta ce
“Ya Zaid dina” ta faɗa hakan tana shiga falon da mugun gudu ta faɗa a jikinsa tare da rungumesa gam kamar wani ze kwace mata shi, ta sanya kuka tana sake matse shi gam a jikinta
Fadlɗi take “Allah yasa am not dreaming,ya Zaid dina pinch me saboda in tabbatar da ba mafarki na ke yi ba”
Idanunsa na zubar da hawayen tausayin kan su ya sa hannu ya mintsuneta a bayanta kana yace
“You’re not dreaming Alisha darling,it’s me your Zaid”
Sake fashewa tayi da sabon kuka bayan ta ji mintsunin da ya mata hakan ya tabbatar mata she’s not dreaming caused she really felt the pain.
“Wallahi na yarda kai ne ya Zaid dina it’s you,Alhamdulillah”
Ta fada cikin muryar kuka me taɓa rai da ɓargo ,yanda ta ke kuka ya nuna tana amayar da duk abubuwan da suka tokare mata kirji ne,tana kuka ne a dalilai da suke da yawa,ganin Zaid ya dawo mata da komai sabo fil tamkar yau ne wannan abu ya faru,ganin Zaid ya tuna mata da rayuwa me dadi da suka yi a tare da junan su,ganin Zaid ya tuna mata da irin azaban da ta sha.abubuwa da dama ne suka dinga dawo dawo mata da ya sa brain din ta ya soma sakar mata wasu irin flash ba ƙakƙautawa.
Shuru su ka ji ta yi, kukan cak ya tsaya,jikinta ya sake? hannunta da ta ƙanƙamesa dashi ya gangaro,ɗan ɗago ta yayi ya ga idanunta rufe kamar me bacci,shafa face na ta yay yana tsura mata ido hawaye na zuba daga idan sa.
Mujahid ne ya ce “ ta suma “
“Yes amini ta suma,Alisha has gone through a lot, yarinyace ƙarama da yakamata a ce she’s achieving her dreams,living her best life,but because of these cowards my sis sister goes through this trauma. Bazan taɓa yafe mu su ba. Yanda suka sa mu kuka sai na sa sun yi na jini ,wannan alkawarin Zaid ne,na tsani jinin makiyi, na tsani alaka da makiyina.” Ya faɗi hakan da wata murya me kaushi.
Ɗaukanta yayi cak kamar ƴar tsana ya kwantar akan three siter. Ruwa Inna ta miƙo masa a kofi,shafa mata ruwan da ya zuba a hannun nasa yayi a fuska a hankali ta sauke ajiyar zuciya ta buɗe idonta tar akan sa.
Yunƙurawa ta yi za ta zauna yai saurin riƙo kafaɗunta yana girgiza mata kai,murmushi ta yi mai
“Ya Zaid,yaushe ne ku ka zo ? Na yi farin cikin ganin ka ɗan uwana rabin jikina. Ashe ina da dalilin ci gaba da rayuwa tunda Ina da kai. Ashe akwai nawa da zan gani in ji sanyi araina,na yi tunanin maraici ne ze ga bayana ashe kana nan,Allah kai ne abun godiya da ka nu na min wannan rana”
Zaid da ke shafa gashinta da dayan hannun sa yana sake jin kaunar ƴar ƙaramar ƙanwar ta sa na ninkuwa a zuciyar sa, ya ce
“ Allah shine abin godiya Alisha darling,Inna ta bani labarin komai,indeed you’re a strong person, after facing so many obstacles you still survived. Sannan har ki ka rubuta jerin list din sunayen shaidanun da suka cutar damu ki ka fara ɗaukan fansa,kin yi abinda yakamata in yi,amma yanzu no more stress am here Alisha, zan tabbatar da na ɗanɗana mu su azaban da sai sun roƙi mutuwa,sai na azabtar da duk wani sasssa na jikin su kafin su bar duniya. Sai sun ne mi ruwan hawaye sun rasa a idanunsu a yayinda ze kafe tsabar wahala. Na rantse sai na bi su daya bayan daya na musu mummunar kisa.” Yanda yake magana kaɗai ya isa in ka ji ka fahimci masifar son ɗaukan fansa dake ransa, muryarsa ya nuna hakan yanda yake fita a dake.
ya ƙara da “Kuma sannan! zaman ki ya ƙare a gidan Ɗan gaske daga yau,dan baze yu ki dinga zama a ƙarƙashin inuwar makiyan mu ba.”
“Ya Zaid zamana a wannan gida yana da muhimmanci,ina son in tarwatsa su ne kafin in kashe Ɗan gaske da ɗansa,ba na son su mutu batare da sun ƙunshi bakin ciki irin wanda mahaifin mu ya ƙunsa ba. Na yi kokari na shiga tsakanin Katanga da kuma Ɗan gaske yanzu gagarumin gaba ne ke tsakanin su,dole in koma in ƙarasa abinda na fara a wannan gida”
Yanda fuskar sa ya sauya lokaci guda ya nuna sam baya son zaman ta a gidan, dan shi Zaid yana da baƙar zuciya da in ya tsani abu ya tsana kenan har gaba da abada hakan yasa ne baya son ta dinga raɓan su,dan da inna take ba sa labari kan cewa tana rayuwa a cikin ahalin Ɗan gaske sai da ya ji ran sa ya sosu.
Ganin yanda Zaid ya ke faɗin bazata koma bane yasa ta fasa faɗa musu aurenta da Haydar da ake shirin yi. ta bari sai ana saura satı guda tukuna ta faɗa musu, dan sarai ta san wanene Zaid ze iya tayarwa da kowa hankali matukar ya ji wa za ta aura.
Taɓatan da yay ne ya dawo da ita daga tunanin da take
“Ni de bana son rayuwar ki a wancan gidan makasan,amma tunda kince akwai abinda ki ke son ƙarasawa na amince da hakan. ki kula min da kan ki sosai kuma sannan,kar ki kuskura wani sabo,tausayi,ko soyayya ya ƙullu tsakanin ki da wani a wannan banzan ahalin ,dan Zaiyad Sagir Lelewal ba ze taɓa lamunta haɗa wani dangantaka da makiyi ba,kin ji ko shalelen ƙanwata”
Tana sakin murmushin farin ciki wanda ta manta rabon da tayi shi ta nodding head na ta
“Kar ka damu da wannan Ya Zaid dina,inde wannan ne ka tsoma ranka a inuwa ”
Murmushi Inna da Mujahid suka yi ganin farin ciki ɗauke akan fuskokin su duka biyu…
Mujahid dake zaune ya zuba musu ido yana murmushi ne ganin darıya akan fuskokinsu wanda ko yaushe wannan shine burin sa,ta kalla motsa bakin ta tayi
“Mujahid” ta kira sa a sanyaye, sai kuma ta sake cewa
“Kai din ka wuce aboki sai de ɗan uwa,ka yi min taimako sosai,ka zauna da Zaid dina, da dadi da ba dadi. kai kuwa wannan karamci a gare mu da me zan saka maka? Allahu shine shaida mutuncinka da nasaba ya sake ninkuwa a idanuna,Allahu ya biyaka ya ji kanka ba dan ka mutu ba,Allah ya bar mu tare”
“Ameen ameen darling sis, bana bukatar komai kuma nayi komai ne domin Allah da kuma so tsakani da Allah. Kamar yanda na faɗa miki Zaid ya zarce matsayin aboki a gurina sai de ɗan uwa”
Sosai maganganun su ya taɓa zuciyar Zaid,hakanin gaskiya a yanzu Kaf duniya daga ƙanwar sa Alisha bayi da wani wanda ya kai masa Mujahid,yana girmamasa yana farin ciki, da gode wa ubangiji wanda shine ya wurgo masa Mujahid cikin rayuwarsa tun yana aji biyu a secondary suka fara abota,yanda ya taimaka masa a lokacin da yake matukar bukatar wani a kusa dashi yayi alkawarin shima sai ya faranta masa rai,duk da yasan be isa kuma be da abinda ze rama halaccin mujahid din a gare sa amma yana fatan kimantawa.
“Nagode Amini kai din mutum ne na musamman a duniyar nan”
Dariya me ɗan sauti yayi “ an ya ban gaji da jin wannan maganganun naka ba kuwa? Tunda ka farfaɗo sai ce min ka ke nagode amini” ya ƙare magana yana kwaikwayon yanda Zaid ke magana.
Duk dariya suka sa kafin inna da alwalarta har ya bushe ba ta samu yin sallah ba ta tsaya ganin wayannan ƴan uwa biyu da suka sha ukuba na fitan hankali a rayuwar su,
“Bari in sako mu ku abinci” ta shiga kitchen din nata, ba da jimawa ba sai ga ta nan ta fito da babban tray ta zuba musu farar shinkafa da miya da tayi ga manya-manyan kifi a saman miyan kamar ka kwala kiran su suce naam.
ƙasa suka sauko su ukun kowa ya ɗau chokali. Alisha na zaune tsakiyar su suka soma cin abinci,zobo da tayi inna ta kawo da kofuna ta dire musu daki ta wuce bayan ta ajiye abubuwan da ta san za su bukata, ta tada sallah.
Sosai ta buɗe cikinta taci abincin har say da ta ji ta zo geji ta ajiye spoon tana dafa hannu a cikinta ta manta yaushe ne rabon da ta ci abinci sosai,ɗan duban ta Zaid yayi ya ga ta ajiye spoon na ta a bakin tray alamun ta koshi,se da ya taune abincin bakinsa ya haɗiye dan gudun karya kware yayin haɗa magana da cin abinci, ya ce
“ Har kin koshi kenan? Dama Inna ta faɗa min sam bakya son cin abinci da yawa “
Ya mutsa fuska tayi tana tura baki, ta ce “ Allah ya Zaid na manta yaushe rabon da in ci abinci haka”
“ Daga yanzu bazan sake yarda kina cin abinci kaɗan ba”
“Thank you ya Zaid”
Mujahid da shima ya koshi din ne ya kife spoon din a bakin tray yana
“Alhamdulillah cikina ya ɗauka”
“Wato ni za ku bar wa suɗin kwano duk kun tashi “
Dariya suka yi ganin shima ya ajiye spoon din sa ya miƙe ya haura saman kujera yay zamansa Inna da tafito da idar da sallah tana jiyo su ne tayi dariya
“Yooo ai da ba ka kulasu ba Babana,ka karasa abincinka kawai tunda su sun ki cin albarka karshen kwano”
“Aikuwa Hajiya Inna bari in dau kifin nan shima ya wadatar “ cewar Zaid yana daukan kifin.
Alisha kam ta kura masa ido se kallon sa take ganin yanda ya dawo bayan an yi aiki kamar ba shine Zaid din da yake kwance be san duniyar da yake ba,yayi kyau sosai ko ina na jikin sa sumul kamar ba shi ba. wata biyu da suka yi a can har wani ɗan kiɓa yayi ya ƙara haske,lallai ta kara yarda babu abinda kudi ya bari in kana da kudin ka tofa bazaka wulakanta ba,kama ta yayi tana kallon sa
“Wannan kallon fa darling ki yi hakuri kar ki cinye ni” ya faɗa cikin barkwanci.
Ba ta tanka ba se murmushin da kawai ta yi tana duba wayarta ta ga shida da ashirin saura.
“Ni zan tafi duhu ya fara saukowa,kar su fara nemana”
Ta kare faɗa tana miƙewa tsam ta ɗauki mayafin doguwar rigarta ta yafa sannan ta je ta rungume Zaid
“Ya Zaid take care se mun yi waya,ga bedroom dina anan za ka kasance,kar ka dinga fita batare da mask ba saboda duniya ta rigada ta sanka ta dalilin social media. Mujahid please ka dinga kula dashi”
Ta yi maganar tana duban Mujahid da ke gyada mata kai.
“Inna se mun yi waya in sha Allah zan dinga zuwa in na samu time”
Ta rungumeta,tana a jikin Inna ta ji muryar Zaid na cewa
“Who is your next target Darling?"
Sake inna ta yi tana fuskantarsa, ta ce “Habibu Katanga “
Ɗaga mata babban yatsansa yayi alamu abinda ta faɗa ya burge sa kana, ya ce
“Nice choice,zaɓi me kyau,ki je ki kawai darling. ki yi abinda ya kai ki gidan Ɗan gaske, ni kuma nan zan ji da Katanga,i will make sure he gets what he deserves “
“I trust you Ya Said, make him pay for his sins”
“Mujahid se mun yi waya” ta faɗa tana fita a falon tayi cikin gida,haka Alisha ta bar gıda batare da ta faɗa mu su hukuncin da ta yanke na auran Haydar ba.
Bayan mangriba ta dawo gidan yawanci duk suna ciki saboda sanyin da ake yi yau, so luckily ba ta samu kowa a falon ƙasa ba har ta haura bangaren Adda ba ta haɗu da wani ba,kai tsaye bedroom din ta ta shige ta cire mayafinta ta shiga toilet tayi alwala ta fito ta gabatar da sallah mangrib da ya riske ta a hanya.
Shin mai ku ke yi har yanzu ba ku yi payment din book two Fansar mace ba? Kar ku manta free Pages Saura kadan ne ya kare.
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
43 & 44_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
43 & 44
Haka kwana ki suka yi ta ja biki sai sake matsowa yake yi, yanzu kam komai ya gama kankama dan saura satı daya rak a ɗaura sure. gaba daya cikin hidima su ke abunka da masu kudi komai a gidan nan se da aka sake shi, daga fenti har furniture da komai na kwalliya sai da aka sa sabo,gida ya sake kyalkyakewa ya yi masifar kyau musamman bangaren da amarya za ta tare wato bangaren ango Haydar,tun da aka shiga satin ma shi sam be zauna ba sosai, binciken da ya ke yi ya hanasa nutsuwa ya fi son se ana saura kwana biyu auren ya ɗauki hutu tunda de babu event ko daya da zaa yi dan daga shi har Alisha raayin su ya zo daya, ba sa son wani raye_raye da kiɗe-kiɗe,fatiha kawai zaa shafa akai amarya dakin ta se ɗaukan hotuna haka suka gama tsarawa. Adda da Hajja Hauwa iyayen ango kuma iyayen amarya se da su ka tabbatar da an yi komai yanda ya dace sannan suka samu nutsuwa,gyara kam Alisha ta sha shi dan an yi mata gyara na gani na faɗa ,fatar nan nata kamar ka taɓa ya tsirtar da jini tsaban yanda yake ɗaukan ido da sheƙi,se ya koma kamar na jarirai. Ga wani kamshi na musamman da take yi wanda ko zama ta yi a guri tofa kamshin ya kama kenan .tayi kyau ga tasha jan lalle da aka mata hannu da kafa ya gyatso yayi brown sosai, bakin dayis kuma se ana gobe ɗaurin aure zaa yi mata shi. Ko makaho ya shafata tofa se ya gane amarya ce.
Tunda Zaid su ka dawo har ta je gidan inna, har yau ba ta sa ke komawa ba kusan satı kenan yanzu saboda ba ta samun daman, fita amma yau ta kuɗurta se ta samu hanyar da ta bi ta fita ko da fisha ne ta je ta dawo,duk da ba ta je ba amma kullum suna waya da Inna,Zaid da kuma Mujahid. Duk da haka ta kasa sanar da su batun auren ta fi so se ta je da kanta ta faɗa musu. Tsakanin ta da Haydar kuwa yau kwana uku lafiyayyu ba ta sa shi a idon ta ba, tun ranan da ya kira ta a waya ya ce yana bukatar coffee ta kai mai a falon sa har yau bata kuma sa shi a ido ba,aiyukan da yake fama da su ya janyo haka se de ya kira ta a waya da safe ka fin ya fita su gaisa shikenan.
A bangaren ƙannen ango kuwa sam ba su zauna ba hidima suke yi ba kama hannun yaro, ba su samu kwanciyar hankali ba se da suka karɓo dinkunan ankon da suka yi su uku da sauran kayayyakin da su ka bayar a dinka musu na fitan biki a gun tela,har da na amarya da aka bayar da turaman manyan atamfofi guda ashirin, da kuma laces guda sha biyar da shaddodi guda goma duk telolin sun kammala sun dawo da su saboda an cake musu kudi cas shisa basu yi wasa da dinkin ba.
Sameer kam busy gaban sa yake yi yanda ka san ba biki ake yi a gidan ba,yana nan yana ta abubuwan siyasan sa dan sosai ya maida hankali akan zaɓen sa kamar yanda Ɗan gaske ya ɗaura sa a hanya,sosai ya ke zubar da kudi wajen zaɓen nan kuma cikin ikon Allah yana samun magoya baya dan yanzu saura ƴan kwana ki ne kaɗan sakamakon zaɓen ya fito. wannan ne yasa sam be zauna ba .ya ɗauki wannan zaɓe da matukar muhimmanci baya wasa da abinda ze taɓa masa zaɓe.
Doguwar farin hijab ta sanya sannan ta ɗauki niqab ta ɗaura a fuskarta babu abinda za ka iya hangowa se manyan fararen idanunta, har za ta fita se ta dakata tana zuwa gaban wardrobe tunawa da memory da ta manta dashi ta ɗauko a inda ta ɓoye sa sannan ta buɗe case din wayarta ta ajiye sa a ciki,kana ta fita. Main falo ta sauko kan ta tsaye ta san Haydar