Showing 36001 words to 39000 words out of 96407 words

Chapter 13 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx

07 Aug 2025

3631

zama abinda ya zama ina tsoron in kai ƙara wayanda suka aikatan su ji su fara farauta na”

“Amma Mujahid a gun waye ka ji wannan abun ?“

Ajiyar zuciya ya sauke “Alisha is a long story yau shekara daya ina neman mafita,ki biyo ni domin samun amsar ki”

Ya yi maganar yana riƙo hannun ta, zuwa yanzu bata da zaɓin da ya wuce ta bi sa din domin sanın yanda akai ya san gaskiya napep ya tara sannan yace “malam Taura za ka kai mu can ciki wajen transforma na biyu”suka shiga tunda suka fara tafiya daga ita har shi babu wanda ya sake cewa dan uwan sa wani abu har suka isa anguwar. tafiya suke tayi can cikin anguwar can ƙarshe-ƙarshe babu kowa se daji. se wani Ɗan ƙaramin gida nan ya cewa me napep din ya tsaya. sauka suka yi ya biyasa nan ma sake riƙe mata hannun yayi har bakin kofan gidan, ya sa key a ƴar ƙaramar kofar ya buɗe suka shiga.

Ƙarewa ko ina kallo ta ke yi gida ne ɗan ƙarami deden zaman mace daya a talauce,an de gama gini an yi plasta amma babu ko fenti kofar falon suka nufa nan ma ya murza key ya buɗe suka shiga katifa ce kaɗai a cikin falon se akwatin kaya daya. Kallansa ta yi ta ga shima ita yake kallo,haka kawai ta ringa jin wani irin yanayı me wuyar fassaruwa jikinta ya yi sanyi sosai idanunta suka fara kawo hawaye ita kan ta bazata ce ga dalilin hakan ba amma tana jin kusancinta da wani sashi na ta.

“Mujahid “ sunan sa kawai ta iya ambata dakyar girgiza mata kai yayi alamar kar ta ce komai sannan ya nuna mata kofar wani daki,kallon kofar ta yi da idanunta da suke tsiyayar da hawaye marasa dalili,dakyar ta iya taka kafarta ta isa bakin kofan ta buɗe ta shiga, lokacin da tayi arba dashi wani irin sarawa kanta yayi kamar ze tarwatse ga mummunar jiri da ya kwasheta da se da ta kusan zubewa a ƙasa,jikin ta ya ɗau kerma zuciyanta na bugawa da karfi kamar ze baso kirjinta ya fito. komai na dakin ya soma juya mata kasa riƙe hawayen ta tayi. Jiki na rawa ta soma isa inda yake, tsayawa tayi akan sa tana kallan sa sosai a hankali da dasasshiyar muryarta ta furta

“Zaid,Zaid da gaske kaine? Ya Zaid dina dama kana wannan duniyar ?” Zaid da ke kwance kamar gawa akan gado na asibiti be ma san tana yi ba fuskarsa manne da oxygen ga wasu igiyoyin na’urorin da suke manne a kirjinsa dakin ma ko ina na’ura ce, fuskarsa ya tara gashi Kamar ba ƙaramin matashi ba, jikinsa ba riga, se guntun wando, saboda daga abinda ya Kama daga tafin kafarsa har zuwa cinyarsa a kone yake gurin yayi wani iri babu dadin kallo. Gaba daya ya sauya kamar ba Zaid matashi ɗan son gayu da kwalisa ba wanda yan matan TikTok da IG suke crushing ba. Hannunta na rawa ta sa ta shafa fuskarsa tabbas Ya Zaid din ta ne wanda take matukar so da kauna, ɗan uwanta da ya ke ji da ita kamar kwai. zuɓewa tayi a gaban gadon ta fashe da marayan kukan da tunda ta dawo hayyacinta bata yi sa ba. kuka take yi sosai tana tuna abubuwan da suka faru dasu cikin kukan ne take cewa

“Ashe akwai ahali na daya yake raye a wannan duniyar? ashe ba marainiya bace gaba daya, ɗan uwana na jini yana wannan duniyar,Ya Zaid ya aka yi ban san da kana raye ba meyasa?meyasa,meyasa? ” ta ƙarishe maganar tana dukan ƙasa sosai take kuka kamar za ta shiɗe, Mujahid dake tsaye a bakin kofa shi kansa hawaye yake yi cike da tausayinsu, mutanen da suke rayuwar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali sune yanzu suka zama abun tausayi cikin mutum biyar biyu ne kawai suka tsira nan ma daya na halin rayuwa ko mutuwa.

Miƙewa tayi ta zauna a gefen gadon sannan ta kwantar da kanta a wuyansa tana ci gaba da kukan ta amma ta sassauta muryar ta.

A can super market kuwa bayan Haydar ya gama wayan ne ya juyo gare ta se de wayam ba ita a gurin da ya barta, dudduba ta yayi a farfajiyar amma babu ita hakan yasa be kawo komai a ran sa ba yai tunanin ta shiga ciki gurin su Yusra hakan yasa ya shiga cikin shima, samun su ya yi suna ta shopping suna ganin sa shi kaɗai kuma tare suka bar su a waje Yusra ne ta soma magana “Uncle Haydar ina Alisha din?”

Kallon me ki ke nufi ya aika mata “kamar ya ina Alisha ba ta shigo gurin ku bane ? " Kallon junan su suka fara yi suna girgiza kai su de ba su ga Alisha a cikin nan ba, saboda a waje su ka bar ta dashi yanzu kuma yana tambayar su ina take

“Meye ku ka tsaya kuna girgiza kai kamar wasu kaɗangaru kun min shuru ina tambayar ku?”

“Uncle Haydar ba ta shigo nan ba fa, ai a waje mu ka bar ku tare. amma gaskiya ba ta zo cikin nan ba dan da ta shigo za mu ganta tunda ta baki-baki mu ke ko Zainab? “ da sauri ta gyada wa Ameeran kai.

“To ina waya na juyo ban ganta ba shine nayi tunanin tana gurin ku” ya faɗa yana danna kiran layin Adda yana so ya ji ko de gida ta dawo, suna waya da Adda ne yake tambayar ta ko Alisha ta dawo amma tace masa ah ah bata dawo ba,, tana kokarin tambayar sa meyafaru ya kashe wayar. Da gaggawa suka fara neman ta a cikin San Hussain super market din amma fa babu ita babu dalilin ta. Zainab ce ta ce “ abun takaici ga shi babu waya a hannunta balle mutum ya kira ya ji lafiya”

Se a sannan Haydar ya san bata ma da waya ya ji haushi sosai dan da ya sani da ya jima da siya mata saboda rana irin haka yanzu ba su san inda ta yi ba.

“Amma mu koma gida kawai ni ina tunanin ko ta je gidan wannan kawun na ta ne da ta je jiya “

Sun yarda da maganar ta dan se yanzu hakan ya faɗo musu amma to meye dalilinta na tafiya ba tare da ta sanarwa kowa ba duk ta daga musu hankali. a haka suka shiga motar, kasuwan waya ya shiga ya siya mata waya iPhone 12 normal irin na hannun Zainab da sim ya koma motar yayi driving na su zuwa gida. A falo suka samu Adda,Meenal,Maryam da jaririnta Aryan suna zaune kana ganin su ka ga damuwa a tattare da su domin tunda ya kira su yake tambayar Alisha suka san something is not right

“Haydar ina ne inda Alisha ta je ta?”

Tambayar da Adda ta fara wurga masa Kenan

Se da ya zauna jiki a mace yace “Wallahi Adda duk bamu sani ba saboda ina fa tsaye da ita a bakin motar aka kirani na juya ina waya, na gama kenan na ga babu ita, kuma ko cikin San Hussain din ba ta shiga ba”

Tafa hannu Adda ta yi ta soma sallallami “ohhh ni Zuwaira ina yarinyar nan ta je to? Allah yasa de kafanta ne ya ja ta ba janta aka yi ba”cikin damuwa duk suka amsa da ameen banda Meenal da ta taɓe baki.

Maryam dake bawa yaronta madara a feeder ne ta ce “kun san fa Alisha ƴar dakin Hajja Hauwa ce ko de ta bi gidan ta ne? ku gwada kira ku tambaya”

“Maryam Hajja Hauwa ba ta gari ,yanzu muka kira ta ma ɗaga mata hankali kawai zamu yi,su Ameera de sun ce ƙila gidan kawunta ta je mu jira zuwa anjuma mu gani in ba ta dawo ba nasan abinda zan yi “ya faɗa yana miƙe wa tsaye da niyar zuwa part din sa,duk sun yarda da maganar sa, hakan yasa suka yi jugum ko siyayyan abinda suka je yi ma basu samu sun yi sa a tsanake ba suka dawo.

“Kun wani ɗaga hankalin ku akan wata banza mara asali,kila saurayinta ta bi kun wani damu kan ku” da zallan mamaki duk suka kalli Meenal da tayi maganar hankalin ta kwance.

Yusra da ta ke bin ta da banzan kallo ne ta ce “waya gaya mi ki kowa ma irin ki ne me shegen biye-biyen maza?ke har kina da bakin magana tsabar mutuwar zuciya kin tattaro kin dawo gidan su saurayi”

Murmushi Maryam,Ameera da Zainab suka yi domin kuwa amsar da Yusra ta bawa Meenal ya musu dadi,Meenal da maganar ya mata zafi ne ta ce “to ai gwara ni, ke fa me neman…”

“Ya isa dallah kar ku cika wa mutane kunne da haukan ku” Haydar ya faɗa a tsawace wanda ya dakatar da Meenal daga ƙarasa maganar ta. aikuwa mit tayi da bakin ta domin duk barikinta tana shakkan Haydar nesa ba kusa ba.

Part din sa ya wuce yana tunanin yaushe ne Alisha zata dawo gida.

Se da ta sha kukan ta sosai ta koshi kafin tayi shuru har zuwa yanzu tana kwance a jikin Zaid jin ta take tamkar ba'a duniyar take ba, farin ciki da bakin ciki ne suka haɗu mata a lokaci daya. tana kwance se sauke numfashi take saboda yanda zuciyarta yake tsananta bugawa

“A daren da wannan abu ya faru Allah ya ƙaddara Zaid yana da dogon kwana, wutar ya faracin jikinsa da kayansa wanda hakan shine ya farfado dashi daga doguwar suman da yayi,a gaggauce ya cire Kayan jikin sa sannan ya je dakin sa dakyar ya lalubo jallabiya ko da ya sa shi ma jiƙewa da jini ya fara yi. Kallon ku yayi ya ga duk babu wanda yake raye hakan yasa ya fice ya bar gidan ya kai kansa karamar asibitin Miyetti dake kusa da ku. An yi sa'a likitocin sun karɓesa suka basa taimakon gaggawa saboda in ba su taimaka ba ze iya mutuwa sakamakon harbi da buguwa da yayi akai ga kuma kunnan wuta. Bayan ya farfado ne suka tambayesa ina ahalinsa yace basa nan amma su bashi waya akwai wanda ze kira. nayi mamaki ganin kira karfe uku da rabin dare kuma da bakuwar number da kamar bazan ɗaga ba se kuma nayi tunanin ko wani daga gida ne yake kiran na. ko da na ji muryar Zaid hankalina ya tashi nan doctor din ya ce min in zo asibitin miyetti a cikin daren na fita,ko da ganin halin da Zaid yake ciki se da nayi kuka kamar raina ze fita. Zama nayi kusa dashi ina tambayar sa me yafaru nan ne ya kwashe komai ya faɗa min harda yanda ya zo asibitin duka yana gama sanar dani kenan ya suma. Likitan ne ya kira ni ya bani result din hoton da suka yi masa akai, ya samu buguwa ba na wasa ba wanda in ba'a ɗau mataki ba ze janyo masa cutar mantuwa ko kuma de ya shiga coma na tsawon lokaci, sannan duka da aka masa sun karya masa ƙashin baya,ga kuma mummunar kunan da yayi duka aiki zaa yi masa kuma baa nan Nigeria ba, in ana so ya warke sumul tofa dole a fita dashi India a yi masa aiki gaba daya. wannan shine kawai mafitar da likitan ya bani,tambayar sa nayi da kudin aikin da expensives din tafiyar mu ze kai nawa budan bakin sa yace min ze kai million ashirin da biyar zuwa talatin. hankalina ya matukar tashi, domin ko mahafina bashi da wannan kudin balle ni komai tsaya min yai cak , lokaci daya masassara ya sauko min abun ya haɗu min biyu ga abinda Zaid ya gaya min ga kuma kudin aikin sa,haka har garı ya waye ina asibiti amma har time din Zaid be farka ba, karfe sha daya na ga ko ina a social media platform maganar ku ake yi kan cewa gidan ku yayi gobara duk kun mutu. ji nayi ina ma ina da power da zan fito in sanar da duniya gaskiya. A haka na kwashe sati biyu a asibiti da Zaid amma fa babu labari,doctor ne ya sanar dani ya shiga coma kuma baze farka ba se an yi masa aiki. Duk wasu kuɗaɗe na nayi amfani dasu wajen yi masa treatment daga karshe ba yanda na iya haka na kawo sa wannan gida shima haya na kama shine aka zo aka shirya dakin nan aka sa masa wayannan na’urorin da ki ke gani”

Share hawayen fuskar ta tayi sannan ta miƙe zaune ta na me kallon Mujahid “nawa ne kace ze iya a yi masa aikin komai da ze warke Mujahid?”

“25 million ze yi komai kamar yanda doctor can ya faɗa min” jinjina kai ta yi ta kuma faɗin “amma ya zaa yi a fitar dashi ba tare da an samu mishkila ba? saboda ba na son duniya ta san muna raye yanzu “

Numfashi ya sauke ya shigo dakin “wannan duk ba me wahala bane samuwar kudin ne wahala Alisha,samun 25 million shine babba “

“Ko nawa ne zan kashe saboda ɗan uwa na. daga yau ka fara shirye-shiryen tafiya ni zan tafi yanzu in ɗauko maka ATM kai se ka san yanda za ka yi dashi “

Be taɓa tsammanin za'a samu kudi har haka a gurin Alisha ba saboda yanda komai nasu ya kone ,amma se gashi tana da wayannan makudan kudaden mamaki yayi ba ɗan kaɗan ba. amma yayi farin ciki da jin haka ko ba komai yanzu abokin sa ze samu lafiya,yana cikin wannan ya ji ta tana mai magana amma da yake hankalin sa na wata duniya be ma ji abinda ta faɗa ba.

“Me ki ka ce?”

“Ina son in ba ka hakuri sannan kuma in gode maka na kokarin da ka yi da ɗan uwana har na tsawon shekara guda, nagode sosai. tabbas kai din abokine na kwarai, aboki da ya riƙe amanar abokantaka, ba kowa ne irin ka ba”

Dafa kafaɗar ta yai “Noo need for this Alisha,ni da Zaid tamkar uwa daya uba daya haka muka ɗauki junan mu. kuma na tabbatar da a ce ni ne a wannan condition din Zaid ze min fiye da haka so please stop thanking me “

Murmushi ta yi hakikanin gaskiya Mujahid yayi gaining respect a gurin ta saboda yanda ya kula mata da jinin ta “ni zan je gidan Inna ta ,zan ɗauko maka komai in ya so se mu haɗu a junction na by pass ko ta gurin kasuwan tare."

A tare suka fito kowa ya hau abun hawan sa daban tana isa gida ta sanar wa Inna sosai ta tayata murna. se da ta watsa ruwa sannan ta ɗauki abinda ya kawo ta sannan tai mata sallama lokacin ana gabannin kiran mangriba,yanda suka yi a bakin tare suka haɗu nan ya sanar da ita nan da kwana uku zasu tafi. Sanar da ita yayi Peter ze shigo gobe kuma ya ɗau aniyar taimaka mata domin ɗaukan fansar ta akan sa.

Bayan ta basa ATM ne ta soma tunanin yanzu ya zaa yi ta koma Ɗan gaske family ? wani tunani ta yi na gobe ne za ta fuskanci Peter kuma in de ta koma gidan Ɗan gaske ba lallai ne ta samu daman fita a lokacin da ta so ba. Gidan Inna ta koma kawai saboda shine kawai solution

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like

21 & 22_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

*NIDA PATIENT DINA*

*ASHE ZAMUGA JUNA*

*ƊAYA CIKIN BIYU*

*MAKIRIN IKO*

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

21 & 22

Kwance yake a bedroom din sa, rabin jikin sa na kan gado while kafafunsa na zube akan carpet, hannunsa riƙe da wayar da ya siya mata se jujjuyasa ya ke babu abinda yake yi da ya wuce aikin tunani, ga shi har yanzu ba ta dawo ba har izuwa yanzu da ya kasance karfe takwas da arba’in amma babu labarinta,yana me jin haushin kan sa da be taɓa tunanin ce mata su je gidan kawun na ta tare ba,da ace ya san gidan to tabbas ze je domin dubawa ko tana can,se kuma rashin waya be taɓa sanın cewa ba ta da waya ba da ya jima da siya mata. Yau tun da suka dawo ya koma sukuku be taɓa sanın ya wani damu da ita haka ba se yanzu da be san inda take ba. Fatansa de shine Allah yasa tana gidan kawun nata yasan inde can ta je to zata dawo. Yana wannan tunanin Meenal ta shigo cikin shiga na Kayan bacci har ta zauna kusa da shi be sanı ba yana tunani,ɗaura hannunta ta yi akan nasa tana duban face nasa

“Uncle Haydar “ da sauri ya ɗago saboda muryar Alisha ya ji batare da ya ga fuskar Meenal din ba ya ce”Naaaam Alisha” turbune fuska tayi jin ya kira sunan ta wato kwanciyar da ya yi din nan tunaninta yake yi. sosai ran ta ya ɓaci shi kuma ko da ya ga Meenal ce ba Alisha ba, hakan yasa shi jan tsaki tare da ɗauke hannun sa da ta ɗaura na ta “ke meye ne ya kawo ki daki na?”

“Tunda kai ka ƙi ka zo mu yi hira ka tsaya tunanin wata can daban shine ni na biyoka,wai meye matsalar ka da wancan yarinyar ne Haydar? tun kallon farko na gane kana son ta amma ka sani ita din ba kalar macen da ta dace da kai bane ni ce nan type din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login