Showing 75001 words to 78000 words out of 96407 words
Chapter 26 - FANSAR MACE Book Complete by Mrs Isham.docx
ba ta iya hakuri ba se da ta dubi Maryam ta ce
“Anty Maryam kin ga”
Karɓan wayan Maryam tayi nan idon ta ya sauka akan wannan video da aka turawa Haydar na Meenal da wani saurayi,a saman video an yi caption da ‘wannan da ku ke gani sunan ta Meenal yar gidan wannan dan siyasan nan Katanga. ana gobe auren ta amma ta je hotel suna sheƙa ayarsu da tsohon saurayinta. Ko da ta gama karantawa sallallami Adda ta doka
“Yanzu fisabilillahi waye ya watsa wannan abu a duniya? Duk da ta yi kuskure wannan ai an ɓata mata suna ne da kuma uban ta da siyasarsa “
Adda ta faɗa tana riƙe haɓa,Yusra ba iya nan ba TikTok ma da ta shiga video ta samu yana ta trending nan ta kuma nu na musu na TikTok din sannan ta shiga Instagram da twitter duk ta ga an poster su. A comment section mutane se tsine mata suke yi suna Allah wadai da abinda ta aikata ana gobe bikinta amma ta je gun wani tana iskanci. wasu kuwa har kafeta suka yi suna magana akan ta da saurayin ta da shi fuskarsa be fito ba.
Ajiyar zuciya ta yi ta ce“Hmmm Allah de ya kyauta,dama a rayuwa in ka ce ba ka ji se Allah ya gwada maka kai ba komai bane ta hanyar haɗa ka da mutanen da suka fi ka rashin kirki” cewar Zainab ta na kwantar da kan ta a kafaɗar Alisha,Alisha da tayi slide smile batare da kowa ya gani bane bayan ta ji abinda Zainab din ta faɗa ,a ranta ta ce
“Maganar ki haka yake Zainab “
Haka suka zauna shuru kamar gidan mutuwa suna jiran dawuwar Haydar dan jin ya ake ciki.
KATANGA’s HOUSE
Duk su ukun suna zaune a falo, Meenal sai hawaye ta ke yi ga Mahaifiyarta Hajiya Balaraba ta sakota a gaba sai faɗa ta ke yi mata kamar za ta cinye ta saboda video Meenal din da suka gama gani yanzu a kafofin sada zumunta.
Yana daga hakimce akan kujera ya ce “Hajiya Balaraba dan Allah ki yi wa yarinyar nan hakuri haka, da wannan faɗan na ki, da wanne ki ke so ta ji?da fasa aurenta da wancan shashashan yaron yayi, ko kuma da Video ta da yake ta yawo a duniya,ko da masifar ki? Ke in wata uwar ce ai tausaya mata yakamata ki yi ,ki zauna ki dinga rarrashinta ba ki sakata a gaba kina mata ihu ba”
Girgiza kai kawai ta yi cike da takaicin sa dan shine nan silar lalacewan tarbiyyan Meenal tun fil azal da a ce be sangartata ba da bazata lalace haka ba.
“Ai wallahi you’re to be blamed for everything Alhaji. Kai ne nan ka ruguza min tarbiyya da na bawa ƴata, ka nuna mata uban ta yana dashi za ka yi mata duk abinda ta bukata a duniya. yarinya ta taso ba ta san Kalmar babu ba,daga nan kuma ta fara yawace_yawace, tun da ka ke ka taɓa yi mata faɗa ko sau daya ne kan yawon da take yi har da su kwana a waje? Wallahi ban ga laifin Haydar ba ko kaɗan,ita ce ta watsar da kan ta har yasa auren ya fasu,in ba haka be ke da zaa yi auren ki jibi menene ya kai ki gun wani ? Ai duk ma abinda ki ke yi tunda aure za ki yi, ya kamata ki watsar da komai ki rungumi rayuwar auren ki. Amma yanzu wa gari ya waya? Ke ba auren Haydar ba,ga shi kin yi abinda duniya yanzu akan ki ake magana, yanzu meye amfanin haka?”
Tana hawaye ta dubi Hajiya Balaraba “Mommy wallahi Allah shine shaida na babu abinda ya shiga tsakanina da saurayin. hassalima ban taɓa sanın sa ba kawai kirana yayi ya ce yana so mu yi magana da na je yake ce min ga bukatar sa, nan nace masa aure zan yi. Hira kawai mu ka yi sannan na koma gida wannan shine iya abinda ya faru ashe ya sa min camera ban sanı ba”
“Dama na faɗa miki My Meenal is innocent, ana so a ɓata min suna ne da kuma image dina yasa aka yi amfani da wannan saurayi dan haka wallahi se na ɗau mataki kwakkwara akan ɗan iskan yaron nan. Daughter ba ni number sa”
Share hawayen fuskar ta tayi “daddy ai tun ranan da abin ya faru nake ta kiran wayar sa amma a kashe har yau be kunna wayar ba,ina ganin wasu suka sa shi ya tozarta ni haka”
Ta ƙarishe maganar tana kuma fashewa da kuka.
Cike da so da kauna ya soma lallashinta tare da mata alkawari ze sa a nemo masa duk wanda yake da sa hannu a fitowan video ta.
KUMO LOCAL GOVT.
Shigowa Falon sa ta yi hannunta riƙe da tray na abinci madedeci kuloli na abinci guda biyu masu kyau da tsada ne akan tray din, har ta shigo ta zauna be san da shigowarta ba,fahimtar da tayi ya tafi duniyar tunani ne yasa ta zauna kusa dashi tana taɓasa a kafaɗa
“Abban su lafiya kuwa? Tunanin me ka ke yi haka?”
Gwauron numfashi ya sauke fuska ɗauke da damuwa ya dube ta
“Hajiya Fatima Sagiru ne”
Kallon rashin fahimta ta masa kana ta ce “ Sagiru kuma? Ban fahimce ka ba”
A karo na biyu ya kuma sauke numfashi “ Kwarai kuwa Sagiru, wato tunda Allah ya mu su rasuwa Hajiya Fatima na miki imani da Allah kullum cikin mafarkin ɗan uwana nake,yana sanye da fararen tufafi tass fuskarsa ɗauke da faraa, ko da yaushe muna cikin lambu muna hira se na kusa farkawa daga bacci se ya riƙe hannuna ya soma faɗin “ya Jibrin kai tamkar uba ka ke a gare ni,dan Allah ka kula min da ahalina, ka riƙe min yayana tamkar na ka” kullum anan nake farkawa har yau na gaza gane menene abinda wannan mafarki yake nufi,kullum mafarkin abu daya nake yi”
Hajiya fatima da ta gama sauraran sa ne ta ce “ kar ka sa kan ka a damuwa Abbansu kasan sha’ani na mafarki, ka ci gaba da yi musu addua. Ka sa mutuwar a ranka sosai shisa har yanzu ka ke ire-iren wayannan mafarkan “
Girgiza kai yayi “ ba haka bane.tabbas akwai sakon da Sagiru ya ke son isar min Allah ka bani ikon gano menene wannan sako”
“Ameen ya Allah, to ko de Sagir yana da wasu ƴaƴan a wani waje ne banda su Alisha?”
“Astagfurullah Fatima, kar ki sake faɗan haka, Sagiru da yana da wata mata ko ƴaƴa da wata matar to tabbas ze sanar dani”
“Afuwan, ga abincinka nan ka samu ka ci kuma ka rage tunani da yawa please “ ta yi magana tana soma serving din sa.
“Ina Khalil yau tunda gari ya waye ban ji motsin sa a gidan ba”
Dariya tayi “haba kai kuwa ka manta jiya yace maka ze shiga Gombe ? Ze yi ko satı uku ko biyu akwai project na yin titi da suke yi a can Gombe “
“Haka shaf na mance kuwa to Allah ya musu jagora”
“Ameen”
Se bayan mangriba Haydar ya dawo gidan be tadda kowa a main falo ba nan ya wuce part din Adda kai tsaye tana zaune akan kujerar falo tana waya da Hajja Hauwa ta na sanar mata abinda ya faru,zama yayi yana jiran ta gama wayar.
“Haydar ka dawo?”
“Ehh Adda”
Alisha dake zaune a bedroom din ta ne ta ji Adda ta ambaci sunan Haydar nan ta gane ya dawo gida,bakin kofanta ta je ta tsaya tana son sauraran abinda suke faɗa.
“Ya ake ciki to ina Baban na ku ko ya wuce bangaren sa ne?”
Da ɗan damuwa a fuskarsa ya ce “Noo Baba a can ze kwana nayi iya kokarina mu samu bailing sa yau amma abun ya gagara. Yanzu sai zuwa gobe zan sake komawa mu ga abinda Allah ze yi”
Murya a sanyaye ta ce “ to amma ya maganar makaman na sa ne? Dan nayi mamakin yanda aka fito da makamai masu yawa a part din sa “
“To shi de yace sam wayannan makamai ba nasa bane an shigo masa dasu gida ne dan a ɓata masa suna, ni kuma ko kaffara bazan yi ba wannan makaman na Baba ne, na jima ina zargin Baba da aikata wasu abubuwa amma ban yi zaton abun na sa ya kai har nan ba”
Ya faɗa yana kallon kofan dakin Alisha
“Hmmmm lamarin Baban ku yana ɗaure min kai matuka,fisabilillah meye ya haɗa shi da safaran makamai?duk makuɗan kudin da ya tara be ishe sa ba se ya yi har da harkallan makamai.”
“Bakomai bari mu ga abinda gobe ze yi. In ya dawo se mu ji abinda ze ce. Alisha ba ta nan ne?”
Itama kallon kofar dakin Alisha tayi “Tana ciki ina ga ta na hutawa”
Kofar ya nufa ya yi knocking three times ze kuma bugawa ta buɗe.
“Barka da dare Uncle Haydar”
“Black Queen bacci ki ka fara?”
Kai ta girgiza sannan ta langwabar da kan tana me yin rau-rau da idanu cike da damuwa ta ce “ba bacci nake yi ba, ina kwance ne kawai,hankalina gaba daya a tashe ya ke shin an samu kawu ya dawo?”
Cikin jin dadin yanda ta nuna ta dawo da matsalar ahalin sa ya ke kallon ta
“Sai gobe in sha Allah . Kar ki sa damuwa a ran ki gobe Baba ze dawo gida in Allah ya yardaa.”
Kai ta gyada mai tana kokarin mayar da kofar ta rufe ya ɗaura hannun sa akan nata hannun dake jikin kofar,dasauri ta kalle sa sannan ta kalli Adda dake zaune a falo tana danna wayar ta hankalin ta ma sam ba ya kan su
“Uncle ka cire hannun ka Adda na kallon mu”
Noƙe mata kafaɗa yayi alamar be ze cire din ba,tunda ya ƙi cire nasa se ta fara kokarin zare na ta hannun ta na Allah-Allah kar Adda ta waigo ta gan su a haka,sai de be ba ta wannan daman ba saboda yanda ya manne hannun nasa akan na ta. Yana murmushin mugunta.
“Ayyah Uncle dan Allah ka yi hakuri ka cire”ta faɗa a marairaice ta na zuba mai narkakkun idanunta.
“ sai kin ce min My Hearbeat good night I love you,kina faɗin haka zan cire “
Hararan wasa ta watsa mai tare da murguda mai baki “ an ƙi din, baran faɗan ba kuma ka ɗaga min hannu”
Ɗage kafaɗa yayi alaman to ai hikenan
“Kin ga se mu tabbata a haka har Allah yasa Adda ta juyo ta gan mu tunda bazaki faɗa ba”
Kamar za tayi kuka, tace “ uncle please let go of my hand “
“Uhmm Uhmm na ƙi din nima”
Satan kallon Adda ta yi ta ga har yanzu de harkan gabanta ta ke yi.
“Wayyo Adda hannu na” ta faɗa tana fashewa da kukan karya yanda Addan za ta jiyo ta.
Ai kafin Adda ta juyo a saba’in ya sakar mata hannu yana “Subhanallahi me ya samu hannun na ki”
Dasauri Adda ta iso gurin ta na riƙo hannun da Alisha ta ke yarfawa cike da kulawa tana “ meya same ki Alisha ?“
Sai da ta kalli Haydar da yake tsaye yana kallon su sannan cikin shagwaba ta ce “ to ba uncle bane yasa kofa ya datse min hannu ba”
Watsa mai Harara Adda tayi
“ wallahi Adda ban mata komai ba” ya faɗa yana shafa sajen fuskan shi.
“Allah Haydar ba na son cin zali,na san sarai za ka aikata. Maza wuce ka tafi part din ka”
Ta yi maganar tana jan hannun Alisha zuwa falo suka bar sa tsaye a gun,waigawa tayi ta kalle sa sannan ta yi mai gwalo
Dariya mara sauti yayi ya fice a part din yana shafa fuskar sa.
Sai da ta ga tafiyarsa kafin ta dubi Adda ta ce “Adda kar ki damu ban ji ciwo ba kuma ma wajen baya min zafi. Sai da safe “ ta faɗa tana shigewa dakin ta
Dariya tayi tana girgiza kai “yaran nan Allah ya shirye ku."
Se mun hadu ranan Monday in sha Allah,kamar yanda ku ka sanı bana posting a weekend 🥰🥰
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍
Today is Friday don’t forget to recite Suratul kahf, sannan a yi wa annabi salati. Allah ya sadamu da alkairin dake cikin wannan rana.
39 & 40_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
*NIDA PATIENT DINA*
*ASHE ZAMUGA JUNA*
*ƊAYA CIKIN BIYU*
*MAKIRIN IKO*
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
39 & 40
Washe Gari suna dinning, suna breakfast yau ma Alisha ce ta yi mu su breakfast ta jera komai akan table yanda ya dace.
Ajiye spoon din hannunta Adda ta yi
“Haydar in ka karya ne za ka fita ko? Yakamata mu san ya ake ciki da safen nan”
“In sha Allahu Adda” ya amsa ta yana kai Kofin tea bakin sa
“Zaman ka jami’i a wannan gida be amfane mu da komai ba” cewar Sameer yana cin abincin sa a tsanake kamar ba shine yay maganar ba. Duk kallon sa suka yi
Maryam ta ce “Haba Daddyn Aryan ya za ka ce haka,Kana ganin yanda Uncle Haydar ya ke ta iya kokarin sa. Kana ganin ba domin shi jami’i bane akwai wanda ya isa ya hana ƴan jaridun jiyan nan watsa wannan magana a duniya? Da wannan magana ya watsu kuma, ƙima da darajan gidan mu se ya taɓu “
Slide smile ya yi ya ajiye kofin a gurin zaman sa ya ɗauki tissue ya soma goge hannunsa
“Kyale sa Maryam babu abinda ya sani akan doka. Doka ya fi karfin kowa, ko da kuwa shugaban ƙasa ne ya yi laifi dole a hukunta sa”
A zafafe Sameer ya ce “ kenan kana tunanin wayannan makaman na Baba ne kenan? Lallai Haydar ba ka da hankali tunda har za ka iya yarda da mahaifin mu na safaran makamai.”
Ƙawata fuskarsa da murmushin da yafi na ɗazun yay, ya miƙe tsaye “ka faɗawa wanda be san halin ku ba Sameer. amma ni nan tarr na ke kallon ku. Adda sai na dawo”
Ya faɗa yana duban Adda dake cin abincinta a tsanake ba ta tanka musu ba se yanzu da ta ɗago gun bayan da tai magana ɗazun.
“To a dawo lafiya,Allah ya bada saa. Jiya na yi magana da lawyer, ya ce ze rigaka zuwa caji office din”
“Ni ma haka mu ka yi dashi,sai na dawo “ ya kuma faɗa yana ficewa a main falo din.
“Aikin banza” cewar Sameer yana barın dinning din ya haura part din su.
“Abincin nan ya yi dadi Alisha “
Ɗan murmushi ta sake “nagode Anty Maryam,Aryan yana bacci ne?”
“ Yana ta shan bacci yana bedroom dina dama dubo min shi ki ka yi ko ya farka”
“To” kawai ta furta sannan ta nufi part din Sameer. Yana falo ya na danna waya ta shigo ko kallansa ba ta yi ta shige dakin Maryam, ai kuwa tana shiga ta same sa idonsa waras yana tsotsan hannu. Ƙayitacciyar murmushi ta yi ta ɗauke sa tana
“My Aryan har ka farka?to zo mu je gun Mommynka ko”
Ta furta tana kokarin barın dakin idonta ya sauka akan gidan memory yashe akan gadon Maryam. sai da ta kalli bakin kofa ta ga babu kowa sannan ta sa hannu ta ɗauka ta duba ciki ta ga akwai memory a ciki. Tambayar kan ta take yi to wannan gidan memory din na meye,sanın ba me ba ta ansa ne yasa ta jefa sa a cikin bra din ta sannan ta bar dakin.
yana nan a inda ta bar sa. Kamar yanda ba ta ko kalli inda ya ke ba haka shima har tafita be tankata ba sai ma kwafa da yayi yana taune lips din sa.
Ko da ta sauko ƙasa a madadin ta same su a dinning, ta iske su zaune a falo suna hira zama tayi tana ɗauke da Aryan.
“Allah de yasa a gama wannan case din Baban yau”
“Ameen ya Allah Yusrah “
Ameera ta amsata.
Zainab ta ce “ Ni fa wallahi ban yi tunanin Baba ze kwana a can ba. na ɗauka zaa yi ɗan bincike ne sai ya dawo “
Cikin son Kawar da zancen Adda ta ce “in sha Allah yau ze dawo, babban godiyan da zamu wa Allah shine maganar nan be yaɗu a duniya ba,Allah yasa de mu dace”
Duk da ameen suka amsa.
Toilet ta shiga tana cire kayan jikinta za ta yi wanka. ta cire bra kenan gidan memory ya faɗi a ƙasan tiles ita sam tama manta da ta ɗauke memory a dakin Maryam,hannu ta sa ta ɗauka ta ajiyesa a gaban toilet mirror din sannan ta yi wankanta,ta ɗaura ɗan ƙaramin towel alwala tayi sannna ta ɗau memory ta fita. Jikin wardrobe din da kayanta suke ta je ta ajiye sa a can ƙasa sannan ta zura abaya da hijab ta tada sallah La’asar,tana kan sallaya tana addua Ameera ta shigo da gudu ta faɗa kan gado tana dariyar farin cikin,ta ƙasan ido ta dube ta sannan ta sallame ta ninke prayer mat din ta ajiye kafin ta ce
“Wannan farin ciki duk na meye shi haka Ameera?”
With an excited voice ta ce “Baba ya dawo shi da uncle Haydar yanzu”
Siririn tsaki ta ja a ƙasan maƙoshi wanda Ameera ba ta ji ba kafi, ta ce
“Kai Alhamdulillah gaskiya na yi murna,haka nan kawai suka bar sa ya dawo?”
Miƙewa zaune ta yi tana duban ta dakyau